Author : Maman Waleed Da Waleedah Category : Romantic Hausa Novels
gobe zamu cire masa duk wani ƙarfe na jikinsa don yanzu a haka ma they not helping him, but hurting him don haka in shaa Allah gobe da ƙarfe 12:00 na safe zamu cire daga nan kuma sai yacce hali yayi" kasa kuka nayi don nasan bashi da amfani
"dr. ya shi aliyun yake"
"well am sorry to say he is not helping at all, zan iya faɗa muku a halin yanzu aliyu is not fighting 4 his life he has already given up, don haka yanzu kawai sai yadda hali yayi, kunsan wataran idan mutum yana da burin ya rayu to sosai yaka taimakawa likita amma aliyi yanzu ko kaɗan baya taimaka ya riga ya losing hope na rayuwa don haka sai haƙuri"
Jikina a sanyaye na fito daga ɗakin, directly ɗakin aliyu na nufa ina kallon sa gobe iyanzu bamu da tabbacin kana raye ko ka mutu ko na faɗa,
Ko da tj ya dawo da daddare mimma ce ta iya faɗa masa kasa cewa komai yayi sai hawaye kawai, kasancewar bama kwana a asibitin yasa da dare yayi tj da ƙyar ya lallashe mu muka tafi ni da mimma
Tunda muka je ɗakin da muka kama na hotel sai muka kasa duk muka zauna mukai jugum jugum nice ma na gaji daga ƙarshe na tashi na ɗauro alwala na fara gabatar da sallah don in roƙi Allah ya kawo mana sauƙi a wannan lamarin, ita ma mimma sai ta bini ta fara sallahr
Ƙarfe biyu dai dai muna cikin ibadar mu naji wayata ta fara ringing ƙirrrrrrrrrrrrr innalillahi wa inna ilaihi raji'un shine kawai abinda na faɗa
Ko da na duba wayar number tj na gani, wayyo Allah na kawai na iya faɗa na je gurin mimma na rungume ta na san yau ta aliyu ta ƙare
Ruƙunƙume juna mukai ni da mimma muna kuka, wayar ce ta kuma ringing again wannan karon tsorata mu tayi ni da mimma inda muka ƙara manne wa da juna
Ko da tayi ringing a karo na uku sai mimma tayi ƙarfin halin ɗaukar wayar ta doka ta da ƙasa ni kuma nabi ta ina tattaka ta don nasan ƙarshen alawa ƙasa ne irin yadda jikin aliyu ya rikice a yau ɗin nan amma ko kaɗan ban kawo zan rasa mijina yau ba
Kuka sosai muka dinga rusawa ni da mimma ni na rasa mijina uban ƴaƴa na ita kuma ta kuma rasa ɗan ta wayyo Allah na
Tj ne tsaye a gaban gawar yana ƙare masa kallo buɗe ɗan mayafin da aka lulluɓe shi yayi yana kallon sa tare da binsa da addua
"abinda kayi mana Alƙah yayi maka Allah yasa mutuwar ka hutu ce a gareka, Allah ya jikan ka ya duba bayan ka" rufe shi yayi sannan wasu suka tura gawar zuwa mortuary don a adana ta kafin safiya sai dai muce Allah ya jiƙan musulmai baki ɗaya
[7:46PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
Page:54🌹
Tj yana tsaye a bakin theater room ɗin sai safa da marwa yake yi tare da roƙon Allah yasa ayi aikin nan cikin sa a,
Tun kusan ƙarfe 01:00 na dare yana cikin sallah yaji hayaniya a cikin asibiti ko da ya idar sai ya fita don yaga ko menene, sai yaga alamar jini a ƙasan alamar anyi hanyar theatet, bai daɗe ba sai ga dr.hisham ya fito ya doshi reception in da mutanen da suke jira suke
Can sai gashi ya dawo da wasu likitoci directly ɗakin aliyu suka nufa sai gashi an fito da shi komai da sauri sauri suke yi ko dana tsayar da su in tambayi ko menene sai likita ɗaya yace an samu heart,
Sujjada nayi shukuriyya ga Allah daya kawo mana wannan zuciyar a lkcn da muka fidda tsammanin samu, sun ɗan jima a theater room sannan sai gashi an turo gawar an fito da ita
Tj ne ya tsayar da waɗanda suka fito da gawar sannan yai masa addua tare da godiya da zuciyar da ya basu duk da dai baji ze yi ba sannan aka rufe aka wuce da shi mortuary,
Tun daga lkcn ya koma kusa da theater room yana ta roƙon Allah yasa ayi aikin nan cikin sauƙi, su mimma ya tuno don haka sai ya ɗauki wayar sa ya kira zainab don ya faɗa mu su abinda ya faru, yai mamakin da suka ƙi ɗauka ko bacci suke yi ya faɗa
Ya kuma kira amma ga mamakin sa sai tana fara kira taji a number busy, daya kuma kira kuma switched off, tooo Allah dai yasa lfy ya faɗa
Basu suka fito daga theatet room ba sai ƙarfe takwas na safe, likitocin duk suka fito fuskar su ɗauke da fara'a wannan ya nuna min alamar aiki yayi kyau kenan
Adaidai lkcn ne wata nurse tazo tace za a ɗauki gawar jiya sai yanzu ma na tuna cewar banyi wa wanda yayi mana signing aka bamu zuciyar godiya ba
Don haka sai na bi bayan dr. Hisham, wata dattijuwa ce zaune da tasbaha a hannun ta idon ta yai ja sosai daga dukkan alama tayi kuka amma idan ka ganta a nutsen ta take, daga gani imani ya ratsa ta sosai
Har gaban ta naje na durƙusa ina kuka ina gode mata da turanci, murmushi tayi min tace min ince wa ɗan uwana ya kular mata da zuciyara ɗanta
Daga haka sai ta fice, bin bayanta nayi da kallo yadda take tafiya da nutsuwa gaskiya indai wannan mamacin yayi halin wannan baiwar Allah to tabbas ɗan uwa yayi sa ar zuciya na faɗa
Gurin dr. Hisham na je nace ko zan samu address ɗin matar sai yace min a madina suke daga nan ma madina zasu wuce ayi jana'izar ɗan nata, sai ta bani tausayi ita kaɗai ce zata tafi da gawar a ambulance, gaskiya dole ne in bita don inga inda take nasan idan ɗan uwa ya tashi dole ne ya so ganin wacca ta taimaka masa
Tambayar ɗan uwan nawa nayi inda dr. Hisham yace ba wanda zai ganshi sai gobe da safe kasancewar ya wahala sosai kafin aikin don haka sun kai shi ɗakin hutu sai gobe zasu fito da shi
Jin hakan ya sani bin matar nan da gudu har motar ta fara tafiya na bita da gudu suka dakata sannan na shiga, kamar yadda nayi tsammanin kuwa haka ne ita kaɗai ne ce a bayan ambulance ɗin tare da gawar ɗan shiga nayi tare da yi mata sallama ta amsa da fara'ar ta
"me kake yi anan kaje ka kula da ɗan uwanka"
"sai gobe da safe zai farka in shaa Allah, kuma wannan ma ɗan uwana ne tunda zuciyar ɗan uwan ne a jikin sa don haka bazan rabu da shi ba har sai naga ya kwanta cikin kabarin sa in shaa Allah"
Bata ce komai ba sai murmushi kawai da da tayi muka fara tafiya, ko da muka zo bakin get sai na faɗa wa me guard idan su mimma suka zo ya faɗa musu na tafi madina jana'iza,
Tafiya ce me nisa sosai daga ta'if zuwa madina,
Mun sauka lfy nai mamakin da naga babu wanda ya zo tarar mu, harami muka wuce da shi directly ni na tsaya a matsayin ɗan uwan sa a lkcn da ake masa sutura, duk da dai ya kasance balarabe ni kuma baƙi 🙍🏻♂🙍🏿♂
sai da aka gama na fito zan kira baiwar Allahn nan sai naga wata yar matashiya da hijab a jikin ta, sai kuma wan yaro da bai wuce shekara uku ba
Matar nan ta gabatar da matashiyar nan a matsayin matar mamacin shi kuma ɗan ƙaramin ɗan ɗansa ne, ɗaukar yaron nayi me suna al amin na sunbace shi
Allah sarki Allah ya haɗa qaddarar mahaifinka dana ɗan uwana dole sai mahaifinka ya rasu sannan ɗan uwana zai rayu
Raka su nayi suka ganshi tare yi masa addu'ar sannan ya rako su cikin masallaci wajen ɓangaren mata suka zauna
Tare da faɗa musu bayan janai'zar zai zo ya kaisu gida, sai da aka sallaci sallahr la'asar sannan aka sallaci yahya, ba abinda zamuce sai dai muce Allah ya jiƙan musulmai
Bayan an idar ya zo ya samu su ya ƙara yi musu godiya sannan ya nemi daya yana son ganin gidan su, amma ummu yahya sai taƙi tace masa ita don Allah ta taimaka musu ba don komai ba
Faɗa mata yayi wanda ta ba zuciyar yana da mata da uwar sa yana son kawo sune suyi mata godiya amma ƙiri ƙiri sai taƙi tace kawai ayi masa addua
Babu yadda zai yi haka ya wuce ta tafi sai ya samu wuri ya ɓoye don yasan idan ɗan uwan sa ya farka yaji be san mazaunin donors ɗin sa ba kashe shi kawai ba zai yi ba
Ko kuma ƙila aɗan uwan sa ya canza koooo? tunda yanzu ba zuciyar da gare shi ba, binsu ya dinga yi a baya tafiya ce me nisa amma suka yi ta aƙafa ya tausaya musu daga gani basu da shine
Sunyi tafiya kusan ta minti 20 sannan suka zo wani gida ɗan ƙarami a wani ɗan lungu suka shiga, sai da ya tabbatar da nan ne gidan nasun sannan ya wuce,
Ko da ya koma ta'if dare yayi sosai, don haka sai ya wuce hotel ɗinsa ɗirectly yai mamakin da wunin ranar beji daga zainab ko mimma, don haka ɗakin su ya wuce directly
*****************
Mimma da zainab kwana sukai basuyi bacci ba,ko da gari ya waye sai suka ƙi fita, sai da suka ga azahar tayi sannan suka fita asibitin suka je, a bakin get suka ci karo da me guard ɗin da tj ya barwa saƙo ya faɗa musu ya tafi jana'iza madina zainab kusan faɗuwa tayi dabadan mimma da ta riƙe ta ba suka shige ciki don su ga abin a zahiri
A maimakon su ƙara tambaya a cikin asibitin sai suka ƙi sukai ta shashancin su, su a tunanin su ya rasu tj ya ɗauki gawar zuwa madina don aliyu ya bar wasiyya in ya mutu a nan a binne shi a madinar, fara haɗa kayan su sukayi sannan suka fito
Reception suka wuce don closing biƙl ɗin amma sai receptionist ɗin tace sai dr.hisham yazo don haka su saurare shi, zazzaɓi ne sosai a jikin zainab don haka sai mimma ta ce bari ta kaita gida in yaso sai ta dawo
Komawar su gida yayi dai dai da dawowar tj, a wajen hotel ɗin suka ci karo shi, zainab tana ganinshi ta fashe da kuka, mamaki ne ya kama shi, ya ƙaraso wajen su
"yayata lfy me kuma ya faru"
Wani kukan na ƙara fashe wa da shi, mimma ce ma ta iya magana
"me yasa ka binne shi ba tare da mungan shi ba" sam se be gane me take nufi ba
"me yasa zaka binne min ɗana ban ganshi ba" ta kuma faɗa da ƙarfi,
"mimma aliyu be mutu ba, wanda ya ba aliyu zuciya ne naje jana'zar sa"
Da sauri muka ƙaraso wajen tj
"kana nufin an samu zuciyar, to ina aliyu yake" tambayoyi muka cika tj da shi shi kuma ya ƙi ansawa sai kawai murmushi da yake yi, tas tj ya larabta mana yadda akayi nayi kuka nayi murna na godewa Allah sosai sannan nayi wa yahya adduar Allah ya jiƙan sa
cikin hotel ɗin muka koma don munji sai da safe zasu bari a ganshi, a daren ranar kasa bacci nayi don kawai ina ɗokin gari ya waye inje inga mijina
ana idar da sallah asuba muka kama hanya amma ko da muka je asibiti sai dr.hisham yace sai 08:00 na safe zamu ganshi don ya ma tashi amma sai ya cika ƙa'idar lkcn daya dace zamu ganshi
koya zanga aliyu na faɗa araina, murna nida mimma kamar me,muna cikin wannan halin ne aka kira tj daga nigeria wai salma tana naƙuda, murna a wajen tj har yana cewa indai namiji ne to in shaa Allah sunan ɗan uwana zan saka
sai ƙarfe takwas muka shiga naga mijina a zaune yana ta murmushin sa a guje naje na rungume shi duk da dai cikin da ke jikina ya hana ni rungume sosai wanda yanzu nake cikin watan haihuwa
Mimma ma rungume shi tayi sannan suka gaisa da tj murna sosai nake ji har na faɗa masa matar tj tana naƙuda
"ɗan uwa ka shirya ka koma nigeria don tara ɗan jariri tunda kaga na warke"
"in shaa Allah ɗan uwa zan koma ko yau ko gobe"
har bayan la'asar shiru shiru salma bata haihu ba hankalina gaba ɗaya ya tashi shima tj ɗin daga gani kawai daurewa yake, in ya kira sai ace masa har yanzu dai, sai magariba sannan sai ga waya a lkcn aliyu yayi bacci
ko da tj ya ɗauka da fara'ar sa
"me na samu" ya faɗa da murnar sa, a maimakon inga yaci gaba da murna sai naji yace
"innalillahi wa inna ilaihi raji'un, salmar ta mutu" jikina ne yaɗau rawa, kashe wayar sa yayi ya saki kuka
rasa abinda zan masa nayi nima sai na saka kuka ko ba komai na san salma sosai kuma jinyar mijina Allah yayi bazasuyi bankwana da mijinta ba
kuka wiwi tj yake yana tausaya wa kan sa da ƴar sa islam nima ina taya shi mimma ce ta lallashe shi sannan tace sa ya tashi ya kama hanya Allah yasa ya samu jirgin da zashi nigeria a ranar
har bakin asibitin muka rako shi mukai sallama tare da ƙara yi masa ta'aziyya har ya tafi sai ya dawo
"don Allah kar ku gaya wa ɗan uwa salma ta rasu ku bari idan ya warke sai a faɗa masa"
gyaɗa kaina nayi nima dama hakan naso yi muka ƙara sallama ya kama hanya babu abinda zamuve sai dai muce Allah ya jiƙan musulmai baki ɗaya
[7:46PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
Page:55🌹
*ina murna sannan da ban godiya ga mmn farida da ta kammala littafin ta samun wuri duk da dai da sannu sannu aka tafi amma dai an kai ƙarshe babu abin da zamu ce sai Allah ya ƙara basira*
*Sannan ina miki murna da fara sabon littafin ki faccala da fa'iza ƴar baba, Allah ya bada ikon gamawa lfy sannan da fatan ba za ai mana tafiyar hawainiya* 🦎😁😁😁
Ko da aliyu ya farka ya tambayi tj sai nace masa ya tafi nigeria, ya nuna jin daɗin sa da matar ɗan uwan sa zata haihu har da addu!ar Allah ya sauke ta lfy na amsa da amin
Sai da tj ya sauka lfy sannan ya kira ni na ƙara yi masa gaisuwa tare da tambayar abinda aka samu sai yace min bata ma haihu ba Allah ya karɓi abar sa, wayyo na tausaya masa sosai
Ya tambayi jikin aliyu na ce masa da sauƙi yana ma ta tambayar sa, yai masa fatan samun lfy sannan mukai sallama
Aliyu ne ya matsa min na kira tj yayi masa ta'aziyyar ɗan kasancewar na faɗa masa ɗan be zo da rai ba amma ban faɗa masa rasuwar salmar ba don yanzu neman hanyar da zuciyar da aka dasa masa ta warke muke yi
Aliyu yana da sati 3 a asibitin na tashi da naƙuda anan asibitin Allah ya sauke ni lfy na samu saurayi na kyakkyawa fari tas da shi duk yafi ƴaƴa na fari har shi ma aliyun ya fi shi haske
Mimma da aliyu sukai murna da wannan ƙaruwar da muka samu a donga waya ina faɗawa mutane ƙaruwar da muka samu, aliyu ne ya kira tj ya faɗa masa, tj yai masa murna da kuma alƙawarin zai zo
Ko da ranar suna ta zagayo aka saka wa ɗana suna *yahya* sunan wanda ya bawa aliyu zuciya mimma ce ta ce a saka sunan nima da aka faɗa min sai naga dacewar hakan don babu abinda zamu iya ce masa sai dai muce Allah ya jiƙan sa
Watan aliyu biyu aka sallame mu, muka koma makka inda dangin mimma suke ta gabatar da da aliyu a matsayin ɗanta da aka ce mata ya ɓata, da ni kuma