DANGIN SA COMPELET HAUSA NOVELS BY MAMAN WALEEDA DA WALEED.txt

Author :  Maman Waleed Da Waleedah Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   4 / 33

9K to 12K   out of 97.7K words

ƙarasa har wajen motar mu ya raka ni



ko bayan da muka shiga wayar tashin ya miƙo min tare da cewa "sai munyi waya" juyawa yayi ya ɓace cikin duhin daren nan kamar walƙiya ajiyar zuciya na saki wanda sai alkcn na fahimci ashe duk waɗan da ke motar hankalin su na kaina zunɓurar baki nayi na ce "menene"



"a ina kika samu wannan yaya" inji maryam ba irin tambayar da basu yi min ni dai bance musu komai hankalin khadija ne yaje kan wayar sa da ya bani


"wannan kamar iphone 7 latest version ko" gefe sadiq ya faka da motar ya karɓa

"ai kuwa ita ce, a ina kika san shi" oho kawai na iya faɗa

"kinsan nawa wayar nan kuwa yaya tana fa kaiwa dubu 350" zare ido na nayi ina kallon wayar da zata kai wannan kuɗin wai a hannuna dariya na ɗan yi ku china ce




dariya suka dinga min wai basu taɓa jin iphone china ba sai a wajena ni dai har ni dai ban kula su har gida su kaini na ɗauki saƙon mama na kayan snacks nai ciki



ko dana koma baban mu bai dawo ba don haka kawai sai na ba mama bata tambayeni ina na samo ba nima ban damu ba sallolina nayi na kwanta amma kuma sai na kasa bacci tunanin ɗan takari ne ya faɗo min to ɗan takari mana muma ƴen uwan mu idan suka je garinsu takari ake ce musu to muma ba dole muce musu takari ba ( har na tuno littafin makawa, ki ci gaba da gashi lbrn nan yana ƙawata mu)



da asuba na tashi da wuri sakaka haka na wuni ba abinda yake min daɗi ko abinci kasa ci nayi abi kaɗan kuma sai induba wayata ko zanga ankirani shiru kakeji



da daddare bayan sallahar isha mun zauna muna kallo har da su baba sai ga breaking news an rubuta da manyan harufa *ajaban caught off guard with wife nd son* sai ga hoton mu da ɗan takari danɓarere akan akwatin tv




baba ne ya fara magana "wannan kamar zainab ko dai ido nane" shiru nayi
"itace mana baha khalil nan ba ɗan wajen khadija"


ni dai bance komai ba sai ga news an ci gaba "a jiyane muka samu daman samun hoton matashin yaron nan me multi billion dollars shipping, company da yayi ƙaurin suna suna a dunuya wato mr ajaban da kuma me ɗakinsa tare da ɗan ƙaramin ɗan su wanda suka je shaƙatawa a beach, rahotanni sun nuna cewar mr ajaban ya daɗe da aure inda ya ɓoye wa ƴen jarida da duniya kasancewar baya san iyalinsa su shiga cikin hayaniya, sao jiya Allah yasa muka samu daman ɗauko hotonsa sai asha kallo lfy"




kamar afilm haka naga abin namu da yadda muke gudu ƴen jarida suna bin mu abin gwanin sha'awa Allah nidai kam ya birge ko don ban saba ba be ohho



saukar mari ne ya dawo dani hayyacina ashe baba yana ta magana banji ba babu yadda ybaiyi ba in faɗa masa ko waye nayi shiru ba urin zagin da ban sha har cewa yayi in ban fidda miji ba cikin satin nan gezawa zai kaini ya bada ni sadaka



Ya gama bam bamin sa ya shige ɗaki ita ma mamahaka kwanciya nayi ina tunanin to wannan wanene shi wane irin suna ne *ajaban* a haka bacci yai awon gaba da ni



kashe gari da sassafe bayan na idar da sallah ina zaune sai naji wayata tana ringing kamar kar inɗau amma sai na daddage na ɗauka a lkcn ta kusa tsinkewa sallamar sa naji wanda ko bacci nakeyi naji muryarsa zan gane na amsa ga drivwr kiyi masa kwatancen gidan ku too kawai nace



drivern ya karɓa nayi masa kwatance sosai yace ya gane sannan ya kashe wayar murna naji ko ba komai zai zo zance, ko yaushe zaizo na tambayi kaina ima murmushi




komawa nayi na kwanta ina tunanin ɗan takari na wani daddaɗan bacci me ya fafa kwasata, kamar a mafarki naji ana buga mana ƙofa kamar za a karya a firgice na tashi wanda yai dai dai da fitowar bbn mu daga ɗakin yana mitar waye



buɗe ƙofar yayi yaci karo da wasu ƙarti su biyu cikin baƙaƙen kayan su da baƙin glass
"sainob in ko" wato ina da zainab
Hannu baba yana rawa ya nuna ni da yatsa


kirawo ƴen uwan su suka yi akan gani nan wasu mata ne suma cikin irin shigar mazan suka shigo suka kama ni suka fara ja zasu fita da ni bbnmu na ruƙo ina kuka, doke min hannu yayi nina aike ki ya faɗa muryar sa tana rawa daga gani atsorace yace




a haka suka jani har waje duk ƴen gidan mu sun fito ganin wannan ikion Allah nikuma sai kuka nake yi ina ihu na a taimake ni amma ba wanda ya kawo min a gaji


a tsakiyar layin mu sukayi parking motocin su waɗanda suka kai kusan guda goma duka baƙaƙe sai ƙyalli suke yi a ta tsakiya suka saka ni suka rufe nayi nayi in buɗe ƙofar amma na kasa sai kawai na saki wani sabon kukan
[7:42PM, 12/7/2017] ‪+234 806 803 7117‬: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀




By mmn walid nd walida mrs aliyu

🎁nasibi writers asso🎁


Page:8🌹




Kuka nakeyi ina yin gunji sannan muna tafiya a hankali, tsaki naji an ja min wanda yai min nuni da cewar ba ni kaɗai bace a motar ba waigowa nayi don inga ko waye hmmm "ɗan takari" na faɗa da karfi da kuma mamaki
"ɗan takari kuma kinga nayi miki kama da takari ne"
"oho maka naga in ƴen nan sunje garin ku takari ake ce musu to muma in kun zo garin mu ba dole muce muku takari ba"

Useless kawai najo yace ya juya ya ci gaba da danna laptop ɗinsa

"me yasa ka sato ni" na tambaya be kalle ni yaci gaba da abinda yake yi ba irin tambayar da ban masa amma ko ƙala baice min ba har muka isa inda zamu,


Parking na ga anyi
"ki fito"
"walƙahi ba inda zan je sai ka gaya min me nayi ma ka sato ni" be kula ni can sai naga waɗannan ƙattin matan nan sun zo sun kuma kamoni ina ihuna ina komai naga mu nufi wani jirgi da yake gaban mu

Nutsuwa nayi donni in akwai abinda da tsana yabi bayan jirgi tun wani haɗarin jirgi da na gani nake tsoronsa
Juyowa nayi na kalli ɗaya daga cikin matan nan mausu jana na fara mata yarbanci akan don Allah kar ta sani cikin jirgin nan mutuwa zanyi, kamar ba da mutum nake


tun ina kuka da roƙon a sanyaye har na fara zunduma ihu za a kashe ni a jirgi kasancewar private plane ɗinsa ne yasa ba mutane sosai muna ƙara dosa jirgin naganshi wani tanƙameme da shi da zuciyata ta buga sai na wani luuuuu zan faɗi ni ban yadda ba na suma cak naji ɗaya daga cikin matan ta ɗagani sama ta ci gaba da tafiya ganin suman nawa na ƙarya bazai min ba yasa ni na wani miƙa sai gani sauran kaɗan in suntumu a ƙasa da saurin ta ta taro ni suka ƙara riƙe ni ita da ɗaya




a matattakalar benen hawa jirgin ma sai da akayi artabu da ni inda daga ƙarshe de sai ɗaukata akayi ina ihu iya ƙarfina, ko da muka shiga jirgin sai na nutsu don gani nake yi kamar idan nace zanyi kokawar sai in ruguza jirgin cikin jirgin ya sha kujeru na aƙfarma har wani bar ne acikin sa inda ake jera lemuka kala, kamar falon wani hamshaƙin me kuɗi sam beyi kama da cikin jirgi tunda a film mun saba gani cikin jirgi kujerunsa a jere suke kamar a class wannan kuwa a zagaye yake kamar kana falo tsayawa nayi kawai ina kallo amma yanzu ba lkcn ƙarewa cikin nan



zaunar dani matar tayi ta ɗaura min belt sannan tayi gaba, ɗan takari ne naga ya fito daga wata ƙofa a jirgin ya doso ni yana murmushi duk da firgice nake amma hakan bai hanani gani kyan da yayi ba


"naga alamar kina tsoron shiga jirgi ko, to da fatan dai baza ki kayar mana da jirgi ba da kokawar nan taki ba idan mun tashi" zare ido nayi alamar tsoro ne tattare da ni, murmushi naga yayi sannan ya juya ya wuce tunda na zauna bani na tashiba har sai da muka sauka ko ƙwaƙƙwaran motsi bana yi don kar in kada jirgin sukuwa sai wani kaiwa da kawowa suke yi ko a jikin su



kasancewar na gama tsorata yasa ko da muka sauka ban wani yi taurin kai ko ma dai ina za a kaini yanzu munyi nisa da gida kokawa ya ƙare,



mota ɗaya aka kuma samu da ɗan takari wannan karan ko kallan inda yake banyi ba har muka isa masaukin mu, fitowa nayi nan ma na bi bayan matan inda muka doshi wani tafkeken gini kamar ba mutun ne ya gina shi ba


door bell ta danna inda wata mata again ta buɗe suka gaisa sannan ta nuna mata ni tai wuce warta ni kuma na tusa kaina ciki


tsayawa faɗin tsaruwar falon nan ƙauyanci, tafkekene na faɗa inda aka sa ma kujeru kusa set 7 a kowane angel inda ba wata kujera da take kusa da ƴar uwarta ga ƙofofi nan barkatai ba iyaka

tafiya mukayi muka ɗan wuwwuce wurare da dama kafin mu zo wata takekiyar kofa buɗewa tayi inda turaren da aka sa ya doki hancina na lumshe ido don tsabar ƙamshin sa ɗaki ne pink komansa pink ne gado, kwaba komai dai na ɗakin pink ne


come in naji tace binta nayi har ciki ta buɗe wata ƙofa nan ma muka shiga sai na banɗakine tafkeke shima ba abinda babushia kamar ɗakin komansa pink ne


wani tafkeken Jacuzzi tub ne a tsakiyar toilet ɗin da girman sa wanda ya gani cike yake da ruwa da red flowers da aka watsa a cikin ruwan sai wsu ƴammata da suka kewaye ruwa su shida ko wacce da uniform a jikin ta


bath her" kawai naji tace, kut tana nufin su min wanka yau fa ake yinta na faɗa araina ruƙunƙume jiki na nayi sai gasu gaba ɗaya sun doso ni kamar wasu karnuka kokawar cire kayan muka dinga inda daga ƙarshe wacce ka ta kawoni tace su ƙyaleni


ko da suka sake ni da murmushinta ta matso kusa da ni
"madam they r going to help u take a bath nothing more"
"no i can bath my self i have being taking my bath since when i was born" dariya tayi
"indeed" ni nama manta ashe sai mutun ya girma yake fara yiwa kaansa wanka


"ok here's how we will do it they will help u nd u Will do d rest okey" gyaɗa mata kai nayi

wani towel ta bani na cire kayan jikina na ɗaiur shi sannan na shiga cikin jacuzzi ɗin ruwan yai daɗi dai dai yanayi, fara massaging ɗina sukayi



wayyo me kwance min kai tanayi me gyaramin ƙafa tanayi me min gyaran hannu kowacce dai ta kama aikin da ta ƙware akai, mun kusan awa anayi min gyaran jiki ga matsa da nake sha akai a kai sai da suka gama sannan suka canza min ruwa suka fita suka barni inyi wanka na



da ƙyar na iya wankan na fito don tsabar daɗin ruwan da nake ji ko da na fito daga toilet ɗin wasu saitin ƴanmatan na kuma gani masu irin uniform ɗin waɗancan suna jirana nan suka jani suka fara aikin su a kaina me gyaran gashi me kwalliya sai da suka ga nayi tsab da ni sannan suka ƙyale ni inda suka ɗauko min wata strapless armani gown na saka daa ganin rigar nan taci kuɗi nan na kalli kaina kamar wata tauraruwa haka na ganni na yi kyau sosai murmushi wanda ya kara min kyau sosai



jagora sukai min zuwa dining room don inyi breakfast sai lkcn na tuna ko break fast ban ba abinci aka shiga jera min kamar abin arziki na kai hannu zan buɗe kenan sai matar da ta karɓe ni tun bayan shigowata wato linda kenan naji ta doke min hannu da bulalar da ke hannun ta *auch* nace na juya na kalle ta tare da zubɓuro mata baki



sawa tayi ƴammatan da ke wajen suyi serving ɗina breakfast ikon Allah, wato ba wani abin arziki a cikin abin,


fruits ne kala kala akai masu wani irin decoration me kyau shi aka fara turo min, hannu na daga zan ɗauka nan ma naji bulalar Linda ƙwal a hannuna *auch* njena faɗa da ƙarfi tare da sosa wajen fork ta nuna min na ɗauka sama sama naci fruit ɗin don ni yunwa kawai nake ji ba kwaɗayi ba
ko

da na ture sai aka kawo min main breakfast ɗina aikin banza na faɗa araina ƙwai ne guda ɗaya jal aka soya wanda ba a kaɗa ba don kana iya ganin ƙwaduwar a tsakiyar sa, sai fatan wake shima baifi cokali biyu ba sai kuma, timatir wanda aka akayi slicing ɗinshi sa bread slice ɗaya, sai tea rabin kofin tangaran



kallan abincin nayi wanna idan na daddage gabaki ɗayan abincin zan kwaso su in musu loma ɗaya a lkc ɗaya amma wai shine breakfast kallan linda nayi inda tayi min nuni da fork nd knife tooo faaa yau ake yin ta wa ya iya cin wai abinci da fork da wuƙa
ɗauka nayi na fara ci bazan dai faɗa muku yanda na ci abincin ba amma na sha bulala ya fi a ƙirga ina gamawa aka kawo min soup na sha shi wannan bashi da matsala don da spoon kawai na sha bayan na gama ne tasa wasu ƴammata suma na daban su fita da ni nasha iska aikin banza mutun be ƙoshi ba amma an sa shi zagayawar dole tashi nayi na bisu ko ba komai na ga guri
[7:42PM, 12/7/2017] ‪+234 806 803 7117‬: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀



By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)

🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺




Page: 9🌹



Mun sha zagaye sosai a cikin gidan inda ƙara ganin girman gidan, tanƙameme ne sosai garden suka kaini inda ya sha shuke shuke masu ƙayatarwa launi daban daban masu kyau da ƙamshi



ga table da kujerun sa daga gefe na zama sai swimming pool wanda kusan guda uku ne kowanne da shape ɗin da aka yi masa, can daga gefe kuma wani fountain ne da akayi masa shape ɗin tukunyar ƙasa inda ta saman ta ke zubar da ruwa cikin ta ƙasan, gurin yai kyau sosai



wuri na samu na zau a kan grass carpet ɗin daya zagaye ko ina yai kore shar da shi ga shi kuma yai lif lif da shi daga gani yana samun kulawa sosai



fruits aka kawo min da juice sai kuma ruwan roba ga snacks nan abin dai sai kace mutane goma ne zasu don tsabar yawan sa, wanda inda ace hankalin mutun a kwance yake sai kaci iya cin ka amma ya za ayi in zauna in ci bayan ban san dalilina na zuwa gidan na ba



kuka na saka me sauti sosai wanda ya janyo hankalin masu kula da wurin da ƴammatan da suka rako,
"madam do u need anything" naji wata tace


Abin takaici bama Hausawa ya haɗa ni zama da su ba ƙabilu ne, harara na doka mata
"where is ur oga" na faɗa in me shaƙar wuyan rigar ta


shaƙar da tajine yasa ta kakari wanda ya janyo hankalin mutane suka zo agajin ta, ko da aka ƙwace ta daga hannu sai na fara zunduma ihun

"take me to ur oga" shine kawai abinda nake faɗa ina ihu, ƙattin matan nan ne dai suka zo sukai ciki da ni sai ɗakin da aka sauke ni da farko garam naji an rufe ƙofar tare da sa key



zaman daɓaro kawai nayi a ƙasan ɗakin ina ci gaba da rafsar kuka na wanda ban san ranar denawa ba ƙila sai ya mayar da ni gida,


sai 1:30 sannan na tashi na gabatar da sallah azahar ban idar ba naji an buɗe ni linda ce
"is time 4 lunch ma'am" naji tace

4 / 33