Author : Maman Waleed Da Waleedah Category : Romantic Hausa Novels
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
Page :27🌹
Yau na tashi duk na gaji da zaman gidan don haka ko da na haɗawa abu haidar breakfast sai na zauna ina yi mai ƴar hira kafin in kawo masa buƙatata
"kinga ni bana fahintar abinda kike ceqa yadda kika ganni nan sauri nake yi zan shiga meeting nan da 2hrs da wasu turawa kuma ko haɗa documents ɗin nawa da zanyi presenting banyi ba don haka ki faɗa kawai" na faɗa ina in'ina
"dama ina son fita ne"
"kije ina wa kika sani a garin nan"
"ni ko ina ne ma nidai kawai in fita" shiru yayi na ɗan wsu sakanni yana tunani, ni kuma Allah Allah nake yi kar yace a a don nasan halin sa
" sai kije sabon shopping mall ɗin dana buɗe a wuse zone 4 dama baki je, kiyi shopping ko ya kika gani" tsalle na daka
"yayi yayi yayi na gode sosai" na faɗa tare zuwa kusa da shi na rungume ni na manna masa kiss
"wow wow wow wow young lady yanzu fa na ce miki ina da meeting amma kina son ki hana ni fita" ya faɗa yana ƙoƙari janye jikin sa, sarai na fahimci abinda yake nufi don haka sai na ɗan sake shi, ya gama cin abincin shi ya fice tare da cewa in ina buƙatar wani abin in kira shi kafin 9:00, har ya shiga mota na bishi
"baka bani kuɗi ba haka zanje shopping ɗin ba kuɗi" na faɗa a shagwaɓe
"sweety nace miki shopping mal ɗinki fa zaki, ai ba sai kin biya ba"
"to in attendant ɗin yace bai gane ni ba fa ko kuma ma ai bai sanni ba ni kuma gaskiya bazan iya tsayawa yi masa bayani ba" atm card ɗinsa ya ɗauko ya bani
"ayi shopping lfy" ya faɗa yana me rufe ƙofar, driver ya ja suka wuce ina ɗaga musu hannu
sai ƙarfe 12:20 sannan na fita nasan zanje in tarar da mall ɗin a cike, i was so excited, nima at last zan fita, nayi shirya tare da shirya ɗana driver ya jamu sai shopping mall ɗin don yin shopping, nasan zan shiga in tarar da mutane sosai din wurin sabo ne gashi kuma a area yake
nayi mamaki sosai da na shiga na ga wurin kamar anyi shara ba kowa sai ma'aikata, sun wani jeru sai miƙo min gaisuwa suke, to me take faruwa ne, dama basa samun customer's ne na tambayi kaina
duk cikin uniform ɗin su blue and maroon colour, dey look really good haka zalika uniform ɗin yai kyau da tanbarin *ajaban* a gaban kowane uniform, manager ne ya matso da kansa don kwasar gaisuwa inda ni kuma na kasa hakuri na tambaye shi ya naga mall ɗin kamar anyi shara ba sa samun customers ne
"no yallaɓai ne yayi waya yace ayi evacuating mall ɗin wai zaki zo shopping shi yasa muka sallami kowa kuma muka hana kowa shigowa har sai kin gama" ya faɗa da fara'ar sa,
raina ne ya ɓaci don me zai ce a kori kowa taya ma za ai in yi shopping ni kaɗai ai it will very boring, wayata na dauko na kira shi
"hello habibti ya shopping ɗin naki"
"wane shopping bayan its boring, me yasa kace a kori kowa amall ɗin"
" so sorry habibti wai don ki sake ki zaɓi abinda ranki yake, kar ki samu damuwa bari insa a gyara"
"tayaya zanji daɗin shopping bayan babu wanda zan gani in tambaye shi
ya kyan product yake"
"am really sorry habibti, bari in gyara kin san nace miki ina meeting yanzu ma ɗan fitowa nayi zan ɗauki abu a office ɗina naga wayar ki"
"ok" na faɗa ina kashe wayar
ɗaukar shopping basket ɗin nayi na fara bi ina ɗaukar abinda nake so, abin mamaki sai ga masu aikin wurin suma kowa ya ɗauki basket sun fara zagaw suna ɗaukar abubuwa, mtsss lallai ma wato ya mayar dani wata yarinya ke nan
na cigaba da abina nayi kamar bansan ma suna yi, wajen cream na nufa don in duba hand cream, wani hand cream na gani na ɗauko, sai naji muryar wata a baya na
"mam wannan cream ɗin akwai pig's fat a cikin sa" juyowa nayi naga wata mace daga gani itama staff ce
"tanks wanne kike ganin ba pigs fat ɗin"
ta nuna min muka ci gaba da shopping ɗin da ita don naga alamar ta san aikin ta sosai har na gama sannan ta rakani counter, na biya aka biyo ni da kayana har mota na kama hanyar gida nidai kawai na fita ne amm ko kaɗan banji daɗin fitar ba mtsss
kashegari da daddare una dinner tare da abu haidar si wayata tai ringing, ina dubaw naga aunty bilki gaba na ne ya faɗi don abu haidar be sn muna waya da auntyn sa ba, a sanyaye na ɗauka
"salamu alaikum kin sauka ne" na tambaya ba tare da na kama suna ba
"wallahi tun la'asar na kasa samunki ne si yanzu, an samu baby girl"
" maa shaa Allah, Allah ya raya ta"
"amin amin ina alin" ta tambaya
"gashi nan"na faɗa ina shafawa haidar kai a matsayin kamar shi ake tambaya
to a gaishe min da shi da jikana"
"zai ji in shaa Allah, Allah ya rya ya baki lfy sai na kira" na faɗa ina katsa wayar don kar ta tambayi abinda bazan iya ansawa ba
"ƙawata ce a lagos ta haihu" na faɗa don kar ya kawo wani abin a ransa duk sai na tsargu kun san ance mara gaskiya ko a ruwa gumi yake
"Allah ya raya" ya faɗa atakaice
har muka gama cin abinci ina soki burutsu na ni gani nakeyi kamar ya gane basarwa kawai yayi amma a zahirin gaskiya bai gane ba, sai da muka gama dinner ya wuce part ɗinsa sannan na ƙule a ɗaki na kira ta mun sha hira sosai har nake tambayar ta iya tace tana nan ƙalau daga ƙarshe dai na buƙaci ta turo min da account number ta don in turo mata ɗan abinda za a asiya wa baby kayan suna, tai murna sosai inda daga ƙarshe tace zata turo min da acc number maƙociyar ta, kamar yadda tace kuwa sai gashi ta turo min
bayan kwana biyu na fita na je kai haidar allura daga asibitin na biya ta bank na tura mata 100k, na kira ta nace ta ɗau 50k ta bawa iya 50k, na sha godiya harda kukan ta, har iya sai da tayi min godiya ni duk kunya sai ta kama ni irin dukiyar da jikan ta ya mallaka ita mai iya kyautar dubu 100 ce amma wai yau anbata 50 shine take irin wannan godiyar, ko da yake dole ne tayin akayi la'akkari da irin yanayin da ta ke ciki Allah ya kyauta gaskiya akwai matsala sosai tsakanin da aliyu da *dangin sa*wanda zanso ace nasan masomin abin da ya haɗa su, wanda nake fatan in kawo ƙarshen sa
watan haidar bakwai da haihuwa na fara period ɗina ban kawo komai ba amma to my surprise tunda nayi sau ɗaya ban kuma bakuma yi ba gashi yanzu kusan wata biyu kenan wannan ya tabbatar min ina ɗauke da wani cikin, ba haka na so ba na so sai ɗana yayi wayo sosai sannan zan kuma haihuwa
amma ko dana faɗawa aliyu shi a ɓangaren shi abin ba haka yake ba yai murna sosai da sosai har wani special tattali nake samu, kasancewar wannan cikin ya zo da laulayin na rashin son cin abinci sai abu haidar ya ɗauko min nutritionist wacce zata dinga kula da zan dinga ci har ma da haidar ɗin kasancewar muna shirin yaye shi, macece me tsauri ba koamai take yarda inci ba har tafi linda tsauri, komai a tsare yake ban isa inci komai ba sai tace for the sake of the baby, da ta ishe ni ba shiri na sa aliyu ya sallame ta na ce masa na warke don bazan iya wannan iyayin nata ba me ciki da aka sani da kwaɗayi amma ni ba daman ince ina sha'awar wani abun sai a ce min for the ske of the baby Allah ya kyauta
[7:44PM, 12/7/2017] +234 806 803 7117: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀
By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)
🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺
Page:28🌹
Gaskiya cikin nan yana gwara nk ba kaɗan ba ba abinda nake da ya wuce kwanciya,
ganin haka ne yasani signing a face book na farayi don ya ɗebe min kewa, tunda haidar yanzu kusan a wajen nanny ɗinsa yake wuni,
duk da dai ban yaye shi ba saboda likita yace sai ya shekara sannan za a yaye shi amma yakan wuni wurin nanny ɗinsa don in samu hutu sosai,
ni cikin jikina sam baya gaba na in da hali da tuni na cire shi don ni naso ɗana yayi wayo sosai amma ya zanyi da abinda ya fi ƙarfina
yau na hau face book wani saƙo ne ya ɗauke min hankali inda naga an rubuta *children are d greatest gift from Allah pls cherish them*
saƙon ya taɓa min zuciya sosai na tsaya na karanta shi ya fi a ƙirga, wanda don tsabar shiga zuciyata da saƙon yayi har ban san lkcn dana tsinci kaina ina shafa ɗan cikin da ke jikina ba
Saving saƙon nayi don yayi min daɗi sannan nayi liking ɗin shi na kuma yi comment *jzk u just save a soul* sannan na fita,
haka na wuni ina juya kalmar nan a raina maganar haka take dubu nawane suke neman haihuwar basu samu ba amma ni na samu ba abinda na rasa amma wai ina kawo wani uzuri nawa mara tushe, Allah dai yasa mu gane
ko da na hau da daddare sai naga baiwar Allahn nan tai min reply da *am happy to be able to help u* naji daɗi saƙon ta na tura mata da ɗan murmushi ☺😊,
tun daga ranar kullum sai matar nan ta turo saƙo akan yadda ƴaƴa suke wata ni'ima ce a rayuwa, babu abinda ya fi su in mun gyara su,
har abada mu zamuci moriyar mu, mu more su muna raye sannan idan mun mutu su zame mana sadaƙatul jariya
ban taɓa hawa face book ba ba tare da na duba profile ɗin baiwar Allahn nan ba wacce sunan ta yake *salma abdul jalal* matar tayi gaskiya sosai,
kusan kullum sai munyi chatting da ita, ga shawarori da take rubutowa akan aure da tarbiyya yara, na zama da miji, *dangin sa* da dai sauran su,
tana bada shawara sosai akan kar mace ta sake ta auri namijin da *dangin sa* basa ƙaunar ta barin ma uwar sa
don kuwa muna ganin kamar idan mace ta auri namji shikenan to ba shikenan ba duk wacce ta auri namiji ba shi kaɗai ta aura ba gaba ki ɗaya da shi da *dangin sa* ta aura,
na kan yi mamaki to ni dai gani nayi aure amma mijina ya nuna min shi kaɗai na aura har baya son mu yi mu'amala da *dangin sa* ya sa katanga ya katange tsakanina da *dangin sa* ya nuna min shi kadai ne babu wani kuma
ganin face book bashi da sirri yasa na tura mata don Allah ina son ta bani contact address ɗinta mu dinga chatting ta whatsapp don ya fi sirri,
ikon Allah ta aiko min, amma to my suprise number nata na turai ne, ko dana koma profile ɗinta sai naga ashe balarabiyar saudia ce take zama a london, sannan likitar yara ce
nayi saving number nata muka fara chatting ta whatsapp da ita, a hirar tamu ne na gano ashe babba ce tama haife ni,
na ce mata nima mijina mamansa ƴar saudiyya ce amma ta rasu, sosai tayi mamaki wai ƙaddara ce ta haɗa mu, nima na yadda da cewar kaddarar ce ta haɗa mu, itama ta bani labarin cewar ta taɓa zuwa nigeria ta haihu amma ɗan ya rasu, na tausaya mata sosai
"kina da wasu ƴaƴan" na tambaye ta
"no babu, tun daga kanshi ban kuma ba , saboda na samu matsala wajen haihuwa, amma ina ruƙon ƴaƴan mijina yanzu" wayyo kuka ne kawai banyi mata ba amma na tausaya mata sosai
muka sha hirar mu sosai ranar mafi yawancin hirar tamu akan yara ne ina bata labarin haidar she was very intrested in hirar ɗan nawa, har na faɗa mata ina da ciki da bana so sai da naci karo da text ɗinta a face book sannan na soma son abinda ke ciki na,
tai min faɗa sosai tare da nasiha mai kashe jiki, naji daɗin hirar mu sosai na kuma gode mata, daga nan ta bani tips akan yadda zan dinga kula da mijina da yadda zan dinga tsara tafiyar da lamarin gidana naji daɗi sosai tunda nake babu wanda ya taɓa zaunar dani ya bani wannan shawarar sai wannan baiwar Allah da na sa mata suna mimma
ita ma taji daɗin sunan har tana cewa ta samu ƴa a nigeria, rayuwar gidana ta sauya sosai domin shi kan shi abu haidar ɗin ya ga changi sosai a tattare dani kuma duk godiyace ga mimma,
irin tattalin sa da nakeyi da irin yadda nake tsara komai ba kamar da ba wani lkcn har cewa yake yi kamar ba zainab ɗin daya aura ba don yanzu duk wata hidima tashi na ɗauke ni nake yi ba kamar da ba da rabi nayi rabi masu aiki suyi,
kullum na hau akwai sabuwar dabarar da mimma zata bani na harkar sha'anin gida da kuma aure kuma idan na gwada kamar yankan wuƙa haka zanga yaci
don haka yanzu mijina ya kuma sakankancewa dani, baya iya aikata komai sai dani ko shawarata wata shaƙuwace sosai ta shiga tsakanin mu da shi wanda har office idan abu ya faru yakan kira ni ya faɗa min inbashi shawara ko tafiya yanzu abu haidar ya daina yi sai dani
dai dai da kayan da zai sa sai ya kirani na nuna masa ko kuma in ɗauko masa in kuwa ba haka ba bazai sa ba har sai na gama abinda nake yi na ɗauko masa, duk wannan shaƙuwar tamu duk ta dalilin mimma ne babu abinda zance mata sai dai godiya
Ga son haidar da takeyi kusan kullum sai ta tambayeshi, ko tace me ya saka yau turo min hoton shi nakan tura mata wanna ne yasa pics ɗin haidar a wayarta sau fi nawa,
page guda gare shi a profile ɗinta na face book, hatta da profile pic ɗinta na face book da whatsapp pic ɗin haidar ne tana son shi ba kaɗan bahar video taping ɗinsa take sani yi mata in tura mata tai ta kallo, wannan ne yasa nima na ƙara son baiwar Allah nan na kuma ƙara sakin jikina da ita kun san ance me ɗa wawa
cikina yana ƙara bunƙasa ina ƙara samun kulawa daga wajen mijina tare da samun shawarwari daga mimma, harya isa haihuwa addu'o'i sosai mimma ta bani na mata masu ciki wanda na kasance ina yin su ba dare ba rana
ranar wata alkhamis da safe na tashi da naƙuda wanda Allah ya taimake ni abu haidar yana gida bai kai ga fita ba yana sunku tata bai tsaya ko ina ba sai asibiti inda bamu wani daɗe da zuwa ba na sauka lafiya tare da samun ɗana namiji
nai murna sosai tare da gode wa Allah ubangiji (swt) da ya bani haihuwa lfy tare da adduar Allah ya raya mana su bisa sunna ma'aiki (saw)
duk murnan nan da nayi ban kai abu haidar don shi har kuka yayi sai dana ɗan tattaushe shi sannan yayi shiru bansan dalilin kukan nasa ba amma nasan cewar wani abun ya tuno shi yasa shi yin kukan ko ma dai menene Allah ya magance mana, na faɗa a raina
bamu wani daɗe da haihuwa ba aka bani sallama gani ni lfy nake haka zalika ɗan ma directly gida muka koma don mu gyara jikin mu, wata mata me suna baba ita ce a gidan yanzu mama ce ta kawo min ita tun cikina yana da wata takwas wai saboda haihuwa ita bata son ƙedaran su dinga taɓa jarirai ba