Chapter 21 Reading DANGIN SA COMPELET HAUSA NOVELS BY MAMAN WALEEDA DA WALEED.txt Arewa Novels

DANGIN SA COMPELET HAUSA NOVELS BY MAMAN WALEEDA DA WALEED.txt

Author :  Maman Waleed Da Waleedah Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   21 / 33

60K to 63K   out of 97.7K words

wai in kira shi to yaje yayi ta zama acen zai ga mara zuciyar da zata kira shi na faɗa a raina



*************


Aliyu yana zaune ranshi ne a ɓace wai ace zainab yauzu watan shi uku amma bata taɓa neman sa ba, kuma har tura mata da number da zata same shi tayi amma sai ta ƙi kiran sa



Tun bayan haihuwar mohd Allah ya bashi sa ar mallakar wani tafkeken jirgin ruwa wanda mutane daya wa suka so mallaka amma cikin ikon Allah me jirgin ya siyar masa,


wannan ne dalilim daya sa bayan sunan mohd ya kamo hanyar china ba shi don ya zo ayi wa jirgin gyaran daya kamata, kasancewar jirgin a bakin teku yake yasa dole nan ya koma tare da ɗaukar ƙwararrun ma'aikata don gyaran sa



jirgin tsohon jirgi ne, don haka dole yana buƙatar gyara sosai, inda yake sam babu service don kuwa can wajen garine sosai anan akaa ajiye jirgin, sai dai local telephone wadda baka iya kira ba sai dai a kira ka




wannan dalilin ne yasa ya aikawa da zainab number don ta neme shi amma cikin ikon Allah so ɗaya bata taɓa kiran sa ba, bata taɓa tunanin haƙin daya ke ciki ba amatsayin sa na mijinta balle tace zata kira shi


ya kai duban sa ga makeken jirgin ruwan da ake ta faman aiki a kai, in shaa Allah nan da wata guda za a gama aikin sa kamar yadda ma'aikatan suka ce, ya tuno irin gwagwarmayar daya sha kafin ya mallaki jirgi amma sai ya ji duk wani harkar jirgin ya fita kanshi idan ya tuno yadda matar sa tai watsi da lamarin sa




akwana a tashi Allah ya basu aliyu damar gama haɗa jirgin sa lfy, jirgin ba ƙananan kuɗi ya ci ba don gyaran jirgin ma ya fi kuɗin jirgin tsaɗa komai sai da aka canza sabo, komai sai da akayi modernizing ɗin sa shi kanshi yana mamakin irin kashe kuɗin da yayi akan jirgin amma idan ya tuna cewa cikin watannni ma zai iya mayar da kuɗin jirgin dana gyaran sa sai ya ji ɗan sanyi




ko yanzu ya saka jirgin a kasuwa zai samu riba sosai amma kasancewar harka da jirage na jigilar kaya shine sana'ar sa yasa shi doe ya bar jirgin sa don ya mori abin sa ba shi kaɗai ba harma da ƴaƴan sa



bayan an gama haɗa jirgin akai launching ɗinsa ya fara aiki, ko da aliyu yaga jirgin ya hau teku ya fara aikin sa sai shima ya fara haɗa ya nashi ya nashi don ya kamo hanyar gida, yana murnar zai zo yaga iyalin sa amma can cikin ranshi yana jin haushin yadda zainab duk wannan daɗewar da yayi bata taɓa kiran sa ba



jirgi ya sauke passangers ɗin sa daya ɗauko daga china lfy a abuja a cikin su kuwa harda aliyu ajaban, sanye yake cikin Texido ɗinsa blue daga gani dollar tayi kuka wajen siyen texido ɗin nan, ya yi shar dashi kamar wanda ya dawo daga honey moon



driver ne yake jiran shi don haka yana zuwa ya shiga mota ya kama hanyar gida, ya riga ya gama shirya rashin mutuncin da zai yi wa zainab har yanzu bata san shi ba tana ganin da ta haifi ƴaƴa biyu bazai iya rabuwa da ita ba, to shima da mahaifiyar sa ya girma kuma gashi nan dam ba abinda ya same shi rayuwar sa yake kamar kowa



ko da aka shige get ɗin gidan ya ganshi fes kamar yadda ya sa ran samun shi da kewar iyalen shi ya dawo amma sai ya dake ya kama hanyar part ɗin sa, ba tare da ya kalli part ɗin natan ba don shi a tsarin shi mace bata isa ya bita ba, don shine gaba da ita




a gaskiya yai tsammanin ganinta amma ga mamakin sa sai taƙi zuwa har dare yayi babu ita balle yaga ƴaƴan sa me kenan zainab take nufi



ita ma dai zainab a nata ɓangaren tana jiran shi ya shigo don taga dawowar sa harda ɗan shirinta don tasan yadda ya kwashe kwanakin nan bai gansu ta san zai shigo ya biɗa haƙƙin sa amma abin mamaki shiru bashi ba labarin sa har bacci ya kwashe ta



duk kowannen su ya kwana tare da bacin ran ɗan uwan sa, abinda bai taka kara ya karya ba ya kai ga masoyan nan cikin tashin hankali kowannen su yana ji haushin ɗan uwansa yana gani ɗan uwan bai ɗauke shi da daraja ba




haka suka tashi kowannen su yana cike da ɗan uwan sa gaba ce sosai ta shiga taakanin su inda a kowane ɓangaren suke cutuwa kuma suna begen juna tare da fatan faɗan nan zai zo ƙarshe amma da yake sun bar shaiɗan ya na yi musu huɗuba sai kowanne ya ɗau fishi tare da ɗorawa ɗan uwan sa laifi



har aliyu sai kwashe wata da wani abun gabar nan tasu babu sauƙi, ya gaji don haka sai ya nufe ta don ya na son sanin me take taƙama da shi da har zata dinga yi masa wannan abun kamar ba mijinta, wannan karon ba zai juri rashin mutunci ta ba inda tayi taga taci riba wannan karon bata isa ba ya faɗa tare da dosar part din natan



itama zainab a nata ɓangaren abin yana damun ta mutumin nan me yake nufi kenan bata wata daraja kenan ya tafi kusan wata huɗu be taɓa neman su ba yanzu kuma ya dawo ko ta kansu be bi ba hidimar sa kawai yake yi, wasu hawaye na takaici suka zubo mata bata bi ta kan hawayen ba sai ta ƙyale su suna zuba da kansu ko taji sanyi zuciyarta



banko ƙofar ɗakin natan taji anyi kamar ana yaƙi da sauri ta goge hawayen da ke zuba tare da juyowa taga waye, gogan ne ranshi a bace yana tsaye tare da riƙe ƙofar da hannun sa fuskar nan tasa kamar me don ya bala'in haɗe rai


"ke wai me kike taƙama da shi ne ki faɗa min, ko an gaya miki bazan iya rayuwa bake bane ko kuma don kin haifa min ƴaƴa guda biyu shine kike tunanin zakiyi min rashin mutuncin da ranki yake so, bazan zauna da matar da bata da mutunci ba wacce bata san mitinci mijinta ba kina ƙarƙashina amma baki san komai na kula da miji ba so kike yi kullum ya kasance ni zan dinga binki, ki kalle ni kyau banyi kama da namiji me bin mace ba ita kuma tana yin rashin mutuncin ta ni ban ɗauki mace a bakin komai ba face abara ajiye wa agida


ko kina tunanin ni da ƴaƴa na bazamu iya rayuwa ba sai da ke ki kalle ni nan tun uwata ta haifeni ta gudu ta barni kuma gani nan daram har nafi wasu mada suka rayu da iyayen su don haka bazan juri wannan rashin mutuncin naki ba tare rashin tarbiyya


ki shirya kayan ki ki koma gidan ku idan kinje kin koyo yadda ake kula da miji kya dawo don bazan iya zama da macen da bata san darajar mijinta ba, har ya fita ya dawo


kuma da fatan bazaki tafin min da ƴaƴa ba ko ɗaya har mohd ɗin ma ki ajiye min abina don bazan bari suje su koyo rashin tarbiyyar da kike taƙama da ita ba


ya fita daga ɗakin tare da banko ƙofar kamar zai balla ta kuka kawai na saki tare da tausayawa kaina, rashin mutunci aliyu ya isheni haka duk abinda yayi min be ishe shi sai daya biyo ni har ɗaki yai in rashi mutunci gaskiya dole ne in bar masa gidan sa na faɗa ina fara haɗa kayana
[7:46PM, 12/7/2017] ‪+234 806 803 7117‬: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀



By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)

🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺


Page:39🌹



Haɗa kayana na fara yi tare da sa na mohd ni ba mahaukaciya bace idan shi bashi da tausayi to ni ina da shi haidar de zan bar masa amma bazan bar masa ɗana me shan nono ba na faɗa araina



Bayan na gama haɗa kayana na fito da su tare da kiran masu aiki su taimaka min su fitar min da akwati na har bakin get naje da mohd a goye a baya na ga akwati na ina ja, amma sai me gadin ya hanani,

"hjy yallaɓai yace kar in barki ki tafi da yaro ko ɗaya" kaina ne ya ɗaure au har faɗawa ma'aikatan sa yayi cewar kar in tafi da yaro ko me



Na kai duba ga mohd wanda yanzu na sauko shi sai baccin sa yake tayi, hawaye naji sun cika min ido ya za ayi in tafi ba tare da wannan yaron ba me yayi, in ni yana ganin nayiasa laifi ɗana fa me yayi yaron da babu abinda yake ci daga nono sai ɗan ruwa in yaga dama



Komawa nayi cikin gidan indai kuwa bazai bari in tafi da ɗana ba to kuwa babu inda zani na faɗa, bai dawo ba sai dare, ya shigowa part ɗina ya nufa fuskar shi amurtuke
"ke da yake bai da mutunci nace ki tafi shine kika ƙi tafiya ko"
"ce maka akai gidan ka aljannah ne da zaka ce na ƙi tafiya, na so tafiya me gadinka ya hanani"



" au da kina nufin da ƴaƴa na zaki tafi"
"ai kai da yake baka da imani shine zaka raba ni da wannan ɗan jaririn" na faɗa ido na taf da hawaye



"rashin imani kike son gani, yau zaki san kin zo ƙarshe"
Ƙwace mohd yayi daga hannun na, bazan iya cewar zan hana shi ba don in muka ce zamuyi kokawa akan yaron shi yaron ne zai cutu,



nanny ɗin sa ya kira me suna hannatu don yanzu na sallami kafiran nan nannies ɗin yara duk musulmai ne, yace ta karɓi mohd ina kallo aka fitar min da yaro na kuka kawai nake yi ban taɓa ganin wulaƙanci irin wannan ba a raba ka da ɗan ka


dawowa yayi kaina yana jana har sai daya kaini waje sannan ya sani a mota tare da driver ɗin yasa lock a motar sai ga kayana an biyo ni da shi har da yar jakar hannun na


window ɗin ya buɗe tare da wullo min purse ɗin a fuskata "duk randa kika san darajar miji kya dawo" kuka na saki me sauti in Allah ya yadda ni aliyu har abada bazan kuma zama da mutumin da be san darajar ɗan adam ba na faɗa



driver ya ja muka fara tafiya sai lagos ina jin shi yana ja wa driver ɗin kunne ya tabbatar da ya ajiye ni a ƙofar gidan mu, sai kace wata yarinya, ranar naci kuka irin wanda ba taɓa yi ba



wai dama haka mutum yake ji idan wanda yake so ya ƙona masa rai don Allah ya za ayi in iya yafewa aliyu irin wannan cin kashin da yayi min, sai asuba sannan muka ƙarasa lagos aikuwa har ƙofar gidan namu ya kaini lkcn gari ya waye ma sosai kasancewar go slow ɗin da muka tarar a hanya



adaidai ƙofar gidan mu yayi parking tare da fita ya ƙwanƙwasa gidan ina zaune cikin motar ina jiran shi don gabaɗaya motar a kulle take har yanzu be buɗe ba



wata yarinya ce tazo ta buɗe, sai shi kuma ya juyo ya zo ya ɗaukar min akwatina tare da miƙawa yarinyar sannan ya buɗe min ƙofar na fita


tooo faaaa yau ake yin ta me zancewa baba kenan, na faɗa araina, ohhh ko ya ɗana mohd ya kwana shi kaɗai ya faɗo min araina naji wasu hawaye, goge hawayen nawa nayi sannan na saka kai na cikin gidan namu yau dai sai yadda akayi da ni



nayi mamakin dana ga falon gidan babu kowa sai yarinyar nan da ta buɗe min daka gani ƴar takwa ce ( ```irin yaran nan da ake ɗauko su daga niger suna yin aikatau```)


"ina maman" na tambaya ina neman wajen zama
"ta tafi shagamu da asuba ita da baba"
"me akeyi a shagamun"
"ɗan ƙanwarta ne ya rasu jiya da daddare shine sukayi sammako don su samu jana'iza" ta faɗa



Allah yayi mama da ƙanne sosai a shagamu don haka sai ban damu da sanin ko wacce bace na dai bishi da addu'ar Allah ya jikan rai


"to ina su amina da su bashir" na kuma tambayar ta ƙannena, wato ƴaƴan mama
"duk tare suka tafi"
"ke kaɗai ce a gidan" gyaɗa min kai tayi, daga gani ta ɗan jima a gidan amma da bata daɗe ba mama bazabta taɓa barin ta ita kaɗai ba



miƙewa nayi aikuwa banga ta zama ba da su mama na nan ne da sai in zauna amma tunda ba wanda ya san na zo gwanda in ƙara gaba don yanzu da sun dawo ni zasu ba rashin gaskiya tare da mai dani wurin wancan mara mutuncin da be san darajar ɗan adam.ba na faɗa tare yin waje da ɗan akwati na




"aunty zaki tafi ne in ta dawo wa za ace mata tazo" shiru nayi ina tunanin wa zance ni yanzu duk na manta ƙawayen maman ma balle in anbaci sunan ɗaya koma zan iya anbata ƙila yarinyar ta san su sai nace mata
"kice mata ƙanwarta ce ta zo su tafi shagamun tare, ko da yake barshi ba sai kin gaya mata ba idan muka haɗu acan zan cemata na biyo ta nan" to kawai tace min nai mata sallama na kama hanyar waje



purse ɗin da ke hannuna na duba naga tabbas kuɗin ciki zasu kai ni kano daga nan tashar mota dake agege na nufa domin kama hanyar kano



*************

duk da dai yasan badace ba abinda yayi mata amma hakan a ganin shi shine dai dai ƙila idan taje ayi mata faɗa, gaskiya yana son zainab sosai amma wani lkc dole ya rufe ido ya taka mata burki idan tanas wani abun nata



madara yaje ya siyo wa mohd, kan a dinga bashi shima sai yanzu yaga kuskuren shi ƙwace yaron da ya bar mata shi ƙiri ƙiri yaro ya ƙi shan madara tunda be saba da feeder ba, don haka sai ya ƙi karɓa yana ta kuka


haidar ganin ɗan uwansa na kuka ya sa shi fara kuka tare da kiran ```ammi na```kuka kawai suka dinga yi daga shi har mohd ɗin, nannies ɗin nasu rasa yadda zasuyi sai suka kira aliyu don ya san a halin da ake ciki




yana zaune a office aiki ne gare shi sosai a gaban sa, amma kusan rabin hankalin sa ya kan wayar sa yasan iyayen zasu iya kiran any moment shi ma so yake yi ta dawo ko don ƴaƴan sa ya faɗa,
"taurin kai gare ki baki iya bada haƙuri ba duk da kin san ke me laifi instead sai ki ka so yi min rashin kunya"



gabaɗaya ya rasa abinda yake masa daɗi, yana cikin wannan tashin hankalin ne ya samu waya daga gida inda aka gaya masa halin da yaran suke ciki



wannan shine tashin hankali akan tashin tashin, haɗe kayan sa yayi ya kama hanyar gida, yana zuwa gida ya ga halin da yaran suke ciki duk sai yaji ya ƙara shiga ruɗani, ya rasa abinda yake masa daɗi, wai me yasa iyayen zainab har yanzu basu kira shi bane ko kuma ƙarya taje tayi masa, ya tambayi kansa



ɗaukar yaran yayi ya sasu a mota ya fita dasu ƙila in sun ga waje sayi shiru, ga haidar wannan abin ya ɗanyi yi masa aiki amma mohd ko a jikin sa yunwa kawai yaron yake ji don haka kuka kawai yake yi babu ƙaƙƙautawa



hankalin shi fa ya tashi sosai da sosai, asibiti ya nufa direct don kar yaron ya kamu da wani ciwon saboda kukan da yake yi, babu abinda aka ba mohd face da aka cewa aliyu yunwa kawai yake ji a bashi abinci, ya roƙi dr. cewar mmn shi ba lfy ta tafi jinya kuma ya ƙi cin abinci



sai da dr. ɗin ta gama yi masa faɗan ta sannan ta sa ya kawo mata abincin babyn ta haɗa masa da ɗan dumi ta bashi da yake yaron yaji yunwa sosai sai kawai ya karɓa ya fara sha, aliyu har wani ajiyar zuciya yayi da gode wa Allah daya ga mohd ɗin ya karɓa, sai daya sha ya ƙoshi dr. ta lallashe yayi bacci sannan ta ba aliyu shi tare

21 / 33