Chapter 17 Reading DANGIN SA COMPELET HAUSA NOVELS BY MAMAN WALEEDA DA WALEED.txt Arewa Novels

DANGIN SA COMPELET HAUSA NOVELS BY MAMAN WALEEDA DA WALEED.txt

Author :  Maman Waleed Da Waleedah Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   17 / 33

48K to 51K   out of 97.7K words

smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺



Page :31🌹



Salma tana zaune ainda ya tafi ya barta, gaskiya dole ne in bar musu gidan su, ta faɗa a ranta, yau ɗinnan kuwa gwanda ko hotel ne ya kama min, kuma da na samu jirgin saudiyya in gudu ta faɗa tana ƙara gyara zaman ta a saman ƴar tabarmar da take zaune

duk ta gaji hankali gabaɗaya a tashe yake sai kace sun ga wani kashi yadda sukai treating ɗin ta kamar ba musulmai, gaban ta ne ya yanke ya faɗi,
"subhanallah" ta faɗa tare da dafe ƙirjin ta, cigaba yayi da faɗuwa inda ita kuma ta ci gaba da kwararo addu'o'i tana mai neman tsari da duk wani sharri da zai zo gareta


Gafara gafara gafara kawai taji ana cewa duk da dai bata san abinda yake faruwa ba amma ta ɗago kanta don taga menene


Mutum taga an shigo da shi an shige da shi ɗakin iya, tsayawa tayi tana tunanin lfy, kukan iya taji tare da kururuwa tana ƙwalawa sani kira, bata san lkcn da ta zabura tayi ɗakin iyar ba, bangaje mutane tayi ta yi har sai da taje kan sa,
"innalillahi wa inna ilaihi raji'un" shine kawai abinda bakin ta yake faɗi


Durƙusawa tayi kjsa da shi ta fara kuka cikkn nutsuwa, iya da ke kansa tana kururuwa ta ɗago don jin mutum a kusa da ita, tana ganin salma tayi kanta da duka da zagi
"mayya daga zuwan ɗana kin lashe masa kurwa" ta dinga dukan ta tana zagin ta



ko kaɗan salma batai yunƙurin hana ta ba don ita raɗaɗin da yake damunta a zuciyar ta ya fi ƙarfin dukan da iyar take mata, kuka kawai take yi tare da yin istigfari ga Allah ubangiji (swt)



hjy tana gidan ta ta kuma jiyo hananiya da kururuwa tare da ƴen koke koke, hijabin ta kawai ta kuma ɗauko wa tayo waje, tana zuwa gidan ta tarar da mutuwar sani da kuma irin jibgar da iyar take yi salmar wanda babu wanda yai yunƙurin hana iyar


da sauri taje ta janye salmar,
"idan kika kashe fa" inji hjy
"na kashe banza na kashe wofi ai nima kashe min ɗana tayi Allah ya isa tsakanina da ke shegiya" ta dinga bin salmar da zagi, ragiwar ƴaƴan iyar suma suka yooo chaaa wai sai sun dake ta ikon Allah



ba shiri hjyr ta janye salmar zuwa gidan ta don taga alamar zasu iya yiwa salmar lahani in aka bar musu ita, gida ta wuce da ita direct, ta ɗauko panadol da ruwa ta ba don taji jikin nata zafi rau da shi oohhh Allah haka yake ikon sa



ko da tasha sai tayi mata shimfiɗa don ta ɗan kwanta don a gaskiya tana buƙatar hutu don sai ta iya shiga wani hali ga halin da take ciki,




har akayi wa sani sutura aka fita da shi salma tana kwance ita ba bacci take yi ba komai ba, hjy ta so ƴen uwan sanin su bar salmar tayi masa kallo na ƙarshe amma ƙiri ƙiri suka ce idan ta zo sai sun lahanta ta me yayi zafi inji hjy



Salma ranar taga baƙin ciki ido da ido ta rasa abinda yake mata daɗi burin ta kawai gari ya waye ta kama hanyar garin su, ko da dai tana tunanin me zata cewa iyayen ta idan sun ganta da ciki amma hakan ita a ganin ta sai ya fi mata kwanciyar akan irin wulaƙan cin da take fuskanta a nan



cikin dare nakuɗa ta kama salma, ta sha wahala sosai, hankalin hjy ba ƙaramin tashi yayi yadda taga salmar tana nunfashi sama sama gashi ta kasa nishin, ita hjy ba turanci balle larabci ita salma ba hausa ba, don haka sai communication yai wuya sosai a tsakanin su ga naƙuda ta zo da matsala sosai, ga dare babu abin hawa, addua kawai hjyr ta dinga tofawa tana ba salmar tana sha wuya sosai kafin daga bisani Allah ya sauke ta lfy gab da asuba, ta samu ɗanta namiji


Shi kanshi ɗan a wahale ya zo don sai da aka watsa masa ruwa sannan yai kuka, hamdala hjy ta dinga yi, inda salma ba abinda take yi sai kuka,


hjy ta haɗa mata ruwan wanka don ta ɗauraye jikin ta, hjy ta kama ta ta kai ta har banɗaki ta ɗauraye mata jikin ta sannan ta haɗa mata ruwan lipton me zafi tace mata ta sha,


ta kuma haɗa ruwa ta wnke ɗan tsaf da shi ta ɗauko sabon zanin goyo ta naɗe shi a ciki ba abinda salmar take yi har yanzu illa shash sheƙar kuka barin ma idan ta kalli yaron, hjy sai ta ɗauka ko tausayin sa take ji



shimfiɗa ta ƙara gyarawa salmar sannan tai mata umar nin ta kwanta, ita kuma ta ci gaba da kimtsa komai, salma kwanciya tayi ta tasa ɗan ta a gaban ta tana kallon sa wasu zafafa hawaye ne suke ta sintiri a idon ta, tausayin sa ne taf zuciyarta,


ko ya rayuwar sa zata kasance ta tuna irin tattalin da sani yake yiwa cikin tun kafin ya zo amma wai yau ga shi ya zo amma kuma ba sani, ya za ayi ta iya tafiya da ɗan da babu uban sa, inda ma ace sanin yana da rai ne da ta tafi da shi, amma yanzu taje tace wa iyayen ta ɗan waye, waye zai yadda cewar ba shege bane


zargin ta za a dinga yi, kuma yaron ya tashi a dinga yi masa kallon shege tunda babu wanda ya san uban sa, kuka ta kuma fashe w da shi, ta rasa mafita, ita baza ta iya zama a nan ba don ƙiri ƙiri mmn sani ta nuna mata ƙiyayya wanda har hakan yai sanadiyyar mutuwar mijinta, idan na tafi da kai bazan taɓa mantawa da wannan baƙin ciki ba, idan na tafi da kai shari'ar garin mu bazavta bari in rayu da kai ba, idan na tafi da kai har abada da tabo zaka tashi, rayuwarkar anan itace rufin asirin mu ni da kai, idan da rabon mu ƙara haɗuwa Alƙah ya sada mu da alkhairinsa ta faɗa idon ta taf da hawaye



ta gama yanke shawarar abinda zatayi, ta kalli yaron ta kallo na ƙarshe ta sinbace shi a kai tare da yi masa addua, sannan ta tashi saɗaf saɗaf tayi waje ba tare da hjy taji ba


ko da hjy ta tashi da asuba kasancewar ta ɗan kwanta bayan ta gama kafin asuba tayi, tai mamaki ganin ɗan jariri shi kaɗai sai ta ɗauka ko salmar ta shiga banɗaki ne, tai jiran har ta gaji don haka sai ta wuce ta duba ta, ba inda bata duba ba ba ita babu alamar ta


har gari ya waye ana neman salma bata ba dalilin ta a haka suka sadauƙar da ta gudu, haka mutan gidan hjy suka haƙura da neman nata suka zubawa sarautar Allah ido


hjy ce ta ɗauki ɗan jariri domin sada shi da *dangin sa* gidan iya ta shiga da ɗan jariri, iya tana zaune a falon ta ana ta cin naman salmar tana sha zagi wai dama shege ne ahi yasa ta gudu ta bar shi, shigowar hjy bai sa sunyi shiru, suka gaisa amma da ƙyar iyar take ansawa


hjy ta ɗauki ɗan ta ɗora shi a cinyar iya, "ga abinda aka samu nan" wani wulli da iyar tayi da jaririn daba dan hjyr tayi sauri ta sa hannun ta ba da tuni jaririn ya sha ƙasa,
"ya zaki ɗauki kazantar nan ta najasa ki ɗaura min kan tsabta taccen hannuna" ta faɗa tana goge hannun ta a ƙasa kamar ta taɓa kashi
"haba iya me yayi miki idan iyayen shi kina ganin sun ɓata miki shi me yayi miki, ko ba komai kya tausaya masa mana ta yadda ya rasa iyayen sa lkc guda"


Wata ƙanwar iyar ce tayi carab tace
"ai mummunar ƙaddara gare shi duk wanda ya ɗauki yaron nan yai ta gamo da mummunar ƙaddara kenan tunda shi haka aka hallice shi da ita tun randa zaizo duniya ƙaddarar tasa ta fara nunawa" nan suka ɗauka haka ne kam babu shakka


hjy tsayawa tayi tana kallon jahilci tsabarsa, tqna mamaki dama hannun ka yana ruɓewa ka yanke ka yar, shiru tayi sannan tace
"to nidai ayi haƙuri atunda ita mahaifiyar shi ta gudu kinga ruƙon yaron nan ya dawo hannun ki a matsayinki na kakarsa"


"uwar shi ma ta gudu saboda ƙaddarar da ke tattare da shi sai ki ɗauko shi ki ce uwar mu ce zata riƙe shi ke me yasa baki riƙe shi ba" inji wata ƴar iyar
"rabu da ita bata san cewar haushin ta neke jiba, don sai yanzu na fahimta cewar babu munafiki sai buhari, don ba gashi ya turo marigayi da wannan karuwar ba, shi ya zauna ya lafe so yake yi idan ƙura ta lafa ya lallaɓo ya dawo ya tunkuɗa ɗana ga halaka ya haɗa shi da ajalin sa, Allah ya isa tsakanina da shi munafiki kawai annamimi, maci amana kawai" ta faɗa tana kuka



abin nan da iyar tayi ba ƙaramin ɓata wa hjyr rai yayi ba tshi tayi tare da sauke ɗan a gefe tayi hanyar waje,
"zo ki ɗauke dawo ki ɗauke don babu wanda zai ɗauki wannan mummunar ƙaddarar a cikin zuri'a ta" tana jin ban bamin iyar da muƙarraban ta na ta dawo ta ɗauki ɗan amma tayi burus da su



bayan ta koma gida ta shige ɗakin ta tafara hidimar ta ,can zuwa anjima ta fara jin kukan jaririn tausayin sa ne ya kama ta ya fara jin yunwa kenan ta faɗa a ranta, ta ɗauka abin wasa ne amma ga mamakin ta sai taji har yaro ya doshi kusan minti talatin yana kuka normal kukan jarirai har yazo yana kuka kamar ana cutar da shi ne


ba shiri hjy ta yayimo hijabin ta ta fice abin mamaki da takaici a tsakar rana a dandamar ƙasa ta ga karirin sabuwar haihuwa, guje taje ta ɗauko shi tana kuka wannan wane irin rashin imani ne dama zafin rana yake kuka, rungume shi tayi ta kara sakin wani sabon kukan tausaya wa yaron, ta juyo ta kalle su kowacce tana sha'anin ta
"in Allah ya yarda sai yaron nan da kuka wulaƙanta ya zame muku inuwa" ta faɗa tana ficewa



baƙaƙen maganganu ne suka raka hjy tana jin su tayi tafiyar ta sune basusan Allah ba amma ita tana da imani kuma tasan Allah koda ace yaron nan shege ne ai bai cancanci ayi masa haka ba amma dubi yadda mutanen nan suka wulaƙanta ta ɗan jaririn da bai ji ba bai gani ba, ta duba fuskar ɗan jaririn da tayi ja jajir saboda tsabar dukan da rana tayi masa
"Allah ya raya min kai ka zama inuwa ga waɗanda suka wulaƙanta ka randa aka haife ka" ta faɗa tana goge ƴar ƙwallar da take fito mata saboda tausayin sa
[7:45PM, 12/7/2017] ‪+234 806 803 7117‬: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*DANGIN SA*
🕊🕊🕊🕊🕊
🥀🥀



By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu)

🎁 *nasibi writers association*🎁
*we shine with the smile of our readers so keep smiling* ☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺☺



page :32🌹


haka hjy ta ci gaba kula da ɗan jaririn wanda ranar suna ta sama masa sunan ɗan autan ta daya rasu wato Aliyu, har gidan iya taje ta kaimata shi tare da faɗa mata sunan da ta sa masa, amma iyar sai ta bita da baƙaƙen maganganu, haka ta taso ta bar gidan zuciyarta duk ba daɗi



satin aliyu uku da haihuwa buhari ya dawo, yai takaici tare da baƙin cikin abinya samu abokin sa, yai kuka kamar ba gobe, sannan ya tausaya wa aliyun ganin irin halin daya shiga tun randa zai zo duniya


har gidan iyar ya shiga don yayi mata bayanin yadda abin yake amma iyar ta toshe kunne ta, ta rufe idon ta ta wanke shi soso da sabulu tai masa tas, ba shiri ya bar gidan ,ko da hjy taga yanayin da ya dawo tasan cewar bai samu yadda yake so ba don haka sai tayi shiru



ko da kayan su sani su ka zo buhari sai daya kwashe duk wani kayan da ba na sanin bane sannan ya kaiwa iyar, amma iyar si ta zo tace wai sai dai abata kayan da buhari ya zo da su gabaɗaya, duk hjy ta nuna mata waɗanda suka ɗauka, kayan jarirai ne kawai, sai hotunan sanin da salmar waɗan da suka ɗauka tare don a ajiye wa yaron ko da nan gaba zai tashi sai ya ga iyayen sa



Ganin irin kayan jariran da suke wajen ba ƙanana bane ga uban yawa ya sa iyar nan fa ta hau bala'i ai ɗan ta ne ya siya kuma basu da gadon don haka sai an bata, buhari ne ya rufe ido yai mata tas hjy bata tanka masa ba don ita ma iyar ta kaita bango


me zatayi da kayan jarirai ba mamaki so take yi ta karɓa ta siyar, hatta kayan salmar an ba iyar amma wai kayan da za a sawa ɗan jaririn shine tazo tana tada jijiyoyin wuya sai an bata, ran hjy ya ɓaci sosai, sai ta ƙyale buhari yai maganin ta, da iyar taga baza ta samu ba sai ta haƙura ta fice tana Allah ya isa wai sun ci haram




haka hjy ta ci gaba da kula da ɗan marayan ɗan ta wanda buhari yai rawar gani sosai wajen tallafawa yaron har ragon sun sai da ya siyo aka yanka masa, duk da dai ragowar ƴaƴan hjyr musammam ma matan basu so hjyr ta ɗauki aliyu ba amma babu yadda suka iya tun da hjyr ta dage





aliyu ya taso da kuzarin sa idan ka ganshi, sai ka rantse nonon uwarsa yake sha yai shar da shi ga kyau kullum ƙara fitowa yake kamar su ɗaya da mahaifiyar sa, kamar tayi kaki ta tofar, wannan abun ne yake ƙara tunzura iyar take cewa yaron ya gado maitar uwar sa


aliyu yana shekara ɗaya da rabi, baba wato buhari kenan yai aure ya auro mama halima daga bauchi, Allah ya haɗa shi da mace ta gari, tana taimakawa hjy kula da aliyu sosai, ta so ɗan sosai da sosai, bata daɗe ba ta samu ciki, ko da lkcn haihuwa tayi Allah ya sauke ta lfy ta haifi ɗan ta namiji wanda yaci sunan bbn buhari wato ahmad amma ance masa tijjani


Rayuwa me daɗi suke ciki da buhari da iyalen sa babu abinda yake rabawa tsakanin aliyu da tijjanin komai ɗaya yake mu babu bambanci wannan abun yana farantawa hjy rai sosai don duk wanda ya kula da ɗan wani Allah zai kular masa da nasa


lkcn da tijjani ya isa yaye sai hjy ta haɗa su da aliyu ta riƙe ita kuma haleema a lkcn tana laulayin cikin ta na biyu don haka sai kawai ta ji da kanta, ko da lkcn haihuwa yayi sai halima ta roƙi alfarma awajen baba buhari na taje bauchi ta haihu be musa ba amma yace mata bazata tafi da su aliyu ba, ba haka ta so ba amma ba yadda ta iya


ranar wata jumma'a suka kama hanyar bauchi tare da buharin don ya kaita, tafiyar da badu kuma dawowa ba, don kuwa a hanya suka haɗu da haɗarin da yayi sakamakon rasa rayuwar su



sai da suka kwana biyar sannan hjy ta samu lbr ba shiri ta kama hanyar bauchin hankali a tashe, ta je ta tarar da wannan tashin hankalin, tun ran da suka rasu aka so faɗa mata amma kasancewar ba ɗan aike ya sa bata ji da wuri ba



haka hjy ta ci gaba da kula da ƴen marayun ƴaƴan ta har guda biyu, gwanda tj shi yakan samu taimako daga ɓangaren mmn sa ko ƴen uwan uban sa, shi kuwa aliyu sai abinda hjy ta samu tayi masa


rayuwa taci gaba da tafiya, Hjy tana kula da ƴen marayin ƴaƴan ta, don ta samu rufun asirin ta sai ta fara sai da alala da manja don kawai ta smu ɗan abun da zasu dinga kau da matsalolin yau da kullum


tj da aliyu suka taso tare tun suna ƙanana suke kiran junan su da ɗan uwa, da wuya kaji sun ambaci sunayen su, shaƙuwa ce aosai tsakanin su, baka taɓa jin tsakanin su ko hjy haka take ganin su ta bar su


aliyu ya taso mara son magana, in kaga hirar sa da dariya to ka tabbatar da hjyr sa ce ko kuma ɗan uwan sa, wannan dalilin ne yasa baya shiga mutane sosai babu

17 / 33