YAR BANGAR SIYASA BOOK COMPLETE By Binta Umar Abbale .txt

Author :  Binta Umar Abbale Category :  Romantic Books

Chapter   15 / 57

42K to 45K   out of 169.7K words

ne." Yace."Alkubus."? Eh tafada tana murmushi....Yace."Ai ko d'awisu ta bani sai naci ko da cikina zai fashe." Duka suka kwashe masa da dariya Khalifa yace." Ai na sani ko ka koshi sai kaci wannan abu ni ban san me kake ji a cikinsa ba fulawa kayan basir." Mikewa yayi yana fad'in"Ballanta na ma ban koshi ba dan har yanzu 'bacin rai ya hanani cin wani abincin kirki." Sai da ya fadi maganar kuma ya dawo yana da ya sani ganin dukaninsu sun sha jinin jikinsu.....To dai babu wanda ya sake tado da maganar suka zauna a danning Hasfa ta zubawa kowa nashi....Ahamdu ya riga kowa cinyewa Ya sake zuba wani da kanshi Hasfa sai tsokanarsa take da fadin"Allah yasa santi yasa ya manta hularsa.


Sai bayan sun kammala cin abincin ne ya kalli Hafsa a nutse yace."Wane guri ake miki d'inkunanki."? Ta kalli Khalifa dake goge bakinsa da tissue! Khalifa yace."Kana so ayi wa amarya kenan."? Ina so dai in siya mata d'inkakku a gurin nasan ba za'a rasa ba.' Khalifa yace." Bari nayi wanka nazo muje Yakasai Gidan Murtala." Yace."Kayi da sauri yamma tayi." Khalifa ya mike ya nufi daki Hafsa tabi bayansa domin hada masa ruwan wanka.....Ahamdu da Zeey suka shiga hira abunda ya shafi harkokin Siyasa da yanda talakawa me faman shan wuya a wannan gomnantin.




Khalifa ne yake draving shi kuma yana zaune a gefansa suna hira Khalifa yace."Yanayin yanda ka shigo dazu ya sanya hankalina ya tashi to amma ganin ka sake kana hira dasu Hafsa yasa hankalina ya kwanta da har nayi tunanin ko kai da mutanan ne."


Tsaki yaja Yace.'' Khalifa nayi abu yazo yana damuna kwata kwata yanzu na dawo ina dana sani da auran wannan yarinyar da nayi tsakanin jiya da yau ta zame min masifa da kyar nayi bacci n dare da sassafe muka tashi da masifa abincin kirki ta hanani naci.....Babban abunda ya 'bata min rai da ita shine na bata waya ta ta kira gidansu, ta kira min wani shege wai ni zata rainawa hankali naji muryar namiji take cewa dani kanwarta ce a take na sumar da ita kasan dai halina in raina ya 'baci."!


Khalifa yace."Subahanallahi! gaskiya Wasila bata kyauta ba! Magana da wani namiji bayan tana da auren wani a kanta......"Za tayi abinda yafi haka ma tunda jahila ce shiyasa na tsaurara matakan tsaro a kanta." Khalifa yace."Kaima matakin da ka dauka yayi tsauri gaskiya ya kamata ka zaunar da ita ka fada mata yanda al'amura suka kasance a tsakaninku nasan halinka da isa da jin kai! Dole ta shiga rudani da tashin hankali tunda katsaham! taji labarin auran kome zata iya yi a wannan lokacin."
"Khalifa yarinyar fa babu irin rarrashin da banyi mata ba ta'kiji saboda tsabar rashin mutunci dazu ni tayiwa Allah ya isa."! Khalifa yace."A kan me? Shiru yayi nauyin fada masa abunda yasa yake....Yace." Dole ne fa kayi hakuri da duk abunda za tayi maka gaskiyar magana kenan kuma kai kanka kasan duk yawancin abokananta maza ne abokan hurd'arta do ka fuskanci wannan matsalar."


"Khalifa kasan Allah kasan Annabi Ba zan lamunci wannan iskanci ba, Zan iya raunatata nayi mata illah mai muni mutukar naga da aurena a kanta tana mu'amula da wani namijin a waje, shine dalilin da ya sanya ma duka na kwace wayoyinta na cire sim car din ciki na karairaya su....Domin nasan tilas mutsiyatan nan ba zasu rabu da ita ba tunda sun san tana musu amfani, Sam kar kayi tunanin ko sonta nakeyi kawai ina kishin aure na ne banda haka babu abunda ya shafeni da duk wata rayuwa da zata jefa kanta a ciki.''


Khalifa yace." Kai ma kuma kayi gaskiya nan, Amma dai duk da haka ina mai baka shawarar karka tsawwala mata da yawa ka tausaya mata." Yace."Idan ta tausayawa kanta shikkenan idan bata tausayawa kanta ba ita ta jiyo."




Sosai ya sissiya mata kayan sawa masu tsada da dinki irin na 'yan burni shaddodi da lesuna sunfi yawa a cikin kayan kwata kwata atamfa hudu ce sai material uku sai dakakkun shaddodi da lesuna wanda aka zuba musu dinkuna masu kyau....Manya manyan ledoji hudu aka cika da kayan....Yaran dake aiki a shagon suka kai kayan mota Ahamdu ya fito da kudi ya biyasu suka fito daga gurin......Sai da ya koma gidan Khalifa ya dauki motarshi kana sukayi sallama da juna ya wuce gida.




Su Uwani da Rashi Da Camas! har magariba suna bakin gate din gidan Ahamdu kamar wasu Mayu sai naci sukewa masu gadi su bude musu sun'ki Daga karshe ma da suka takura musu bulala suka fito da ita sukace idan basu bar gurun ba sai sun zanesu, babu shiri suka bar gurun ransu idan yayi dubu ya 'baci!




Tun bayan futarsa a dakin take kwance a gurun tana tsiyayar da hawaye sai wata iriyar makyayata takeyi tana zabura sanyi sai ratsa jikinta ya keyi 'kashushuwan jikinta tana jinsu tamkar ana kwankwasa su da duste takure jikinta tayi guri guda jikinta sai d'ari yake yi yana mazari!!! Kafin kice kwabo ta soma ficewa daga hayyacinta.










Littafin na kudi ne......!
Kika futar min da book Ke da Allah! Kika karanta baki biya ba kema Ke da Allah! Whasap numbar
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
[07/08, 11:49 pm] +234 803 238 4602: 'Yr Bngr Sys
*26*
Yana tura kofar dakin ya ganta a kwance inda iya ajiyeta tun safe zuwa wannan lokacin ta riga ta gama fucewa daga hayyacinta domin idanunta sun juye sunyi fari tas ya tsun hannuwanta duk sun tankware sun tsaya cak! babu abinda yake aiki a jikinta a lokacin sai saman idonta dake dan harbawa kadan kadan Numfashi kuwa da kar take jawo shi yana kufcewa.....Da mugun sauri ya dire ledojin dake hannunsa ya nufi inda take, hannu yasa ya tattaro ta jikinsa yana tatta'ba ta, Yayi gaggawar cusa hannunsa cikin rigarta wani mugun zafi yaji a jikinta ya cire hannunsa sauri ya kinkimeta ta mike sambal tamkar Matacciya kan bed ya kwantar da ita, juyawa yayi da azama! sai kuma ya dawo kanta ya tsaya duk ya rude kansa ya juye ya rasa ma wane taimako zai mata....da alama daf take da shekawa barxahu ganin yanda take jin jiki da jawo nufashi da kyar! A gaggauce ya nufi toilet dinshi ya ciko karamar roba da ruwa ya dauki karamin towel ya tsoma a cikin ruwan......Yana zuwa ya cire rigarshi ya janyota jikinsa ya zare mata jallabiyar jikinta, tayi tik da ita tamkar yanda uwarta ta haife, yarda ya kalli sassan jikinta ba dalili baya so wani abu ya darsu a zuciyarsa taimako zaiyi ba wani abu....manne ta yayi a jikinsa suka sauko kasan kafet, ya ware kafafunsa ya sanyata a tsakiyar shi, Ruwan ya shiga tsanowa da towel din yana goga mata a jikinta sa'ko da loko ko ina yake shafa mata yanayi yana korar shaidan tare da kau da kansa daga barin kallon muradan zuciyarsa, Ya jima yana matsa mata ruwa a jikinta ko gezau ba tayi ba, a lokacin yaji wata iriyar nadama ta kamashi yana tsoron kar yarinyar mutane ta mutu a hannunsa, Kwantar da ita yayi ya mike da sauri yaje ya dauko wayarshi.....Kai tsaye numbar dector din sa ya kira yace maza yazo gidanshi akwai mara lafiya Emagency.....Ya dawo inda take yana kallon saman idonta dake motsawa, tsuganawa yayi ya sanya hannu ya dan ta'ba gurin! Yaji ta sauke wata iriyar ajiyar zuciya!! Da sauri ya cire hannunsa ya rike tafin hannunta sai yaji tana motsawa, ya damke hannun cikin nasa yana kiran sunanta a hankali........Hawaye sirara yaga suna zubowa daga idanunta gasu a rufe....Hamdala yayi ga Allah tabbas tunda yaga hawaye na fita daga idanunta ta dawo....Ya ciccibeta ya dora kan bed ya zauna kusa da ita hannunsa na rike da nata ya tsurawa fuskarta ido.......So yake kawai ta bude ido amma babu hali tsabar ciwon da kanta ke mata ya sanya idanunta sunyi nauyi sam ta kasa budewa jijiyon kanta sun tashi rad'a-rada hatta saman idanunta sai da jijiyo suka bayyana......Karaf! idanunsa suka sauke kan tsayayyun nonowanta da suke kallon rufin dakin....Yayi axamar dauke kansa yana sauke wata gawurtacciyar ajiyar zuciya, ji yayi gabanshi na wani irin zillo! yana so ya sake kallonsu yana jin tsoron abunda ka iya zuwa ya dawo, sai ya mike hannunsa ba tare da kalleta ba ya janyo bargo ya rufe mata jikinta still hannunsa na makale da nashi.


Jin saukar bargo a jikinta ya sanya tayi wata iriyar zabura!! Idanunta ta bude suka sauka a kanshi! tayi saurin mayar da idanunta ta rufe tana jin wata iriyar tsanarsa cikin ranta da tana da yanda zatayi a kansa da sai tayi ta kassara shi bashi da imani bashi da tausayi nema yake yaga bayanta a duniya bata da babban makiyi da ya wuce shi.......Jin d'umin hannunaa cikin nata ya sanya ta tattaro ragowar karfin da take dashi ta fizge hannunta.....Ya dan kalleta, ta mayar da idanunta ta rufe hawaye na sake zuba....Mikewa yayi ya fita daga dakin ba....Yana fita dector Nasir ya shigo, suka gaisa kana yace dashi yana zuwa,Dakin ya koma tana kwance amma ta sake takure jikinta....."Tashi ki dan sa riga Dr zai shigo ya dubaki." Cikin taushin murya yayi maganar. Tana jinsa tayi masa shiru ya sake maimaita maganarsa nan ma kamar da dutse yake magana, bai sake cewa Uffan ba ya nufi inda ledojin kayanta suke ya dauko wata dakarkariyar shadda wacce akayi wa dingin doguwar riga ya nufe ta da rigar a hannunshi.....Jin tayi ya yaye bargon jikinta, tayi saurin bude idonta, Zabura tayi da mugun sauri! ta fuzge bargon hannunsa tana kare jikinta dashi wata lafiyayyar harara take! watsa masa, bai damu ba ya mika mata rigar a sar'ke yace."Karbi kisa a jikinki."! Kin 'karba tayi tana ji tamkar taje ta shakeshi tabbas ita dai tasan akwai kayan a jikinta jallabiyarsa da ya bata to ya akayi kuma ko dai shine ya cire mata to waye kuwa in bashi ba, sai ta shiga motsa kafafunta taji wai ko yayi mata wani abun, ba taji wani sauyi ba a jikinta ta sauke ajiyar zuciya ta koma ta kwanta tabarshi da tsaye da riga a hannu.....Hawa bed din yayi ya janye bargon tayi azamar mikewa zaune kallon juna sukayi ita dashi Yace."Bana son taurin kai kar'bi suttura kisa baki da lafiya likita zai shigo ya duba ki." Fuzgar rigar tayi daga hannunsa ba da son ranta sai dai kawai dan bata son katsalandan din da yake mata sai wani bude mata jiki yake....A gabanshi ta zura rigar tana gyarawa yana taimaka mata, mikewa yayi yaje ya dauki ledar pant cikin kayan da ya siyo mata ya farke ya ciri guda ya mika mata! Karba tayi tana kauda kai, Yace."Yi azama kisa Yana tsaye yana jiranki." Kin sawa tayi saboda nauyi yayi tsaye a kanta saboda rashin kwarin jiki sai ta koma ta kwanta tana takure jikinta.


Yarinyar nan na so ta jaza masa matsala pant din dake hannunta ya karba ya runkufa kanta rigar jikinta ya soma tattarewa yana daga kafafunta da pant din a hannunsa yana kici kicin zura mata, Lokacin ta dinga jin wani irin hajijiya da rashin karfi a jikinta dalilin da ya sa ta kasa hanashi tana ji ya yaye rigar gabad'aya ya zura mata pant din sai gogar mata jiki yake mussaman duwawukanta ya matsa su da hannaye sa babu a dadi kafin ya sa mata pant din....Tabbas ba karya tayi ba Ahamdu sai da yayi ta maza ya iya sakin kafafunta dan a lokacin ji yake tamkar ya afka mata ji yake babu abinda yafi dadin ta'bawa a duniya kamar mazaunanta wani irin taushi da santsi ya dinga ji a fatar hannunsa yaji da hannuwansa zasu dawwama gurin mulmula gurun ba zai ta'ba gajiya ba, Ya jima zaune a gefanta yana saisaita kansa da tunaninsa gudun kar Dr ya ankara da wani abu, sannan ya mike ya fita.


Tare suka shiga dakin da Dr Nasir dake rike da jakarshi irin tasu ta likitoci.
Dr Ya tsaya a kanta da fad'in "Sannu Madam."! Daga masa kanta kurum tayi ba tare da ta bude idonta ba, Dr Yace."Madam ya kike jin yanayin jikin naki Yallabai yace zazzabi ne ke damunki."? Bude idonta tayi Kallon Farko da Dr din yayi mata ya gane cewar bata da ishashen ruwa a jiki kana kuma akwai alamun zazzabi mai zafi a tare dai ita.


Ya kalli Ahamdu dake tsaye yana kallonta " Yallabai Madam na bukatar ruwa leda uku yanzu kuma alamu sun nuna tana jin jiki kwarai da yunwa da kuma gajiya, Yanzu dai ko yaya ne tasa wani abu a cikinta sai na daura mata ruwa insha Allah zata samu relief. "


Ahamdu yace."Okey." Wayarshi ya kira Rabe (kuku) yace ya kawo abinci plate daya, Minti biyar Rabe Ya kwankwasa kofar dakin yayi azamar bude kofar ya karbi abincin....Dr Yace."Yallabai bari naje palo kafin ta gama cin abincin....."Okey." Abinda yace kenan Ya karasa bakin gadon hannunsa rike da plate din abincin.


"Tashi kici." Yafad'a babu alamun wasa a tare dashi.
Ta mike zaune hannunta na rawa ra karbi abincin ganinsa yasa jikinta har kyarma yake tsabar yunwa....Loma uku tayi amai ya dinga taso mata ta dai daure tana ci tana ya mutse fuska.....inaaa! da sauri ta jefar da plate din ta mike da sauri tana tangal tangal ta iske toilet ta dinga kakarin amai dan wanda taci sai da ta amayar dashi.


Bakin toilet din ya tsaya yana kallonta tana rike ciki saman goshinta duk ya tara zufa sai hawayen wahala take, Tausayi ta bashi ya shiga toilet din ya debi ruwa yana wanke mata baki da hannuwanta da kafafunta, ya kamo hannunta suka fito sai lauyewa take tana lanjarewa jiri na dibarta, zubewa tayi tsakiyar dakin....Ya dauketa cak ya kaita bed din ya ajiye....Gumi kawai take shar'bawa tana dafe kirjinta, sosai ta bashi tausayi da gani tana jin jiki kamar yanda Dr din ya fad'a....Plate din abincin ya dauka ya de'bo cikin cokali ya kai bakinta.


Kauda kanta tayi tana ya mutsa fuskarta kokari ma takeyi ta kwanta Yace."Yi kokari kici loma uku ko hud'u sai ki kwanta ko kin dai san yunwa ce ta janyo miki wannan aman." Shareshi tayi Ya sake magana tayi masa banxa, duk sai yaji rashin dadin hakan ya ajiye plate din ya fita.....Minti biyu suka shigo da Dr din yana fadin "Dama dole abinci ya'ki zama a cikinta saboda dad'ewar da tayi ba taci ba ta tara yunwa tayi mata yawa Yanzu bari nasa mata ruwa insha Allahu za taji kwarin jikinta idan tayi bacci ta tashi da kanta zata nemi abinci." Yace."Okey babu matsala." Dr Nasir ya soma hada ruwan shi kuma ya zauna kusa da ita yana me zura hannunsa cikin bargon yana kokarin fito da hannunta guda tana no'kewa had'e da fuzgewa ga idonta a rufe duk wasu maganganu da sukeyi tana jinsu......Rike hannun yayi da kyau duk kokarinta ta kasa kwacewa ya shiga matsa hannu yana nemo jijiya....Dr yayi saurin kama hannun inda ya gano jijiyar ya daura ruwan akai.....Ta danji zafi kadan ta dai daure har aka gama, ya mike hade da gyara mata bargon suka fita dashi da Dr din.....Lumshe idonta tayi bacci na fuzgarta tana tunanin Mahaifiyar ta da Kanwarta yanzu ko cikin wane hali suke tasan dai duk inda suke suna cikin damuwa da tashin hankali.










_*Akwai Wani sirri da zan fad'a muku wanda ba kowa ne yasan wannan sirrin ba, Idan kinyi kin gwada to karki manta da Binta๐Ÿ˜€๐Ÿค๐Ÿป Aha!! Kina fama da 'karanci ni'ima da bushewar gaba! Ko kuma idan mijin ki na saduwa dake kina jin zafi gurin na tsagewa yana miki zafi da rad'dadi a maimakon kiji dadi sai kuma a samu akasi shi oga na kwasar dadi ke kina cije baki na wahala, ni'ima itace tu'kahon duk wata 'ya mace komai kyanki da dirin ki idan baki da ni'ima kin zama hoto a gurin mai gida zakiyi ta fuskantar Matsaltsalo iri iri....Wannan dama ce ta samu a garemu a sau'ka'ke!!!!๐Ÿ™‹๐Ÿปโ€โ™€๏ธ*_






_*Matsala ta budewar Gaba na da ala'ko'ki dabab daban budewar gaba babban kalubale ne a gare ki 'yar uwa akwai matakan da zaki bi gurin ganin kin gyara matantakar ki duk domin kiyi martaba da mutunci a idon mijinki๐Ÿ™‹๐Ÿปโ€โ™€๏ธ*_








Littafin na kudi ne.....!
Kika futar min da book ke da Allah kika karanta baki biya ba kema ke da Allah! Whasap numbar
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
[07/08, 11:50 pm] +234 803 238 4602: 'Yr Bngr Sys
*27*
Uwani da Rashida ne zaune a palon gidan Wasila abin duniya ya taru yayi musu yawa, ga dai abubuwan more rayuwa da jin dadin amma kuma rashin Wasila a tare dasu ba karamin gi'bi yayiwa rayuwarsu ba, suna mutukar kaunarta mussaman mahaifiyarta Uwani, tabbas sai yanzu tayi tunanin irin had'arirrikan data jefa kanta duk dan suji dadi su samu walwala, Wannan al'amari da ya faru da Wasilar ba ko wane ya silar shi ba sai mai allo Saboda haka taci alwashin zuwa har can inda yake tayi masa wankin babban bargo, ta tabbatar da cewar Ahamdu kudi yaje yasa ya siyi Wasila a hannunsu su kuma sunga kudi suka yanke wannan hukuncin ba tare da saninta ba a matsayinta na mahaifiyar ta dan haka dole taje ta nemi hakkinta kuma ta ci musu mutunci iya son ranta.


Rashida tace"Gaskiya Uwani da zaki bi shawara ta da sai nace kiyi hakuri ki bar wannan maganar, mutumin fa da aunty Wasila ta aura babban mutum ne mai kudi wanda duniya tasan shi, kema in baki manta ba nasan ba zaki mance alkairinsa ba shine fa mutumin nan da ya taimake mu ranar da mukaje siyayya da daddare 'barayi suka biyo mu, ni a ganina ma kamar gata Kawu Malam yayiwa aunty Wasila da daura mata aure da mutumin wallahi ba tsaran auranta bane." Uwani tace"Koma dai menene ni ba zan yarda ba sai naje naji ba'asin abinda ya faru, a kan me zasu daurawa 'Yata aure ba tare da sanina ba.'' Rashida tace"To sai dai ki tafi ke d'aya ni bazan biki ba dan gaskiya ina jin kunyar hada ido da Kawu Malam." Tace"To ai dama kin fi kaunarsa a kaina sam! bakya kishina Rashida to sai me! kije kiyi tayi shiyasa nake alfahari da Wasila saboda tana kishina da kaunar abinda nake so." Uwani ta dinga

15 / 57