YAR BANGAR SIYASA BOOK COMPLETE By Binta Umar Abbale .txt

Author :  Binta Umar Abbale Category :  Romantic Books

Chapter   36 / 57

105K to 108K   out of 169.7K words

ta dinga tunanin abubuwan da suka dinga faruwa a baya da irin kud'ad'en da 'yarta ta rike da samun nasarar auran Ahamdu tayi, Yanzu ne ta gane auran Ahamdu da 'yarta shine rufin asirinsu tasan da Wasilan na gidanshi har yanzu da tuni basu shiga wannan gararanbar ba.
Kuluwa ta shigo dakin hannunta rike da wata katuwar langa tana kallon Uwani tace"Naga kamar kema kina cikin alhini da damuwa to Allah yasa dai ba abin kunya kukayi a can ba kuka gudo nan dan naga alamun ciki a tattare da waccan 'yar taki."


Uwani ta kalleta ranta ya 'baci da maganarta amma saboda sanin halinta yasa tace"Eh kuluwa ki daina shakka ko kokwanto Wasila na da ciki amma kuma da Ubanshi."


Kuluwa ta ta'be bakinta tana fad'in "To yanzu naji zance Allah ya rabasu lafiya sai ki kira su kuci abinci gashinan babu yawa dai aci da hakuri tunda ban san da zuwanku ba." Uwani tace"To mungode." Kuluwa ta fita daga dakin, tana gyara daurin zaninta wanda yayi da'kal! da'kal da daud'a!


Uwani ta le'ko tana kiransu Wasila dake zaune jikin bishiyar darbejiya dake gidan.........Rashida da kyar ta lalla'bata suka koma dakin....suna shiga ta fito da sauri tana fad'in "Rashida ba zan iya ba wallahi mutuwa zanyi zuciyata tashi takeyi." Karaf a kunnan Kuluwa cikin fusata tace"Ke! buhun ubanki nace! Buhun ubanki kaji min shegiyar yarinya ciki haukane da zaki zo min gida kina min iskanci! har ki dinga cewa zuciyarki tashi takeyi to bari malam ya shigo wallahi kinji na rantse ba zaki zauna min a gida ni ba'a kawo min iskanci ehe! dama ai baku bane tilashin mu ita Uwanin itace tilas dinmu dan haka sai ku koma inda kuka fito abin arziki baya zama na tsiya." Takarashe maganar tana kumfar baki kai daka ganinta a fusace take! Uwani ta fito daga daki tana bata hakuri saboda tasan halin ta zata iya cewa su Wasilan baza su zauna a gidan ba kamar yanda ta fad'a, Hakuri take bata tana karyar dai muryarta sai rawa take! Kuluwa ta cigaba da aikinta tana sababi! da zagin Wasila




Uwani ta dauko langar abinci ta dire a gabansu tana fad'in " Ku kiyaye da wannan matar idan kuna son zaman lafiya bana son abinda kikeyi Wasila kinga bamu da gatan da yafi nan, Kuluwa macace mara hakuri zata iya sa Kawu yace ku bar mishi gida kamar yanda ta fad'a saboda haka duk abinda zakiji na tashin zuciya ki dinga daurewa kina hakuri haka take muguwar kazama ce tun tana da kuruciyarta gashi har girmanta......Wasila bata iya magana ba rashida ce mai magana tace"Gaskiya Uwani gidan nan baiyi wallahi duba fa ki gani ko ina kazanta da kashin dabbobi dubi bandaki babu kofa sai buhu kiji warin masai dake tasowa har nan kawai mu zamu tafi Garko ke kiyi zamanki nan tunda kece tasu."


Uwani ta marairaice fuskarta muryarta na rawa tace"Rashida kin san yanda nake son ku kuwa ? bana so kuyi nesa dani shiyasa na'ki aure na 'kare rayuwata tare daku, ina 'kaunarku saboda nasan bani da kowa sama daku, Uwata ta mutu Ubana ya mutu mijina ya mutu sai ku kawai nake kallo naji dadi idan kuka tafi Garko kuka barni wace irin rayuwa kuke tunanin zanyi a cikin garin nan."!?


Tausayin mahaifiyar tasu ne ya kama su, sai suka hau goge hawaye, suna adduar Allah ya kawo musu dauki da gaggawa amma hak'ikanin gaskiya mahaifiyar tasu tasha wuyar rayuwa ta kuma yi wahala dasu bai kamata su guje mata ba,


Zama tayi kusa dasu tana bud'e langar abincin aikuwa sai wani irin towon dawa ba'ki'kikirin yayi musu sallama! towon sai shaining yake ga wata uwar miya kamar fitsarin jaka, sai wake guda guda a cikin miyar tana ta warin daddawa......A guje Wasila ta mike ta nufi bakin rariya ta dinga kakarin amai tana zubar da kwalla! Kuluwa tayi azamar fitowa daga kicin da ludayi a hannunta....Wannan karon Uwani da kanta taje ta rirrik'e 'yar tata tana mata sannu ita kuwa sai rike ciki take tana mur'kususu da kiran sunan Allah! Kuluwa ta dinga kallonsu bakin cikin duniya kamar ya kasheta 'Kwafa tayi ta koma kicin din! Yau ba gobe ba zasu bar mata gidanta dan bata ciki da iskanci da wulakanci......Kawu Madu ya shigo gidan yana sa'be babbar riga sai kawai ya gansu cirko cirko Uwani da Rashida kan Wasila dake durkushe tana kakari......Yace."A'a Uwani meke faruwa ne Me yasa me ta take amai haka."? Kafin Uwani tace wani abu Kuluwa tayi zuruf ta fito daga kicin fuskarta a murtuke tace" 'Kyankyamina takeyi shine take amai tunda suka shigo gidanan basu shiga dakina ba can bakin bishiya suka zauna saboda suna kyankyamina saboda haka yau ba gobe ba zasu bar min gidana dan wallahi ba zan dauki wannan iskancin ba." A take Kawu Madu ya sha kunnu yana kallonsu rai a bace yace."Ashe baku da tarbiya dama? matar tawa kuke 'kyankyami!? to shikkenan dama ai baku ne tilas dina ba Mahaifitarku ce saboda haka zaku bar min gidana tunda baku da mutunci." Uwani ta shiga share hawaye tana fad'in "Kawu ba haka bane wallahi yarinyar nan nada ciki mai laulayi yana bata wuya dama tun a mota take amai har yanzu ba wai suna 'kyankyamin Kuluwa bane."


Yace."Uwani."! ta amsa yace."Shin yaushe kikayi wa yarinyar ki aure babu labari gashi nace tana da ciki."! Kuluwa tace"Nifa malam ban yarda ba wallahi wannan yarinya cikin shege tayi shine suka kwaso jiki suka gudo nan sabida gudun abin kunya dan haka wallahi ba'a gidan nan ba idan kuma kace tilas sai sun zauna to ni zan fice na baku guri."


Hankalin Kawu Madu ya tashi, Yace."A'a ba za'ayi hakaba Kuluwa ai duk wannan magana ma bata taso ba, ke Uwani zo ki zauna kiyi min bayanin abinda ke faruwa."


Uwani ta bishi kan tabarma suka zauna tare Kuluwa ta 'karaso gurin hannunta rike da ludayi ta zauna kujera 'yar tsugo tana fad'in "Eh ai gwara muji bayanin komai domin mu samu kwanciyar hankali." Uwani ta share hawaye a hankali ta soma warwarewa masa abubuwan da suka faru da rayuwarta ita da 'yayanta komai bata rage masa ba sai da ta fad'a mishi......Kuluwa tace"Duniya kenan yanzu ke Uwani bakiji kunya ba, wato lokacin da kuka samu kudi kuka samu dad'in duniya baki tuna damu ba sai da wahala ta taso ki sannan zaki tuna damu ki kwaso jiki ra'be ra'be da 'yaya kizo ki d'ora mana nauyi to ba zata ta sa'bu ba! Mu ba zamu dauki nauyin ki kuma mu d'auki nauyin 'yayanko ba, Dan haka gobe gobe yaran nan zasu bar gidanan suje can dangin mahaifinsu tunda suna raye, kema abinda yasa ba zamu kore ki ba saboda mun san ko kinje can gidan Kawunki ba zai kar'be ki ba saboda haka ke kad'ai zamu ri'ke saboda kece tamu."
Kawu Madu yace."Kwarai kuwa Kuluwa wannan magana taki gaskiya ce, Yaran nan baxa su zauna mana a gida ba sabida bamu da hakki a kansu dan haka kamar yanda kika fada hakane kwana guda zasuyi su bar mana gida suje can cibiyarsu.........Uwani ta dinga kuka tana fad'in "Haba Kawu ku duba al'amarin fa kada kuyi min haka bani da kowa sai 'yayana bani da uwa da uba bani da miji sai 'yayana su nake gani naji sanyi a raina." Kuluwa tace"To ai tunda hukuncin da muka yanke bai miki ba to sai ki bi 'yayan naki haba! wannan 'kulafucin son 'yaya dame yayi kama.'' Ta mike tana jan tsaki ta shiga dakinta.....Kawu Madu ma ya mike yana fad'in "Na fad'a miki Uwani na yanke hukunci Kuluwa ta yanke hukunci saboda haka shawara ta rage gareki." Ya buge babbar rigarsa ya 'kara gaba.


Wasila da Rashida kam! basu ciwo ba dalili dama sunfi son su tafi can garkon shiyasa sukaji dadin hukuncin da Kawu madu ya yanke a kansu amma basu nunawa mahaifiyar tasu ba, sai suka shiga kwantar mata da hankali da fad'in ko sun tafi insha Allahu zasu dinga zuwa a kai akai suna dubata.....Uwani dai jinsu kawai takeyi abin duniya ya taru yayi mata yawa bata ta'ba nadamar rayuwa ba irin yau.


Kuluwa ta dinga shige da fice a tsakar gidan tana sakin 'ba'kaken maganganu wanda ya sanya jikin Uwani yi sanyi taji a zuciyarta gwara kawai su Wasila su bar gidan dan ba zata iya jurar rashin mutuncin kulawa tana aibata mata yara da kiransu karuwai watarana tana ganin zata iya mayar mata da martani kan maganar da takeyi, ta dinga jin wani irin d'aci! da bakin ciki a raina ashe haka abun yake da ciwo a duk sanda aka danganta d'anka da wannan suna (karuwai) gaskiya ta gode Allah da ya bata 'yaya masu hankali da hange nesa tasan da bada hakan ba da tuni sunanan da kuluwa ke kiransu dashi ya tabbata tunda ita da kanta ta dinga turasu karuwancin, tagode Allah da yasa wannan cikin dake jikin Wasila ta sameshi ta hanyar halak ba haram ba.




Kuluwa na ganin irin tsarabar da suka kawo sai ta hau washe bakinta ta dauki turmin atamfofi irin na leda guda biyu tace wannan ni zan d'inka in sa a jikina wannan yadin kuma na malam ne, sauran kuma Iya mai waina da Tabawa su kasafta a tsakaninsu." Su dai kallonta kawai sukeyi duk tabi ta kwashe kayan ta shige dakinta dasu sai murna takeyi ko Kawun ma bata nunawa ba.


Sai dare suka samu suka sanya abinci a cikinsu shima abincin Inna Tabawa ce ta kawo musu cikin katuwar Samira shinkfa da wake ne da manya da wani uban yaji da yaji gishiri da citta! haka suka cuccusa dan gwarashi kan narkeken towon dawan da Kuluwa ta kawo musu, Wasila dai kad'an taci tasha maganinta ta nemi gefenan tabarma ta kwanta tana mai da nuffashin wahala.............Duhu sosai gidan babu wadatacciyar fitala sauro da kwari ka sukayi sallama! Wasila ta gigice ta dinga soshe soshe kukan sauro duk ya cika mata kunne! Uwani tace "Ku tashi mu koma daki mu kwanta kunga mutanan gidan sun shige sai mu kadai a tsakar gida ga sauro." Rashida tace "Yanzu cikin wannan kazantar zamu mu kwanta ga yara nasan suna fitsarin kwance." Uwani tace"To ya zakuyi ai da zama cikin sauron nan gwara cikin rumfar." Wasila tace"Uwani ku shiga ku ku barni anan Rashida ki dauko min zanin atamfa cikin kayanmu in rufe jikina." Uwani tace"Akwai fa damuwa kwanciyar ki anan." Tagoge kwallah tace"Uwani nan yafi min kan in shiga dakin nan inzo ina kakarin amai da daddare d'an abincin da naci ya dawo, kuma wannan matar tazo tana miki masifa."


A sanyaye Uwani tace"Shikkenan ai." Ta mike a hankali ta shiga dakin rashida tabi bayanta......Nan su kaga yara birjik a rumfar ko wanne ya wargaje kafafunshi wasu sun soma sakin fitsari abinsu sai barci suke.....Uwani ta ra'ba can wata kusurwa ta karkad'e wani buhu ta shimfida ita kuma rashida ta nufi dakin Kuluwa dan jakkunan kayan nasu na cikin dakin........Nan ta tarar da Kuluwa ta bude musu kaya sai bunkice takeyi musu, tana ganin rashida sai ta diriri ce ta hau ya'ke...."Am...dama ai nace bari na gyara muku kayan naku in adana muku su guru guda." abinda tace kenan tana sosa kanta....Rashida bata ce komai ta dauki zannuwa uku na atamfa ta fito daga dakin....Ita kuluwa tana ganin rashida ta fita daga dakin sai ta cigaba da bincika kayan ta dauko manya manyan shaddodin Wasila masu uban stone work ta d'aga 'kasan katifarta ta sanya ta mai da katifar......Da sauri ta gyara jakkunan kayan ta fito daga dakin tana zare ido.


Wasila kudindine jikinta tayi. ita kadai kwal a katon tsakar gidan ko tsoro bataji gari yayi shiru sai kukan tsintsaye kawai ke tashi.......... Cikin ikon Allah bacci mai nauyi ya dauketa ta dalilin magungunan da takesha


Fitowar Kawu Madu daga dakinsa ne ya tayar da ita Sai taji ana kiran sallah da alama asuba tayi, Kawu Madu ya kalleta yana mamaki yace." Ke anan kika kwanta." Sunkuyar da kanta tayi kawai sai ya girgiza kanshi ya nufi bandaki da buta a hannunsa........Yana fitowa ya daura alwala ya nufi masalaci,
Kasa shiga bandakin tayi sai kawai tayi gaggwar tsugunawa a bakin rariyar tayi fitsarinta ta kwara ruwa, kana ta matsa gefe guda ta daura alwala ta bar gurin.


Shimfidar data kwanta ta dauke ta cire dankwalin kanta ta gyara hijab dinta ta tada sallah......Uwani da rashida suka fito a tare suma alwalar suka daura nan tsakar gidan sukayi sallah domin dai cikin rumfar babu guri bayan haka kuma ko ina kasa 'kafarka fitsari ne.






Suna zaune a tsakar gidan gari yayi haske Kuluwa ta fito tayi alwala ta goge bakinta da gawayi kana ta shiga kichin ta kunna wuta ta dora ruwan kunu sannan ta nufi daki domin yin sallah.


ၥYaran dake dakin suka soma fitowa su kusan bakwai wasu jikinsu da fitsari wasu babu ba tare da sunyi alwala ba suka soma wasa a tsakar gidan wasu kuma tuni sun fice waje da abubuwan wasan su......Su Wasila suka dinga mamakin wannan rayuwa....Nan rashida take shaida musu abinda taga kuluwa nayi musu da kayansu....Fitowarta yasa tayi saurin yin shiru to itama Kuluwar a kunyance take dan haka sai tayi saurin fadawa kichin tana sosa kai! Wasila abin dariya ya bata sai ta shiga girgiza kai tana fad'in ''Ni dariya ma take bani wallahi." Rashida tayi dariya kasa kasa tana kallon kicin din.


Wani tsalan kunu ta kawo musu cikin kwanon sha da kufuna guda uku sai 'kullin sikari akai....Uwani ta gaisheta tanayi mata sannu suma suka gaisheta Ita kuwa ta kasa tsayawa a gurin kunyar hada ido da rashida take......Tana shiga kicin Wasila ta saka fuskarta cikin hijab taci dariyarta ta koshi, kai mara gaskiya dai ko a ruwa gumi yake.


Fitowa tayi daga kicin din da katon farantin silba da narkeken d'umamen towo an yanyanka shi sai miya tsululu towon sai iyo yake cikin miyar....Ta kalli rashida tana fad'in 'kawata ga d'umame nan idan kunsha kunun sai kuci kwaji dad'in tafiya da karfinku." Rashida tace"Mungode Kuluwa." Da sauri ta bar gurin tana kwalawa yaranta kira wai suzo su dauki kununsu da duk ta zuba musu a kufuna 'kudaje sai bin bakin kufunan sukeyi.....aikuwa da d'ai- da d'ai yaran suka dinga shigowa suna daukar kufonan kunun suna sha ba tare da sun wanke bakinsu ba.


Kawu Madu ne ya shigo da sauri yana fad'in "Ina Wasila da Rashida." Sukace gamu Kawu Yace." To maza ku fito ga motar abokina ya kawo ice yanzu zai fita cikin gari sai yaje ku a tasha ku shiga mota." Suka mike da sauri Rashida ta shiga dakin domin dauko musu jakar kayansu, dama tasu daya ce ta uwani daya.


Uwani ta mike tana yakar zuciyarta hawaye ne yake so ya 'balle mata tana mayar dashi, suka je bakin kichin din da Kuluwa ke ciki tana zaune dirshan gabanta da karon bokintin da ta dama kunu tana katsewa gefanta kuma tukunyar miya ca bude ga ludayi a kasa....Uwani tace"Zasu tafi." Sai ta hau washe baki tana fadin"Bari na taso inyi rakiya ni kuwa me zan baku. 'Yayan nan."? Fitowa tay ta shiga dakinta da sauri ta dauko wata yar takarda fara ta mikawa rashida tana fad'in 'Kawata ga yariruka kwa sanya ku gaishe da kawunan naku." Rashida ta karba tana godiya tabi bayan Wasila da Uwani da suka riga sukayi gaba.










Littafin na kudi ne.....!
Kika futar min da book keda Allah kika karanta baki biya ba kema keda Allah Whasap numbar
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
*BINTA UMAR ABBALE*alliya:
'Yr Bngr Sys
*59*
Tun a mota yake jin alamun zazzabi zazzabi a jikinsa yasan kuma ba komai ne ya jawo mishi faruwar hakan ba sai alhini da damuwar da yake ciki idanunsa sun kad'a sunyi jawur! jijiyar kanshi ma ta tashi, yanda le'bunanshi suke a bushe haka ma'kogwaron shi yake dan rabonshi da ruwa ko abinci tun jiya da daddare da yasha coffee kafin ya kwanta, sam ya ma manta da wani abinci saboda tsananin damuwar da yake ciki....Yana kallon khalifa na tu'ki yana kur'bar lemo amma shi sha'awa ma baya bashi bakinsa duk ya bushe yana jin wani irin abu ya tokare masa a ma'kogwaronsa.
Ganin tashin hankali murarar a tartare da abokin nasa yasa ya d'an kalleshi bayan yayi parking din motar cikin gidanshi, Yace."Kayi hakuri abinda zan iya cewa da kai kenan! ka cigaba da addua kawai kan Allah ya tsare maka cikinka da ita kanta yarinyar wannan damuwar duk ba ita mafita ba, tunda dai Allah ya raba ganawa sai ka bar mishi ikonshi, ni munyi magana da ita a jiya ta kuma shaida min cewar mutukar ta haihu to zata kawo ma'ka d'anka har inda kake." Saurin kallonsa yayi yace."Okey ashe da sa hannunka ta gudu kenan." ? Khalifa yay saurin girgiza kanshi yana fad'in" No ka fahimce ni mana! Jiya nake fad'a mata cewa dole sai na sanar maka da maganar cikin ta nuna bata so nace mata ai tilas ka sai ka sani shine tace ko anfad'a maka ko ba a fad'a maka ba in ta haihu zata kawo maka d'anka kaji dalilin da ya sanya nayi maka wannan maganar amma wai maganar da sanya hannuna a cikin guduwarsu bata taso ba."


Girgixa kanshi ya shiga yi yace."Ban san a ina zanga 'kawarta ba mybe a samu wani labari a gurinta." Khalifa yace."Eh to ai kuma inda za'a sameta ne aiki." Yace."Zan duba wayarta baza'a rasa numbar ta ba." Khalifa yace."Yawwa hakan yayi kyau Allah yasa a dace yanzu dai ka kwantar da hankalinka mu shiga ciki kaci abinci ka huta tukkuna insha Allahu komai zaizo da sauki."


Girgiza kai kawai yay yace."Khalifa hankalina ba zai ta'ba kwanciya ba sai naga yarinyar nan, na 'kwallafa raina kan cikin jikinta burina kawai in ganta kuma in tabbatar lafiyar abinda ke cikinta." Khalifa yace." Shine ai nace damuwa da tashin hankali bashi ne mafita ba addua itace mafita kawai ka kwntar da hankalinka ka cigaba da addua.''
Murmushi mai ciwo yay khalifa bai san yanda yake ji a zuciyarsa ba shiyasa yake cewa ya kwantar da hankalinsa a maganar kwanciyar hankali ta 'kare a gurinsa yanzu mutukar ba ganin yarinyar nan yayi ba. A
Tare suka fito daga motar tamkar wanda 'kwai ya fashe musu a ciki suka nufi cikin gidan. ga

36 / 57