YAR BANGAR SIYASA BOOK COMPLETE By Binta Umar Abbale .txt

Author :  Binta Umar Abbale Category :  Romantic Books

Chapter   56 / 57

165K to 168K   out of 169.7K words

ta karashe maganar, itama Wasila taji zuciyarta na kokarin karyewa tuno mahaifinta da tayi sai dai kawai ta daure ta cigaba da yi masa adduar samun rahamar Allah a cikin zuciyarta.
Inna Hajara bata bar gidan Malam ba sai da ta tabbatar da Wasila ta shanye roman 'yan shillan nan sannan tayiwa Bitan Sallama ta tafi gidanta.
Koda malam ma ya dawo suka ke'be suna sake gaisawa da tambayar bayan rabuwa Wasila tace"Malam ji nake kamar nafi kowa murna da farin cikin da kasantuwar wannan abu kai da Uwani Allah Ubangiji ya sanya alkairi a ciki."
Mai allo ya dinga amsa cike da walwala da farin ciki, Yace."Hakan shine suttura da kuma mutumcin mahaifiyar taku."




****


Sai bayan goma da rabi ya shiga gida a gajiye sosai dan bayan sun bar garin Garko can 'karamar hukumar *Gaya* suka Wuce shi da Khalifa da jama'arsu, sai yamma lis suka dawo saboda yasan masu gidan basa nan yasa ya yada zango guest house dinshi Khalifa ya zauna yana d'eba masa kewa Sai da Hafsa taga dare yayi mijinta bai dawo ba ta kirashi a waya, sannan ne suka rabu kowanne ya tafi gidanshi


Yana sane ya'ki kiranta a waya sabida yana so yaga shin zata manta dashi ko a'a bini bini zai duba wayarshi babu text dinta babu kiran wayarta gashi sha biyu na dare har ta wuce........Allah sarki Wasila tana can network ya sakata a gaba tun bayan tafiyar Inna Hajara take ta kiran numbarshi tana 'kin shiga ko kuma data fara ringing sai ta katse har kuka tayi saboda bakin ciki kowa na kwance a daki cikin dare ta fito tsakar gida wai ko dakin ne babu network nan ma tayi tayi kiran baya tafiya, sai ta koma daki ta kwanta lamo tamkar mara lafiya bini bini ta duba wayarta ko zataga test dinshi shuru duk ta rasa abinda ke mata dadi da kyar bacci ya dauketa.




To shima nashi 'bangaran hakane, da kyar bacci ya daukeshi wanda tun yana saka ran ganin test dinta ya cire ya rungume filo kamar wani maraya yana fizgo bacci da karfi, gabadaya gani yay dare yayi mishi tsayi, dan haka uku da rabi nayi ya tashi yaje ya dauro alwala ya hau dadduma yay nafila, kafin ta dauki cazbaha ya wuce masallaci.


Da safe da kyar ta karya duk takaici ya isheta, ga mutane sai shigowa sukeyi wai sunzo gaisheta sai kawai ta koma daki ta kwanta tace da Rashida duk wanda yazo tace musu bacci takeyi.
Haka kuwa Rashida ta dinga sallamarsu, da cewar bacci take wasu masu naci zama sukeyi wai sai ta tashi sun gaisa da ita Wasu kuwa sai suce bari su tafi sa dawo da yamma.
Wasila na ciki tana ta famar kiran wayar tashi wannan karon tana shiga sai dai kuma bai daga ba, nan ma zuciyarta ta sake hasala ta goge hawaye tana mikewa zaune......Sake kiran wayar tayi a karo mara adadi dai-dai lokacin da ya fito daga toilet da alama wanka yay dan ga jikinsa nan duk ruwa, da sauri ya karasa inda wayar take ya dauka, ajiyar zuciya ya sauke ya zauna gefan bed kana ya daga wayar.
Kuka ta fashe dashi harda shashsheka, yaji duk jikinsa yay sanyi gabakidaya a rayuwarsa ya tsani yaji tana kuka....
A tausashe yace."Menene."? Tace"Me yasa ka ki daukar waya zuciyata kamar zata fashe."
Ya sauke ajiyar zuciya yana furzar da wani huci daga bakinsa, yace."Sai kuma kiyi kuka babu sallama da gaisuwa da tambayar yaya na kwana."?
Tace."Duk hankalina ne a tashe wallahi zuciyata sai sa'ke sa'ke take min."
Yace."Ina Mommyna." A hankali tace"Tana can gurin Bitan."
Yace."Kun tafi kun barni da damuwa ko."? Tace."Wallahi nima da kyar nayi bacci ban san haka nake sonka ba sai da na kasa samunka a waya ji nake kamar nayi tsuntsuwa nazo inda kake."
Yaji wani irin dadi na ziyartasa, yace."Nima haka naji na kuma gane kece mahad'in rayuwata." Dariya tayi tace"Nagode mijina, yanzu kayi break fast ko."
Yace."Nakasa komai tunda na tashi kinga ni da kyar ma nayi wanka." Tace."Wayyo babyna da ina nan Wallahi ni zanyi maka wanka in rungumeka in shafa maka mai in saka maka kaya."
Yayi wani killer smile kafin yace."Tunda ni baby ne idan kinyi min wanka kin shafa min mai kuma kin sa min kaya sai ki bani nono nasha ko."
Ta saki dariya da shashsheka tace"Allah da ina kusa zan baka kasha."
Yaji tsigar jikinsa ta tashi Yace."Mu bar wannan maganar kada kisa nazo inda kike yanzu."
Ta 'kyal'kyale masa da dariya tace"Ai dama kaina ka fara maganar." Yace."Tom na daina maganar." ya cigaba da cewa yau zan tafi katsina amma kuma komai dare zan dawo insha Allah." Tace"Wayyo Habibi Katsina me zakaje kayi."? Yace."Zanje Gurin abokina mana mutumin da yazo dubaki lokutan da baki da lafiya."
Jiki a sanyaye tace"To Allah ya tsare min kai ya dawo da kai lafiya." Ya amsa da "ameen." Yace."Kinga yanzu na dan samu sassauci zan iya cin abinci sabida kin bani kulawa duk da bakya gabana naji dadi sosai Allah yay miki albarka."
A nutse tace"Ameen." Bari na bari ka nutsu kayi break sai na sake kiranka ko."
Yace."Okey my Princess! Murmushi tayi ta kashe wayar tana fad'in "Nazama gimbiya kenan.....Cike da nishadi ta fito tsakar gidan gidan malam ta cigaba da hada hada da jama'a masu shigowa.




Gangami!! da turnu'kun!! haya'ki!!! nake hangowa kan titin zuwa gidan gomnati wato government house, mutane sunfi dari biyu sun kashe titi sai 'kone -'kone sukeyi suna tada 'kura gami da 'kona tayoyi suna watsa fetur suna 'kyasta ashana, sai ihu sukeyi suna buga ganguna, guri ya hargitse da hayaniya gami da haya'kin! wuta, dan wasu ma har sun soma galabaita duk da sune suka saka kansu abunda sukeyi din basu sare ba so sukeyi su shiga cikin government house din domin su cimma manufarsu kan mai girma governor Lawan Rabo, mafi akasarin jama'ar da suka tada wannan tarzomar iri-iren wad'anda aka rusawa gidaje ne da masana'antu gurun aikin titin jirgin 'kasa wanda ko rabin aikin ba'ayi ba an dakata gashi su kuma anyi musu al'kawari za'a biya su diya shuru kakeji malam yaci shirwa kullum 'karya daban ta gobe daban sam basa gajiya da shiga gidan redio suyi karya, sukuwa suka ga rainin hankalin yay yawa kawai suka yanke wannan hukuncin duk da sun san wannan abun da sukeyi din xai iya barazana ga rayuwar wasu daga cikin amma dai duk da haka sukaji suka gani domin suna so su kwaci hakkinsu da'aka danne musu,
Mai girma governor Lawan Rabo hankalinsa yay masifar tashi sosai ya lura Jama'ar Jahar kano suna so su ga karshen sa dan duk abinda ke faruwa a kan titin yana gani ta cikin CCTV Dan haka sai kawai ya umarci Securities kan suje suyi aman wuta da alburusai a gurun wanda kwanansa ya 'kare shi ya jawo kansa.
Ba tare da 'bata lokaci ba kuwa, Police din gidan gomnatin suka shiga motocinsu suka durfafi kan titin suna sakin harbi ko ta ina!














Littafin na kudi ne.....!
Kika futar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya ba kema keda Allah! Whasap numbar
07084653262
*BINTA UMAR ABBALE*alliya:
*'YAR BANGAR SIYASA!!*
*END🔚*


*ALHAMDULILLAHI*


*85*
Gurin ne ya sake hargitsewa da hayaniya dalilin zuwan Securities din, kafin kice kwabo jama'ar da sukayi dafifi a kan titin sun soma gudu saboda gabakidaya harbin bindigar da Police din keyi yayi masifar razanasu, sai kowa ya soma kokarin ceton ransa, amma dai duk da haka sai da harbin ya samu wasu daga cikinsu suna kwance a gurin suna ihu jini tamkar yay magana kan titin yayi kaca kaca sai hayaki ne yake tashi a gurin gashi gari ya soma duhu magariba ta gabato.....Governor na ganin abinda ke faruwa ya kira d'aya daga cikin mutanan da ya tura yace."Maza a kwashi wa'inda suka jikkata akai su asibiti, Allah sarki mutum kusan bakwai sun mutu 'yan uwansu sai kuka suke suna d'ora hannu aka hade da tsinewa Lawan Rabo albarka suna tur da wannan mulki nashi....Amadu na katsina tare da Abokinshi Alh Muktari labari ya samesu dan sai da suka ga abinda ke faruwa a labarai, hankali a tashe sukayi sallama da abokinshi ya dauko hanyar dawowa gida.....Koda ya iso bai nufi gida ba kai tsaye gidan redio na *Salama* ya umarci Garba ya saukeshi, abinda bai ta'ba faruwa ba kenan wai ya shiga gidan redio dan ya yad'a manufarshi,
Tashar redion Salama taji dad'i sosai da zuwanshi, kafin kice me sun fara sanarwa yanzu yanzu d'an takarar governor kano mai girma *Amadu Musa* zaiyi magana dangane da abubuwan dake faruwa a wannan jahar.
Jama'a duk suka maida hankalinsu gurin sauraran jawabinsa.....Ya fara da bisimillah had'e da addua kamar yanda annabi ya koya mana kana yace."
*Hak'ika banji dad'in wannan abunda ya faru ba a yau! hankalina ya tashi matuka! ganin yanda jama'a suka jikkata wasu har suka rasa ransu, Duk abinda wannan gomnati tayi muku bai kamata ku dauki irin wannan mataki ba, don yin hakan ba zai amfanar daku komai ba sai 'bacin rai gami da nadama da dana sani, na tabbata yau wasu daga cikinku suna nan cikin bakin ciki da damuwa rashin Iyaye da 'yan uwa mata na gida suna kuka saboda wannan tashin hankalin Wata mijinta ya mutu wata mijinta ya 'kone ko ya karya, duk saboda wannan hatsaniyar data afku, wannan abun da jama'ar wannan jaha sukayi bai dace ba shi wanda kukeyi dominsa din baza ku ganshi ba ballanta ku cimma burinku akansa, duk abinda hakuri bai baku ba rashin sa ba zai baku ba, kuyi hakuri ku barshi da Allah bisa ga zalintarku da yayi sannan kuma cigaba da yi mana addua kan Allah ya cika mana burinmu a cikin wannan tafiya, mutukar Ubangiji Allah ya dam'ka min mulki wannan jahar zan share muku hawaye zakuyi mamaki sannan dukanin wanda yay asarar gidanshi ko masana'antar sa wannan gomnatin insha Allahu Ni Amadu! na kar'bi wannan mulki nayi muku alkawarin biyanku hakkinku, wannan titin kuma da suka d'auko gadan! gadan! sunayi ni dama nasan ba iyawa zasuyi ba ku zuba musu ido, mu idan muzo namu salon daban yake da nasu, babu wani abu nasu da suka bari wanda zamu d'ora aikinmu akai komai sabo zamu 'kir'kira! babu algus babu almundahana a ciki, zamuyi mulki bisa amana da tsoron Allah Insha Allah! Daga karshe nake muku fatan alkairi al'ummar wannan jaha mai albarka ku cigaba da addua kan Allah ya kawo mana sauyi mafi alkairi sannan kuma na umarce ku da kada ku kara tada wata tarzoma, saboda yin hakan bashi ne mafita ba, mafita shine ku bamu had'in kai aranar za'be! kowa ya fito ya za'bi Jam'iyyar mu mai albarka tun daga sama har 'kasa, ku za'bi Jam'iyyar CPC Sa'a! Wasalamu alaikum."*


Amadu na gama Jawabinsa gari ya dauka anata hayaniya kowa na fadar albarkacin bakinsa, haka can ma gidan gomnatin Governor Lawan Rabo da mataimakinsa da kuma mabiya bayansu hankalinsu yay bala'in tashi, governor Lawan Rabo ya dinga da ya sanin hukuncin da ya yanke na tura securities da yayi suka dinga harbi, yasan har duniya ta nad'e jama'a ba zasu ta'ba mantawa da zamaninsa, ba, aikuwa yana jikin wannan jimamin kiran mai girma shugaban 'kasa ya sameshi, lallai yau yake so ya nufi Abuja domin yana so ya zauna dashi.
Lawan Rabo ya shiga rudani mutuka yayin da mataimakinsa yayi nasa guri dama shi d'an ba ruwa na ne tunda duk shawarar da zai bashi baya dauka yanzu data kwa'be masa sai y


aje yaji da matsalarsa.
As da sauran jama'arsa ne suka rakashi can fadar shugaban 'kasar.




Duk da suna cikin karkara sai da labari ya samesu, dan Wasila har jawabin mijinta sai data saurara, hankalinta a tashe ta dinga kiran wayarshi domin taji lafiyarsa, wayar bata shiga da alama dai gidan Malam bai da network me kyau.




Sai misalin goma shaura na dare ya shiga gidanshi, yay wanka ya fito palo wanda yay dai-dai da shigowar Khalifa suka zauna suna sake tattauna maganar.........A dai-dai lokacin ta sake gwada kiransa a waya a kaci sa'a wayar ta shiga, zazzafar ajiyar zuciya ta sauke tace"Habibi sannu da hanya ina fatan ka dawo lafiya."
Yace."Na dawo lafiya lou har yanzu ban samu sukunin kiran wayarki ba."
Tace."Nima tun dazu nake ta neman wayarka network yana hanawa, na saurari Jawabinka dazu kano babu lafiya ashe." Yace."Eh gashinan jama'a nata fama wai sai sun halaka governorn ku Lawan Rabo."
Tace"Dan Allah daina cewa governor mu wallahi na tsaneshi mugu ne." Yace."A haba dai yanzu kin fita daga jam'iyyarsu kenan."? Kamar zatayi kuka tace"Ka bari bana so dan Allah."
Ya dan shafa saisayayyar sumarshi yace."To na bari ina Mommyna." Tace"Tana goye a bayan Bitan." Yace."Wai ita wannan Bitan din bata gajiya da hidima ne."?
Murmushi tayi tace."Mutuniyar kirki kenan." Yace."Ina kaunar matar sosai saboda tana kaunarki gashi yanzu tana gwadawa kan Mommyna." Mirmushi kawai tayi, yace."Kin san wani abu."? Girgiza kanta tayi tana lumshe ido yace."Gabad'ayansu Malam Kawu Habibu Inna Hajara Momynmu da ita Bitan! Dukaninsu zasuje Umara insha Allah sati biyu masu yawa." Wani irin farin ciki ne ya lullubeta kamar tayi masa ihu a wayar sai dai ta daure ta dinga zabga masa godiya da addua muryarta sai rawa takeyi......Yace."Babu komai ai dangina nayiwa meye abin godiya." Tace"Eh duk da haka nagode." Yace."Idan sun dawo zamuje namu umarar." Tace"Tom shikkenan yanzu kuwa zanje na fadawa Kawu wannan albishir din." Murmushi yay yace."Sai Allah ya kaimu gobe ko."? Tace"Tom Allah ya kawo ku lafiya."
Kashe wayar yay yana murmushi, suka hada ido da Khalifa dake zaune ya zuba masa ido, hummm! Wai Amadu ne ke hirar soyayya wanda da idan ance zaiyi sai yace shi bashi da lokacin yin haka.
Murmushi yay yace."Dama kana nan a zaune."? Khalifa ya murmushin takaici yana jan 'karamin tsaki yace."Ai baza ka gane ina gurin ko bana gurin ba tunda idanunka sun rufe."
Ya dan shafa kanshi As'usel da murmushi a fuskarsa yace."Khalifa ina son yarinyar nan wallahi." Khalifa ya mike yana fad'in "Ai ba sai ka fada ba duk ga alamu nan sun nuna." Mikewa yay ya bashi hannu suka tafa suna dariya a tare suka fita daga palon.


Wasila ta sanar da Malam alherin da Amadu yay musu, malam ya shiga tsananin farin ciki mara misaltuwa ya aika aka kira masa Kawu Habibu shima ya dawo gida saboda daurin auran ya tarasu ya shaida musu abinda ke faruwa, Inna Hajara ta dinga rangwada 'buda a gidan tana fad'in "Haihuwa mai rana Yau ni Hajara nice zanje wannan guri sai ta fashe da kuka tana fyatar hanci tace" Allah ya ji'kanka dan uwana insha Allahu kana aljannar furdausi, Bitan tace ta dinga rarrashinta da ta daina kuka domin yin hakan zai sanya su Wasilan hankalinsu ya tashi, da kyar Inna Hajara tayi shiru ta kama Wasila ta rungume a jikinta tana mata addua gami da hud'uba kan zamantakewar aure.




****
Alhamdullhi an d'aura auran Uwani da malam a gidan Kawunta dake Tudun maliki, bayan daurin aurane sai suka kuma nufi can pataskum din domin gaisuwa sannan kuma da dauko amarya, malam sai washe baki yake yana baza babbar riga Shi kuwa Amadu kunya ce take kamashi wai daurin auran Uwar matarshi ake sai dai kawai ya girgiza kansa yana murmushi.




Uwani tayi ado dai-dai gwargwado kuruciyarta ta sake fitowa tamkar bata haifi Wasila ba wani cewa zaiyi yayarsu ce anyi mata kitso da jan lalle tana sanye da sabuwar atamfa 'yar ingila jama'a sun cika gidan Kawu Madu sai hidima ake Kuluwa sai washe baki takeyi tana karbar baki, Kuluwa yanzu ta dan rage kazanta dan Kawu Madu ya soma dawowa hayyacinsa asirin da tayi masa ya karye dan da ya farga da irin kazantar da takeyi yace."Wallahi ta kuka da


kanta idan ya tashi aure zai aure mace mai tsabta 'yar gayu tunda shi ba kazami bane."
Aikuwa Kuluwa ta tsorata sai ta dage da wanka da wani had'e da kitso akai akai kuma garin Allah yana wayewa zata sa brush ta wanke bakinta tun yana futar da jini har ya daina, amma duk da wannan abun da takeyi Kawu Madu bai saduda ba yana nan da bazawarsa 'yar 'kwalisa har sun tsayar da ranar daurin auransu, Kuluwan bata sani ba sai dai jama'a da yawa sun sani shuru kawai akayi mata ana jiran ranar da amarya zata zo aga me zai faru.




Amadu kasa shiga gidan yay sai ya zauna cikin motar.....Kunyar hada ido yake da mahaifiyar matar tashi, to itama Uwanin tunda taji jama'a nata surutu da amabatar sunan mijin 'yar tata sai ta kasa fitowa tsakar gida ta zauna cikin daki abinta
Kawu Madu da kansa ya fita har bakin motar da yake ciki suka gaisa cikin mutuncin da karamci sannan fa mutane suka farga dashi sai suka dinga zuwa daya bayan daya suna gaisawa, ganin hakan kamar bai dace ba yasa ya fito daga motar yana gaisawa da jama'a cikin sakin fuska da dattako.




Karfe shida sun iso gidan......Lokacin Rashida da Wasila sun saka turare mai kamshi a dakin mahaifiyar tasu wanda ya sha jere mai kyau kuma na zamani, katon gado ne da katifa mai kyau sai katuwar sif mai murfi shida akwatinanta akai sai mudubi da drowars guda biyu koran kafet ne malale a dakin labule koraye da net dinsu, dakin yayi kyau sosai.
Su Kuluwa da Ina Tabawa da Ita mai waina suka rako Uwani dakinta Bitan ta karbesu hannu bibbiyu aka gaisa cikin mutunci da mutuntawa............Wasila bata samu sun ke'be da mahaifiyarta ba ya dinga kiranta a waya ta fito su tafi saboda dare ya soma yi....Uwani tace"Ki shige ku tafi daga baya sai ki dawo ina laifi ma da ya barki kikayi kwanaki biyu, Babu yanda ta iya haka tasa yara suka dauki jakar kayanta Rashida kam fujirewa tayi wai tunda babu makaranta ba zata bisu ba sai jarrabawarsu ta fito, Uwani kam bata ce mata komai ba itama zata fiso ta zauna a gabanta.....Wasila ta fito tana sallama da jama'ar dake gidan duk zuciyarta babu dad'i Inna hajara tasa yara suka fitar mata da kayayyakinta wajan motar......Ita Kuluwa fad'i take "Kice ina gaisheshi." Wasila ko kallonta batayi ba ta fice daga gidan, sukayi karo da malam zai shigo sai ta zube a kas tana kuka, Yace."meyasa kike kuka Wasila. Tace"Wallahi Kawu bana so na

56 / 57