YAR BANGAR SIYASA BOOK COMPLETE By Binta Umar Abbale .txt

Author :  Binta Umar Abbale Category :  Romantic Books

Chapter   31 / 57

90K to 93K   out of 169.7K words

tafi wata uku sai dai takanzo duk bayan sati biyu to wannan karon ma kinga satin ta uku bata zo ba." Wasila tace"Ayya! mybe tananan tafe." Asabe tace"To Allah yasa." Shiru sukayi kafin su ta mike Asabe tace"Har zaku tafi bazaku tsaya kuci abinci ba." Wasila tace"A'a Asabe mungode." Har soro ta rakosu tana fadin su gaishe da Uwani da kyau kafin tazo.


Suna fitowa Wasila tace na fad'a miki dama kinga munyi asarar kudin motarmu ko? gashi bamu dana komawa gida tsakanin dorayi da tishima akwai nisa sosai dan da kyar ma aka kawo su a dari biyar kona pure watar basu dashi.....Rashida tace"Mu shiga gidanmu wanda muka bawa malam 'Dayyabu nasan idan yananan zai bamu kudin mota da zamu koma gida." Wasila taji dadin maganar Rashida sai suka nufi layinsu na da, suna shiga layin suka hango, gidansu ya koma katin sai da kayan provision! tsayawa sukayi suna mamaki! wani yaro da yazo wucewa ya shiga kallonsu yaso ya ganesu Wasila tace"Kai waye cikin provision din can." Yaron yace."Jazuli ne na gidanmu malam d'ayyabu ne ya siyar masa da gidan shi kuma ya ruge yayi kanti." Wasila da rashida suka shiga mamaki! ashe malam dayyabu haka yake sun bashi gida domun ya zauna ya siyar ya kar'be kudin ya gwammace yayi ta yawon haya da yara da mata, cikin unguwar dama su Wasila da gidan malam dayyabu sune talakawa, gwara su wasila ma gidan kansu ne shi kuwa malam dayyabu gidan haya ne duk lokacin karbar kudi sai anyi rigima dashi masu unguwa sun taru a kanshi sannan zai bada kudin, shinda wasila ta tausaya masa suka bar mishi suna ganin tunda sun samu wani me zasuyi dashi ashe bayan tashin su da sati biyu malam dayyabu ya siyar da gidan ya kama haya ragowar kudin yasa a aljihu yana cin karansa babu babbaka dasu.......Ajiyar zuciya suka sauke a tare suka kama hanya suka bar gurin zuciyarsu cike da wasi wasin yanda zasuyi.




Sosai suka dingi tafiya kan titi wanda tun suna magana suka daina tafiya kawai sukeyi suna yanke yanken hanya har Allah yasa suka fito titin gadon 'kaya! Rashida ta sharce gumin dake goshinta tana haki! tace"anti wasila zama zanyi na huta na gaji wallahi." Wasila tace"Mu samu guri mu zauna nima nagaji." Suka sami guri dai-dai Gate din shiga Management suka zauna suna hutawa, sunanan zaune daliban dake makaranta suka soma fitowa 'yan mata maza zawara da matan aure wasu na fitowa da motocin su wasu wasu kuma na tare abin hawa! Wasila ta dinga kallonsu suna bata sha'awa suna da gata suna da galihu sunyi dacen iyaye sun tsaya musu kan ilimi su kuwa fa! sune nan sune can! Sai taji zuciyarta ta karye hawaye ya tsinke mata! tayi gaggawar sunkuyar da kanta kasa tana sharewa bata so Rashida ta gani sannan kuma jama'ar dake gurun suma bata so su gani, tana dago kanta suka had'a ido da Suhairat ita da kawayenta bakin wata mota! Zasu shiga macace take driving din, da sauri ta kauda kanta gabanta na faduwa tace"Rashida tashi mu tafi." Rashida tace"Anti wasila dan bari mu sake hutawa wallahi gurin akwai iska." Tace."Rashida hutun jaki da kaya kikeyi kawai ki tashi mu tafi mu samu mu fita babban titi na sabon titi." Rashida ta mike tana yafa mayafinta sukayi gaba.......Motarsu Suhairat ce taci burki a gabansu, da sauri suka matsa baya Suhairat ce ta bude motar ta fito sauran suna ciki suna hangensu


Gabansu ta tsaya tana watsawa Wasila kallon banza tace"Ke matar babban mutum ina zuwa haka? ya naga kina yawo a kasa ko satar hanya kikayi kika fito yawon tazubar d'in da kika saba."!? Wasila tayi shiru tana kallonta Rashida tace"Haba Suhairat wace irin magana ce wannan? kin manta anyi muku tsakani da anti wasila meye ruwanki da ita yanzu." ? Suhairat tayi dariya tana gyara zaman glass din dake idanunta tace"Rashida daga tambaya sai cibi ya zama 'kari! ai gani nayi bai dace ace kamar wasila matar *Ahamadu Musa* na yawo 'kasa ba, ai kamata yay mu ganta cikin katuwar mota


wacce ta amsa sunanta, ko da yake dai ina jin satar hanya tayi ta fito, Okey karfa ku damu da maganata, ba wani abun nake nufi ba, saboda haka na barku lafiya." Wasila da Rashida suka bita da kallo har ta shige motar tasu suna kallonta tana she'ka dariya tare da tafawa da 'kawayenta tana nuna wasila da hannunta su kuma sai dariya sukeyi, kafin wacce take driving din ta figi motar a guje suka bar gurin.


Wasila ji tayi gwiwowinta sunyi bala'in sanyi ta inda har ta kasa motsa kafafunta da niyar tafiya sai kawai ta nemi gefan titi ta zauna rana na kwallare mata fuska zufa! ta shiga ketowa daga jikinta


Rashida itama ta zauna kusa da ita tana fad'in"Amma wallahi suhairat din nan bata da mutunci shegiya guzumar banza wacce ta rasa mashinshine anti wasila ki kyaleta don Allah mybe suna da labarin Ahamdu ya sake ki shiyasa suke murna da dariya amma babu komai ai duk abinda mutum yayi kanshi.


Ba tace komai ba tana dai sauraran Rashidan da duk rarrashin da take mata ita kuma sai nanata kalmar innalilihi wa'inna ilaihi raji'un takeyi a zuciyarta, ji tayi komai na rayuwa yayi mata zafi ta dinga nadamar kuskuran da tayi a baya, kanta ne ma ya soma yi mata ciwo, rana ce ko damuwa ce ko kuma rashin bacci ne? babu wanda ya sani sai Allah.


Kusan mintina ashirin suka dauka a zaune a gurin masu babur din a dai-dai ta sahu sai tayi suke musu wai ko zasu shiga kowa na ganin lamun ba shiga zasuyi ba sai ya buga babur dinshi yayi gaba!..................




Cikin 'kwalleliyar ranar dake kan ganiyar ta, suka fita, titin sabon titin gidan 'kankanra lokacin sunyi masifar galabaita mutuka gashi ko na pure watar babu Wasila taja hannun Rashida suka fake wata inuwa still dai a bakin titin suke zaune suna mai da numfashi suna kallon ababen hawan dake shige da fice a gurun......."Wasila anti Wasila yunwa nakeji da shiru kinji ma'kogwarona kuwa kai anya ba zamu nemi taimako ba kuwa."?


Wasila tace"Nima nagaji Rashida taimako a ina zamu nema."? Anti wasila mu nemi left gurin masu motar gida sai sunfi sauki akan masu a dai-dai ta sahu tunda su kinga sana'a suka fito." Wasila tace"anya kuwa Rashida."


"Allah anti wasila ba zamu iya kai kanmu gida ba akwai fa nisa gashi ko rabi ba muyi ba." Wasila tace"Akan muyi left din nan ai gwara mu tambayi wannan me shagon na tsalleke watakila ya taimaka mana." Rashida tace"Bari naje ki zauna dan na lura kamar jiri ke d'ibanki." Tace"Wallahi jiri nake rashida yi sauri kije Allah yasa ko dari biyu ya bamu." Rashida ta tsallaka titi domin zuwa gurin me shago........Mai shago najin bukatar Rashida yace "Duba daya ma zan baki amma shigo ciki na aunaki." Rashida ta gane abinda yake nufi duba da irin yanayi kallon da yake mata na iskanci! sai kawai taja tsaki! ta fita daga shagon......Ba tayi shawara da Wasila ba kawai ta soma d'aga hannu tana tsaida motacin mutane........ Khalifa dake driving yay saurin kallonshi hankalinsa na kan jaridar dake hannunshi yana dubawa yace."Duba wacan yarinyar kamar Wasilan ka." Yay gaggawar hanya nan ya hango rashida na d'agawa motarsu hannu, ya mai da kanshi kasa ya cigaba da abinda yake! Sai da suka kusa isa gurun rashida khalifa ya gane ba ita bace amma kuma gaskiya suna kama sai dai ita wannan tafi wasila haske! A hankali ya tsaida motar dai-dai inda Rashida take tayi gaggawar zuwa gurin........."Khalifa ya sauke gilashin motar a hankali yana kallonta, rashida ta marairace fuska muryarta na rawa tace"Dan Allah Yayana ka taimaka mana ka rage mana hanya nida 'yar uwata wallahi tun daga d'orayi muka zo nan a 'kafa kudin motarmu ya 'kare." Tunda rashida ta soma magana yake jin wani iri, maganarta sak! data Wasila, ta gefan ido ya dan kalleta, sai gabanshi ya fad'i! wannan fuskar ai kamar ya santa yarinyar nan ce kanwar Wasila, shiru yay bai ce komai ba, shi kuwa khalifa da bai san abinda ke faruwa ba yaji tausayin rashida yace."Ina 'yar uwar taki." Rashida tayi saurin fad'in gata can tsallaken titi." Yace."Yi maza ki kirata." Cikin farin ciki rashida ta tafi, dake hankalinta na kan khalifa sam! ba tayiwa Ahamdu cikkaken kallo ba ballanta ta gane shi.


"Anti Wasila taso ga mota can zat


a daukemu Allah sarki wallahi me motar nada kirki." Wasila na daga inda take zaune ta dinga kallon had'addiyar motar tana mamaki! anya kuwa, wata zuciyar tace wasila idan baku shiga motar nan fa babu wanda zai taimakeku gwara ku shiga ko bakin asibiti ne sai ya saukeku in yaso sai ki siyar da zoben hannunki." Sai ta yarda da shawarar da zuciyarta ta bata, ta mike tana karkad'e jikinta suka nufi motar.


Khalifa tun kafin su karaso yake mamaki! Fuskar wasila ba bakuwa bace a gurinshi itace wallahi." Ya furta ba tare da ya sani ba, kalmar ta sanya shi dago kanshi yana kallon inda yake kallo, kawai sukayi ido hudu da ita, sai dai ita bata ganinshi shike ganinta kasancewar gilashin motar me duhu ne.


Yace."Mutukar zaka dauki yaran nan cikin motar ka ka saukeni dan Na rantse ba zan had'a nuffashina dana wannan yarinyar ba." Khalifa ya dinga kallonshi cikin tsananin mamaki! yace."Haba! taimako ne fa shin bakaji abinda 'yar uwarta ta fad'a ba, tun daga dorayi zuwa nan a 'kafa akwai wahala, kayi hakuri kawai a daukesu ai ba wani abun bane." Sai kawai ya hau kokarin bude mota zai fita.....Khalifa yace." A'a me yayi zafi! bari kawai na basu kudin abun hawa ba sai ka fita ba." Yace."Hakan shi yafi maka alkairi." Khalifa ya bude ma'adanar kudinshi dake cikin motar dubu ashirin ya 'kirga ya zuge gilashin motar, suka had'a ido da Wasila sai tay saurin matsawa baya gabanta na faduwa, dan ta hango gefan fuskar mutumin nata kanshi a kasa yana kallon jarida......Khalifa shima bai nuna ya ganeta ba, sai ya mikawa Rashida kudin yace."Kanwata 'karbi kudin nan ku hau abun hawa, kinji ko abokina nada uziri shiyasa amma da da kaina zan dauke ku na kaiku har gida." Hannu na rawa Rashida tasa ta kar'bi kudin tana godiya ta kalli Ahamdu tana fadin"Mungode sosai Allah ya saka da alkairi." A nutse ya dago kanshi yana kallonta, itama ta shiga shock ganin fuskarshi, Yace."Ki godewa Allah." Sai ya mai da kanshi 'kasa, Khalifa ya kunna motar yana fadin"A gai da gida ko." cikin nauyin baki tace"Mungode." ta bar jikin motar, sai da motar ta bar gurin sannan ta wuce cikin sanyin jiki ta nufi inda Wasila ke tsugune kusa da wata bishiyar darbejiya kanta na kasa gabanta sai faman faduwa yake tana fadin"Innalilihi wa'ina ilaihi raji'un a zuciyarta.








*_Ba cinye wa bace ba kuma burgewa bace ki dinga cushe cushen maganin matsi a matantakarki, ruwan d'umi kawai ya isa ya sanya gabanki ya matse ko da kuwa kinyi haihuwa goma ne, yana da kyau idan kin haihu a gida kije asibiti domin a duba matantakar ki ko kin samu matsala a gyara miki in kika zauna a gida bakije asibiti ba, akwai matsala idan kin 'karu guri ya had'e a haka mijinki ya shiga yaji kwararo! shikkenan kuma matsala ta afku a tsakaninku🙋🏻‍♀️_*












Littafin na kudi ne......![13/08, 6:37 pm] +234 906 803 2427: 'Yr Bngr Sys
*53*
Malam mai allo na shirye shiryen tafiya tsangayarshi, su Ahamdu suka sauka a garin......Tanimu d'anshi na biyu shine ya shaida masa zuwan ba'kin, Ya fito cikin babbar riga da koren rawani a nannade a kanshi, ganin su Ahamdu tsaye jikin motarsu ya sanya ya washe bakinsa, ya shiga yi musu barka da zuwa yana fad'in"Gwara da Allah bai sa na fita ba, dama yanzu nake shirin fita gurin karatu da sai da muyi sa'bani sannuku da zuwa sannuku." Cikin gidan suka nufa akwai wani babban zaure a soro wanda yake saukar baki a ciki dama kullum sai Bitan ta shiga ta gyara ta kunna turaran wuta dan haka ma yanzu dakin sai kamshi yake yi, Ahmadu da khalifa suka zauna......Malam mai allo ya zauna kan buzunsa yana fad'in"Wallahi ko jiya sai da nayi zancen ku nake cewa Hajara da Bittan su shirya suje suga dakin yarinyar nan akwai kuma 'kwan zabi dana aje mata sunanan da yawa nace su tafi mata dashi ta soya tunda nasan in tazo nan garin tana yawon soyawa taci."


mirmushi kawai Ahamdu yay yana tausayawa mutumin bai ce komai ba ya shiga gaisheshi ya amsa cikin walwala da farin ciki kai kana ganinshi kasan yana cikin farin ciki....suka gaisa da khalifa cikin farin ciki da barkwanci kafin ya tashi da sauri yana fad'in"Bari nasa bitan ta kawo muku abinci da ruwa."


Yana fita dakin yay shiru Khalifa yayi gyaran murya yana kallonshi yace."Yanzu baka tausayawa wannan mutumin ba! ya kake tsammanin zaiji idan ka sanar dashi abinda ka aikata dan Allah ka janye kudirinka ka kudurta a ranka ka mayar da ita, kar ma ka fada masa komai kawai kace kazo gaisheshi ne."


Shiru kawai yay baice komai ba, a zahirin gaskiya mutumin ya bashi tausayi sosai yasan zai shiga tashin hankali mutukar yaji da abinda yake tafe dashi, ammafa duk da hakan baya tunanin yanje kudirinshi shi kanshi a yanzu ya rasa wace irin 'kiyayya yake wa yarinyar sam yanzu baya ma so a dangantashi da ita, dan haka gwara kawai ya sanar mishi da abinda ke faruwa hausawa nacewa ta inda aka hau tanan ake sauka.




Malam mai allo ya shiga dakin yana gyara babbar rigarshi, sai fara'a yake yace." Kamar na sani yau na tashi Tanimu da sassafe ya tatso nono ashe ina da baki kai masha Allah naji dadin zuwanku Ahamdu." Yafada yana gyara zamanshi kan buzunsa.....Bitan ce ta shigo hannunta rike da wata kwarya me zane zane da fefe a samanta da ludai guda biyu tana fadin"Sannunku da zuwa."Khalifa yay saurin kar'bar kwaryar furar yana amsawa, ta dan tsuguna gefe tana gyara lullu'binta suka fara gaisawa, Ahamdu duk nauyi da kunya ya isheshi ganin yanda mutanan ke rawar jiki a kansu, Bitan na kokarin fita Kawu Habibu da Haraja suka shigo suma suna cike da murna da farin ciki, Mai allo ne ta tura danshi, Tanimu yaje ya sanar musu da zuwan su.....Suka gaggaisa cikin mutunci da mutuntawa Ahamdu duk jikinsa yayi sanyi da karamancin mutanan, Mutanan nada kirki da mutunci da kara babu shakka da karamcinsu Wasila ta dauko to da taji dadi, wannan mugun halin mybe daga can dangin uwarta ta daukoshi, abinda yake ta fada kenan a zuciyarsa......Khalifa ne ya iya shan furar shi kam ko ludai daya bai sha ba, tun daga sannan mai allo yasha jinin jikinshi dan bai san Ahamdu da irin wannan fuskarba babu walwala babu sakewa tun dazu suke hira da khalifa yayi shiru abinshi sam ba'ayin doguwar magana dashi zaiyi shiru mai allo jikinsa yay sanyi sosai,
Gyaran murya yay ya mai da hankalinsa kan Ahamadu yace."Jikina na bani akwai babban al'amarin dake tafe daku dan hauwasa sukance labarin zuciya a tambayi fuska hakikanin gaskiya alhaji Ahamdu ba haka nasan fuskarka ba, a sanin da nayi maka kai mutum ne mai walwala da sakakkiyar fuska ina fatan ba wani laifin wannan yarinya tayi maka ba, dan dama kullum cikin addua nake ubangiji Allah ya zaunar da ita dakinta ya kareta daga rudin duniya dana mahaifiyarta."


Khalifa dai 'kas yay da kanshi kunyar had'a ido yake da mai allo din da kaninshi Habibu, dan yanzu da ya sani ma yake da bai rako ahamdun ba sam baya son abinda zai daga hankalin mutane......'Dan numfashi ya sauke a hankali kafin yay gyaran murya yace."To Alhamudullihi arrama! naji dadi da ka dan fuskanci wani abu daga kallon yanayi na, Da farko dai kaine ka bani auran wannan yarinyar ni kuma biya sadaki na kar'ba bisa amana, to wani babban dalili ya sanya na yanke hukunci a kanta wanda nasan ba zai maka dadi ba, kayi hakuri haka Allah ya kadarta bazan boye maka ba Allah ya gafarta malam naso na rike amanar da ka bani amma zuciyata ta'ki aminta, da hakan.......Wannan yarinya tayi min abun da ya sanya naji na tsaneta gabakidaya bani son ganinta cikin gidana, ba kuma na son cigaba da zama da ita a matsayin matata, dalili kenan da ya sanya ni na saketa saki day........Kafin ya 'karasa mai allo yayi saurin fadin kalmar "Innalilhi wa'ina ilaihi raji'un!!!! Ahamdu yayi kasa da kanshi, mai allo ya shiga goge zufa da babbar rigarshi gumi ne kawai yake karyo masa,


Kawu Habibu kuwa fad'i yake " Garin yaya haka ta faru!? me yarinyar nan tayi maka me zafi da har zaka saketa Alhaji Ahamdu kada kayi mana haka."


Shi dai shiru yayi kawai kanshi a kas......Mai allo yace."Alhaji Ahamdu ka sanar min abinda ke faruwa me wasila ta aikata maka ka saketa nasan dai tabbas ba zaka aikata wannan abu ba sai da kwakkwaran dalili ina so kar ka rufe min komai ka shaida min abinda ke faruwa.


Cikin nutsuwa ya shiga warware musu irin badakalar dake faruwa ya kuma kunna musu muryar Wasila da As din a lokacin da suke kulle kullensu, ya kuma tabbatar musu da cewar dalilin kenan da ya sanya yaji zama da ita ya fice masa daga rai! bayan haka kuma koda ya zauna da ita to zuciyarsa za tayi tai masa wasiwasi a kanta ba zai iya yarda da ita ba........Mai allo yace."Banga laifinka ba Ahamdu banga laifinka. Hakika yarinyar nan ta cuci kanta ta cuci rayuwarta, tunda irin rayuwar data za'bawar kanta kenan to babu mu babu ita, duk wani hakki nasu munyi kokari mun saukeshi amma kullum cikin bin zugar shaidan takeyi da bib zugar mahaifiyarta, Wasila ta cuci kanta ta samu dama ta watsar babu komai Ahamdu mungode sosai da jajurcewa kuma naji dadi matuka da kazo kasanar dani abinda ke faruwa dan da baka sanar dani ba ba zan sani ba, kullum zan ta tunanin yarinyar na dakinta tunda dai ni nasan ba zasu zo inda muke ba, amma babu komai, zamu kyalesu mu zuba musu ido dan ba

31 / 57