YAR BANGAR SIYASA BOOK COMPLETE By Binta Umar Abbale .txt

Author :  Binta Umar Abbale Category :  Romantic Books

Chapter   48 / 57

141K to 144K   out of 169.7K words

domin ingantuwar lafiyarki! Bayan haka kuma dole ne kafin ki komawa miji sai an gyara miki jikinki domin haihuwar da kikayi duk wata ni'ima da kike dashi babu nida a tunanina ma ina so idan zan tafi gida muje tare dake can in gyaraki sosai da sosai to amma tunda naga take taken mijinki to zan tattara nawa nawa na tafi dama akan dole nake zaune a gidan, bana so yazo ya dinga jin haushina ko ya fahimci cewar nice nake hanaki biya masa bukata."


Tun kafin Inna hajara ta 'karasa maganarta ta rike hannuwanta tamau! tana kuka sha'be!sha'be! "Wallahi Inna ba zaki tafi ba sai nayi ar'bain sai kace wata mara gata da galihu! ai haihuwar fari nayi kuma koda zanyi haihuwa goma a gidanan kina da damar da zaki zo ki zauna tare dani tunda ina cikin gidan.....Inna nasan abinda nakeyi nima bazan yarda ya haike min ba kawai ya cuceni bayan ban gama dawowa dai-dai ba, na amince zan jure ko wane irin fushin da zai dauka dani nasan idan ya gaji zai daina.."
Inna hajara tace"A'a Wasila ni bazan so kullum ki dinga kwana da tsiniwar Allah da mala'ikunsa ba, kibi mijinki sau da '


kafa kiyi masa biyayya kan abinda yake so ni dai na fad'a miki yau yau zan tafi dan naga kamar haushina yake ji to zai dawo ya tarar na bar masa gidansa.
Wasila ta dinga kuka tana bata hakuri Inna Hajara ta rufe idonta ruf ta fita daga dakin domun zuwa ta had'a kayanta.......Hannunta na kyarma ta d'auki wayarta ta shiga kiransa.....Lokacin yana cikin company sa tare da ma'aikatansa yaga kiran wayar tata ya'ki dauka har yanzu haushinta yake ji
Ta kira ya kai sau biyar bai dauka ba sai kawai ta aje wayar ta fito palo tana goge fuskarta tasan haushinta yake ji shiyasa bai dauki wayarta ba, tana fitowa palo ta tarar Inna hajara da hajja suna fafatawa, Inna Hajara taurin kan tsiya ne da ita ta'ki sauraran hajja hannunta ri'ke da jakar kayanta ta kama hanya ta fita Wasila tabi bayanta har wajen harabar gidan......Garba ya iso gurin da sauri ya karbi jakar kayan hannunta shi baiyi tunanin wani abuba saboda ya dauka inna zata tafi gidane....Can parking ya nufa da jakar kayan ya fito da mota har inda suke tsaye Inna hajara ta bude ta shiga tana 'bata rai! Wasila kallonta kawai takeyi domin ita har ta gaji da magiya da bata hakuri, tana tsaye har garba yaja motar suka fita daga gidan, ta girgiza kanta ta juya domin komawa ciki tana kokarin mayar da hawayen dake so ya zubo mata.
Tana shiga ta tarar da Hajja a tsaye a tsakiyar palon itama tana cikin alhini na tafiyar Inna hajaran Tace"Wasila kodai wani abu akayiwa hajara ne irin wannan tafiya haka da gaggawa, kuma na lura kamar dai ranta a 'bace yake."!
Ta d'an d'auke hawaye a hankali tace"Haka kawai ta tubure wai gida zata tafi babu abinda akayi mata."
Hajja ta zauna kan kujera jikinta a sanyaye tace"To ai shikkenan Allah ya sauketa lafiya." Ta amsa da "ameen tana kokarin shiga d'aki.




****
"Haba Uwani wai dan Allah tun yaushe nake miki magiya kan ki kaimu muga d'akin yarinyar amma kin'ki kaimu kullum nayi miki magana sai kice zamuje to sai yaushe zamuje? kada fa ki manta da cewar kwanaki dani dake mukayi lissafin watannin cikin yarinyar har ki kecewa cikin ya isa haihuwa nace watakila ma ta haihu to kinga yana da kyau muje muga halin da ake ciki." Kuluwa ce zaune a gaban Uwani take wannan maganar cikin 'kas'kantar da kanta.......Uwani ta sauke ajiyar zuciya tana kallon Kuluwan kamar ba itaba wai yau an wayi gari Kuluwa nayi mata magana cikin kalami mai dad'i lallai duniya kenan.


Tace"Kuluwa ba wai bana so muje bane gaskiya bana so muje gidanan kiyi wani abu da zai sanya kima da mutuncinmu ya zube mutumin nan ba karamin mutum bane kuma kinga mu sirikai ne dole mu kama girmanmu ke kuma kuluwa baki da girma sai na jiki idan kin amince cewar xaki kiyaye kuma zaki nutsu sosai to shikkenan sai mu shirya idan Allah ya kaimu dani dake da Kawu da kuma su Inna mai waina muje muga abinda yarinyar ta haifa."
Cikin kwantar da kai Kuluwa tace"Haba Uwani wallahi bazan aikata abin kunya ba zan kula sosai bazan baki kunya ba insha Allahu." Uwani tace"Shikkenan to yanzu zan tashi na shirya na nufi gidan Inna Tabawa domin na shaida mata halin da ake ciki." Kuluwa tace"To hakan yayi bari idan na sauke abinci sai na d'an d'umamaki ruwan wanka kafin ki tafi kiyi sai kinfi jin dad'i." Mikewa tayi ta nufi kicin........Uwani tabi ta da kallo cike da mamaki.










Littafin na kudi ne!
Kika futar min da book keda Allah kika karanta baki biya ba kema keda Allah Whasap numbar
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*alliya:
'Yr Bngr Sys
*76*
Koda Rashida ta dawo ta tarar Inna hajara ta tafi itama sai da taji rashin dad'i tayi ta tambayar Wasila dalili, kunya ta hanata fad'a mata kawai sai tace"Rashida kin san dai rigimar Inna hajara dama da kyar na samu ma ta zauna tayi wad'annan kwanakin amma babu wani abu da akayi mata wanda zai sanya ta tafiya kawai dai dama tayi ra'ayi ne." Rashida ta amince da maganar Wasila suka zauna suna jimamin tafiyar Innar tasu.


To can 'bangaran su mai girma governor Lawan Rabo sun tada aiki sosai shida mu'karrabansa duk dan ganin yanda al'ummar jahar suka tashi hankalinsu gurin ganin sun rusa tafiyarshi da kuma jam'iyyar da yake ciki gabakid'aya jamiyyar da yake ciki dashi kansa sun daina power gabakidaya jama'a nata komawa jam'iyyar *CPC* jam'iyyar su Amadu kenan duk ta doke sauran jam'iyyun da suke adawa da junansu......Hankali mai girma governor yayi masifar tashi, babu shakka idan ya tsaya kallon ruwa to kuwa kwad'o zaiyi masa 'kafa, tuni ya kira 'yan fadarshi irin su As da mataimakinsa suka zauna zaman meeting inda suka yanke shawarwarin da suke ganin zasu taimaka musu gurin campaig, governor ya fitar da miliyoyin kudi ya rabawa 'yan gwangila irinsu As yace aje ayi duk abinda ya kamata a cikin jahar domin a jawo hankalin jama'a jam'iyyarsu........As suka fara aiki gadan gadan inda suka fara rushe rushen gidajan jama'a da masana'antu wai zasuyi babban titin da jirgin 'kasa zai dinga wucewa, jama'a da yawa suka shiga halin damuwa an rushe musu muhalli ba'a basu diya ba masu sana'oi suma an rugaza musu guri ba'a biyasu ba, a mai dasu gida an tsuganar, takaici ya ishesu sai kawai suka soma shiga gidan redio suna zage zage da fad'in Allah sai ya saka musu wannan zalincin da ake musu.....Mai girma governor ya tafi katsina gurin abokinsa ya samu labarin abinda yake faruwa a jahar tashi, a take ya kira As yace ya shirya da kanshi ya shiga gidan redio yayi bayani wanda zai dauki hankalin jama'ar gari su amince da manufarsu.
As ya shiga gidan redio na salama ya dinga zabga 'karya da 'karairayi kan cewar mutukar jama'ar gari sun sake za'bar lawan rabo to babu shakka zasuji dad'i a wannan karon komai zaiyi sauki za'a samu sauyi na rayuwa sannan yace."Duk wanda aka rushe masa gida da gurin sana'arshi a gurin aikin titin da sukeyi to duk su kwantar da hankalinsu za'a biya su hakkinsu......Ashe jama'ar gari sunyi dafifi a wajen gidan redion koda su As suka fito dashi da 'yan rakiyarsa da 'kyar suka sha dan ma da akwai security a tare dasu amma dai dik da haka sai da sukayi raga raga da gilashin motocinsu suna tafad'in "bamayi! kano ta d'an musa ce."


Ranar Amadu da Khalifa sun sha dariya hankalinsu kuma ya kwanta sosai ganin suna samun nasara a cikin tafiyar tasu kullum 'kara samun masoya sukeyi ta ko wane fanni.




Tun ranar da Inna hajara ta bar gidan a tsakaninsu suka daina samun jituwa wanda gaisuwa ce kawai take had'asu daga haka shikkenan zai fice harkokinsa, kuma koda ya dawo gidan yaga bai ga Inna Hajara baice mata komai ba itama ba tace masa komai ba, dukaninsu sun shiga cikin damuwa mai tsanani babu kamar ya ita kullum sai tayi kuka, ita bata ga abin fushi da daukar gaba ba ta lura yana da hakuri sosai amma bai iya fushi ba dan haka sai ta yanke shawarar tunkararsa ta bashi hakuri idan ya hakura shikkenan idan bai hakura ba zata rabu dashi duk ranar da ya gaji ya sauko dan kanshi.............Yau da wuri ya shigo gidan dan goma ma ba tayi ba, sai da ta bari Hajja da Rashida sun bar palon tukkuna ta fito daga dakinta tayi kwalliya sosai sai 'kamshin turare take.
Murd'a kofar dakin tayi ta shiga da sallama a bakinta.....Babu kowa sai dai tana jin alamun motsi a toilet dinshi ta dan zauna gefan gadon tana bin dakin da kallo yaushe rabonta da shigowa tun ranar suna gashi yau kwananta talatin da bakwai da haihuwa saura kwana uku tayi ar'bain......Tana zaune tana sa'ke-sa'ke ya fito daga toilet d'in 'kungunsa daure da towel da karami a hannunsa.
Had'a ido sukayi tayi saurin sunkuyar da kanta gabanta na fad'uwa.....Kadaran kadahan ya kalleta ba tare da yace komai ba ya 'karasa bakin mirror ya dan tsaya yana sake


goge fuskarsa.....A sanyaye ta mi'ke ta isa inda yake tsaye ta 'karbi towel din hannunsa tana so ta goge masa jikinsa, sai kawai ya bar mata gurin, Ta bishi da kallon mamaki yaje ya nemi guri ya zauna gefan gado yana shafa vasillin a jikinsa, ba tayi zuciya ba ta isa inda yake a hankali ta sanya hannunta ta 'karbu vasilin d'in tana marairaicewa, Ya mi'ke kawai ya barta a gurin........Wardrobe ya nufa domin daukar jallabiyarsa, da gudu taje ta rungume faffad'an bayansa tana shashshekar kuka tace"Kayi hakuri kaji." Ajiyar zuciya ya sauke yana dan jin sassauci cikin zuciyarsa, shima dik abinda yake daurewa kawai yake yi yana dai so ya nuna mata kuranta ne, amma ba dan ya cuzguna mata ba, idan da ta kwantar da hankalinta shima ai yasan abinda yake yi ba zai ta'ba cutar da ita ba, amma ranar nan ya kwadaitu da ita mutu'ka ya kuma nemi ta a gaza masa ta'ki! dashi d'in manemin matane to babu shakka a ranar sai yaje ya biyawa kansa bukata amma haka ya hakura ya cireta daga cikin ranshi duk dan ya nuna mata kuskuranta


A nutse ya jiyo da ita suna fuskantar junansu, kasa hada ido tayi dashi ta sunkuyar da kanta 'kasa tana goge fuskarta, a hankali ya sanya hannunshi ya goge mata hawayen fuskarta ya tallafo fuskarta sosai cikin tafin hannuwansa ya kallonta.
Takasa d'aga kanta ta kalleshi saboda kunya da kuma tsabar kwarjin da Allah yayi masa.
Murya a kasa kasa yace."Me kikayi min kike bani hakuri."? Sai ta dago fuskarta tana kallonsa.


Ya sanya d'an yatsansa saman le'banta na 'kasa yana shafawa a hankali a hankali shi dai yana masifar son le'bunanta.


Kasa cewa tayi komai ta maida kanta 'kasa tasan yana sane yake tambayar ta yafi kowa sanin kan abinda yasa take bashi hakuri.
Murmushi yayi a hankali ya cika fuskarta ya juya ya dauko jallabiya cikin wardrobe yana fad'in "Ina momyna ko tayi bacci."? A hankali ta d'aga kanta tace" Yanzu nan na lalla'bata ta kwanta.....Hannunta ya ri'ke yace."Muje parlo yau ke zaki bani abinci a gajiye nake."


Taji dad'in yanda ya saki jikinsa sosai wannan ya sake tabbatar mata da cewar ya hakura da fushi da ita kuma ta lura dama kamar daurewa kawai yakeyi yana hakuri.


Ya zauna kan kujera yana dan dubawa babbar wayarshi yace."Ki had'o abincin ki kawo min nan zanci." Da sauri ta nufi daining din ta had'a mishi abincin komai da komai ta kawo gabanshi ta ajiye......'Kasa ya sauko hankalinsa na kan wayarshi yana dan juya abincin da cokali, sai ta kar'bi cokalin ta fara d'ebo abincin tana sa masa a bakinsa.......Kar'ba ya din gayi ba tare da ya kalleta ba hankalinsa gabakidaya yana kan wani text da Zeey tayi mishi.
Kafin ma ya gama karanta text din kiran wayarta ya shigo wayar tashi.
Dama tuntuni ya goge number ta cikin test dinta ma dan tasa sunanta ne ya ganeta.
Ganin numbarta tace ya sanya shi daga wayar a nutse yay sallama dake hands free ya bud'e Wasila najin muryar Zeey tana fada'in "Ranka ya dad'e barka da dare yau dai naci sa'a an d'auki wayata."
Gabanta ne ya shiga fad'uwa sai hannnta ya soma rawa tana kokarin sanya masa a bacin a baki cokalin ya su'buce daga hannunta abincin ya zube a jikinsa sa kasan gurin.
Dan dubanta yay yana dan gyarawa hankalinsa nakan maganar da zeey ke masa yace."Zainab ya kike ya gida ya kwana biyu."
Zeey tace"Alhamdullhi yallabai Wallahi kwanaki nayi ta kiran wayarka domin nayi maka Allah ya raya baka dauka ba nace to ko wani laifin nayi.'"?
Murmushi yay a hankali ya dan koma saman kujera yace." Ai ke bakya laifi Zainab mybe lokotan da kike kiran wayar ina da uziri ne shiyasa amma nagode kwarai kuma naji dadi da kulawarki."
Zeey tace"Ai har taron suna nazo sai dai ban dad'e ba na tafi domin a ranar ana bikin wata friend dina ne." Yace."Masha Allah kema ai yana da kyau ki futar da miji kiyi aure Zeey kin kwana biyu fa."
Zeey tayi dariya me shashshe'ka tace"Yalla'bai kenan aini da aure sai dai inga anayi namiji daya nake so a duniya amma ya'ki aurana."
Yasan inda maganarta ta dosa sai ya nuna bai gane komai ba, Yace."Zeey meye abunki? kina da ilimi sosai kana kina da kyau dai-dai gwargwado me kuma ake nema."?
Murmushin takaici Zeey tayi tace"Duk da ina da abubuwan da ka


fad'a yanzu to shi banyi masa ba."
Dariya yasa yana d'an sosa gemunsa yace."Haba dai sai kace makaho ni da ba dan nayi aure ba da kawai na shigo anyi dani." Zeey tayi wata dariya me shashsheka tana sake ma'kale murya tace"Ashe kasan inda maganata ta dosa tunda naga ka d'auko hanya, Yallabai ko yau kazo ni a shirye nake dama ai Ubangiji cewa yay kuyi Hud'u mutukar zakuyi adalci." Ya bud'e bakinsa zaiyi magana yaga ta jefar da cokalin hannunta ta mi'ke rai a 'bace ta bar gurun......Ya bita da kallo har ta bude daki ta shiga ta bugo kofar da karfin gaske.....sai kawai ya girgiza kansa ya cigaba da hira da Zeey inda take ta tsara masa kalamai ita dole sai ta samu shiga a gurinsa........Yace."Ki bari zan duba maganarki a tsanake zan kira ki a waya." Cike da farin ciki da jin dadi Zeey tace"Shikkenan Yallabai ina sauraranka." Kashe wayar yay ya ajiye ta kusa dashi ya gyara zamansa sosai ya cigaba da cin abincinsa.




Koda ta shiga dakin kwanciya tayi kan bed taci kukanta ta koshi ta kuma dauki al'kawarin yi masa rashin mutunci tunda dai shi bai san hakkin d'an adam ba in bansa wulakanci da rashin mutunci ya rasa ma a inda zaiyi hira da budurwarsa sai gidanshi kuma a gabanta lallai zata nuna masa cewar ta san abinda takeyi duk da take jahila to tasan ciwon kanta.




Sai da ya kammala cin abincinsa a tsanake tukkuna ya bita dakin, lokaci har tayi wanka ta kwanta tana bawa baby zahra nono ta tashi daga bacci, yazo ya tsaya kansu yana kallonsu, ganin yanda tayi bala'in shan kunu ne ya sanya ya kasa cewa da ita komai sai kawai ya tsuguna ya mannawa 'yarshi sumba a saman goshinta ya mi'ke ya fita daga d'akin.




Da 'kyar bacci ya dauketa saboda tsabar bakin ciki da takaici, ta tashi da safe cikin rashin walwala har Hajja ta shigo dakin suka gaisa ta shirya zahra har taso ta fahimci wani abu amma dai ba tace mata komai ba itama so take ta cika ar'bain ta tafi ai tayi abinda tayi, Hajja na fita da Zahra ita kuma ta shiga toilet domin yin nata wankan.
Kafin ta fara wankan sai da ta shiga cikin ruwan d'umi tayi minti goma sha biyar sannan ta fito tayi wankanta da sabulai masu kyau da kamshi ta fito daure da karamin towel iya cinyarta.........Ashe yana zaune a dakin ya shigo tana toliet sai ya zauna zaman jiran fitowarta.......Ganin ta a haka fatar jikinta na wani irin she'ki da sul'bi ga santala santalan cinyoyinta a waje dik sai ya rasa nutsuwarsa ya dinga binta da wani mayen kallo har ta wuceshi ta nufi mirror tana zum'buro bakinta tare da sauya salon tafiyarta.
Kasa daurewa yay ya mi'ke ya nufi inda take......Tana sane ta bude towel din wai zata sake d'aurawa aikuwa ya hangota ta madubi hankali a tashe yaje ya ri'ke towel din yana kokarin fuzgewa daga hannunta.
Ta dan tureshi kadan ta bar masa gurin......Matseta yay jikin wardorbe yana rarraba idanunsa a jikinta..........Ta dinga ture kirjinsa tana son yin kuka amma dai ta daure saboda bata so ya dinga raina mata hankali....."Wai dan Allah meye haka bafa girmanka bane hakan da kakeyi ka kyaleni ni nasa kayana, kuma gidan nan dole ne ma na barshi dan ba zan zauna a inda ba'a bukatar dangina ba.'' A kausashe take maganar tana tuttureshi daga jikinta
Muryarshi ba sosai take fita ba yace."Wace irin magana kikeyi ne waye baya kaunar dangin ki da har kike ikirarin barin gidan auranki."
Sai ta fashe da kuka tana wani irin bubbuga 'kafafunta ta tureshi da 'karfi tana haki ta matsa gefe tana kallonshi tace"Eh dama zaka fad'i haka mana yau kwanan Inna Hajara nawa da tafiya ka ta'ba tambayata dalilin tafiyar ta!? Sannan yau kwanana nawa da haihuwa me yasa baka ta'ba tunani koda sau d'aya ne kace bari ka tura d'aya daga cikin yaranka domin yaje ya dauko mahaifiyata kan tazo taga abinda na haifa, na sani dama tuntuni na san da cewar baka dauki Uwata a matsayin komai ba dan da ka dauketa da daraja to da duk inda take kaje ka gaisheta da kanka kuma ka shaida mata na haihu da abinda na haifa.....To nagaji ni ba shashasha bace nasan kuma inda ke min ciwo zanyi tafiyata in yaso sai ka auro wacce kake ganin Iyayenta sune dai-dai da kai da kimarka."
Tana gama maganarta ta bude wardorbe ta duba kayanta t


a dauki riga da sket na wani had'addan swiss less ta shirya jikinta duk yana tsaye kamar gunki

48 / 57