Author : Binta Umar Abbale Category : Romantic Books
yasa dai an samo wasu kudin.....Wasila ta cire hijab din jikinta ta ta shiga zazzage kudin da suke cikin jakarta......Uwani ta razana! ganin uban kudi gaban Wasila sun tassama dubu dari biyar! Sai kawai ta dora hannunta a saman hancinta ta dinga rangwada bud'a yi takeyi kamar zata tsine hancinta. Sai da tayi mai isarta sannan ta iso inda suke zaune Rashida sai faman irga kudin take tana ihu!!
" Kai jama'a! ashe dai zanga wannan rana ni Uwani, ashe idona zai ta'ba ganin irin wadannan uban kudade masu yawa lallai wannan sana'a tafi irin wacce nakw cewa kiyi 'yata Wasila ina alfaharin haifarki Allah yayi miki albarka Wasila." Uwani ta gigice sai sambatu takeyi Camas da Rashida sai dariya suke mata....Wasila kam mikewa tayi jikinta duk ya mutu duk sanda ta tuni artabunsu da *'Kumdum!* sai gabanta ya yanke ya fad'i shikkenan fa idan da da tsautsayi da karar kwana da tuni ta zama tarihi domin ta lura babu imani a cikin zuciyar dan daban ta wani gefan kuma guy nan ya taimake ta dan sai yanzu take nadamar zagin da tayi masa kuma ta lura ya gani ya kuma ji rashin dad'i, sosai abun yake dan ta'ba zuciyarta babban mutum ne da shekarunsa suka wuce tayi masa haka domin zuwanta gidanshi na farko bata tantance kamaninsa da shekarunsa ba sai ganin da tayi masa a dazu.....Ganin zuciyarta na damunta ya sanya ta tattara ta watsar da al'amarin babu wani abunda zai faru dan ta zageshi ai Siyasar 'kasa ce kowa yana da 'yancin yin abunda yake so ga wanda baya so....Wanka tayi ta fito ta tarar Camas ta tafi gida ta kalli Rashida dake zuba musu abinci tace"Idan anjima zamuje Sto muyi siyayya dukanin abunda bamu dashi walau naci dana sha da daurawa." Rashida tace"Shikkenan bari nima nayi wankan sai muci abinci mu tafi."
Uwani kam sai faman juya miya takeyi tana murmushi Ah!! Allah maiyin yanda akeso dare daya Allah kanyi bature Arziki ya sakko musu lallai babu abunda yafi haihuwa rana a duniya shiyasa masu karin magana ke cewa ko kana gudu haifi ka jefar ita dai gashi haihuwa tayi mata rana.
_Muje Zuwa_
*BINTA UMAR ABBALE*
[7/13, 10:52 PM] Bintu: *'YAR BANGAR SIYASA!!*
🌺 romantic love story🌺
*NA:*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*
*🌍Manazarta Writes asso*
_'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_
~~~~~~~~
*NA KUDI NE.......!*
_Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko orange_
*Free Pege 8*
Suna idar da sallahr magariba suka fito har Uwani domin tace itama zata bisu kasuwar suka sanyawa kofar gidan katon kwado kana suka fito titi domin samun abun hawa, suna tsayawa wani mai d'an sahu ya tsaya gabansu Wasila tace" Al'Ikilas zaka kaimu." Yace."An gama hajiya nawa zaku bayar."? A ya tsine tace"Muje dan Allah bana son harkar fatara ko nawa ne kudinka zan baka."
Me dan sahu yace."A'a hajiya daga magana karfa ki zageni dan wallahi kika zageni ba yarda zanyi ba." Rashida tace"Kai dan Allah muje kana jan duguwar magana ai laifinka ne meye na tambayar nawa zamu bayar mu ba mutsiyata bane." Yace."Bana son in dauke ku ne bamu daddale daku ba sai kunzo sauka ku kawo min kauli da ba'adi shiyasa nake so naji nawa ne kudina." Wasila taja tsaki! tana kokarin shiga babur dole ne ta siyi sutturu masu tsada saboda ta lura suma 'yan a dai-da ta basu da kirki daga sunga mace da kod'addiyar atamfa sai su hau wulakanci in kuwa suka ga mace da dankareran lesi da gwala gwalai har rubibin daukarta sukeyi saboda sun san ko nawa sukace ta basu zata basu.
Wasila har waya take so ta sauya sai dai kuma abun yayi yawa dole gobe ma su sake fita dan yau kayan kwalliya zasu siyo da atampopi da mayafai da takalma, har bakin super Sto din ya ajiyasu ta dauko dubu daya dal ta mika masa baiyi tsammanin haka daga gareta ba ya dauka zaiga ta fito da dukukkunanniyar dari biyu canji yake kokarin dauko mata tace''Rike na barka maka." Ya sako baki yana kallonsu sun juya suna tafiya, kai! ammafa yayi mamakin lamarin nan ashe arziki ne yake binsa yana basarwa duka kudinsa dari uku ne gashi ya tashi da dari bakwai sun isheshi karin kummalo da safe dan haka sai kawai ya nufi gida ya tashi daga aiki sai kuma gobe.
Su Wasila kuwa zagaye Store din suke suna so suga iyakarsa sun kasa babban store ne da sai wane da wane ke zuwa gurin duk abunda ke cikin gurin ba na yarwa komai kudi ne Wasila suka dauki atampopi kusan kala bakwai suka d'ibi lesuka da mayafai sannan suka nufi gurin kayan make up nan ma ta dinga hada kayan kwalliya so take ta dawo babbar mace ta dinga cin kwalliya dama can ita bata yarda da karamar shiga ba, Can bagaran turirrika ta nufa su Uwani da Rashida suka tsaya gurin gwala-gwala sai 'kyauyanci sukeyi..........Yana kai hannunsa kan wani kwallin turare itama ta kai nata hannun ya sauka akan nashi.
Da sauri ta dauke hannunta tana kallon zatinsa gaggausa mutum ta gani tsaye a kanta yayi mata rumfa kasancewar ta mace mara tsayi sosai.....Sai ta daga kanta tana kallon fuskarta a lokaci guda taji wani irin miyau! ya tsinke mata a baki ganin wanda yake tsaye kusa da ita. *Ahamdu* Da sauri tayi 'kasa da kanta tana adduar Allah yasa bai gane ta....'Kokarin wucewa takeyi taji yo muryarshi na fad'in"Zo ki dauki turaranki na samu wani." Gaba tayi ba tare da ta amsa masa ba, suka hadu da Garba wanda yake kokarin isa inda ubangidansa ke tsaye.....Sarai! Garba ya ganeta sosai dan har waiwayenta yakeyi Ahamdu yace."Kai! kula dallah! kallon me kakeyi ne."
Da sauri yacs."Sir baka gane waccan yarinyar ba."? Tsaki yaja yana d'an ya tsine fuska yace."Meye ya dame ni da ita da zan tsaya tantance wacece."? Garba yace."Sorry sir yarinyar nan ce fa ta d'azu." Ya zare gilashin dake fuskarshi yana kallon Garba da mamaki yace."Da gaske."? Garba yace."Wallahi itace sir wai baka gane yanayinta bane ai naga a furgice ta bar gurin nan."
Murmushi yayi kawai ya mai da gilashinsa, ashe ita ta ganeshi shiyasa tayi gaggawar barin gurin yanzu ya gane Jagaliyarta ta 'karya ce tunda bata iya tsayuwa a gabanshi ta mai da masa da martani....
Suna tsaye a gurin biyan kud'i ya 'karaso gurin sai taga ana bashi girma duk ma'aikatan gurin na kiranshi da Sir tayi 'kasa da kanta tana jinsa na magana cikin had'addan turancinsa da babu tangarda a ciki duk sai ta raina kanta gaskiya ilimi yayi addua takeyi Allah yasa kar ya waiwayo ya kallesu..........Ya kalli Manager gurin da Hausa yace."Cikin wannan satin Salim zaije saudia wani na'uin turare da babu a gurin nan sa ka rubuta masa gudun mantuwa.''
Yace."Insha Allahu." Wucewa yayi ba tare da yayi kuskuran kallon inda suke tsaye ba, suna fita Uwani tace"Oh wannan turanci sai kace wani ba amuruke da alama dai shine shugaban gurin.....Manager da ba hausa yake ji sosai ba ya d'aga mata kai alamar Eh......Rashida tace"Gaskiya aunty Wasila mutumin nan yayi wallahi kun dace dake dashi dama yace yana sonki." Wata harara ta watsa mata "Dallah kwaso kayayyakin mu wuce kin tsaya kina shashanci dare yayi." Rashida ta dauki manya manya ledoji guda biyu Uwani ma ta dauka itama ta dauka haka suka fita hannunsu ni'ki ni'ki da kaya su ba mota ba, sai da suka fito ne ma suka fahimci dare yayi sosai dan goma ma ta gota.....Da kyar! suka samu mai babur ganinsu da kaya ya sanya ya lafta musu kudi wai dubu biyu Wasila tace"Muje zan baka." aikuwa da sauri yaja babur din suka dauki hanya.
Sai da suka zo dai-dai titin makarantar legal tayar a dai-dai tar tayi faci!!! Tofa ga dare gashi babu masu faci a kurkusa ga gurin tsit! sai kukan tsintsaye....Uwani ta fito tana salati da sallami motocin gida jefi jefi ne suke wucewa suma kuma da gudu suke wucewa saboda sun samu arhar titi babu go solow, Wasila ta fito daga babur din tana fad'in"Yanzu ya za'ayi? kai innalilihi gaskiya banji dad'i ba wallahi." Mai babur yace."Ni wallahi na rasa ma ya zanyi dana sani nake wallahi dan idan ban samu wanda zaiyi min faci ba dole in bar babur din a gurin.......Wasila tace"To mu kuma muyi yaya kenan."? Yace."Hajiya dan Allah ki kyaleni naji da abunda ya dame ni ai kuna da kafafu ku karasa mana a kafa."
Rashida tace"Ka duba tazarar dake tsakanin nan da dorayi fa akwai sauran tafiya gaskiya mu dai kasan yanda zakayi damu."
Haushi yasa mai babur din fad'in"Ai sai ku kwana a gurin ni kunga tafiya ta." Ya zare key dinsa daga jikin babur din ya dauki hanya ya barsu a tsaye a gurin.......Sai da suka daina hangoshi sannan suka tabbatar da cewar da gaske ya tafi din Wasila tace"Ai sai ku dauki kayan muma mu daura damarar tafiya da kafafunmu dan babu wani alamun babur a kan titin nan."
Suka d'addauki ledoji suka saici hanya suna tafiya fakam fakam! ga nauyin kaya ga gajiya sunyi masifar galabaita......Sunyi nisa d a tafiya sosai suka hango ana haske su da touch Dukaninsu sun razana! ganin wasu tsagerun matasa sun durfafo inda suke "Kai! matanan daga ina kuke ne."? Uwani tace" Ku bamu hanya mu wuce munyi dare zamu koma gid.....ai kafin ta rufe bakinta na kusa da ita ya wafci ledar hannunta yana zazzagewa.....Wasila tace"Kai meye haka kuk.....Ita taji ya fizgo jakarta dake rataye a kafad'a ya zazzage a kasa uban kudi suka watse a gurin....Ihu!! suka zumduma! suna fad'in Kai!! ashe yau mun fito a sa'a Kwashe mana su mana jeka bunciki jikinsu kaga ko da akwai sauran wasu idan da gold a jikinsu ka ciro." Babban cikinsu ne ke wannan maganar....."Kar ka kuskura ka ta'bani wallahi hannunka ya sauka a jikina sai nayi maka illah."!! kamar mahaukaciya take maganar....babban cikinsu ya taso yana haskata da touch "Wow!! yafada yana lasar le'be." Baby wannan jikinki naki ai bana banza bane ke kanki kin san sai an mora da har kike maganar zakiyi wa yarona illah to kafin kiyi masa ni bari nayi fara miki."
Yana kai hannunsa jikinta ta gaura masa wani lafiyyan mari!!!! Ya kurma wani ihu! "Ni kika mara!? kanta yayi ta goce a guje tayi kan titi yabi ta hijab dinta ya take da kafafunsa tayi dubarar zare hijab din ta mike a sukwane ta sake ranta a na kare gashin kanta duk ya warware ya zubo mata a fuska da kafada......... tana tsallaka titi taga haske fitilar mota ta doso, tun kafin ta karaso take daga hannunta sama......Yace." Garba rage gudun motar nan babu lafiya waccan kamar yarinya mace Allah yasa ba fyade za'ayi mata ba." Garba yace."Ai kuwa sir ga dukanin alamu hakad'in n.... ai kafin Garba ya rufe baki Goga ya iske inda Wasila take suka hargitse da kokawa......Da sauri yace."Subahannahi Garba kashe mota." Garba ya kashe mota da sauri ya bude motar ya fito wanda yayi dai-dai da lokacin da Wasila ta samu nasarar kwatar kanta daga Hannun Goga, a jigace! ta iske! inda yake tsaye ta afka kansa ba tare da ta sani ba, yayi saurin dafe bayanta da hannunshi guda yana kallon Goga ya dumfaro gurin......Yana isowa ya kai masa 'kwakkwaran naushi! da hannunsa guda ba tare da 'bata lokaci ba Goga ya zube a gurin hancinsa na zubar da jini
*'YAR BANGAR SIYASA!!*
🌺 romantic love story🌺
*NA:*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*
*🌍Manazarta Writes asso*
_'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_
~~~~~~~~
*NA KUDI NE.......!*
_Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko orange_
*Free Pege 9*
Yaran Goga na hango ogansu a kwance a 'kas yana matagugu! sai suka ranta a ana kare ko wannesu na neman mafaka a tunaninsu jami'an tsaro ne sukayi basaja, a gurin......Uwani da Rashida suka iso gurin hankalinsu a tashe Uwani fadi take"Shegu tsinannu 'yan iska kawai mu samu kudinmu da 'kyar! su biyo dare su 'kwace ai gaskiya 'barawo baiyi ba."
Ahamad ya d'an ja jikinsa kadan ganin ta daina rawar jikin da takeyi ya dan tsira mata ido fuskatara na kallon 'kasa ta kasa dago kanta har yanzu da akwai furgice a tare da ita sosai ta tsorata da goga a duniya babu abunda takeji dashi kamar budurcinta
Rashida ta 'karaso inda take tsaye tana mika mata hijab dinta ta kar'ba ta zura Uwani tace"Amma dai babu abunda yayi miki ko." Daga kai kawai tayi tana goge fuskarta 'kamshin turaran da mutumin yake yi shine ya dabbeta tana ji kuma kamar tasan me irinshi
Muryarsa ce ta daki dodon kunnata wanda yasa tayi saurin dagowa sai taga ya juya yana tafiya bayanshi kawai ta kalla ta gane shi! *Ahamdu* ne Garba yace."Yallabai yace."Ku shigo motar sai mu aje ku a gida amma yana da kyau ku daina tafiya irin wannan ku kai dare kasancewarku mata akwai 'bata gari a ko ina zasu cutar daku."
Wasila ta dago kanta tana kallon Garba ya kalleta da mamaki! sai yanzu ya ganesu sune ashe!? to anya ma kuwa Yallabai din ya gane su.....Uwani ta hau daukar kaya ta nufi motar Garba yace."dan dakata tukkuna." Motar ya nufa ya tarar dashi a kishingide idanunsa a lumshe wata iriyar kasala ce ta dabaibaye shi sakamakon rungumar da yarinyar tayi masa duk ta gwaggoga nasa nonowanta a kirjinsa tsigar jikinsa sai wani irin mikewa takeyi sanyi sanyi ma yake ji burinsa ya isa gida ya kwanta ko samu sauki......"Sir." Garba ya kira sunanshi yana runkufar da kansa ya bude lumsassun idanunsa yana kallonsa yace." Shin ka gane ta kuwa? naji kace su shigo mota yarinyar nan ce fa mara kunya wacce ta zage ka dazu gurin kamfen." Ya tsirawa Garba ido yana kallonshi da mamaki a tare dashi.....Garba yace."ai da kana gurin kasa dago fuska tayi saboda itama tasan bata kyauta sai bayan ka bar gurin ne ta dago fuskarta nan na ganeta.......Jim! na minti biyu kafin yace."Kyaleta kawai shigo dasu muje dare nayi taci albarkacin abokanan tafiyarta."
Garba baiyi tsammanin hakaba saboda yasan halin Ogan nashi baya barin bashi babu shakka yarinyar nan na samu dama a gurinshi..........Wasila kam masifa ta hau yiwa su Uwani wai lallai sai sun shiga motar tunda Allah yasa zai tamaike su ita kuma kunya tasa tace dole su dauki kayansu su karasa da kafa ai sun kusa isa gida babu yanda zasuyi da ita suka dauki ledojin suka hau tafiya fakam! fakam!!! Garba ya cimmusu yana fad'in"Yallabai yace."Ku shigo muje ku kawo kayan." Ya hau kar'bar na hannun Rashida ta sakar masa dan dama ita ta riga ta gaji tsoron masifar wasila takeji Uwani ta kalli Wasila dake cigaba da tafiya tace"Haba Wasila ki tsaya mana a taimaka mana kinsan fa kafin muje gida mun galabaita gashi kin san inada ciwon kirji idan ya tayar min kamar zan mutu.
Tace"Tunda dai kun nace sai mun shiga muje amma meye saura anan mun kusa zuwa 'yan babura fa." Rashida tace"Eh duk da haka dai aunty Wasila ai ragi ragi ne." Shiru tayi musu suka kawai tabi bayansu a zahirin gaskiya bata son shiga motar dan dai kawai sun nace ne! Yana hango zuwansu gurin ya fito daga bayan motar ya bude gaban motar ya zauna gilashinsa ya gyara, ya tamke fuskarsa yayi dakacen hada jiki da ita ko da yake ai itace ta rungumeshi........Yana da tausayi sosai mussaman kan 'yaya mata shine dalilin ma da ya sanya ya tsaya amma da yasan yarinyar nan ce mara kunya babu abinda zai sanya ya tsaya ya 'bata lokacinsa Hanyar biri daban ta mota daban.
Suna shiga motar sanyi Ac da kamshi ya bakunce su, Uwani ce a farko sai Rashida Wasila ta zama karshen shiga motar sai dauke kai takeyi bata so su hada ido dashi gashi sun zauna a site daya tana kallon fuskarshi ta mirror ya hade rai! sai itama ta hade nata ran! tayi kasa da kanta, ita sam wannan taimakon baiyi mata ba saboda babban abun kunya ne guy nan yaje yaga makwancinta duk da haka dai ba zata bari su shiga ciki ba a bakin titi zasu sauka.
Jin surutun da su Rashida yayi yawa yana nema ya karasa wata damuwar bayan wacce yake ciki......Sai ya sanya hannunshi ya kunna redio karatun alkur'ani ya soma a tashi daga bakin *Ahamd Sulaiman* Duk da haka dai su Uwani basuyi shiru ba sai surutu suke suna ta zancan 'barayin da suka tare su.
Gyaran murya yayi sai suka yi shiru suna kallonsa....Wasila ta dan ja tsaki kadan tace"Dan Allah kuyi shiru idan munje gida kwayi maganar haba."
Shiru sukayi basu sake cewa komai ba motar ta cigaba da tafiya.
A hankali ya dago idanunsa dake sakaye da gilas yana kare mata kallo ko da wasa baza kace ita yake kallo ba saboda yanda yake wani basarwa.......Yarinyar nada kyau! sosai sai dai bata da kunya ko kad'an! shi kuwa baya shiri da mara kunya marasa ganin girman na gaba dashi.
Dai-dai bakin titin 'yan babura Wasila tace"Ajiye mu anan ba sai ka shiga damu zamu karasa da kafafunmu.
Uwani tace"Haba 'yar nan ki bari mana a karasa damu mana mutumin nan fa taimakon yake yi kar ki katse masa hanzari." Dan Allah aunty Wasila ki bari a karasa damu." Rashida ta fadi maganar tana karyar da kai.....Sai magiya take mata kamar zatayi kuka."
Yace."Garba shiga da motar nan ka kaisu har kofar gidansu kar ka dakata maganar ta." Yace."Angama Yallaba.'!
Uwani tace"Mungode sosai Allah yayi albarka alhaji Allah yasa a gama lafiya, Allah ya raya zuria." Ya amsa da "ameen." yana duba wayarshi....Wasila kam! sai shan kunu takeyi sam bata so haka ba dan dai kawai