Author : Binta Umar Abbale Category : Romantic Books
hankali bakinshi na motsawa da alama addua yake yi a nutse ya tofe musu jikinsu bakid'aya kana ya ja bargon sosai jikinsu ya rufe idanunsa yana adduar Allah ya taimakeshi bacci mai nauyi ya daukeshi, cikin ikon Allah kuwa baccin ya daukeshi, kuma baccin da ya jima baiyi Irinshi ba.
Wajejen karfe hud'u shaura na asubah ta farka da wata matsananciyar yunwa, jiki na kyarma tayi yunkurin mi'kewa, yay gaggawar rike ta idanunsa ya bude ke kyace dama ba bacci yake yi ba, Amadu bashi da nauyin bacci ko kad'an, a hankali yace."Menene."? Shiru tayi tana mutsika idanunta, sai ya mi'ke zaune yana me cire bargon dake jikinsu ya sanya hannunsa guda a jikinta ya shafa wuyanta, babu alamun zazzabi a jikinta, Yace."Menene? ko zakiyi wani uzirin ne? muryarta na rawa tace"Yunwa nakeji." Yace."Yunwa."? Daga kanta taji hawaye na kokarin zubo mata, Yace."Dama baki ci abinci ba kika kwanta."? "Naci dama duk dare ina tashi naci abinci." Ya shiga girgiza kanshi a hankali ya mike ya sauka daga bed din ya fita daga dakin
Kicin ya nufa yayi dube duben shi babu abinci sai kawai ya jona kettle ya dora ruwan tea yana tsaye yayi ya juye mata a cup ya nufi dakin dashi, lokacin ta fito daga toilet daure da alwala dan an soma kiran sallah." Ya aje tae din kam bedside yana fad'in "Ga tea nan babu abinci a kicin din wallahi." Zumbura bakinta tayi ita me zatayi da wani tea banda ya sata jin wata yunwar, Fita tayi daga dakin Yabi bayanta kicin ta nufa, ya tsaya bakin kofar kicin yana fad'in "Ki koma ki kwanta bari na tashi hajja sai ta sarrafa miki wani abun." Girgiza kanta tayi tace"Kawai tana baccinta sai a tasheta tayi girki nima zan iya." Shiru yay yana kallonta tana kunna gass cocar, Shi da kansa yayi alkawarin daukar dukanin laluranta baiyi tsammanin harda shiga kicin ba, a lokacin da suke tare a can baya bai santa da wannan cin abincin ba yanzu dai yafi tunanin cikin da take dauke dashi ne ya sanya ta, kicin din ya shiga ya kar'be tukunyar hannunta wai zai d'ora mata abincin......Tausayi ya bata ta kar'bi tukunyar taje ta zuba ruwa ta tazo ta dora tukunyar gefanta ta bude taga lafiyayyar miya wacce taji nama zu'ku zu'ku.....Sai kawai ta bud'e sto ta dauko supargetti guda d'aya, yay daurin kar'bar taliyar a hannunta, ta rike tana girgiza mishi kai tace"Ka barshi zan dafa babu wuya fa." Ya d'an tsira mata idanunsa itama shi take kallo tana sake jin wani irin yanayi a jikinta gaskiya ta lura ya mato akan sonta, da girmanshi da komai ya dinga biye mata da dukanin abinda take so.....Yace."Kin tabbata zaki iya." Daga kanta tayi yace."Okey bari nayi wanka da alwala na wuce masjid.'" ya wuce ta bishi da kallo tausayi tausayinsa take ji a cikin ranta.
Tana tsaye taliyar tayi ta tsaneta kana ta juye cikin fulas ta dauka ta nufi daki dashi, lokacin har yayi wanka ya sanja jallabiya hannunsa rike da cazbaha, sai kamshi yake ta matsa mishi hanya shi kuma ya fita ba tare da wani yace da dan uwanshi komai ba.
Kicin din ta koma ta dauko plate sannan ta samu wani abu ta zuba miyar a ciki ta dawo dakin ta zauna kasan kafet a nutse ta zuba abincin ta soma ci sai da taci ta koshi sannan tayi sallah ta koma ta kwanta, bacci na fizgarta taji shigowarshi.......Ta bud'e idonta a hankali tana kallonshi lokacin da yake kokarin karasowa kusa da ita......Zama yayi gefanta a nutse yace."Tashi zamuyi magana." Ganin babu wasa a tare dashi yasa ta mike xaune tana wasa da hannunta.....Cikin kulawa ya kalleta yace"babu gaisuwa ko."? Ta dan kalleshi da gefan ido sai taga ya tsirawa jikinta ido, kanta ta sunkuyar a hankali tace "Ina kwana." Ya amsa da sakakkiyar fuska kana yace."Ya kwanan boy." Shiru tayi yace."Kamata yayi ma kafin mu fara magana na fara gaisawa dashi." ba tace masa komai ba, dan janyota jikinsa yana laluben jikinta, hannunsa ya d'ora saman mararta yana shafawa, ta dinga jin hucin numfashinsa a fuskarta, rintse ido tayi gabanta na faduwa tsigar jikinta na tashi, ya d'ora bakinshi saman goshinta tare da fad'in "Allah yayi miki albarka." Ta bude idanunta dake rufe tana kallonshi, mikar da ita yayi zaune yace"Yanzu hankalina ya kwanta na duba yarona yana da kyau ma muje kuga Dr insha Allah." Ba tace komai ba tana dai kokarin gyara rigarta, sai da ya tabbatar ta samu nutsuwa kana ya kalleta a nitse yace."Wane guri kika tsaya a karatun ki na al'kur'ani da hadisai nasan dai kinje isilamiyya ko.'? Taji gabanta ya fad'i! ta kalleshi idanunta na kokarin kawo ruwa, ina suka ga gatan da zasuyi karatu....Shiru tayi masa tana wasa da yatsun hannunta, Yace."Koda yake dai yanzu ku kin fad'a min ga inda kika tsaya bai da amfani tunda dai ba tilawa kikeyi ba, yanzu ki shirya ko ince ku shirya keda kanwarki insha Allahu kullum da asubah zamu dinga zaman karatu dani daku zamu fara tun daga fatiha da izinin Allah zamu sauke al'kur'ani mai girma mutukar kun bani had'in kai! Idan kin san ba'ki kin iya karatun al'kurani da sauran litattafan addini insha Allahu karatun nasara (boko) ba zai miki wuya ba zan d'anko muku mai muku lesson kafin ki haihu sai ku koma makaranta ko bakya so."? Yafada yana kallonta cike da kulawa......Hawaye ta share murya na rawa tace"Ina so mungode." Yace." Kin kammala secondary skul ko." ? Shiru tayi kunya duk ta isheta, ya sake maimaita tambayarshi, da kyar tace "Tunda muka fad'i jarrabawa muka daina zuwa." Yace."Okey duk ba wani abun bane insha Allah zakiyi karatu mutukar kin mai da hankalin ki ni kuma zan tsaya miki da yardar Allah." Hawaye taji sun zubo mata a fuskarta, tace"Mungode Allah ya saka da alkairi." Sai ta fashe da kuka harda shashsheka, rungumeta yayi sosai yana rarrashinta tare da shafa kanta, tayi luf a jikinshi tana sauke ajiyar zuciya.....Ya dago ta daga jikinshi yana goge hawayen fuskarata yace."Ki rabu da wannan 'kawar taki wacece sunana? bata da kirki duk wani lalacewa da rayuwarku tayi da ita da kuma rashin gata wanda baku dashi amma insha Allahu nine zan zama gatan ku in dai zaki zauna dani da tsarkakkiyar zuciya abinda ya faru a baya ya wuce a gurina na yafe miki insha Allah Allah ya yafe mana gabad'aya." Hannunsa cikin nata tace"Dama tuntuni mun rabu da Camas! nagane ita ke zugani ina yin wasu abubuwan marasa kyau tunda abun nan ya sameni ta gujeni ta gudu da kudina kusan miliyan biyar har yanzu ban san ina take ba."
Yace."Duk abinda kikace ta aikata miki zata iya domin nima na nemi taimako a gurinta lokacin da muke neman ku kafin kuje gurin mai allo, yarinyar ta'ki ta bani cikakken bayani 'karshe ma sai ta daina d'aga waya ta idan na kira." Girgiza kanta ta shigayi tana mamakin halin dan adam ko a mafarki idan ance mata Camas za tayi mata haka ba zata yarda ba sai gashi babu shakka mutum abin tsoro ne.
Yace."Je ki kira Rashidan mu fara zaman karatun yanzu." A hankali ta sauka daga bed din ta fita daga dakin, Ya dauke idonsa bayan fitar ta yana girgiza kanshi, yana jin zai iya sadaukar da farin cikinsa da duk wani jin dadinsa mutukar yarinyar zata samu walwala da farin ciki.
Lokacin da ta shiga
dakin, Hajja na zaune kan dadduma da carbi a hannunta ita kuma rashida ta idar da sallah tana kwance kan daddumar bacci na kokarin dauketa.......Ta samu guri ta zauna a nutse suka gaisa da Hajja tana tambayarta jikinta, Tace jiki da sauki alhamdullihi." Rashida ta mike tana mutsika idanunta suka gaisa tace"Kizo zamuyi karatu." rashida ta mike tare da zura hijab dinta suka fita daga dakin, hajja kuwa ido tabisu dashi haka kawai take tausayawa yaran.
Palo suka taddashi zaune kan katuwar dadduma gabanshi da al'kur'anai da kuma sauran litattafan addini........Ya bawa ko wacce al'kur'ani guda d'aya ya umarce su bude 'kasa, zasu fara daga fatiha ne.
Ko wacce ta bude nata a nutse yayi bisimillah ya soma karatu cikin nutsuwa da 'kira'arshi mai kyau da dad'in saurare, nutsuwa sukayi sosai suna saurarashi, sai da ya maimaita musu fatiha da fala'ki da nasi sau uku sannan yace su karanta masa yaji." A tare sukayi bisimillah suka soma karatun cikin nutsuwa, ya dinga sauraransu har suka kammala, yaji dadi sosai yanda ya biya musu haka sukayi, yace su rufe alkur'ani suka, Ya dauki littafin ahlari yana dubawa, a nutse ya soma karanto musu yana musu bayani dalla dalla bayanin jinin haila da hukunce hukuncensa bayanin janaba itama da hukuncinta shuru sukayi suna sauraranshi, dan wani gurin idan ya fada kunya ce take rufesu sai suka lura shi bai damu ba karatunsa yake yana so su fahimci abunda yake so su fahinta, bayan sun kammala karatun sai ya sallami Rashida ya mai da hankalinshi kan Wasila tana zaune jikinta duk yayi sanyi bata ta'ba tsammanin yana da ilimi irin hakaba sai taji ya sake yi mata wani kwarjini a idonta, A nutse yace" Wasila meye banbanci a cikin wankan haila da janaba niyya iri d'aya ake ko kuma ta bambamta."?
Ta dan kalleshi a nutse tace"Akwai bambamci mana." Yace."Kiyi min bayani sosai." Tace"Niyyar wankan haila daban niyyar wankan janaba daban amma duk wankan iri d'aya ne." Yace."Meye janabar meye kuma haila."? d'an tura baki tayi tana mi'ke kafafunta ita tagaji da wannan tambayoyin yace."Idan baki min bayani ba zan dauka baki da ganewa da saurin fahimta."
Tace"Janaba itace "Kamar mutum yayi rayuwar aure da mijinshi to janaba ta hau kanshi sai yayi wanka wanda ya zama farillah kamar yanda annabi ya koya mana."
Yace."Na gamsu da wasu bayanan naki sai dai kuma har yanzu baki fayyace min meye janaba ba da yanda zan fahimta kince rayuwar aure ni dake yanzu haka rayuwar aure mukeyi ina so ki fahintar dani shin rayuwar aure wace iri? Kamar zata fashe da kuka tace"Kamar yaya."? Yayi murmushi yana kallonta a nutse yace."Kamar yanda nayi miki bayani." shuru tayi mishi yace."Nasan rashida ta fiki gane karatu bari na kirata tayi miki bayani kuma mutukar tayi miki bayani abinda nake so ku fahimta sai nayi miki bulala! ita kuma nayi mata kyauta.'' mi'kewa yake kokarin yi ta rikeshi tana kuka "Ni wane bayani zanyi to bayan nayi maka bayanin abinda na fahinta! Ni kar ka kira rashida me ta sani a cikin abinda kake fad'a ai har gwara ni nafi ta fahinta." Ya koma ya zauna yana dariya, yace."Ai saboda nasan kin fita fahintar ne yasa na sallameta ke nace ki zauna kiyi min bayani, to gashi kin kasa min bayani gamshashshe wanda zai sa na gamsu."
Hawaye ta share tana zumbura baki, gashi ta rirrike masa riga kusan ma rabin jikinta duk yana jikinsa, Cikin kasalalliyar murya yace."Tashi muje ciki ni nayi miki bayanin yanda abin yake, in yaso bayan na gama sai ki fahimci yanda janaba take a kan mutum." Shuru tayi tana sauke ajiyar zuciya, ya dan janyeta daga jikinsa yana kokarin mikewa ta rikeshi! ita bata so ya kira Rashida ai abin kunya ne ma ya tambayi rashida yanda janaba take! Shima dama wasa yake yi......Yace." bakya jin kunyar wani ya fito ya ganki haka kina kuka kamar kankanuwar yarinya."? Tace"Dan Allah kada ka kira Rashida wallahi na fahimta." Yace."Nima da wasa nakeyi ai, ai nace muje d'aki na nuna miki ko." Sauka tayi daga jikinsa ta koma gefe guda tana ya mutsa fuska......Girgiza kanshi yay ya mi'ke a nutse yana fad'in "Kinbi kin nukurkusa min jikina yana tsami! kizo kiyi min tausa." Kallonshi tayi kawai ya wuce bedroom dinshi Yana shiga ya cire jallabiyar jikinshi ya kwanta bed yana rintse idanunshi, da so samu ne ya samu ko dan romantic ne ya samu yayi to amma sam baya son takurawa yarinyar zai dai cigaba da daurewa Allah yasa zai iya............Bacci me nauyi ya daukeshi ita kuma ta zauna a palon saboda tana jin tsoro ta shiga dakin yayi mata wani abun, Hajja da rashida suka fito daga dakin.........Dai-dai da lokacin da Rabe ke shirya musu daninng, Wasila na kallonsu suka nufi daninng din tayi zamanta a inda take har suka kammala suka isketa Hajja tace"Lafiya baki karya ba ko bakijin dadi ne."? Tace"Hajja kafin asubah naci abinci bana jin yunwa yanzu sai zuwa anjima nasan zan nemi abinci." Hajja tace" To shikkenan ki dai dunga ci kina koshi domin ki samu kuzari da kwarin jiki duk da nagani baki wasa da cin abinci." Rashida tace"Ai hajja wannan baby nasan kato ne anti wasila fa kullum cikin cin abinci take babu dare babu rana." Hajja tasa dariya tana fad'in "Ai lafiyace ta jawo haka ana so mai ciki ta dinga cin abinci sai kiga ta haifi yaro lafiyayye mai ban sha'awa." Wasila dai murmushi tayi kunyar hajja take, sai ma ta mike ta nufi daki tana murmushi ita kanta tasan dolene ta haifi katon d'a dan ganin irin abincin da take narka sai kace jaka.......Kusa dashi taje ta kwanta a hankali ta d'ora kanta kan kirjinsa tana lumshe idanunta, sai taji saukar hannunsa a bayanta, tayi yunkurin mikewa ya riketa sosai! idanunsa a rufe! sai tayi luf a jikinsa tana sauke numfashi, jin baiyi mata komai ba yasa ta saki jikinta sosai bacci ya dauketa a jikinshi.
Littafin na kudi ne!
Kika futar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya ba kema keda Allah Whasap numbar
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*alliya:
'Yr Bngr Sys
*67*
To haka rayuwarsu ta cigaba da tafiya cikin kwanciyar hankali gami da samun nutsuwa, sosai Amadu ke kula da Wasila ita da abinda ke cikinta, sunje asibiti likita ya tabbatar mishi da lafiyarta data yaronshi, yanzu itama ta saki jikinta sosai dashi tana zama suyi hira sosai in yana gida kuwa ta dinga kwanciya kenan a jikinshi daga tace wannan sai tace wancan Hajja da Rashida suyi ta kallon drama dan wataran ma idan sukayi wani abun hajja barin gurin takeyi, Rashida ma tayi ta jin kunyarshi tana mamakin yanda yayarta ta samu sake a gurinshi take zuba sangarta gami da shagwaba iya yanda take so shi kuma yana biye mata.......Idan suka zo zaman karatu da asuba ma sai sun gama rungume rungumensu kafin Rashida ta fito, dan wani sa'in idan wasilan ta rikitashi baya iya yi musu karatu me tsayi zaije ya kwanta yace sa had'u da daddare, to ka yaje ya kwanta haka zata bishi ta nan'ika da jikinshi, dole sai ya marmatsata sannan hankalinsu ke kwanciya ita dashi, akwai ranar da yaso ya sadu da ita ta hanashi, gashi ya kai 'kolulowa gurin bukata idonsa jawur ya fita daga d'akin, tayi kwance a bed tana hawaye, ita tsoronta Allah tsoranta annabi kar garin jin dad'insu yaronsu ya samu matsala, shiyasa bata so yace dole sai yayi sex kawai dai su tsaya iya romantic din har Allah yasa ta haihu........Ranar fushi yayi da ita ya shirya yayi ficewarsa harkokinshi, sai bayan tara da rabi na dare ya shigo gidan lokacin ita da Rashida ne a palon zaune suna kallon wani india film Rashida tayi mishi barka da zuwa ya amsa cike da kulawa yana tambayarta hajja tace"Taje ta kwanta.....bedroom dinshi ya nufa, yana jiyo muryarta nayi mishi sannu da zuwa, ya'ki amsawa, ta mike a hankali dan cikin nata ya fito sosai yanzu zama take da 'kyar ta mike da kyar tunda yanzu cikin ya kai watanni bakwai, bayanshi tabi wanda tana murd'a kofar dakin taji a rufe, ta tabbata key ya sanya, jikinta a sanyaye ta dawo ta zauna kusa da 'yar uwarta idanunta na kawo ruwa, wannan alamun da ya nuna ya nuna mata fushi yake da ita.....Rashida tace"Anti Wasila akwai abinda ke faruwa tsakaninki da Mijinki dan naga alamu tun a gurin karatu." Tace"Wane alamu kika gani.'? Tace"Yanzu fa ya shigo Kinyi mishi sannu be amsa ba, anti Wasila Allah kina 'kure hakurin mutumin nan sai bashi wuya kike nasan laifin naki ne wallahi." Cike da mamaki take kallonta tace"Har kike rantsewa laifina ne."? Rashida tace"Eh mana ni dai tsayin wata biyu da nayi a gidan nan banga abinda mutumin nan yayi miki na 'bacin rai ba kullum.cikin kyautata miki yake yi yana rarrashinki da kula dake, kinga kuwa dole nace laifinki ne." Shiru tayi tana nazarin maganar 'yar uwartata, babu shakka tsayin wata biyu da sukayi a gidan idan tace ga laifinsa tayi masa sharri kullum cikin tattashinta yake watarana ma abinci shike bata a baki, ta haye jikinsa tayi ta nu'kur'kusa bai ta'ba gajiyawa ba, tabbas laifi daga gurinta yake,
Ta kalli rashida a nutse tace"Nasan dai ke me hankali ce rashida idan na fad'a miki dalilin da ya saka yake fushi dani zaki daina ganin laifina, a gabanki komai ya faru kuma a gabanki likita ta gindaya min sharad'ai, kinfi kowa sanin irin 'bakar wuyar da nasha kafin wannan cikin na jikina ya zauna, duk wani 'kokari inayi masa domin na biya mishi bukatarshi duk hakan bai isheshi ba dole sai ya kwanta dani ni kuma ina tsoron wani abun ya faru dani da yaron dana ke dauke dashi a mahaifata." Rashida tace"Lallai anti Wasila dama saboda wannan matsalar ne yasa kike ta bashi wahala, gaskiya kin zalince shi wallahi ai itama likitan ba tace kar ayi ba cewa tayi a dinga d'aga 'kafa, tun a lokacin da cikin yake 'karami take wannan maganar to yanzu kuma ya girma ni ina ganin babu abinda zai same ki da yaron dake cikin ki kawai dai dan kin kasa kwantar da hankalinki ne yasa kike ganin kamar wani abu zai faru dake."
"Gaskiya Rashida bana jin zan iya amincewa da bukatarshi dan ni 'kadai nasan irin 'bakar wuyar da nake ci babu ciki ma ballanta yanzu da wannan cikin ai nasan mutuwa zanyi kawai yayi hakuri Har Allah yasa na haihu.'' Rashida tace" Ni wallahi bana so naga kina 'bata masa rai duk sai
naji babu dadi dan Allah ki bashi hakuri anti."
"Ki kyaleshi zai huce da kanshi, ni ba zan iya