Author : Binta Umar Abbale Category : Romantic Books
dan tsaya tana kallonshi lokacin da yake kokarin zama kan kujera yana dariya da fad'in "Zeey rigimarki yawa gareta yanzu yanzu na fito daga wanka naga kiran wayarki nima ban jima da shigowa gida ba."
Taji gabanta yayi muguwar fad'uwa jin hannunta na rawa ya sanya ta ri'ke baby zahra da kyau! Yarinyar ta soma kuka tana cilla kafafu! da sauri ta dauke kainta ta juya ta cigaba da tafiya dakinsu Hajja ta nufa.
Kukan momynsa ne ya sanya duk abinda yake yi ya fita daga ranshi dan a rayuwarsa ya tsani yaji tana kuka yay saurin datse wayar yana fad'in "Ki bari zan kira ki anjima yanzu ina da uziri." Mikewa yay yabi bayanta dakin.
Sai ya tarar da babyn Zahra hannun Hajja tana duba cikinta da ya dan kumbura. Yarinyar sai kuka takeyi, Hajja tace"Kuma da kika bata nono ta kar'ba."? Murya na dan rawa tace"Eh mana bacci fa takeyi kawai ta tashi tana kuka nasa mata nono a bakinta ta'ki kar'ba shine nace to ko cikinta ne ke ciwo."
Hajja tace"Da alama dai cikin nata ne ke ciwo dan gashinan ya nuna alama."
Yakarasa kusa dasu dan har jikinsa ma na gogar nata ta kauce da sauri ta bashi hanya, ya tsaya gaban Hajjan yana kallon babyn yace."Hajja meke damunta ne."?
Hajja tace"Cikinta ne ke ciwo da alama dan gashinan ya kumbura."
Ya dan tsuguna yana duba yarinyar hannunsa ya sanya ya dan bubbuga cikin yaji dummm! hankali a tashe ya kalleta tana tsaye itama jikinta dik yay sanyi yace."Ina magungunanta."? Tace"Suna d'aki." Cike da bada umarni yace."Kije ki dauko." Fita tai daga daga d'akin,
Ta dawo dakin hannunta rike da wani d'an kwando da kwalayen magunguna a ciki.
Kar'ba yay yana duddubawa, kwata kwata babu maganin ciwon ciki a ciki.
Hajja Tace."Ai duk ba wannan ba ke Wasila maza jeki kicin ki d'an had'a ruwan d'umi da gishiri kad'an ki kawo min na bata insha Allah ko yaya inda ya shiga cikinta za tayi gyatsa watakila kin bata nono a kwance ne."
Wasila tace"Ina bata nono bacci ya daukeni sai kawai na kwanta ina kuma kwanciya ta fara kuka shine na bata nonon a kwance."
Hajja tace"Ai kinji matsalar dama! dan Allah ku daina bawa 'yayanku nono a kwance yana janyo musu illah babba har 'kwa'kwalwa yana ta'ba musu idan suka 'kware a haka sai kiga an samu matsala." Ta bude baki kenan za tayi magana ya katseta, fuska a daure murya a kausashe yace."Ai rashin hankaline dama kawai ki kwanta kina bawa yarinya nono a kwance meye amfanin hakan, ke zaki iya cin abinci akwance ne? Abinda kika kasan ba zaki iya ba to kada ki sake kwatantashi kan yarinyar nan! gashinan kin jawo mata lalura."
Ba tare da tace masa komai ba ta kad'a kanta ta fice daga d'akin zuciyarta kamar zata babbake saboda tsabar bakin ciki da takaici.....Koda ta shiga kicin din ma kasa kata'bus tayi dan tama manta abinda ya shigar da ita, zama tayi kan wata kujera tana kuka ya kufce mata.
Wai shin dame zataji ne? a cikin gidanan kullum babu kwanciyar hankali abu kadan sai masifa daga kawai ta bawa yarinya nono a kwance sai ace taja mata lalura duk dai so da kaunar da yake wa yarinyar bai kai ya nata ba itace ta haifeta tasha wahalar daukar nauyin cikinta kafin tazo duniya kome zai nuna akan yarinyar bai kai ya ita ba............Jin shuru bata dawowa yabi bayanta a fusace!
Ya lura sa yarinyar nan so take ta kashe masa 'yarsa....Sai dai me? yana shiga kicin din ya tarar da ita ta had'a kai da gwiwa tana kuka, sai kuma jikinsa yay sanyi a hankali ya shiga kicin din motsinsa ya sanya ta d'ago kanta da sauri! ganinsa ya sanya ta saurin mai da kanta, bai kalli inda take ba ya soma dube dube a kicin din kwalbar gushirin ya d'auko dake saman kanta ya bud'e ya samu cup karami ya zuba kadan kana ya tsiyayi ruwan d'umi dai-dai misali ya dan motsa ruwan da gishirin suka had'e sai da ya fara sawa a bakinsa yaji dai-dai sannan ya wuce ya fita daga kicin din hannunsa rike da cup din ba tare da ya kalli inda take raku'be ba.
Yana shiga da'kin da ruwan gishirin a hannunsa Hajja ta kar'ba a hankali ta dinga dandala mata a bakinta tana tsotsewa sai da tayi mata sau uku sannan ta mike tana kokarin sata a kafad'a, Rashida tace"Hajja koma ki zauna kawo in dan zagaya da ita."
Hajja ta zauna tana fad'in " A kafad'a zaki sanyata insha Allah yanzu za tayi gyatsa." Rashida ta kar'bi babyn tasa a kafada ta shiga zagaye da ita a dakin.....Cikin ikon Allah kuwa ta daina kukan da takeyi ta shiga sauke ajiyar zuciya tana sakin gyatsa.
Hajja tace"Alhamdullhi yanzu zakaga tayi bacci."
Yace."Ai gwara tayi baccin Hajja yarinya kankanuwa cikinta yay irin wannan kumburin wanda ko a gurin babba ma zaiji jiki ballanta yaro karami irinta."
Hajja tace"Mafi akasari dama 'kananun yara kamarta sunayin irin wannan kumewar cikin, sai hankali suke dainawa wasu kuwa sai suyi kwana da kwanaki ma basuyi bayan gari ba." Yace."Idan hakane kuwa al'amarin akwai ban tausayi wallahi." Hajja tayi murmushi tare da gyara kwanciya tana fad'in " to nidai sai da safe jama'a ina baccina tsohuwa ta tasheni dan dai kawai sunan kishiyata ne da ita shiyasa na saurareta da badan taci darajar sunan Yafindo ba to da sai dai ta nemi wanda zai rarrasheta."
Rashida tace"Kai Hajja ai yanzu ma bake kika rarrasheta ba Momynra ce."
Hajja na hamma tace"Haka kika ce ko."? Rashida na dariya tace"Ai gaskiya na fada Hajja gani ina rarrashinta har tayi bacci kice kece kika rarrasheta."
Hajja tace"Shikkenan dan dai ba'a fatan cuta ne da sai nace gobe ma rana ce."
Rashida tasa dariya tana dan bubbuga bayan baby zahran wacce ke lumshe ido bacci na fuzgarta.....A hankali yace."Kawota nan Rashida kema kije ki kwanta an tasheku kuna bacci ko."
Cike da jin nauyi ta mika masa yarinyar tace"Haba babu komai Wallahi kaga ma bacci zatayi." Ya kar'be ta tare da rungumeta a jikinsa, yace."Ki dinga yiwa yayarki fad'a har yanzu ta'ki hankali." Kanta ta sunkuyar tana d'an murmushi, ya kama hanya ya fita daga dakin rungume da yarinyarsa a jikinsa.
Tana kwance a gado tana tunanin rayuwa ya tura kofar dakin ya shigo, rufe idanunta tayi taki yin kwakkwaran motsi mugun haushinsa takeji dan duk wani girma da 'kimarsa da take gani ada yanzu sun zube a idonta.
A hankali ya kwantar da babyn a gadonta, ya dan tsaya a kan yarinyar minti biyar ya tofe mata jikinta da addua kana ya juya da niyyar fita daga dakin.
Ja yay ya tsaya yana tunani, sai kuma ya bud'e kofar dakin ya fita, tana jin fitarsa ta bude idanunta ta mike zaune tana jan tsaki! Yarinyar ta dauko ta dawo da ita kusa da ita ta kwanta tare da rufe jikinta da bargo, bacci har ya soma daukarta taji an bude dakin an shigo shine dai ya kara shigowa, dake ta kashe fitilar dakin sai ya kunna wayarsa yana duba gadon babyn, wayam babu ita, da sauri ya kalli bed din ya gansu a lullebe! a jiyar zuciya ya sauke, ya kashe wayarsa ya aje saman bedside ya zare jallabiyar jikinsa dake akwai singlet a jikinsa da gajeran wando sai kawai ya shiga cikin bargon nasu yay kwanta rigingine fuskarsa na kallon rufin dakin, ya dora hannuwansa a kirjinsa, yana addua, sai d
a ya gama tukkuna ya tofe musu jikinsu gabad'aya kana ya rufe idanunsa, Wasila gabanta tun yana fad'uwa har ya daina fad'uwa ganin tunda ya kwanta baiyi kuskuran koda rik'e d'an yatsanta ballanta yay mata wani abun asali ma ya bada tazara mai yawa a tsakaninsa da ita sanda tayi dubarar juyawa ta fahimci hakan......Al'amarin yay masifar 'bata mata rai! da kyar ta samu bacci ya dauketa, saboda tsabar damuwa da 'bacin ran da take ciki.
Littafin na kudi ne.....!
Kika futar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya ba kema keda Allah Whasap numbar
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*alliya:
'Yr Bngr Sys
*79*
Wajejen 'karfe uku da rabi ya farka ya lalubi wayarshi ya kunna haskenta yana dubasu Baby Zahra bacci take sosai da'alama kuma tana jin dadin baccinta, fuskar Wasila ya haske ya dan tsira mata ido sai yaga kamar fuskarta ta ta d'an kumbura mussaman fatar idonta alamu ya nuna kafin tayi bacci taci kuka ta koshi, ya jima yana kallon fuskarta yana jin wani irin tausayinta na ratsa jikinsa, ya girgiza kanshi a hankali ya mika hannunsa kan hannunta data dan kwanta akansa hakan zai iya janyowa hannunta data kwanta akai yayi mata tsami! gyara mata yake kokarin yi ta bud'e idonta tana dan mi'ke kafafunta, hakan da tayi sai ya dan rankwafo jikinta, tayi gaggawar mikewa zaune shi kuma yay saurin sauka daga bed din ya kama hanya ya fice daga dakin, Shuru tayi tana tunani to da me zaiyi matane? bata da mai bata amsa, sai kawai ta kunna fitilar dakin haske ya gauraye ta kalli agogo taga hudu saura minti ashirin har an soma kiran sallahr farko....A hankali ta dan gyarawa baby kwanciyarta ta mike ta nufi toilet
Wanka ta soma yi kafin ta daura alwala ta fito ta shirya cikin duguwar riga da hijab mai tsayi ta hau kan dadduma, nafila tayi raka'a biyu bayan ta idar ta daga hannunta sama tana addua tana hawaye kan Allah ya za'ba mata abunda yafi alkairi dangane da zamanta da mijinta.
Al'kurani ta dauka ta fara karantawa tun daga fatiha har sai dai tayi izifi biyar tukkuna ta rufe al'kur'anin ta tada sallahar asubahi.......Tana idarwa baby zahra ta tashi ta soma kuka da neman nono,
Da sauri ta cire hijab din jikinta ta dauki yarinyar ta ciro nono tasa mata a baki.
Yarinyar na tsotsar nono ita kuma tana share hawaye daga haihuwar fari har gishiri ya salamce daga jikin kaza ashe dama duk k'aryace ba wani sonta da yake tunda gashi tun ba'aje ko ina ba yana wulakanta kan abinda bai taka kara ya karya ba, ta tabbata jiya yana sane ya'ki daukar wayarta kawai saboda ya wulakanta, kuma tasan domin ya kuntata mata ne yake waya da budurwarsa a gida insha Allah ba zata sake kiransa a waya ba domin tana masifar jin ciwon rashin amsa mata da yakeyi.
Gari ya dan soma yin haske ya shigo dakin ya sauya jallabiya yanzu ba'ka ce a jikinsa mai gajeran gannu da dogon wuya jallabiyar dai larabawa sunfi anfani da ita, hannunsa rike da cazbaha ya 'karaso gabanta.
Kanta a 'kasa tace"Ina kwana."? Idanunsa kan baby zahra Ya amsa babu yabo babu fallasa." Shuru tayi fuskarta a cukune.
Yace."Ya jikin Mommy."? Da sauki." tafad'a a takaice. Yace."Ki fito yau zamuyi zaman karatu." Shuru tayi masa, ya kama hanya ya fice daga dakin.
Palon ta fito cikin hijab hannunta rungume da baby ganin Hajja bata a palon sai ta nufi dakinta, tana kokarin fitowa suka gaisa ta mi'ka mata yarinyar tace"Yau zamu koma karatu Hajja ga 'kawarki."
Hajja tace"Dama yanzu nake shirin shiga ai nayi mata wanka."
Wasila tayi murmushi tace" Ai kam da wuri ta tashi tayi ta tsotson nono ina shirin mata wanka Babanta yace zamu zauna karatu." Hajja tace"To bari nayi mata wankan anan na shiryata.
Tace"Bari na dauko miki kayanta."
Tana fitowa palo ta tarar dashi da Rashida sun soma karatu, ya dago kansa suka hada ido sai tayi saurin dauke kanta ta wuce dakinta. minti biyar ta fito rike da kayan a hannunta dakin hajjan ta nufa ta mika mata ta fito ta zauna gurin karatun.
A'lkur'ani ta bude dai-dai inda suke ta cigaba da sauraranshi har ya gama musu karatun yace su biya mishi yaji.
A nutse suka soma biya mishi aya goma yake musu da safe da dare shi kanshi yana mamaki da yanda Allah yayi musu kwakwalwar saurin daukar karatu sam basa bashi wuya gurin karatu nan da nan suke daukewa, mussaman Wasila.
Sauran littafan ya biya musu yana musu bayanin yanda zasu fahimta sosai, bayan sun kammala ne ya kalli Rashida a nutse yace."Rashida ya karatunki na boko ina fatan komai yana tafiya dai-dai kina fahinta."? Tace"Eh ina ganewa wallahi dan mun kusa jarrabawa tunda ina cikin wad'anda zasuyi jarabbawar fita." Yace."Alhamdullhi Ya kalli Wasila da hankalinta ke kan littafin zaduzjaujen Yace."Kema ki shirya insha Allahu za'ayi yanza za'ayi ki shiga cikinsu kiyi jarrabawa tunda naga babu lefi kina ganewa i
dan Allah jarrabawar tayi kyau xanyi magana da abokina Prof 'Dalhatu Nuhu dake jami'ar Bayaro a sama muku gurbin karatu a makarantar insha Allahu." A hankali tace."To mungode, mikewa yay ya nufi dakinsa, itama ta mike jikinta a sabule ta nufi nata dakin, ita kanta rashida jikinta yay sanyi ta lura kamar akwai matsala a tsakaninsu dan duk sanda suka zauna zaman karatun kafin su fara sai sunyi wasa da dariya a tsakaninsu, dan wataran ma idan sunayi ita har kunya suke bata, amma yanzu taga ita dashi sun bawa kansu tazara ko wanne fuskarsa a had'e.
Mikewa tayi tabi Wasilan dakinta.....Lokacin tayi wanka tana shiryawa rashida ta zauna gefan gado tana kallonta so take tayi mata magana amma kuma tana jin tsoro kar tayi mata masifa.....Wasila ta shirya cikin atamda java ja da baka d'inkin fetted gwon yay masifar fito mata da sharp dinta dan har sai da ta d'an saki zuf din rigar ta baya dake ta kwana biyu bata saka kayan ba, yanzu rigar ta matseta ire iren d'inkunanta ne na fitsara lokacin tana harkar siyasarta, Rashida tace"Anti Wasila dama wannan kayan suna nan." Tace"Gasu kuwa kin gani." Rashida tace"Yanzu sun matseki ba kamar da ba." Tana fesa turare a jikinta tace"Eh na dan yi 'kiba shiyasa.
Dankwalinta ta daura ta nannad'e gashinta dashi ya fito ta ciki ta danyi make up kadan a fuskarta tasa jan janbaki a le'bunanta, wani masifar kyau tayi tamkar ka sace ka gudu." Rashida tace"Anti Wasila atamfar nan nayi miki kyau sosai."
Tace."Nima shiyasa nake sonta."
Rashida tace"Anti Wasila dan Allah kada kice nasa miki ido wai me yake faruwa ne tsakaninki da maigidan naga tun bayan tafiyar Inna Hajara ke dashi kuka rage walwala magana ma da kyar kukewa junanku.
Wasila ta dan kalleta tana mamakin maganarta, ashe dai duk yanda take kokarin 'boye al'amarin sai da aka gane, jikinta a sanyaye tace"Rashida abokin kuka shi ake fadawa mutuwa, ke 'kanwata ce kuma nasan kina da hankali kin kai munzali kuma kin san abinda ke faruwa, yanzu dan Allah kece ace ki haihu kisha wuya sannan ayi miki d'inki gurin be warke ba sannan mijinki yazo miki da bukatar yin sex dake shin zaki yarda ki amince dashi ya lalata miki aiki ko ba zaki yarda ba."?
Rashida tayi shiru tana tunani tace"Gaskiya mutukar gurin be warke ba bazan yarda ba dan idan d'inkin ya lalace inaji ina gani za'a sake min wani kuma shima mijin nawa daga ranar ya daina ganin amfanina amma idan na tabbatar da gurin ya warke zan amince na biya masa bukatarsa tunda hakkinsa ne."
Wasila ta sauke ajiyar zuciya tace"To abinda ke faruwa kenan a tsakaninmu lokacin Inna Hajara nan tana nuna kulawarta a kaina shine yake jin haushinta wai ita ke zugani, na nuna masa ba haka bane shine yake fushi dan da Inna Hajaran ma ta tafi baice komai ba ya nuna yaji dadin tafiyarta, Rashida ni ban hanashi hakkinsa ba da ya amince da sai na dinga biya mishi bukatarsa ta wata hanya har Allah yasa gurin ya warke amma sai ya nuna shi dole sai ya shiga gurin ni kuma na'ki amincewa saboda nasan halinsa, shine fa yake ta fushi na bashi hakuri yaki hakura, Ina ga ma neman aure yake dan kullum sai sunyi waya da budurwarsa." Ta'karasa maganar muryarta na rawa tabbacin abin na mutukar damunta daurewa kawai take.......Rashida tace"To anti Wasila kema kina da gaskiya dan gaskiya kika sakar mishi jiki bayan kuma kin san da ciwo a gurin aiki ya 'baci ke zai bari a ciki, amma ga shawara me zai hana ki koma asibitin su duba miki su tabbatar gurin yayi dai-dai idan hakane sai kawai ki shirya ki cigaba da kula da mijinki."
Ajiyar zuciya ta sauke tace"Rashida tun Inna Hajara na nan da mukaje asibitin suka tabbatar aikin yay kyau dan gurin ya dawo normal kawai ni ina jin ciwo kadan kadan ne wallahi kuma ina jin tsoro kada wannan abun ya sanya wani abun ya faru sannan kuma kinga banyi wani gyaran jiki ba na fiso na gyara jikina sosai kafin sannan gurin ya sake yin 'kwari yanda ake so."
Rashida tace"Gaskiya wannan ba dubara bace anti Wasila to shi kuma sai yayi ta zama da lalura kawai dan biyan bukatarki, ai tunda an tabbatar miki da lafiyar gurin ki amince masa da bukatarsa."
Shuru tayi tana tunani tace."Shikkenan na dauki shawarark
i zan amince masa idan ya sake nema nima sam bana son irin wannan zaman da muke." Rashida tace"Nima abin Bayayi min dadi gashi kuma naga kamar ya damu wallahi daurewa kawai yake." Ta'be bakinta tayi tace"Ni idan ta nine magana ta wuce ko yanzu ya nema shikkenan idan kuma yayi zuciya shi ya jawo." Rashida ta mike suka fita palo a tare
Shi kadai ne zaune a daning yana karyawa Hajja na zaune a kujera da baby zahra a hannunta tayi mata wanka tsaf ta shiryata cikin kayan sanyi kasancewar ranar an tashi da lillimi baby zahra sai kamshin turare masu dadi takeyi, sosai yarinyar take kara kyau da ki'ba saboda tana samun kulawa ta ko wane bangare.
Tun sanda suka fito daga dakin ya dora idanunsa kanta ya rasa nutsuwarsa, dan idonsa ya tsurata yana binta da wani mayataccen kallo tana tsaye tsakiyar palon suna magana da Hajja! Ya 'kura bayanta ido da yake a d'an bud'e saboda ta saki zuf din rigar kadan dan har brexiyar ta ta fito daga ciki, ajiyar zuciya ya dinga saukewa gabanshi na wani irin fad'uwa ji yay yawun bakinsa ya tsinke! kwata kwata ya gaza dauke idonsa daga kanta idanunsa sunyi masifar galabaita gurin kallon d'uwawunka da suka fito dam! dam cikin rigar kamar zasuyi magana ga lafiyayyar fatarta dake she'ki da daukar ido lukwi lukwi da ita da wani irin kwantaccen gashi a kai.
Tsigar jikinsa ta dinga tashi sanyi ya soma ratsa jiki da 'bargonsa.....Rashida tayi saurin