Author : Binta Umar Abbale Category : Romantic Books
kan cinyarta. Da sauri ta kalli Wasila dake zura kanta tagar motar tana shakar iska tace"Anti Wasila kinga Khalifanan ya sake kira." Tace"Ki daga mana to." Rashida ta d'aga wayar tare da fad'in "Hello." Khalifa dake driving yay sauri mika mishi wayar ya kar'ba da sauri yana kokarin kara wayar a kunnensa ta fad'i 'kasan site sakamakon rawar da hannunsa yake yi....Kasancewar wayar ta bugu da karfi yasa ta mutu ya dauko da sauri ya kunna ta bude, ya lalubi numbar yana sake kira, A dai-dai lokacin ne kuma wasu matasa suka shigo motar direban motar ya Umarci rashida ta gyara sosai domin su samu gurin zama garin gyarawa wayar dake cinyarta ta fad'i kasan motar ba tare da ta sani ba....Aikuwa shi wanda zai zauna kusa da ita ya sanya hannunsa ya dafe ta, a take yay dubarar cire sim din lokacin da Rashidan ta juya suna magana da Wasila ya jefa wayar karkashin kayanshi, Rashida matsatsi da xafin mota ya sanya ta manta da wayarta burinta kawai su tashi saboda zafin ya isa.....Aikuwa sai da direba ya cika motarsa tsaf sannan ya shiga ya zauna maxauninsa ya tashi motar suka fita daga cikin tashar suka dauki hanya
Abin kamar al'mara kiran wayar yake ana ce masa a kashe take, ya kira ya kai sau ashirin maganar dai daya ce wayar a kashe take! Ya d'ago kanshi yana wata irin zufa bakinsa na rawa yace."Khalifa wai meke faruwa ne? Wayar nan fa ta'ki shiga kana ji da kunnanka a kashe take Why! Wad'annan yaran naso su sanya zuciyata ta buga!!!!!!! Khalifa tsorona Allah tsorona Annabi kar cikin nan ya zube, ko a samu wata matsalar nasa raina akanshi."Ya 'kareshe maganar cikin rauni da sarewa da al'amarin.
Sosai ya bawa Khalifa tausayi yace."Ni ina tunanin network ne matsalar Amma kar ka damu abokina insha Allah cikin nan ba zai samu matsala ba muje tashar kabuga insha Allah xamu samesu idan ma motarsu ta tashi ai mun san inda suka nufa kai tsaye sai mu wuce can garkon ni da kaina zanyi wa mai allo bayanin komai."
Hularshi ya cire ya ciro hankici ya goge fuskarshi da saman kanshi, Yana jin wata irin fargaba na kamashi yanzu da wane ido zai kalli mai allo to me ma zaice masa idan sunje? Yace"Khalifa bani da wani bayani da zan iya yiwa mutumin nan saboda ina jin kunya wallahi in ce masa saboda d'ana ko 'yata dake cin Wasilan zan dauketa kasan da akwai nauyi." Khalifa yace."Kar ka damu zanyi mishi bayani."
Ya shiga girgiza kanshi yana fad'in "Kamar nasan abinda zai faru shiyasa jiya nace maka muje inda suke da yanzu duk hakan bata faru." Khalifa yace."Ni nayi mamaki wallahi saboda jiya lafiyar Allah muka rabu dasu ko da wasa basu shaida min cewar zasu tafi wani gurin ba amma basu kyauta ba wallahi kuma Wasila tayi wautar gaske."
Girgixa kanshi kawai yake yana adduar Allah yasa su samesu a tasha don shi kam yana bala'in jin kunyar had'a ido da mai allo.
Khalifa ne kawai ya iya fitowa daga motar bayan shigarsu tashar ya kutsa cikin mutane direbobin motoci yana dube duben motocin mutane, ko kusa ko alama bai hango koda kyallin mayafin wata daga cikinsu ba, haka ya gaji ya nufi inda motar su ke fake.....Shi kuwa uban gayyar tamkar wani zautacce ko kuma mara kunne yana ri'ke da waya a hannunshi sai kiran numbar Rashida yake tamkar mai kunnan 'kashi ko kuma kurma yana jin abinda matar nan ke fad'a masa cewar wayar a kashe take amma ya kasa daina kiran wayar.......Ganin Khalifa ya doso motar tasu cikin sanyi jiki ya sanya shi rarraba ido yana jiran karasowarsa...
Khalifa yace."Babu fa alamun yaran nan cikin tashar nan kawai shiga mota muje." Jiki a mace ya bud'e mota ya shiga duk yayi wani laushi kamar mara lafiya....Khalifa yaja motar suka fita daga tashar duk rayukansu babu dad'i.......Sai da suka hau kwalta sosai kana ya sauke numfashi yana huci! yace."Khalifa Allah banta'ba ganin sukuwar uwa irin uwar wad'annan yaran ba, ni yanzu ma ita nake jin haushi wallahi." Khalifa yace."Gaskiya tayi wauta itama data d'auki yarinyar nan da wannan lalurar suka dauki hanya bayan sai da na fad'a mata dokar da likita ta kafa kan 'yar tata shiyasa wallahi mace komai shekarunta watarana ta tafka maka wani abun haushin sai kaji kamar ka d'ora hannunka akanka.
Yace."Nifa babu ruwana Allah cikina ya samu wata matsala sai na dauki mataki kanta da ita da uwar tata." Khalifa yace."Ai kaji irinta wai kai me yasa kake hakane? Matar nan fa ta tabbatar min da cewar sunzo har gidanka da maganar cikin basu samu damar ganinka ba suka hakura suka koma kan me yasa za kaga laifinta anan bayan tayi kokarin ganin an fita hakkina."
Tsaki! yay yaja bakinsa yayi shiru yana muzurai! da ya tuno wani abu sai gabanshi ya fad'i! gaskiya yana bala'in son cikin nan nashi a yanzu ji yake zai iya hakura da komai na rayuwa mutukar cikinsa zai tsira.
Tafiya suke mota na gwajab gwajab yayinda ciwon ciki da mara ya tsananta a gareta ta! ta dinga sunkuyar da kanta tana zufa da kiran sunan Allah gumi ko ta ina d'iga yake a jikinta, tsabar yanda take jin jiki sunan Allah kawai take kira tana jin wani irin imani na ziryartar ta anya kuwa wannan cikin bashi ne ajalinta ba? abinda take fad'a kenan cikin zuciyarta.
Sun isa garin Garko Lafiya sai da kuma lokacin mai allo ya jima da fita tsangaya, Tanimu ne yay musu jagora har makarantar tashi.....Mai allo na tsakiyar al'majiransa ya hango zuwansu sai ya mike a nutse yana fara'a yana musu barka da zuwa......Cikin wata rumfar kwano da babu kowa a jiki suka nufa. Ma allo da kanshi ya karkade musu tabarma suka zauna sai aka shiga gaishe gaishe, Ahamdu sai sunkuyar da kanshi yake duk kunya ta dabaibayeshi sai yanzu yake jin kunyar dattajon yaga shi kuwa sai fara'a yake yana tambayarsa gida da harkokin yau da kullum. Khalifa yace."Alhamudllhi malam komai na tafiya yanda akeso sai da aita tayamu da addua." Mai allo yace."Addua munanan munayi har sai da numfashin mu ya dauke."
Khalifa ya ja gwaron numfashi kafin ya gyara zamanshi a nutse yace."Allah shi gafarta malam dama mun biyo sahun yaran nan ne wato ina nufin Wasila da 'kanwarta da kuma mahaifiyarsu, domin muji shin sun iso lafiya! sannan kuma muna da tabbacin cewa nan suka nufo dalili basu da wani gurin in ba nan d'in ba, Allah shi gafarta malam babu maganar rufe rufe cikin maganar nan Yarinyar nan Wasila na dauke da ciki har na tsayin watanni uku da satika kuma akwai matsala mai girma tattare da ita da d'an dake jikinta wannan shine babban dalilin ma da ya sanya shi Abokin nawa yace."Lallai ilallah sai munzo domin mu tabbar da zuwan nasu cikin 'koshin lafiya."
Mai allo ya dinga kallon Khalifa cikin mamaki da kad'uwa ya d'an gyara zamanshi kafin yace."To Idan na fahimci inda maganarka ta dosa anan shine kana so ka sanar dani cewar kun biyo sahun su Wasila domin kuna tunani ko nan suka zo kamar yanda ka fad'a hakane ko? Khalifa yace."Hake Malam." Mai allo yace."To a gaskiya ni dai har na fito daga gida banga zuwansu amma ban sani ba ko bayan na fito suka iso bari nasa yaro yaje ya duba a gida." Ya mike ya fita daga inda suke.
Ahamdu ya kalli Khalifa cikin sarewa da tsananin damuwa yace."Anya Khalifa anya yaran nan suna nan kuwa? jikina na bani ba nan suka zo ba." Khalifa yace."Ka dai bari tukkuna mybe bayan ya fito daga gidan suka sauka garin kamar yanda ya fad'a d'in in banda abinka idan ba nan suka zo ina zasuje da yafi nan d'in." Yay shiru yana jin wata irin zufa na karyo masa, mikewa yay ya fito daga rumfar kwanon ya kama kallon hanya sai kace wani zautacce ga rana sai kwalle masa ido take.
****
Misalin 'Karfe biyu da rabi na rana suka sauka garin Fataskum, bayan sun sauka daga mota Uwani ta dinga rarraba ido tana dube dube hanya dan garin gabad'aya ya sauya mata yau kusan shekaru goma sha biyu da rabonta da garin, tin tana goyon Rashida lokacin Yahuza na dan da mutuwa tunda tayi wannan zuwan bata sake waiwayar garin ba, dama mutum hud'u ne suka rage musu a dangi Babban yayansu mahaifiyarta da suke kira da Kawu Madu sai Mai binshi Kawu Isa sai kuma Iya mai waina da Tabawa dama su biyar iyayensu suka haifa mahaifiyarta itace ta uku ita ke bin Kawu Isa sai Iya mai waina sai kuma Tabawa! Mahaifiyarta itace kawai tayi aure a wani gari, amma dukaninsu cikin garin Fatskum suke tare da iyalinsu mutukar sun fita daka garin to sunje wani garin ziyara.....Tun bayan rasuwar mahaifiyar Uwani Kawu yaso daukarta domin su dinga kallonta a matsayin 'yar uwarsu, mahaifinta ya'ki lamince masa haka suka hakura suka bar mishi 'yarshi, gashi bashi da cikakkiyar lafiya shima a lokacin ya hana a tafi da itane domin ya dinga kallonta tana d'ebe masa kewar mahaifiyarta.......Sai da cutar ajali ta kamashi ne 'kaninshi ya daukeshi ya kaishi gidanshi dake akwai shago a wajen gidan nan ya ajeshi yake kula dashi, to shine fa tun daga lokacin Uwani ta soma shan wahalar rayuwa gidan Kawun nata har mahaifinta ya kwanta dama, a lokacin ta 'kara shiga tsaka mai wuya ga wuya ga maraici ga tsananin azabah! Saboda zalinci irin na Kawun ya siyar mata da gidan da ya zama gadonta ya sanya kudin a aljihunsa ya cinye matansa na zugashi da fad'in Ai idan yaci Allah ba zai tuhume shi ba tunda dai shima yana ciyar da ita...........Sai da sukayi aure da Ayuba ya jagorance da kanshi sukaje can Fatsukum din dangin mahaifiyarta da kwatance, to tun daga sannan ta gane hanya........Saboda matsatsi da talauci da kuma rashin kudin mota ya sanya bata zuwa garin a kai a kai, sai ta dauki shekaru masu yawa kafin taje to wannan karon dai shekarun data dauka ba taje ba sun fi na baya.......Da tambaya suka iske gidan Kawu Madu dake shi d'in ba 'boyayyen mutum bane a garin yasa basu sha wahala ba,
Suna zaune kan katuwar tabarma shida abokanansa gabansu katon farantin silba ne jere da kwanuka, da jug jug na ruwa da alama abinci suke shirin ci ya hangosu, Sai ya shiga wasiwasi da tunani to sai da suka iso inda suke ya tabbatar da cewa su d'in ne Yace."Uwani ko ba ita bace."? Tace."Nice Kawu."! Sai ya washe bakinsa yana fad'in "Kece kike tafe da ranar nan babu shakka yau an tuna damu kenan gaki ga zuriarki lallai yau patskum nada manya 'baki sannuku da zuwa." Mi'kewa yay yana 'kwalawa yaran dake wasan langa langa a 'kofar gidanshi kira.....Suka rugu a guje yace."Maza ku kwashi kayan nan ku shida dasu gida.....Yaran suka dinga ihu! suna fad'in "Yeeee! munyi 'baki daga birni da gudu suka runtuma cikin gidan suna jan akwatinan kayan nasu
****
Can ya hango yaron da aka tura gidan ya fito daga wata hanya yaji tamkar yaje ya tareshi ya tambayeshi, sai dai kawai ya daure ya bi yaron da kallo har ya isa inda mai allo yake ya tsuguna yana masa magana." mai allo ya Umarceshi da ya koma gurin zamanshi kana ya mike daga kan kujerarshi Ya nufo inda yake tsaye babu yabo babu fallasa a tare dashi, tun kafin ya karasa inda Ahamdun yake ya hango damuwa da tashin hankali a tare dashi, sosai ya shiga mamaki yana tunanin to bayan rabuwarsu ya mayar da ita ne har ta samu cikin ko kuma bayan ta fito daga gidan cikin ya bayyana ? babu me bashi amsa sai su ya sauke ajiyar zuciya lokacin da ya karasa inda yake a nutse yace."Alhaji mu shiga ciki sai muyi maganar." Ga yanayin yanda mai allo ke masa magana yasa ya fahimci akwai damuwa, jikinsa babu kuzari ya juya yana tafiya me allo ya bi bayanshi.
Mai allo ya zauna kan tabarma yana kallon Ahamdu A nutse ya soma magana kamar haka
"Yau shekaru takwas kenan rabon da Wasila da 'yar uwarta Rashida su tako 'kafarsu garinan! shiyasa nayi mamaki mutuka! a lokacin da kuka zo min da wannan maganar, amma kuma banyi muku musu ba saboda nasan hakan zata iya kasancewa tunda muma kullum cikin tunanin zuwansu muke nasan duk tsiya yarinyar bata da wasu iyaye sai mu, kuma nasan dole watarana zata kawo kanta inda muke duk kuwa da tsananin 'kiyayyar da suke mana ita da 'yar uwarta......Ni da 'Yan uwana da sauran dangi kullum cikin saurare muke da kallon hanya muna jiran tsammanin zuwansu garinan, tun bayan rabuwar auranka da ita muka yanke shawara kancewa mun dauke hannunmu da kansu gabakid'aya wanda har 'Dan uwana Habibu da ya fusata yace. Duk ranar da suka shigo garinan to sai ya koresu ni ne na hanashi nace mutukar sunzo inda muke to zamu kar'be su hannu biyu amma idan basu nemi in da muke ba to zamu kyalesu da halinsu da kuma mahaifiyarsu, to a gaskiya ni nafi gazgata zaton cewar Yaran nan sun bi bayan mahaifiyarsu can garinsu." Mai allo ya 'karashe maganarshi yana so ya tabbatar musu da gaskiyar lamari......Khalifa ne kawai ya iya magana Yace. "Allah shi gafarta malam ko zamu iya sanin garin su mahaifiyar tasu."? Mai allo yayi shiru yana d'an tunani kafin yace." Wallahi sunan garin ya kwanta min a raina, tun da kasan can d'in ba nan ne inda cibiyar mahaifinta yake ba, shi kanshi 'kanina Yahuza a hannun Kawunta ya aureta amma dai na ta'ba ji sau d'aya 'kanin nawa ya ambaci sunan garin har yace watarana zai daukeni ya kaini mu gaisa da danginta to kuma sai Allah ya dauki abinshi.
Khalifa da gogan naku bakinsu ya mutu murus! Saboda dukaninsu sun rasa tudun dafawa sun ma rasa wane tunani zasuyi shin yanzu ina zasu samu yaran nan? Su dun tunaninsu babu inda suka dashi sai nan dan suna tunanin itama Uwanin a nan take ashe ba haka bane! Gashi gurin wanda suke tunanin samun cikkaken bayani shima yace bai ma sannan sunan garin da suka nufa ba........Innalilihi wa'ina ilaihi raji'un!
Littafin na kudi ne.....!
Kika futar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya ba kema keda Allah Whasap numbar
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
[14/08, 12:04 pm] Farida Books: 'Yr Bngr Sys
*58*
Cike da farin ciki da walwala ya shiga gidan nashi yana kwalawa matarshi kira..........Kuluwa ta fito daga wani guri wanda alamu suka nuna cewar madafi ne (khicin) hannunta da wata katuwar mara da alama kwasar towo take, tace"Malam ganin nan Allah yasa lafiya irin wannan kira hak.....Kafin ta rufe bakinta sai idanunta ya sauka kansu Uwani da 'yayanta, lokacin 'kan'kani ta kirne fuska tana fad'in "A'a yau kuma Uwani ce a garin."? Uwani dasu Wasila duk sunga sauyin fuska a tare da ita, lokacin da take maganar da alama dai batayi maraba da zuwan su garin ba.......Kawu Madu yana washe hakoransa yace." Wallahi kau nima nayi mamaki sosai dan baki ji dadin da nakeji ba, abinci zamuci dasu malam tsalha na taso domun in shigo dasu gidan." Kuluwa tace"To sannunku da zuwa ku shigo ciki." Kawu Madu yace."Uwani ku shiga ciki a baku abinci ku huta ai da alama ma kun kwaso rana." Uwani tace"Aikuwa wallahi munsha zaman mota da gajiya." Kawu Madu ya juya ya fita yana fad'in "Bari nasa Ayuba yaje can cikin kasuwa ya siyo muku ruwan sanyi."
Uwani da Rashida suka shiga daukan jakkunansu dake yashe a tsakar gidan suka nufi dakin Kuluwa, suna shiga katuwar rumfa ce sai dai babu shinfida a cikinta sai guntattakin tabarmi da ledoji ko ina kaca kaci da kwari ka 'kananin kyankyasai ga wani uban 'kuda da yake tashi a rumfar da wani kafirin zarnin fitsarin yara......Tun lokacin da suka shiga rumfar Wasila ke yatsine ya tsinen fuska zuciya sai masifar tashi takeyi aikuwa kafin tayi wani yun'kuri amai ya kece mata! a guje! tayi waje ta nemi bakin rariya ta tsuguna ta dinga kelayashi tana kwallah......Rashida ce tsaye a kanta tana mata sannu duk ta shiga damuwa. Bayan ta gama aman ta bata ruwa ta wanke bakinta da fuskarta kana ta mike jiri na d'ibarta......Rashida ta rike hannunta wai su koma cikin d'akin girgiza kanta tayi da kyar tace"Rashida rabu dani don Allah zuciya tashi takeyi idan na koma gurin nan zan iya yin wani aman." Aikuwa karaf a kunnan Kuluwa ta rike baki tana fad'in "Ke ja'ira yarinyar me kike nufi? daga zuwa zaki fara yiwa mutane sanabe da iyayi kina nufin kazama ce ni kome." Rashida tayi saurin girgiza kanta tana fad'in "Ba haka take nufi ba baba." Kuluwa tace"To me take nufi da har zata shiga dakina ta rugu waje da gudu tana kwara amai." Rashida tace "bata da lafiya ne dama tun a mota cikin ta ke ciwo." Kuluwa ta girgiza kanta tana fad'in "Maji ma gani dai idan tusa zata hura wuta, kome kuke tafe dashi dai-dai nake daku to kaji."! Tana gama maganar ta ta shige madafi domin cigaba da aikinta.
Uwani na cikin dakin abin duniya yayi mata yawa, tunani takeyi yanzu wace irin rayuwa zasuyi cikin gidanan! tun da can baya tasan Kuluwa macace mara mutunci da muguwar kaxanta sam bata so kowa yazo inda take tabi ta asirce Kawu Madu sai abinda tace yayi yake ji shima wani lokacin tsoranta yake yi, Ta dinga tunanin irin wuyar da zasu sha ita da 'yayanta a gidan dan ga dukanin alamu Kuluwa ba tayi maraba da zuwansu ba, tunani take ko su tafi gidan Kawu Isa ne? sai ta tuno shi kuma ai bai da gidan kanshi haya yake kuma daki guda ne suke gamutsuwa dashi da matarshi da 'yayanshi.....Iya mai waina kuma ba ita kadai bace a gidanta tana da kishiyoyi kuma babu wadataccen gurin zama, dole dai gidan Kawu Madu din shine gurin zamansu, Kwallace ta taru a kwarmin idanunta tayi saurin gogewa, lokaci guda duniya ta juya musu baya, sun fara d'and'anar jin dadin rayuwa kuma sun koma gidan jiya............Sai a lokacin nadama mara amfani ta kamata