Author : Binta Umar Abbale Category : Romantic Books
iri a jikinta tabbas duk wanda yayi rashi iyaye nagari yayi babbar asara, Ada babu mai nuna mata ga yanda za tayi itace ke zartar da hukunci kan mahaifiyarta da 'yar uwarta dan sai abinda tace sannan Uwani da Rashida keyi, shiyasa takejin wani irin a jikinta, gaskiya babu abinda za tacewa mai allo da Hajara da ita kanta Bitan din dan sun nuna mata kauna da so da kulawa, duk mutumin zai fad'a gaskiya yayi maka fad'a kan wani kuskure naka to babu shakka masoyinka, dan haka sai ta dauki aniyar zama lafiya gidan Ahamdu kamar yanda suke bukata ta kuma yi musu alkawari kan insha Allah za tayi mishi biyayya iya iyawarta."albarka suka shiga sanya mata suna cike da farin ciki mara misaltuwa
Wannan karon cikin babbar mota (Sieana) sukaje garin wacce ke dauke da kayan abinci dana masarufi, Ahmadu yayi niyar farantawa mai allo kamar yanda shima ya faranta mishi saboda ya fahimci tsayuwar shi kan Wasilan da abinda ke cikinta yasan bashi da abinda zai biyashi a bisa abinda yayi mishi, sai dai hausawa nacewa yaba kyauta tukwici.....Almajirin malam ne ya hangi zuwansu lokacin da yake kokarin shiga gidan malam din, dan haka koda ya shiga gidan sai yake shaidawa malam din zuwansu, Wasila taji gabanta ya fadi har sai da ta rasa miyau a bakinta, tayi shiru tana kokarin maida kwalla ita har ta gaji da zubda hawaye..........Mai allo ya shigo dasu, cikin gidan yana musu barka da zuwa, Garba da Hadi sune suka shiga shigo da kayan abincin cikin gidan malam ya cika da mamaki yana so yayi magana Khalifa yayi saurin tareshi da fadin malam kada kace komai don Allah ba wai munyi hakan bane domin mu biyaka mun san bamu da abinda zamu biya dashi wannan ihisani ne kawai mukayi maka saboda karamcinka." Mai allo ya girgixa kanshi yana fadin anya abun baiyi yawa ba kuwa? Khalifa yace."Beyi yawa ba malam ka sanya albarka kawai." Yace."To nagode kwarai Allah ya sanya alkairi ya kara arziki da wadata." Khalifa ya amsa da ameen ya rabbi."
Inna Hajara kuwa mamaki take sosai ita bata ta'ba 'karewa mijin Wasilan kallo ba sai yau! sai take ganin kamar ma yafi karfin wasilan dama haka Allah ke tsara lamarinshi Addua ta shigayi kan Allah ya xaunar da ita lafiya a dakinta.
Malam ya sanya Tanimu ya dauki jakar kayansu ya kai motar, kana dukaninsu suka fito daga cikin gidan......Ita dashi aka bari a baya, sai ta dinga ra'bewa tana so yayi gaba shi kuma ya'ki tafiya da sauri yana tafiya sannu sannu yana kallonta ta gefan ido sai 'boye fuskarta take ci
kin mayafi, tana kauda kanta, tuntu'be tayi da bakin 'kofa yayi gaggawar rike mata hannunta yana d'an janyota jikinsa, da sauri ta bude fuskarta tana zumbura bakinta, jikinta ta janye daga nashi, ya danyi gyaran murya a hankali yace."Meye amfanin rufe fuskar da ki keyi ke ba amarya ba."? Shiru tayi mishi ta dan 'kara sauri gabanta na fad'uwa bata so wani ya juyo ya gansu suna jerawa, ganin yanda take tafiya da sauri da sauri yasa shima ya 'kara sauri har suka iske inda motar take......Khalifa da kanshi ya bude mata bayan mota ta shiga, Rashida na kokarin ta shiga ta zauna kusa da ita yace."kanwata zo ki zauna nan." Sai ta zauna inda ya nuna mata,Inna Hajara kuwa hawaye ta fara sharewa ta kasa daurewa, ganin hakan ya sanya su Wasila suka fara kuka mai allo yace."Wannan shirme ne hajara Alhaji ku tafi kawai idan ba haka yanzu xata sanya yaran nan koke koke."! aikuwa yana ganin Wasilan na kuka yayi saurin shiga motar ya zauna kusa da ita, yana d'aga musu hannu mai allo ya mi'ka mishi ma dai-dai ciyar jarkar rubutun dake hannunsa yace."Kullum ta dinga tsiyaya tana sha safe da dare tana kuma shafe cikinta dashi." Ahmadu ya kar'bi rubutun yana godiya da fad'in "Insha Allah malam Allah ya biya bukata."
Mai allo ya d'aga masa hannu yana fad'in "Ku sauka lafiya Allah ya tsare Alhaji Allah ya saka da alkairi." Shi da khalifa suka amsa da "Ameen malam Allah ya saka da alkairi." sai da motar ta 'bace daga gurin sannan suka koma gida duk jikinsu a sanyaye mussaman Bitan da Inna Hajara, to shima dai mai allon daurewa kawai yake yi saboda yayi mutukar sha'kuwa da yaran kuma yana jinsu cikin ranshi.
Hawaye take sharewa tana d'an kauda kanta tare da kare fuskarta da mayafinta, 'kamshin turaranshi da hucin numfashinsa duk ya isheta ta rasa ya za tayi gabanta sai fad'uwa yake, sai kawai taji hannunshi a jikinta ya kamo hannunta dake cikin mayafinta ya ri'ke cikin nashi a hankali ya soma murxawa yana kallonta ta gefan idonshi.......Kokarin cire hannun nata ta shigayi ya rike tam! ya had'e 'yan yatsunsa da nata guri guda ya rintse gam gam! kamar wanda yake bata amana ko kuma yake d'aukar mata al'kawari!!! Ajiyar zuciya ta shiga saukewa ta kauda kanta tana kallon hanya, a hankali taji hucin numfashinsa dai dai fuskarta, a razane ta juyo sai kawai fuskarsu ta had'u guri guda! bakinshi ya sauka kan nata bai jira komai ba, ya sanya harshensa ya lashi le'bunanta yana sakin ajiyar zuciya! ya d'auke fuskarshi ya gyara zamanshi kamar bashi ba,
Ta dinga jin wata irin fargaba da fad'uwar gaba sai kawai ta shiga rarraba idanunta cikin motar tana kici kicin kwace hannunta dake rintse da nasa.........
Littafin na kudi ne.....!
Kika futar min da book keda Allah kika karanta baki biya ba kema keda Allah Whasap numbar
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
*BINTA UMAR ABBALE*alliya:
'Yr Bngr Sys
*63*
Jin yanda yake sake rintse hannunta dake cikin nashi ne ya sanya tayi saurin kallonshi, suka had'a ido tayi saurin saukar da nata 'kasa tana motsi da bakinta, so take tayi magana amma saboda tsabar kwarjinsa ya sanya takasa, sai kawai ta cigaba da kallon gefe guda tana jin yanda yake shafa tafin hannunta a hankali a hankali, lokaci 'kankani taji duk jikinta yayi sanyi idanunta suka soma lumshewa da alamun bacci a tare da ita, kanta ta dora jikin murfin motar tana takure jikinta hade da runtse idonta gam! wannan abin da yake mata sam bata so wani ya gani a cikinsu khalifa dake gabansu, Allah ma yasa hirar da sukeyi ta dauke musu hankali da yake rashida akwai saurin sabo duk garin da suka wuce sai ta tambayi khalifa sunan garin shi kuma ya fada mata tare da cikakken bayani.......Yana kallonta ta takure jikinta a jikin murfin mota idanunta a rufe, sai ya sake matsawa jikinta sosai ta bude lumsassun idanunta da suka soma sauyawa bacci ne ko meye oho! a hankali ya kamo ha'barta ya d'ora kanta kan kafad'arshi kana ya zura hannunsa 'kar'kashinta ya ri'ke 'kugunta sosai ya matso da ita jikinsa ya ri'ke da kyau!! Rintse idonta ta sakeyi tana sauke ajiyar zuciya gabanta na d'an fad'uwa kad'an-kad'an! Kamshin turaran jikinsa ne yayi masifar tafiya da imaninta abinda ya sanya ma kenan ta sakeyin luf a jikinsa tana sauke ajiyar zuciya, jikinta ya soma shikawa bacci na fizgarta mai dad'i......Jin shirun tayi yawa ne ya sanya Khalifa d'an juyowa yanayi masa magana, sai kawai idanunsa ya gane masa abinda ke faruwa, Abokin nashi ya gani ya wani yi la'kas! dashi hankalinsa kacokan na kan Wasilan da bacci me nauyi ya dauketa a jikinsa, shi kuma ya kurawa fuskarta ido fuskarshi dauke da wani munafikin murmushi.....Khalifa ya danyi gyaran murya yana fad'in "Kaga yanzu mun wuce gaidan! garinsu Alhaji Yunusa mutumin nan dake kawo mana shanun sallah." Ya dago kanshi yana kallon khalifan yana ya mutsa fuska yace."Nagane shi koba wannan madamfarin mutumin ba? kasan akwai sallahr da ta gabata nasa shi ya kawo min shanu irin wanda nake sadaka dasu, ya kawo marasa lafiya cikin guda goma uku ne suka rayu naji ciwon abinda yayi min shiyasa na daina siyan shanu a gurinshi." Khalifa yace." Nima tuntuni munyi hannun riga dashi dama ai nine na had'aku dashi ko?" Gyad'a kanshi kawai yayi ya sake gyara zamanshi wanda hakan ya sanya kanta ya sauka a kirjinsa a maimakon kafadarshi, gyara ta yay sosai ya tallafeta da hannunshi guda.....Khalifa ya kalleshi shima ya kalleshi sai yayi mishi nuni da Rashida da bakinshi, basarwa yayi ya nunawa Khalifa shi ina ruwanshi da wata rashida! Abinda basu sani ba kuwa shine ba rashida ba har su Garba sun d'an hango abinda ke faruwa basarwa kawai sukayi......Murmushi kawai Khalifa yayi ya juya yana mamakin abokin nashi, idan ance masa yana son yarinyar sai yace ba hakaba gashi lokaci 'kan'kani duk ya wani susuce a cikin mota.
Kuluwa ta fito daga cikin d'akinta hannunta rike da wani 'kullin kaya, wanda zanin da aka d'aure kayan yayi da'kal-da'kal da daud'a, ta nufi inda Uwani ke sunkuye da wata 'katon baho a gabanta, wacce ta cika ta da kayan wanki ta zuba klin da sabulu a hannunta tana cud'awa! Kuluwa ta dire 'kullin kayan dake hannunta tace"Uwani idan kin gama wankin dan Allah ki d'an sa'be wa 'kananan yaran nan kayansu tuntuni nake so nayi wanki bani da sabulu kina dai kallo kwana biyu gidan sai a hankali yanzu Kawunki baya fita komai ya rinca'be mana." Uwani ta d'ago kanta cikin tsananin wahala da gajiya tace"Kuluwa kinga dai sabulun nan banawa bane na mutane ne dan Allah ki bari a wankewa mutane kayansu ya fita wai me yasa duk sanda zanyi wanki sai ki kwaso min kayan yara kice na wanke alhalin kin san sabulu da omo ba nawa bane nima aikatau nakeyi a biyani."
Da jin abinda Uwani ke fada sai Kuluwa ta fusata ta soma sirfa mata masifa da fad'in wallahi duk sanda ta sake yi mata musu kan abinda ta umarce ta dashi to sai ta bar mata gidanta." Uwani dai ta cigaba da gurxar wankinta bakin ciki duniya kamar ya kasheta, tun safe take wankin jama'a har yanzu bata karya kummalo ba, ko da yake sai ta g
ama wankin ta kai sannan zata samu kudin da zata siyi abin karin dashi dan tuntuni Kuluwa ta daina bata abin kari a gidan, da daddare kawai take bata abinci shima d'an mitsitsi idan towo ne kuwa sai ta lakata mata 'karshen kwasa cikin kwano wanda yaro 'karami ma yaci ba zai isheshi ba.
Tana gurxar wanki hawaye na 'kokarin su'bce mata, wannan wace iriyar masifa ce take cikinta? tayi dana sani tayi nadama tayi da ace abinda ya wuce zai dawo baya data yi gaggawar gyara kuskuranta, wannan wuya da take sha tasan duk itace ta jawowa kanta, Allah ya kawo musu dauki ita da 'yarta ya had'ata aure da mai kudi mai mu'kami amma sabida hange da mummunar kaddara ta dinga zugar 'yar tata ta kashe auranta, yanzu wa gari ya waya? wahalar da take ciki a yanzu ta wuce wacce taci a baya, a gidan Kawunta ana bata abinci taci ta koshi anan kuwa sai dai ta nema ta ciyar da kanta, Kawu Madu sallamamman namiji ne mijin tace sai abinda kuluwa tace ayi a gidan yake yi shiyasa duk abinda yake faruwa da rayuwarta baya tofawa, tun bayan tafiyarsu Wasila da kwana uku Kuluwa ta soma gallaza mata kyara! da hantara! da masifa! da kuma horan yunwa! ganin hakane ya sanya Ta nemi Inna Tabawa tana kuka take shaida mata halin da take ciki, itama Tabawar ta tausaya mata sosai sai da bata da yanda za tayi tunda itama talakace, sai kawai ta bata shawarar kan cewar ta kama sana'a sai ta rike kanta, saboda ba komai ne yake sanya Kuluwa nayi mata rashin mutunci ba saboda tana bata abinci ne." Uwani tace"Dama can baya nayi sana'ar wanki indai zan samu anan to wallahi zanyi na rufawa kaina asiri." Tabawa tace"Kada ki damu idan Allah ya kaimu gobe kizo gidana mu tafi cikin gari Unguwar amare zamu mubi gidajen mutane idan suna da wankau su bamu." Uwani tace"To shikkenan."
Aikuwa gari na waye wa Ta shirya ta tafi gidan tabawa, suka dauki hanyar cikin gari.......gida biyar suka samu wanki aikuwa Uwani ta zage ta wanke musu kayansu ta shanya musu tsaf suka biyata kudinta, ranar sai yamma suka dawo gida, Uwani ta bawa Tabawa kudi cikin kudin da samo ta 'boye sauran a jikinta......Tun daga sannan Uwani ke zuwa unguwar amare tana musu wanki watarana kuma ta d'oro kayan saman kanta ta tawo dashi gida sai ta wanke su bushe tsaf sai ta kai musu su bata kudinta.
Da 'kyar Rashida ta iya gane hanyar gidan ta dinga nunawa Garba hanya yana bu ta cikin kunyar gonakin mutane gwajab gwajab din da motar take ya sanya ta bud'e idanunta tana d'an motsawa, sai kawai taga duk rabin jikinta a jikinshi, yayin da shi kuma yayi wani irin zama a cikin motar kamar wanda zai kwanta yayi hakan ne domun taji dadin yin baccin a jikinsa........Da sauri ta mike zaune tana gyara xamanta had'e da gyara mayafinta ta d'ora saman kanta.......Ya mi'ke zaune sosai yana ya mutsa fuskarsa, hakuri kawai yake yi amma wannan kwanciyar da tayi a jikinsa ta ya mutsa shi, sosai ya d'an saci kallonta sai yaga tana hamma! da alamun baccin bai isheta ba, sai kuma ya mutsa fuska takeyi cikinta ne ya soma 'kullewa yunwa na sasakarta dama 'ka'ida ne idan tayi bacci ko yayane ta farka sai taci abinci.......Jikinta ne ya soma rawa, ta dinga zare ido tana mutsu mutsu ta rasa ya za tayi a yaron dake cikinta yana mata wani irin motsi da zillo tare danno mararta kamar me shirin fitowa waje, cikin rawar murya tace"Rashida ina kayanmu suke."? Rashida tayi saurin juyawa tana kallonta ganin yanda idanunta suka kad'a ne ya sanya ta gane yunwa takeji da sauri tace" Suna bayan mota." Still murya na rawa tace"To sai kizo ki dauko min kin san dai cewa nayi ki rike min a hannunki saboda zan iya bukatarshi cikin ko wane irin yanayi me zai sanya kisa a cikin akwati.'' Rashida tace."Yi hakuri anti Wasila ai mun kusa sauka." Tsaki taja tana motsa bakinta.....Ya kalli Rashida cike da kulawa yace."Menene."? Tace." 'kwai dafaffe ne Bitan ta bata shine tace na ri'ke mata a hannu na ni kuma wallahi na manta nasa a cikin jakar kayanmu gatacan a bayan motar." Shiru yayi kawai ya juya bayanshi da kanshi ya kinkimo jakar kayan nasu ya d'ora saman cinyarshi ya zuge zif din jakar ya soma dubawa.....Nan ya d'auko daurin leda yaluwa da dafa
ffan 'kwai a ciki kusan guda ashirin, a jikinta ya d'ora ledar ya mai da zif din jakar ya zuge kana ya maida ita inda take ya gyara zamanshi yana kallonta a nutse yace."Gashinan karkiyi kuka gama naga shi kike shirin yi." Shiru tayi masa ta cigaba da kokarin kwance ledar.......Kar'ba yay ya kwance mata ya d'auko d'aya ya soma 'bare mata , ya mi'ka mata ta kar'ba da sauri gutsira biyu tayi masa ta cinye.....Tana kallon hannunshi dake kokarin 'bare mata wani, Haka dai yayi ta aikin 'bare mata kwai tana taunewa sai da taci guda tara sannan ta hakura ya mi'ka mata ragowar ruwan swan din da yasha d'azu ta 'karba tana sha tana lumshe idonta sai yanzu taji dama dama a jikinta.
Uwani na tsaka da shanya kan katanga taji tsayuwar mota, dake katangar bata da tsayi sosai ana hange na waje kafin ta ankara taga Rashida ta fito daga cikin motar Wasila ma ta fito da sauri ta ajiye rigar dake hannunta ta nufi cikin dakin da take kwana mayafi ta dauko tayi hanyar fita tana kokarin yafawa a jikinta, a soro sukayi kicibus da Rashida sai ta rungumeta tana fad'in "Rashida sai yau kuka tunani dani ko? ke da waye a cikin mota ina Wasila ya jikin nata."? Rashida ta dinga kallon mahaifiyarta ta ganinta gaje gaje yayi masifar daga mata hankali, Wasila ta shigo ta gansu sai itama ta shiga bin Uwanin da kallo jikinta sharkaf da ruwa......Gashi duk tayi wani wujuga wujuga da ita. Uwani ta rumgume Wasila tana hawaye tace" Yarinyar nan kullum dake nake kwana nake tashi a raina Alhamudullihi jiki yayi kyau masha Allahu ga cikin ki ya girma dama ai nasan mutukar kun koma gaban mai allo zai kula daku mutum ne shi mai tausayi kuma yana kaunarku." Wasila da Rashida suka shiga binta da kallo jin abinda take fad'a kan mai allo wai yau Uwani ce ke yabon mai allo lallai duniya.
Gidan suka shiga gabad'ayansu, Wasila ta dinga bin gidan da kallo ko ina kaca kaca da kazanta iri iri ga wani wari na tashi da alama shaddar gidan ta cika tana bukatar agaji warin yayi yawa.....Ta dinga bin mahaifiyarta da wani irin kallo na tsantsar tausayi da jin kai. a hankali tace"Uwani wannan wane irin 'kuraje ne a jikinki? dubi yanda fatar jikinki ta kod'e kinyi wani iri duk kin rame."! 'Kwallah ta cika kwarmin idon Uwani tace"Ku mu shiga ciki babu komai." Bin bayanta sukayi suna mamaki tabbal akwai abunda ke faruwa da mahaifiyar tasu.........Kuluwa ta fito daga dakinta kirjinta daure da dadd'aud'an zani!!! kanta babu d'ankwali tamkar hammatar d'an iska yayi wani cibiri cibiri dashi dan saboda tsabar dauda gashin kan nata har ya soma d'aukewa da kanshi wani guri da a kwai wani gurin babu.....Ganinsu Wasila yasa tasha kunnu tana fad'in "Ku kuma yaushe kuka zo."? Wasila tayi saurin kauda kanta daga kallonta dan ji tayi tsigar jikinta na tashi kallon gashin kanta ya sanya mata tashin hankali amai na taso mata....Rashida tace" Yanzu muka zo Baba mun same ku lafiya."? Kuluwa tace "Lafiya lau ina fata dai yau zaku juya domin dai muma bamu da abinda zamu baku koda yake dai ga uwarku nan na neman kudi zata iya daukar dawainiyarku." Babu wanda yace mata ta tafasa ballanta ta sauke suka shige dakin ina Uwani ke zaune tana jiran shigowarsu......Nan suka tarar da ita a zaune a gefen wata guntuwar tabarma ta zabfa tagumi! Wasila ta dinga bin dakin da kallo daki sai kace zai rufta ya durkushe gashi babu labule babu ledar kasa sai