Author : Binta Umar Abbale Category : Romantic Books
yana ganin hakan zaifi masa saukin shiga unguwarsu tasu ta tudun yola, duk wannan yanke yanken da Ahamdu yake yi da mota, Motar su *Mada!* na biye dashi amma saboda tsananin taku mutum ba zai gane hakan ba, Sosai yake gudu sam baya son ruwa yayi karfi wanda zai tilas tashi yatsawa a kan hanya shiyasa ya kara karfin motar, Wanda ita kuma sai zazzare ido takeyi kamar kace kyat! ta ruga a guje tunani takeyi ko tana ina su *Mada!* zasu fito........Kasancewar ruwan ya soma 'karfi ya sanya masu siye da siyarwar dake kan titin kansakali mahad'ar 'yan rake ya sanya suka fara kwashe kayaiyakinsu kowa na neman tsira titin tayi shiru hanya tayi tsit! sai saukar ruwa sai kuma ababen hawan dake ta sharara gudu kan kwalta kowa na so ya isa gida.
Yana fitowa daga tsukin titin kansakali ya hau titi sosai, yana kara karfin motar! Kawai motar su *Mada!* ta daki tashi motar wanda ya sanya hannunsa ya goce daga kan sitiyarin motar ta gangara wani layi! Dake titin dama motoci basu fiye binshi ba ya sanya jama'a basu ankara ba, bayan haka kuma ga ruwan da akeyi babu kowa a gurin masu wuce wa a baben hawansu basu fahimci komai ba dan dik wanda yaga motar Ahamdu cikin layin zai dauka a fake take dan bata nuna komai ba da zai dauki hankalin jama'a.
Ya jima yana kiran sunan Allah kafin yayi gaggawar bud'e motar ya fito ruwa na dukanshi, Can ya hango motar su *Mada!* ta silalo gurin.......Ya tsaya yana kallon motar har tayi parking kafin ya ankara yaga sun fito su uku ko wanne fuskarshi rufe da ba'kin abu, dake namijin duniya ne bai wani razana ba sosai! suka durfafo inda yake! Mada ya fito da wata bindiga yana saita shi da fad'in"Kud'i ko kuma mu dauki ranka."! Yace."Ai babu mai daukar ran mutum sai wanda ya halliceshi! *Lauje* ya kai wa bakinshi duka da sauri ya rike hannunsa yana girgiza masa kai! Yace."Kuce kawai na baku kudi sune bukatar ku amma kada ka kuskura ka ta'ba min lafiyata."
Zuruf! ta bud'e motar ta fito, sai ta fashe da kuka tana wata makyarkyata sosai tsoro takeji gani takeyi anya su *Mada!* ne kuwa, ganin sun saita shi da bindiga yasa gabanta faduwa ta shiga kuka tana basu hakuri."
Da sauri *Lauje* yaje ya bud'e motar ya hau dube dube a ciki a take ya bude wani gurin cikin motar ya fito da daurarrun kudi a hannushi, ya dinga jefewa ! 'Kwage! yana cafewa! Wasila ta isa inda yake a hankali tace"Lauje." Yace.'Yar gaske maxa ki fece daga nan.'' Data tabbatar da sune sai kawai ta silala ta bayan motar zata gudu, tana waigowa ta hangi Ahamdu da Mada suna kokawa! saboda tsabar tsaurin ido irin na *Mada* so yake ya lalube jikin Ahmadu, ya dauke masa wayoyinsa shi kuma ya hanashi, Sai kawai taga *Mada!* ya daddage! ya sakar mishi duka a 'kirji! Ihu! tayi da 'karfin gaske! wanda ya sanya shi saurin juyowa, yana goge ruwan fuskarshi, dan har lokacin ruwa ake me 'karfi! Can ya hangota tana 'kwarma! ihu zata tsallaka titi! Yayi nufin binta, *Mada!* ya tad'e kafafunsa, santsin gurin ya sanya ya zube 'Kas! cikin zafin nama ya rike kafafun shi shima ya makar dashi a gurin! a gaggauce! ya mike! da azama! ya murd'e? hannunsa ya 'kwace! bindigar dake hannunsa! ya saita wuyanshi......
*Mada!* ya hau 'kif'kifta ido! Yana kare fuskarsa da hannunsa!....A kausashe yace."Waye! ya aiko ku."? *Mada!* yayi shiru yana yi wa *'Kwage!* Inkiya da idanunshi, *Kwage!* ya lalla'bo ta bayan Ahamdu ya kir'ba mata wani irin duka! Ahamdu yayi taga taga zai fad'i! da sauri *Mada* ya tureshi ya mike a guje! sukayi inda motar su take suka shiga, Ahamdu ya saita bindigar hannunsa zai harbesu wayam! babu bullet sai da ya duba ta sosai sannan ya gane ashe ta gaibu ce! Can ya d'ago kanshi ya hangi motarsu ta fice daga layin......
Wata irin walkiya akayi mai hasken gaske! Walkiyar da ta zame masa madubi gurun hango Wasila tana kurd'awa wata hanya tanayi tana waiwayen bayanta, Da sauri ya nufi motarshi ya shige ya kunna da gudu yabi hanyar da bi, Ganin hasken mota yasa ta juya da saurin tana waigen bayanta, bata tantance cewar shine ko bashi bane, ta juyo da sauri tana cigaba da sauri aikuwa facal? ta fad'a cikin wata kwatuwar kwata mai zurfi! Kuka tasa tana kiran sunan Allah! ganin ruwa ya shanyeta har yuwanta shikkenan mutuwa tazo, sai kawai ta dinga kwarma ihu! tana fad'in"Azo acece ni! Azo! aceceni!" Jin wannan sautin ya sanya As dake cikin motarshi a can gaba ya fito a gaggauce! ya durfafi inda yake jiyo sautin muryartata, To shima Ahmadu hankalinshi ne yayi masifar tashi, dan gani yayi ma kamar motar bata guda ya bude ya fito ya soma gudu yana so ya cimma inda yake jin ihunta!
Had'uwa sukayi da As! d'in, sai suka shiga kallon kallon, Ga Wasila tsakiyar kwalbati ruwa na neman tafiya da ita dan ma ta rike wani karfe ne da tuni ruwan yayi gaba da ita!
Ahmadu na gane Waye baiyi wata-wata ba ya kir'ba! masa wani irin naushi a 'kirji! As ya ri'ke kirjinsa yana tari! Ahamdu ya sake kir'ba mishi wani naushin da yafi na farko! As ya zube a gurin yana jawo numfashi da 'kya!!! Facal! facal! d'in da yaji a cikin ruwan ne ya sanya ya dawo da hankanlinsa nan ya hangota tana d'ad'dago kanta sama! da hannunta guda! Da sauri ya afka cikin ruwan, dan har sai da yayi motsi saboda yawan ruwan da ya taru ! Daukota yayi a kafad'a ya daddafo ya fito yana kwantar da ita, ta sume a gurin......
A hankali a tashe ya ciro wayarshi da ruwa ya jika jagab! baiyi tunanin idan yay kira da wayar zatayi ba saboda yanda take digar ruwa, amma abin mamaki yana fara kiran yaga tana shiga ajiyar zuciya ya sauke, Stion ya kira yay musu bayanin komai da kuma kwatancan garun! Ya mai da wayar jikinshi bayan ya gama, inda take yazo ya tsuguna ya fara danna 'kirjinta a hankali a hankali ruwa ya dinfa fita ta bakinta da hancinta kafin wani ruwa yayi fit ya fito ta hancinta ta bude idonta a razane! ta mike tana zazzare! idonta! Ganinshi tsugune gabanta ya sanya ta fashe da kuka jikinta ya soma karkarwa shikkenan kashinta ya bushe! Bai ce mata komai ba, Ya mike tsaye tare da goya hannuwansa a bayansa ya nufi inda As ke sheme!!! Yana tsaye a kanshi yana nazarin shi motar Police ta shigo gurin.....suka fito su kusan biyar suna haske gurin da torchlight din hannuwansu, Ganin Sananniyar fuskar Ahamdu ya sanya su mamaki! sosai gaisawa sukayi yace."Yanzu babu lokacin bayani ku daukeshi kawai ku wuce dashi stion da safe zan shigo." Suna haska fuskar As suka razana! Ganin sanannaniyar fuskarsa Ahamdu yace."Kuyi abinda nace kawai."Sanin halin Ahamdun da rashin wasa ya sanya suka bi umarinsa, bayan haka kuma dama sun gaji da mulkin *Lawan Rabo* baya basu albashi kan kari babu promotion da sauransu wasu daga cikin ma'aikatansu ma duk ya koresu daga aiki acewarsa wai basa aiki shiyasa ya sallamesu, dama suna ciki dashi da masu bashi shawara, irin su As din dan haka suka ga su baza su 'ki bin Umarnin Ahmadun ba, suka fito da wani gadon karfe cikin motarsu suka dora As a kai suka haura dashi motar, kana sukayi wa Ahamdun sallama suka bar gurin.
Ya juyo inda take takure kanta tsakanin kafafunta tsananin razana da fargaba ya sanya jikinta maxari sai kace wacce aka kad'awa gangi tsoro nadama gami da dana sani duk sun baibayeta yanzu da badan Ahmadu ba da tuni ruwa ya cinyeta! hakika fadawarta cikin ramin kwatar yasa ta sare ta sadakar da cewa mutuwa zatayi sai gashi wanda take 'kokarin gujewa shine ya ceceta, wata irin nadama takeyi sai kuka takeyi ma'kogwaronta ya bushe 'kamas!!! Taga inuwarshi a kanta, Idanunta jage jage da hawaye ta d'ago tana kallonsa, ganin fuskarsa a daure ya sake fad'ar mata da gaba, kawai sai taji wani masifaffan fitsari ya matsota! Cikin ba'kin ciki da takaici ya buga mata tsawa "Tashi mu tafi."!!! Gurin sai da ya amsa da sautin muryarahi, Ta mike jikinta sai kyarma! yake tana d'igar da ruwa duk tabi ta 'kankame! hannuwanta a jikinta, ya nuna mata hanya da hannunsa,
Tana cire 'kafa da niyar tafiya fitsarin dake cinta ya kufce! sakin sa tayi kawai ta cigaba da tafiya tana kyarma! Bayanta yabi hannuwansa goye a bayansa yana jajanta al'amarin.
Gaban mota ta bude za ta shiga yace." Rufe min mota." Da sauri ta rufe! ta bude murfin baya ta shiga ta zauna tana kuka da nadamar rayuwarta.... ya shiga a gaggauce ya Kunna motar suka bar gurin.
Gwajab! gwajab! din da motar takeyi ne yasa As dawowa hayyacinsa ya mike zaune a zabure! yana fad'in' Karya kakeyi Ahmadu! Ba zan jima ina shuka ba ranar girbi tazo kace ban isa inyi ba, Wallahi sai ka saki yarinyar nan ko ni ko kai, a fad'in garin nan.""!! Daya daga cikin police din yace."Yallabai yi a hankali shin wai meke faruwa ne tsakaninka da Ahmadu Musa." As yayi saurin dawowa hayyacinsa yana bin motar da kallo sai ya ganshi tare da 'yan sanda, gabanshi ya fad'i! Yace."Kai ina zaku kaini."!? "Yallabai Ahmadu ne ya kiramu a waya ya shaida mana muzo gurin nan domin mu dauke ka mu kai ka stion mu rufe." Ya buga musu tsawa da fad'in"Ina ce dai bai fad'a muku abunda ke tsakaninmu ba."? Dan sandan yace."bai fada mana komai ba, amma kuma ga yanayin maganganun da kakeyi munso mu fahimci wani abun." As yaji gabanshi ya yanke ya fad'i! A duniya ya tsani mutuncinsa ya zube gurin mutanan gari da kuma iyalinshi, yanzu idan Ahamdu ya sanar da Media cewar yayi nufin daukar matarshi me duniya da mutanan cikinta zasu daukeshi, sai kawai gumi ya soma yanko masa daga ko wace kusurwa ta jikinshi, Yace."Maza ku saukeni a gida Ahmadu bai da hurumin daureni domin bai da wani mu'kami a siyance idan dauri ne ma nine zanyi masa." Babban cikinsu yace."Sam! ba haka dokar aiki take ba ku da kanku kuke fad'in cewar ba mayin aiki tsakani da Allah bama bin doka dan haka babu wani karin albashi da za'ayi mana, saboda haka daga yau zamu fara aiki tsakani da Allah a kanka." As ya shiga rarraba ido yana kallonsu ma'kogwaronshi ya bushe kamas! yace."Kunfi kowa sanin mukami na a siyasa me zai sanya kuyi min haka ku fad'i ko nawa kuke so zan baku ku kaini gidana kuma bana so kowa yaji wannan maganar." Mai maganar cikinsu yace."Yallabai alamu sun nuna mana kaine mara gaskiya tsakanin ka da Ahmadu, saboda haka dole ne muje stion dake domin yin aikinmu kamar dai yanda na fad'a maka da farko cewar kuna fad'in bama aiki kan 'ka'ida shine zamu fara ta kanka." As yayi kwata'kes! yana zazzare ido cikin motar.............
*_Tofaaa! Karshen tika tiki tik! 'Karya fure take bata 'yaya! Tsalle d'aya za kayi ka fad'a rijiya sai kayi dubu baka fito ba._*
Littafin na kudi ne.....!
Kika futar min da book! keda Allah kika karanta baki biya ba kema keda Allah! Whasap numbar
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
Littafin na kudi ne.......!
Kika futar min da book keda Allah kika karanta baki biya ba kema keda Allah! WhatsApp numbar
*07084653262*alliya:
'Yr Bngr Sys
*48*
Shashshekar kukunta ne ya dameshi yana draving yana jan tsaki ya rasa ma wane irin mataki zai dauka kanta, domin tayi mutukar bashi mamaki! sam! bai ta'ba tsammanin za'a iya had'a baki da ita a cutar dashi ba, ashe dama ita da akwai abinda take shiryawa shiyasa tun jiya yaga ta saki jikinta tana ta zumud'i, to wai idan ta bi As din ina zai kaita? shi da kansa yake tambayar kanshi da kanshi, tabbas yarinyar ba 'karamar mara hankali bace wato ita tafi so tayi ta yawo a gari tana shiga cikin maza tana cakuduwa dasu! da auransa a kanta zata bi As suje inaaaa? Sitiyarin motar ya daka da karfi har sai da ya kufce daga hannunshi motar tayi wani irin abu!! Jikinta na bala'in rawa tace"Kay....hakuri dan Allah."! Ko kallonta bai ba ya kunna motar a guje yake janta yanayi kamar ma yace ta fice masa daga mota saboda tsabar haushi da takaici.......Lokacin da suka isa gida ruwa ya dauke ma'aikatan sa na katuwar rumfar da suka saba zama suna jiran dawowarshi. kafin ma yay parking din motar sun isa inda yake suna masa barka da zuwa, ba tare da ya bude motar ba ya amsa musu, kana kowa ya koma inda yake. Ya bude motar tashi ya fito itama ta bude ta fito jikinta na wani irin d'ari da karkarwa....Bin bayansa take simi simi har yanzu bata daina zubda hawaye ba.
Bai wani saurareta ba ya shige bedroom dinshi domin yay wanka ya sauya kayan jikinshi zazzabi zazzabi ma yake ji a jikinsa kasancewar dama shi tunfil-azal ba mutum ne me son ruwan sama ya dake shi ba......Ta jima tsaye a parlon tana kuka kafin ta lalla'ba ta shige nata bedroom ta hau cire kayan jikinta ta daura towel ta nufi bandakin, to kafin tayi wankan ma sai da taci kuka ta koshi kana ta fito kanta nayi mata wani irin bala'in ciwo mara misali, tana kuka taje ta kudundune jikinta da bargo, tana rufe idonta......Shigowarsa dakin ya sanya ta mike zaune da sauri tana matsawa lokon gado dan tana ganin kamar zai daketa ne ko yayi mata wata illar mugun tsoronsa takeji tunda ta lura idan ranshi ya 'baci bai iya hukunci ba.
Kayan sanyi ya sanya a jikinsa masu kauri kanshi sanye da hular sanyi ya rufe har kunnanshi mugun sanyi yake ji mai shiga jiki ga zazza'bi na damunshi haka kawai ta janyo masa lalura.
Kafin yace komai ta soma kuka tana d'ad'daga hannuwanta sama da fad'in"Don Allah kayi hakuri wallahi ni babu ruwana, dama shin......Kasa karasa maganar tayi ta hau inda inda tana rawar baki." Ya zuba mata idanunsa yana kallonta fuskarshi babu walwala ko ta kwabo, yace."Ki nitsu ki daina wannam firgice firgicen da kikeyi." Hannunta tasa ta rufe bakinta hawaye na ambaliya a fuskarta, ya zauna gefan gadon yana kallonta har sanda ta dan samu nutsuwa, Kawai taji sautin muryarshi yana fad'in"Me kuka shirya akaina ke da mutanan naki? Kuna so ku kasheni ko.'!? Tayi saurin kallonshi tana girgixa kanta......Yace."Hakane mana." " Wallahi ba haka bane." Yace."To naji, Ina zaki bi As kike gudu."? Sai hawaye ya soma shatata! yace."Ba kuka nace kiyi min ba." Tayi shiru tana kallonshi, yace."Kiyi min bayani dallah dallah kan a'lamarin.'' Tayi shiru tana me sunkuyar da kanta kasa! Tsawa ya buga mata yace."Zazzabi nakeji a jikina yi min bayani abinda nace ba kuka nace ki min ba." bakinta na rawa ta shiga wassafa masa yanda suka tsara ita da As da yanda in ta kufce daga hannunsa zasu gudu fataskum sannan kuma ta kaishi kotu shi da mai allo kana idan al'kali ya raba auransu ta dawo ta cigaba da harkokinta, Ya dinga kallonta yana girgiza kanshi, Mahaifiyarta bata da hankali ko d'an! abinda yake ayyanawa kenan cikin ranshi, to idan ba rashin hankali ba me zai sanya ki zauna kina tsarawa 'yarki shirme da abinda zai cuceta har ta dinga kokarin kashe mata aure, amma babu komai shi ya san abinda zaiyi musu.
"Na yarda babu abinda ke damunki sai jahilci da da'kikanci! Allah yayi miki suttura kina nema ki butulce masa, me nayi miki? me kuma me allo yayi miki da har kike nufin tozarta mu ki kaimu gaban al'kali! kan anyi miki alkairi ke zaki mayar da sharri! ko da yake tarbiyace baki samu ba tun farko ku kusa ko alama ni bana ganin laifin Kawunki saboda yayi iya bakin kokarinshi a kanku, k
eda 'yar uwarki da ita kanta 'Yar uwar taki! amma dake keda da maman taki duk taron mahaukatane kuna adawa dashi Okey ni Ahamdu mutukar na cika d'an halak! sai nayi muku abinda kuke bukata, kafin ki tozartani ni zan tozartaki! Ni Ahamdu ba'ayi min na bari! idan kinga na bar abu nine nayi niyyar bari, Yau zaki gane asalin waye ni."!!!!
Kuka take sosai tana fad'in"Don Allah dan annabi kayi hakuri wallahi kuskure nayi kuma bazan 'kara ba nayi nadama ni na hakura ma da komai zan zauna da kai nasan kai mai kaunata ne tunda har ka ceto ni lokacin dana fad'a ruwa nagane rayuwa ba'a bakin komai take ba."
Yace."Tubanki na banxa ne Siyasar banga da Jagaliya kike so kiyi to zan baki lasisi a hannunki." Yana gama maganarshi yasa kai ya fice daga dakin." Ta kwanta tare da takure jikinta tana ta kuka da makyayatar jiki.
A daran ya kira dr Nasir yazo ya danyi mishi treatment ya bashi maganguna dan zazzabi da mura mai karfi ce ta kamashi, abinci yaci yasha magani kana ya shige bedroom dinshi ya rufe yayi kwanciyarshi akwai bacci me nauyi ya daukeshi.
Yanda taga dare haka taga rana, lokaci zuwa lokaci gabanta na wata irin faduwa, idanununta sun kada sunyi jawur tsabar kuka da damuwa da kuma tsananin zazzabi da ciwon kan dake damunta...........Asubah nayi taje tayo alwala ta fito ta duba doguwar riga mai hula mai dan nauyi tasa a jikinta kana ta tayar da sallah......Kwanciya tayi kan dadduma tana lumshe ido bacci mai dad'i yana fuzgarta, ya turo kofar dakin ya shigo, a zabure! ta mi'ke zaune tana gyara zaman hijab dinta da ya karkace.......Yana sanye da jallabiya fara tas da ita har yanzu kanshi na sunkufe da hular sanyi har kunnanshi kafafunshi ma safuna ne farare ya iske inda take zaune kanta a kasa tana watsa da 'yan yatsunta! Hannunsa guda dake cikin aljuhunsa ya zaro ya fito da wata takarda fara a nannad'e ya mi'ka mata......Dake kanta a 'kas! yake bata ankara ba sai da yace."'Kar'ba." tayi saurin d'agowa tana kallon hannunshi, gabanta yayi wani irin bugu! Innallihi wa'ina ilahi raji'un! Sai le'bubanta suka soma rawa suna had'uwa!!! "M....me zan kar'ba." Tafada tana kallonsa da gwala gwala idanunta da suka