Author : Binta Umar Abbale Category : Romantic Books
yace."Afnan iyayenki sun saba miki da shan za'ki ko!? ga yanan ha'koranki duk sun soma ru'bewa." Bata fuska tayi wai yace. hakoranta sun rube shine takejin haushi! Ya zauna kusa da khalifa yana fadin"Dan Allah ku daina bama yarinyar zaki kar yayi mata illah."
Khalifa yace."Ga mai laifin nan a gabanka tana jinka, ita ke bata kayan zaki, kuma kaima kasan halin Afanan da rigimar tsiya kan alawa da buscit.'' Yace."Afnan ki daina shan kayan zaki idan kina so mu shirya kin jiko."?
Tace."Dadyna ni ba zan daina ba sai dai in rage ina shan kad'an." Ta kyalkyale da dariya." girgiza kanshi yayi kawai yana lakuce mata hanci, ya mai da hankalinsa kan Khalifa dake masa magana......Khalifa ya kalleshi tare da fadin ''Ka shanya mu a parlo tun dazu shin ina amaryar take nema."? Ba tare da ya bawa maganar tashi mahimanci ba yace."Wanka take yanzu zata fito.'' Hafsa tace"Okey da har mun yanke shawarar tafiya kar muyi rashin hankali a gidan amare." Hararar ta yayi yana 'bata fuska, suka fashe da dariya, Yace."Hafsa kinci tuwo a kaina amma nasan abinda zanyi miki." Tace"Ai gaskiya na fada." Ya kalli Khalifa yana kanne masa ido yace."Wai ina wannan beb d'in nan dake sonka ya ma sunanta naga ranannan kunyi musayar numbar da ita." Khalifa yace."Nabila kake nufi tanan ko jiya ma munyi waya da ita." Aikuwa Hafsa taci kunu ta fara hura hanci! Ahamdu ya kwashe da dariya yana nunata da hannu ita kuma sai hararar Khalifa takeyi, shi kuma yasha kunu yana latsa wayarshi! wayar ta fuzge daga hannunsa ya kalleta cike da mamaki! Tace"Sai na duba numbar shegiya na goge dama ai ki baku fada nasan abunda kukeyi idan kun futa waje."! Yace."To ke da kina tunanin da ke kadai abokina zai zauna."? "Eh ko ba'a zauna dani kadai ba ai a barni nasha miya haka kawai sai ayi min kishiya." Bilhakki take maganarta sai faman hura hanci take....Ahamdu ya dinga yi mata dariya,, ita kuwa duk ta dauka gaske ne bata san kawai tsokana ce ba.
Mikewa yayi ya barsu suna artabu ya shiga bedroom din Wasila dai-dai lokacin da ta fito daga toilet daure da towel iyakacinsa cinyarta, a hankali ya mayar da kofar ya rufe!! Tayi bala'in bata fuska, ta wuce da sauri gaban dreesing mirror ta tsaya, tana goge fuskanta....Ba san ya iso inda take ba sai hucin numfashinsa taji dai-dai wuyanta, gabanta ne yayi wata mummunar faduwa, tayi saurin matsawa har towel din na barazanar kwancewa daga kirjinta tayi saurin tare shi da hannunta guda.
Mazewa yayi yace."Tun dazu kin shanya mutana a palor suna jiranki kar kiyi tunanin ko bakina nane naki ne domin ke suka zo saboda haka kiyi maza ki shirya ki fito ku gaisa."
Kamar ta fada masa bakar magana sai ta share shi ta dauki mai ta wuce shi bed ta zauna ta fara shafa man gabanta sai faduwa yake, tsoro takeji kar ya sake ta'ba ta sake shiga irin wahalar data shiga dazu!
Shikuwa ai ji yayi ba zai iya kyaleta ba dan ba karamin sha'awa ta bashi ba, sai ya bita bed din ya tsaya a kanta.....Ta dago kanta tana kallonsa taga ya kurawa kirjinta ido! hannu tasa ta kara tamke daurin da tayi da towel, ta fara kokarin mikewa, hannunta ya rike cikin nasa, Ta cire zata bar gurin sai ya dan tura ta da kirjinsa ta fadi kan bed din, ya runkufa kanta, dauke fuska tayi tace."Wai meye haka."? Murya na rawa ta fadi maganar,
Ba tare da yace komai ba ya dan sa d'an yatsan sa a kirjinta yana yawo dashi, tayi saurin turewa tana ja da baya, ya sake matsarta yana yawo da hannunsa kirjinta har ya samu damar kwance daurin da tayiwa kirjin nata ta rike towel din da kyau! yana ja tana ja! Kuka tasa masa! "Wai me yasa kake so kaga tsaraicina ne? alhalin baka bani sadaki ba."? Da jin wannan magana da tayi sai yayi saurin kallonta, " Ina Sadakin da na baki ranar dana kawo ki gidanan.''
Harara ta watsa masa, "Wallahi Wasila tafi karfin wannan sadakin da kake magana akanshi idan kana so kasan wacece Wasila kaje ka sake sabon daurin aure kuma nice zan fad'i iya adadin kudin da zaka biyani na sadaki."
Ya kalleta da mamaki a tare dashi!! "Ke kina da ilimin addini kuwa."? Dauke kanta tayi....Yace." A'ina kika ta'ba jin mace ta yanke sadakin auranta da kanta? Shiru tayi masa, yace."Na lura kina da masifar son kudi......Me zaki dasu? nan ma ba tace komai ba, yace."Kar ki sake min magana makamaciyar wannan ranki zai 'baci! Sadaki na auranki na baki tuntuni, ke kika san yaya kika da kayanki kuma kin jawo sai na amshi sadakina yau dan haka ma ki shirya." Yana gama maganarshi ya sauka daga bed din yana tattare fuska yace."Malama ki shirya ki fito suna jiranki." Ta mike tana sake damke kirjinta dake daure da towel taje tana nemo kaya.........Super Holland ta dauko cikin kayayyakin da ya siyo mata, yana kallo ta wuce shi ta nufi toilet da kayan a hannunta, wai ba zata shirya a gabanshi ba da sauri ya tare mata hanya yace."In dai ba zaki saka kayan a gabana ba to zanja ki a haka na kai musu ke ." Ranta a bace tace"To wai me yasa kake takura min ne? yanzu sa kayan ma sai nayi a gabanka."? Yace."Kin mata da d'azu na gama ganin abinda kike 'boyewa to meye na damuwa.''?
Takaicinsa ne ya kamata! ta wuce ta barshi tsaye a gurin.....Babu yanda ta iya haka ta dinga kare karen jiki wai kada ya ganta tasa breziyya tana kokarin zura riga ya rike! taji tsoro sosai dan ba tayi tsammanin ya iso gurin ba, wuyan rigar ya shiga kana hannu guda ya shiga daya hannun ne bai shiga sanadiyar rike rigar da yayi!!!! Taga yana mata wani shu'umin kallon da ya kusa sanyawa ta zube a gurun! Ji tayi kafafunta na rawa, kafin ta ankara ya daga hannuwanta sama ya zare rigar! ya jefar manneta yayi a jikinsa ya zagaya hannunsa bayanta ya 'balle breziyyar ya jefar, ajiyar zuciya suka sauke a tare......Fatar bayanta ya shiga shafawa yana hadawa da kwantaccen gashin kanta, ta dinga jin tsigar jikinta na mikewa sanyi na ziyarta ta bata san sanda ta shige cikin jikinsa ba, ya sun jima a haka kafin ya d'ago fuskarta idanunta na rufe ya sumbaci le'bunanta ta bude ido a hankali ta sauke su a kanshi.....Murmushi ya sakar mata wanda ta kasa fahimtar ko na menene! Taji yace."Kiyi hakuri sai dare zanyi miki abin dazu yanzu kinga muna da ba'ki."! Kunya ce ta lullubeta sai tayi 'kas da kanta duk ta rasa ya za tayi, wai me yasa take saurin bada kanta ne gashi har ya gane ta daga ya ta'ba ta sai ta hau network! kamar mara lafiya haka ta zama sukuku! tana ji tana gani ya sanya mata breziyar da kanshi bayan ya gama lugwigwita nonowan sannan ya dauki rigar ya sa mata, mika mata zanin yayi yace."Wannan ne ban iya daurawa ba daura abinki."
Ta karba da mataccen jiki ta daura, tana ji kamar ta fashe da kuka ji take ta tsani kanta da kanta yanzu yanzu tagama cin alwashi kan sadaki amma gari banza ta bari yaga abinda take boyewa, ta dauki dankwalin ta yafa ba ta daura ba, yace."Kisa kwalli a idonki kamar ba amarya ba." Kamar ta gaura masa mari haka taji, zuciyarta sai zafi take, ya dauko mata kwallin ya bata, jefar dashi tayi....Ya daga kafada alamun bai damu ba, "Wuce muje ko."! yafada yana tsareta da ido, Simi simi tayi gaba, ya bi bayanta yana murmushi shi wataran ma idan tayi abu dariya take bashi a kwai kuruciya a tare da ita...........Dan sai-saita fuskarta tayi yayin da ta fito, kafin ta ankara Afnan ta tawo a guje ta ru'kun'kume ta tana fad'in" Aunty amaryata aunty amaryata ce."
*_'Yar Uwa yana da kyau a duk lokacin da ki kigama al'ada ma'ana jinin haila! Ki sanya miski ki goge gabanki kana ki dan goga zuma ki tsuguna a turaran suguno, sannan ki d'an sha kayan marmari, domin ni'imar ki ta dawo, duk lokacin da mace ta zubar da jini ko na haihuwa ko na al'ada ni'imarta na dan raguwa gurin na bushewa yana bukatar gyara sosai domin ki tar'bi mai gidanki da aka kwana biyu ba'a had'u ba🙋🏻♀️_*
Littafin na kudi ne......!
Kika futar min da book ke da Allah! Kika karanta baki biya ba kema ke da Allah! Whasap number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
[07/08, 11:50 pm] +234 803 238 4602: 'Yr Bngr Sys
*34*
Rike hannun yarinyar tayi tana dan murmushi tare da fad'in"Oyoyo baby ya sunanki."? Afnan tace."Halimatu amma ana kirana da Afnan." Tace."Ashe ma mamana ce daga yau sunanki momy." Afnan tasa dariya tana fadiin"Laaa! Dadyna wai na zama momyn aunty amarya." hannunsa ta rike tana kyalkyala dariya murna take yi wai Wasila tace ita momynta ce....Yace."Eh mana tunda kikaji ta fadi haka da gaske take." Yarinya ta ruga a guje inda iyayenta ke zaune tana fada musu. 'Karad'in yarinyar ya sanya Wasila dariya, ta 'karasa inda suke a nutse tace"Sannuku." Khalifa yace."Sannu da fitowa gimbiya amarya ." Murmushi tayi kawai ta zauna tana kallon Hafsa dake kallonta tana murmushi, tace."Ina kwananku." Hafsa ta amsa tana dariya tace."Ai kin cancanki a kira ki da wadannan suna, amarya ya gida ya bakunta." Tace."Alhamdullahi, cikin ranta tana jin yanda famliy din Khalifa suka burgeta ta lura matarshi na kirki shima kuma ta lura yana da mutumci ba kamar abokinsa ba......Khalifa yace.''Ga 'kawa nan na kawo miki ku gaisa ku san juna Matata ce ga yarinyata anan Afnan duk naji lokacin da take gabatar miki da kanta."
Murmushi tayi tace"Afnan akwai karad'i Allah ya albarkaci zuria mungode da ziyara." Khalifa ya dinga mamakin hankali da nutsuwar yarinyar ashe duk kallon da suke mata na lalatacciya ba haka abin yake ba........Duk wannan gaise gaishen da sukeyi Ahamdu na can tsaye bakin window yana kallon harabar gidan nashi........Wasila ta kalli teble din gabansu ta taga ko ruwa babu, sai taji nauyi, ta mike a nutse tace"Bari na kawo muku ruwa ko."Hafsa tace "Mungode." kicin din ta nufa, Afnan tabi bayanta, tana fadin"Aunty amarya zan raka ki." Hannunta ts rike tace."To muje." Tana kokarin shiga kicin din ya juyo suka hada ido tayi saurin dauke nata ta shige kicin din da sauri shi kuma ya dawo inda su khalifa suke lokacin Hafsa na gulmar Wasila.....Khalifa yace."Gatanan tana gulma. Ya zauna kusa dashi Yana kallon Hafsan dake murmushi kunya ce ta kamata duk da ba wata mummunar magana ta fada kan wasilan ba.
Khalifa yace."Wai cewa takeyi amaryar yarinya karama kuma akwai karancin ilimi a tare da ita amma kuma tana da hankali." Murmushi ya danyi ya ta'be baki yace."Khalifa bana jin wannan yarinyar ta cika 20yeares fa, duka bata fi 17 ba, karatu kuwa dama ai ba'a maganarshi a gurinta, bana tunanin tana da takardar scondry School." Hafsa ta bude baki! Yace."Yes hakane mana ai babu nutsuwar da zata sanya tayi karatun....Hafsa tace."Allah sarki amma dai yana da kyau ta koma makaranta gaskiya magana matar governor guda ace bata da takaradar kammala karamar makaranta gaskiya akwai babban kalubale.
Yace."Hafsa ke kike tunanin wannan itafa wannan yarinyar a yanzu bata da wannan burin burinta shine ta samu hanyar da zata fita daga gidanan."? Tace"To a kan me."? Dake duk abinda ke faruwa ba tasa ni ba, khalifa na da amana sosai baya futar da sirrin abokinsa.
Share maganar kawai yayi shima saboda ya lura da cewar batasan abinda ke faruwa ba kuma bata san yanda akayi auran nasu ba gaskiya yana mutukar alfahari da abokinsa yana da sirri sosai matarshi ma bai yarda taji labarin ba.
Ta fito hannunta rike da wani madai-daicib tire da goran ruwa da lemo a kai sai kananun cups ta ajiye kan teble din tana fadin ga ruwa sannuku." Khalifa yace."Yawwa sannu amaryamu." Murmushi tayi kawai ta kama hannun Afnan suka nufi dakinta, ba tajin zata zauna in dai yana gurin a zaune..........Khalifa yace."A'a ya zaki gudu kuma." Karaf! yace."Kunya takeji wai ita amarya." Hafsa tasa dariya tace"Ai kunya halal ce! a gurin 'ya mace gaskiya mungode da tar'bar da akayi mana amarya." Ba tace komai ba ta bar suna ta surutu....Tana jin sanda yake fad'in"Ita wannan amarya bata da wata kunya dan ta ganku ne take sunkuyar da kai." Hafsa kuwa sai tare mata takeyi tana fadin "Sam! ba haka bane."
Afnan ta hau kan bed dinta tana tayi mata surutu da labarin skull dinsu ita dai jinta kawai takeyi, ta rasa wane tunani zatayi da ta sa'ka wancan sai ta kwance sam! wannan gidan ba gidan zama ba hankalinta har yanzu na kan harkokin siyarsar ta, taga sai wani gayyato mata mutane yake sai kace wata wacce tazo zama."
Sun jima suna hira dan sai da suka dauki kusan awa biyu tukkuna sannan suka niyar tafiya, har lokacin Afnan na tare da Wasila suna hira dan tun tana biye mata da surutun ta har tayi mata shiru itama ta gaji ta kwanta bacci ya dauketa....Ya shigo dakin ya same su kwance kan bed a tare ita Afnan din baccinta yayi nisa sosai itace dai take ta kokarin gayyato baccin yazo yaki zuwa.
Mikewa tayi zaune tana daura dankwalinta, ya tsaya kusa da ita a nutse yace."Yarinyar nan fa tun bata sanki ba, take zumudin ganinki gashi ta makale miki ya za'ayi ne momynta tace zata kwana biyu a gurinki kina ganin babu matsala ko."?
Yafad'i wannan maganar ne saboda kawai baya son shiga hakkinta idan taga zata iya daukar yarinyar shi bai da matsala,
Jim! tayi itafa bata so ta sha'ku da kowa ballanta hakan yazo ya dameta wane irin zama za tayi a gidan! da har za'a na'nika mata yarinya,
Domin kar ta watsa wa maman yarinyar kasa a ido yasa tace."Ni meye nawa a ciki gidanka ne fa, tayi zamanta." Yace."Eh ai nasan gidana ne ai kece matar gidan dole kina da hakki akai.'
Shiru tayi masa, yace."alamu sun nuna kin amince kenan? Kallonsa tayi ya d'aga mata girarshi guda tayi saurin dauke kanta gabanta na faduwa, yace."Ki fito zasu tafi sai kuyi sallama ko."
Mikewa tayi, ya juya baya yana tafiya kallonshi kawai takeyi sai wani magana yake mata yana dage mata gira kamar wani dan saurayi mutum da girmanshi da komai sai iyayin tsiya,
Su Khalifa na tsaye suna jiran fitowarsu, dukaninsu basuyi tsammanin Afnan zata zauna ba sai suka gansu sun fito babu ita, cike da mamaki! Hafsa tace"Ina Afnan din."? Ahamdu yace."Ina ruwanki da ita kuma yanzu." Rike baki tayi tace"Nifa duk wannan abin da nakeyi wallahi cikin wasa nakeyi ko kayanta daka gani saboda kar tayi min kuka ne yasa na had'o mata muzo dasu, amma ni nasan rigimar Afnan ba zata barku kusha ruwa ba a gidanan."
Khalifa yace."To nima dai haka nake gani amma dai shikkenan." Wasila tace"Kai don Allah ku kyaleta mana ai babu wata matsala bacci ma takeyi ai ni nasan ba zatayi kuka ba."
Khalifa yace."Shikkenan ai dama bamu ce komai ba." Murmushi kawai tayi tace"To ku gaida gida mungode.' Hafsa tace"amarya yaushe zaki kawo min ziyara ne."? Dan murmushi tayi takasa magana sai shine yace."Idan ta kwana biyu zan kawo miki ita amma bana son gulma." Hafsa tace"Kasan kuwa idan mun hadu sai munyi gulmarku." Yace."To na fasa kawo ta tunda d'abia mara amfani zakuyi." Hafsa ta dinga dariya tana fadin"saboda rashin gaskiya ba, ai da kafarta nasan zata zo inda nake mu kashe mu binne."
Murmushi kawai yayi bai sake cewa komai ba, suka nufi kofar fita a tare, Wasila tana tsaye daga inda take tana musu fatan alkairi da sauka lafiya.
Sai da ya tabbatar motarsu ta fita daga gidan sannan ya koma cikin....Parlo yay zamansa yana kallo da tunanin yanda zai kai kansa gurin yarinar da daddare baya jin zai iya daga mata kafa a yau din nan.
***
Camas! kuwa lokacin da ta bar gidan Wasila kai tsaye gidanta dake tishama ta nufa, lokacin su Uwani da rashida abin duniya ya damesu sun tasa lafiyayyan abinci a gaba sun kasa ci sai tunini suke, Da jin labarin da Camas tazo musu dashi sai hankalinsu ya kwanta, jin cewar Wasilan na cikin koshin lafiya gashi har ta bada sallahun a fada musu cewar tanan kalau kuma su kwantar da hankalinsu tanan fitowa ta cigaba da rayuwa a tare dasu, Uwani ce kawai taji dadin wannan magana amma ita Rashida sam bata sha'awar wasila ta fito daga gidan Ahamdu tana ganin Allah ya gama yi mata suttura tunda ya gamata da miji nagari kamar wannan bawan Allahn.
***
Camas! bayan ta bar gidan su Uwani sai ta wuce can getshouse din As wato Alhaji Tasi'u lokacin yana tare da baki sai da tayi jira tukkuna ta shiga.....Yana ganinta yace."Tuntuni nake saka ran zuwanki shiru da yanzu nake tunanin kiranki a waya.
Tace."Wallahi kuwa ai ina tafe na dan tsaya wani guri ne." As yace."Okey bani labarin yanda kukayi kin samu ganin Wasila.....Tace."Kwarai kuwa har mun shirya shawarar yanda za'ayi." Tiryan tiryan! ta fada masa yanda sukayi da Wasila da irin alkawarin da tayi kan in ta fito daga gidan Ahamdu to ya saka ransa cewar ta zama mallakinsa.
As ya dinga washe baki yana shafa sumar kanshi tabbas idan hakane to ko nawa ne zai iya kashewa duk dan ta samu nasarar fitowa daga wannan gidan....Yace."Yanzu abinda za'ayi shine ki bani accont numbar naki zan miki sending din kudi masu dan kwari, wanda zasu isa kuyi abinda zakuyi dasu, gaskiya naji dadin wannan labari naki dole ne ma nayi miki alkairi."
Camas! dadi ya isheta tasan As bashi da kwauro mutum ne shi mai sauki da dogon hannu har yaso yafi governor mi'kawa, itana wasilan duk da bazarsa take rawa, ta bashi account numbar dinta a take ya tura mata dubu dari hudu yace nata duba dari dubu dari uku kuma taje tabawa masu gadin gidan Ahamdu idan sunki amincewa ta dawo zai kara wasu.
Godiya tayi sosai sukayi sallama da juna, tare da sharadin gobe zata fara aiwatar da aikinta...
***
Tun yamma Hadari ke had'owa daf da magariba gari ya turnuke sosai da kura iska na tashi da ledoji.....Dai-dai wannan lokaci Afnan ta tashi daga baccin da ya dauketa tun bayan tafiyar