YAR BANGAR SIYASA BOOK COMPLETE By Binta Umar Abbale .txt

Author :  Binta Umar Abbale Category :  Romantic Books

Chapter   16 / 57

45K to 48K   out of 169.7K words

zazzagawa Rashida masifa kamar za tayi mata baki kan kawai tace ba zata raka ta Garko ba gurin malam mai allo.




'Bangaran Gidan Governor kuwa duk wanda ya san muhimancin Wasila a tafiyarsa ta siyasa sai da ya jajanta al'amarin mussaman governor da babu irin zagin da baiyiwa Ahamdu ba, shawarwari suke 'kullawa kan yaya za'ayi su fito da Wasila daga cikin gidan.....Camas! da yanzu ta zama a madadin Wasila tana zaune kusa da mutumin nata Alh Ma'aruf tace"Ga shawara nasan za tayi mutukar tasiri da amfani." Duk suka maida hankalinsu kanta....Tace." Mai zai hana kawai a dauki matakin she'kashi barzahu ta hanyar 'Yar gasken Tayi kwance kwance ta saki jiki dashi tanan ne zamu samu dama mai sauki a kanshi a take sai kaga anyi masa kwaf daya ba tare da mutane sun ankara ba, kaga mun ci riba biyu a kansa.


Governor yayi murmushi yana fadin"Hakika wannan yarinya 'kwalkwarki naja sosai wannan shawara taki itace dai-dai a halin yanzu duk abunda mukayi jama'a zasu gane mu da sauri shi kansa ma zai gane mu abinda zamuyi shine mu dauke hankalinmu daga kanshi ta bangaran auranshi da Wasila, mu cigaba da harkokin siyasarmu kamar yanda mukeyi......As yace."To yanzu meye abinyi."? Camas! tace"Ku bar komai a hannuna da sannu zan aiwatar mana da 'Kudirinmu insha Allahu duk yanda zanyi zanyi in samu nasarar shiga gidan duk dai ya zuba matakan tsaro amma hakan bai zai hana na samu hanyar shiga ba, zan samu Wasila zamu tattauna kan maganar da muka yanke daku."
As yace."Ban ta'ba ganin d'an akuya ba kamar *Ba Iya ka!* ashe kwance kwance yayi mana, yasan wannan yarinya nada amfani a tafiyarmu sai da ya san hanyar da yabi dare da rana ya rabamu da ita, Zai gane shayi ruwa ne."!!!!




To kamar yanda Dr Nasir ya fada hakane ya kasance da Wasila misalin karfe goma shabiyu na dare ta farka lokacin ruwan da aka daura mata ya kare, Ta farka da wata matsananciyar yunwa cikinta sai 'kugi yake, hannunta ta dan daga kadan tana rintse ido sosai hannun yayi mata tsami! ta sanya daya hannun ta cire abin da akayi mata karin ruwan tana dan matsa gurin.....Tana zuro kafafunta da niyyar sauka daga bed din ya turo kofar dakin ya shigo.....Yana sanye da Pyjamas kirjinsa a bayyane kasancewar bai daure igiyoyin rigar ba....Da sassarfa ya karasa kusa da ita yana tambayar ta jikin nata....kasa kallonsa tayi ta rasa wane irin iskanci ne wannan haka kawai sai ya dinga zuwa inda take da kirji a bude shi gashi 'kato, duk sanda idanunta suka sauka a kan faffadan kirjinsa takan ji wani iri a tare da ita, shiyasa ko da wasa bata son kallonsa cikin irin wannan shigar....Yana tsaye yaga ta mike tsaye jikinta da kwari bata tangadi da layi irin na dazu nan ya fahimci ta dan samu rangwame ya bita da kallo har ta shiga toilet......Minti biyar tayi a ciki ta fito,Bakinta ta wanke ta dan dauraye fuskarta babu abinda take muradi sai abinci ko wane iri ne....Ta zaune gefan bed, shi kuma ya fita, Bai jima ba ya shigo dakin hannunsa rike da plate mai murfi ya ajiye mata kasan kafet...A nutse yace."Ga abinci nan dauki kici kafin kisha magani." Ya dauka za tayi masa musu sai yaga ta sauko kasan kafet din da sauri ta bude plate din abincin, tana juyawa.....Pride rice wacce tayi kayan lambu da hanta a take taji yawun bakinta ya tsinke ta ciko cokali da sauri ta tura a bakinta....Fita yayi da niyar dauko mata magungunanta, Yana dawowa ya iske ta cinye abincin nan tas! ko 'kwallon shinkafa ba ta bari ba, sosai ya shiga mamaki! ya dinga kallonta yana kallon plate din....Kunya ce ta kamata sai ta dinga dauke kanta tana zumbura baki.....Gyaran murya yayi yace."Kar'bi magani kisha idan kuma abincin bai isheki ba akwai a kicin Okey."!


Kamar ta'ki karbar maganin sai dai ta karba sai taga kuma kanta zata cuta ta mika hannu ta karba....Ya kama hanya ya fice daga dakin abinsa......Ajiye maganin tayi tana tunani, Ita abincin nan bai isheta ba gashi tana jin kunyar zuwa ta 'karo....Mikewa tayi ta bude kofar dakin a hankali! Taga baya palon ta dauki plate din ta fita, da lalube ta iske kicin din, ta tsaya tana kare masa kallo, kicin sai kace d'aki anyi masa jere iri iri da na'urori har da Ac freezer irin na kwance guda uku shin kanshi Gas din dake kicin din bata ta'ba ganin irinshi ba, kicin din yayi masifar burgeta, ta dinga kalle kalle sai da ta gaji ta bude tukunyar dake kan gas din ta d'ebo abincin ta fito......Sun kusa buga karo dashi yayin da yake kokarin shigowa cikin palon ita kuma ta fito daga kicin din...Da sauri ta matsa gefe gabanta na faduwa! Ya kalli plate din hannunta yaga ta ciko da abinci , kamar yayi magana sai kuma yaja bakinsa ya kulle, ya nuna mata hanya da hannunsa, Simi-simi ta wuce kunyar duniya duk ta isheta karfa guy nan ya dauka ita mayunwaciya ce ko zulamammiya asali ma ita abinci bai dame ta ba takan iya yin ci biyu kacal a rana ko taci sau daya in dai za tayi ciye ciyen ta.




Koda ta sanya abincin a gabanta kasa ci tayi tunda tayi loma uku sai ta ajiye cokali ta zabga uban tagumi tunanin rayuwa ta shiga yi, tun da suka taso ita da 'yar uwarta da mahaifiyarta suke shan wahala a duniya babu irin wuyar da mahaifinta bai sha kan asirinsa ya rufu har wanki da goga yayi kana kuma yayi faskaran ice ya sai da kayan miya duk wata sana'a da Yahuza mai rasuwa yasan zaiyi yanayi duk dan asirinsu ya lullu'bu! Sai dai kash! Allahn da ya hallici Uwani ya hallice ta ne mara godiyar Allah duk irin dauki ba dadin da Babansu yake yi a kansu bata gani, tun suna yara kananu take so ta koya musu bin maza tallah babu irin wanda bata dorawa Rashida, saboda itace mai dauka ita kuwa duk ranar data dora mata tallah to sai ta zubar da kayan a kwata tana sane dan haka sai ta daina dora mata, lokatan baya samari yan banabakwai har sun soma latse Rashida tun bata kai shekarun hakaba, wannan dalilin ne ya sanya bacin rai ya kwantar da Yahuza ashe kwanciya yayi wacce ba zai tashi ba yazo yayi mutuwa fuju'an!! Sai suka sake shiga tsananin takura da damuwa da rashi da kuma kangi na talauci!


Uwani itama marainiya ce ita sam bata ma taso tare da iyayenta a hannun Kanin babanta ta rayu rayuwar da tayi a gidan Kawunta mara dadi ce tasha wuya sosai matansa suka mayar da ita yar aiki komai itake musu ga yayansu baza su sanya su aiki ba sai ita tanaji tana gani zasu tura yayansu makaranta amma ita tana zaune dan da Kawun nata yayi niyar sanya ta a makaranta sai su ka nuna rashin amincewarsu saboda suna ganin duk sanda ta fara zuwa makaranta to aikin gida zai dawo hannunsu, shi kuwa dama mutum ne da baya kaunar bacin ran matansa da yayansa, sai ya kyale Uwani ta dawwama cikin bauta babu a rabi babu boko...
Gurin yawon cefane suka hadu da Yahuza a lokacin yana siyar da kayan gwari! Aikuwa tsabar kyawunsa ya sanya Uwani makancewa a kansa, duk da a lokacin manya mutane masu hannu da shuni sun fito suna sonta, ciki harda Ubangidan Kawun nata, tace Ita Yahuza take so, Kawu yayi yayi da ita ta amince da Ubangidansa ta'ki fafur! Gefe guda Matansa na kara ingita kar ta auri Alhaji Bala, domin suna ganin idan ta aureshi to ta wuce takaici sai suke bakin cikin hutun da zata samu suka dinga zugata da fadin"Idan ta aureshi matarsa sai ta kasheta dan Hajiya Larai bata zama da kishiya tasha haukawa kishiyoyinta, da jin wannan magana tasu sai Uwani ta sake rikicewa ta tsorata ta tuburwa kawu dole ta sanya yace da ita maza maza ta sanya Shi Yahuzan ya turo magabantanshi......Yahuza ya dauko Malam mai allo da Kawunsa suka zo har gurin Kawun Uwani aka tsaida maganar daurin aure........... Ranar da aka daura auran Kawun ya bata sadakinta a hannunta yace."Uwani tunda ke baki dauke ni a matsayin uba ba kina bujerewa umarnina to shikkenan kije na yafe ki daga zuria ta tunda Yahuza kika zaba kije babu ni babu ke kar in sake in sake ganin kafafunki a gidana duk sanda kika zo min gida to sai nayi miki korar kare kije yan uwan Yahuza su zama yan uwanki." Uwani ta dinga kuka tana bashi hakuri, fatafata! yayi mata ya kore ta....... Wannan shine dalilin da ya sanya Uwani take rayuwarta ita kadai daga ita sai 'Yayanta, kuma tun sanda Kawunta ya koreta bata sake taka kofar gidansa ba kana kuma bata barin su Wasila suje gidan.
Abinda ya janyo musu rashin jituwa da Kawu mai allo lokacin da Yahuza ya mutu da yazo ya dauke mata 'yayanta tayi magana ya farfada mata magana mai zafi! ashe dama tun lokacin daurin auranta da Yahuza Kawunta ya dinga fadawa Malam din bata da hali bata jin magana gararrariya ce bata da biyayya dalili kenan da ya sanya yayi mata aure, to tun daga lokacin Kawu Malam yake mata kallon mara tarbiya gaba mai muni ta shiga tsakaninsu A cewarsa ai tunda ba tayi wa Kawunta biyayya ba to waye kuma za tayi wa....Da fadin wannan magana tasa ita kuma sai ta kudiri aniyar cewar in dai itace mahaifiyarsu Wasila to itama ta dauki alkwarin ba zasu ta'bayi masa biyayya ba zai ga rashin tarbiyarta a zahiri.




Wasila kuka take sosai tana 'kara kulatar malam mai allo a ganinta duk shine silar fadawarta cikin wannan halin da take ciki, haka kawai zai kama ya daura mata aure da wanda bata so alhalin bashi ke ciyar da ita ba kuma bashi ke shayar da ita ba asali ma kullum cikin aibatasu yake ita da mahaifiyarta ta tabbata kudi Ahamdu ya sakar masa shiyasa ya rude ya yanke mata wannan hukuncin tayi al'kawarin insha Allahu daga shi har Ahamadun sai ta basu kunya auran da suka daura dashi da babu duk daya domin tananan a kan bakanta, sai ta kufce daga gidan.








*_A jikin d'an yan zogale akwai Wani abu kamar fure zaku ganshi saman zogale to wannan abin ba karamin sirri bane a tattare da 'ya mace yana mutukar saukar da ni'ima nan take! duk bushewar ki da rashin ni'imar ki idan kina tauna wannan abun na jikin zogale kina matsi dashi sai kin zama 'korama! 'yar uwa ki gwada ki gani zaki bani labari! Ki cire ki sa a bakin ki ki tauna yayi laushi sai ki cusa a gabanki kina zaune a inda kike zakiji wandonki ya jik'e yini zakiyi kina tsarki, amma kuma 'yar uwa ki yawaita tsarki da ruwan d'umi domin in kina da ni'ima! kuma a bude kike kinga anyi biyu babu namiji naso yaji gam!gam! sannan yaji ruwa na gudana a jikinki inda yana sanya jijiyarsa a jikinki zai shi tamkar a cikin teku.....Wannan sirri na baku saboda kauna, ki gwada 'Yar Uwata🙋🏻‍♀️_*








Kika futar min da book! Na barki da Allah! Kika karanta baki biya ba kema ke da Allah! Whasap numbar
*07084653262*[07/08, 11:49 pm] +234 803 238 4602: 'Yr Bngr Sys
*28*
Da sassafe Uwani ta shirya tsaf lokacin ma Rashida bata tashi ba ta kama hanyar Garin garko....lokacin da ta isa garim Malam mai allo na tsangayarsa, ta iske matarsa bitan tana aikace aikace kamar yanda ta saba, Bitan ta shimfida mata tabarma tana mata barka da zuwa Uwani sai cika take tana batsewa tana fadin"Ni fa ba zama nazo ba nazo gurin mai gidanki." Bitan tace."Ayya aikuwa yana tsangaya tare da almajirai sai bayan sallahr azuhur zai shigo! Uwani tayi shiru tana dan tunani, Bitan ta kawo mata ruwa cikin kwanan silva ko kallon ruwan ba tayi ba ta mike tana fadin"Ni zanje tsangayar tashi domin inyi abinda zanyi in tafi." Bitan! tace"Haba Uwani idan hankali ya 'bata nutsuwa aka sawa ta dubu shi kiyi hakuri ki zauna mana har ya shigo gidan sai kuyi maganar ni nasan abinda yake tafe dake.
Da fadin wannan magana ta Bitan Sai Uwani ta hau masifa dama 'kiris take jira tace"Ashe kin san abinda ke tafe dani amma kike cewa na zauna wato tare dake aka hada baki aka daurawa 'yata aure ba tare da na sani ba ko? kunga kudi kun rud'e daka ke har Mijin naki gashinan lokacin kankani har naman wuya kinyi to wallahi da sake kamar yanda malam ya tozartani ya wulakantani ya nunawa duniya ni ban isa ba to nima sai na kunyata shi gaban almajiransa.


Bitan tace"Ki daina wannan maganar Uwani itafa rayuwa da kike ganinta 'yar sannu ce wannan balo'kokon da kikeyi duk a banza tunda dai aure an riga an daura ai magana ta kare kuma kina maganar munga kudi karya kikeyi mu ba makwadaita bane abin wani bai dame mu kije ki tambaya kiji yanda al'amari ya faru.''


"Babu wanda zan tambaya aini ba yarinya bace da zaki zaunar dani kina min wannan maganar na dauka wallahi idan nice na haifi Wasila sai nasa ta kunyata mijinki tunda bai san ya kamata ba."


Bitan! tace"Ai sai kije kiyi tayi mai dora 'yayanta kan turba mara kyau kece zakiyi nadama mara amfani." Uwani ta zura takalmata tana fadin" Ke da mijinki ne zakuyi nadama amma bamu ba aure kun daura saboda kuna samu kwabo da dari to ba zaiyu ba sai na kwance wannan auran wallahi."


Bitan! ta bita da kallo cikin tsananin mamaki! tabbas babu abinda yake damun Uwani sai jahilci a irin wannan zamani 'yarki ta auri mutum mai hankali kamar Ahamdu amma kice sai kin warware auran tabbas gaba tana tare da nadama.


Uwani na fita kai tsaye tsangayar malam mai allo ta nufa, tun kafin ta 'karasa ya hangota domun uwani ba bakuwa bace a gurinsa, Sai ya gyara zaman sa kan kujerar karfen da yake zaune yana sauraran isowarta,


Ganin ta iso inda yake tayi masa 'kerere a ka tare da fadin"Gurun ka nazo." sai ya fara kokarin mikewa daga kujerar ta daga hannunta "Dakata malam yi zamanka ba sai ka tashi ba." Ido ya zuba mata suma almajiran tun sanda ta fara magana suka dakata da karatun da takeyi suna kallonta.


"To an yanka ta tashi! duk wani 'kumbiya 'kumbiya da munafurcin da kuka kulla ya fito sarari Allah ya toni asirinka ni Uwani na samu labarin abunda kukayi wa yarinyata Wasila, Na farko dukaninku da kai da 'yan uwanka baku san ci da shan Wasila da Rashida ba tsawon shekaru goma sha, kwabonku bai ta'ba shiga tsakaninmu daku ba, Kuna katsina muna daura muyi aikatau muyi sirfau muyi daukau da duk da sana'ar data kama domin mu ciyar da kanmu kuna a matsayin iyayen Wasila da Rashida baku sani ba, to tur! da wannan zumunci naku Allah ya wadaran irin wannan zumuncin......Sai da na gama shan wahala da 'yayana suka girma suka kawo munzali sannan ne zaka nuna min iko a kansu! bai zai yiwu ba! Shin malam wane irin zagi ne ba kayi min ba wace irin kalma ce bakayi jefe ni da ita ba ! amma kuma saboda tsabar son zuciya katsaham! sai na tsinci labari a gari cewa ka daurawa 'yata aure saboda kwadayin abin duniya! Yanzu bakaji kunyar wannan abun da ka aikata ba."!? Ta kare maganar tana tsare shi da manyan idanunta.


Malam jikinsa yayi kwata'kes! tunda yake a duniya ba'a ta'ba tsinkashi cikin jama'a ba irin yau!!! amma babu shakka Uwani ta gawurta gurin rashin kunya da rashin arziki.....Ta sake tsareshi da ido tana fad'in"Kai nake jira ka bani amsa malam."? Gefan babbar rigarsa yasa ya goge gumin goshinsa, Yace."Idan kin koma gidana a nutse zanzo nayi miki bayanin yanda al'amura suka kasance."


"Babu wani gidanka da zan koma in koma inyi me? hukunci na riga na gama yankewa shine idan kana takamar kaine waliyin Wasila to nice nan na tsuguna na haifeta saboda haka ka kwana da shirin wannan auran da ka daura shi da niyar biyan bukatar ranka sunanshi lalatacce don ko sati biyu baza'a cika ba sai Wasila ta fito, mu zuba ni da kai." Tana kare maganarta ta kade zaninta ta kara gaba, zuciyarta wasai! yau ta rama irin rashin arzkin da malam yake mata shekara da shekaru.


Uwani na barin gurun malam ya sunkuyar da kanshi 'kasa masifar kunyar al'majiransa yake yi babu shakka dukanin maganganun da Uwani ta fada a kanshi gaskiya ne, tun bayan rasuwar dan uwansa Yahuza da ya dauko su Wasilan suka bujere masa tsayin shekaru goma sha biyu bai sai waiwayar inda suke ba daga shi har sauran 'Yan uwanshi, Uwani ita ya kasance take dauki ba dadi da 'yayanta har Allah yasa suka kai munxalin girma.....Hakikanin gaskiya yanzu shima ya gano laifinsa, zumunci ba abun wasa bane a lokacin da su Wasilar suka bujere masa a kwai kuruciya a tare dasu bai kamata yace zai wofintar dasu ba a matsayinsu na wad'anda basu da kowa a garin kano Uwani tayi namijin kokari a kansu da rayuwarsu.......Yanzu ya gano abunda suka aikatawa yaran sam bai cancanta ba kuma duk abinda Uwani tayi masa a halin yanzu bata dai laifi tabbas hakane kamata yayi kafin daurin auran a sanar mata kome zatayi dai na lokaci kankani ne magana ta wuce amma ga yanayin yanda yaga ta dauki lamarin da zafi dole yayi wa tufkar hanci idan ba haka babu shakka tana iya zuwa ta girgid'e wannan auran da ya daura wanda yake sanya ran mutuwa ce zata rabashi.....Ya sake sanya gefan rigarshi ya goge gumi kana ya dago yana kallon almajiransa sai hayaniya suke! bulala ya d'aga Yace."To a cigaba a cigaba.''!!! Su rud'e da karatu ko wannensu da allo a hannunsa.


*****


Camas! na tsaye a bakin gate din gidan Ahamdu suna fafatawa da masu Gadi! Magiya take musu suna sake botsarewa "Kinga Hajiya Wanzu Mai gidan ya fita kuma bai sanar damu zuwanki ba, a 'ka'idar shiga wannan gida sai kana da shaida idan kina

16 / 57