YAR BANGAR SIYASA BOOK COMPLETE By Binta Umar Abbale .txt

Author :  Binta Umar Abbale Category :  Romantic Books

Chapter   52 / 57

153K to 156K   out of 169.7K words

daukar abinda zata dauka wanda zata karya dashi ta bar daining din dan ta lura hankalin Yayan nata nakan yayarta wanda ta fahimci kamar ma baya cikin hankalinsa dan har ta gama abinda za tayi a gurin be kalli inda take ba.


Wasila ta juyo tana dariya da fad'in "Kai Hajja! idan kin tafi ai ba Kishiyarki ce kadai zatayi kewa ba har damu dan Allah ki zauna kada ki tafi wallahi ba zamuji dadi ba." Hajja tace"Tafiya kuwa ta zama dole gobe i war haka na sauka a gida." Tana tafiya domin isa dainnig din take''Gaskiya Hajja ba zaki tafi ba zamu shiga cikin wani hali na kew.......Kasa 'karasa maganar tayi ganin ya zuba mata ido yana mata wani irin masifaffan kallo tamkar zai cinyeta, a take ta dai-daita nutsuwarta ta dan rage walwalar fuskarta, ta dan gyara kujera ta zauna tana ya mutse fuska, ita sam bata lura ma dashi a palon ba, haba wannan kallo kamar mawuyanci."
Tea take kokarin had'awa hannunta ya shiga kyarma! sakamakon idanunsa masu mugun dafi da ya zuba mata, ta dan kalleshi a sace sai taga hankalinsa gabadaya nakan jikinta yana kallon brest dinta da suka fito ta saman riga........Taji dad'in hakan dama yaushe zai iya daurewa tasan halinsa sarai! sai ta dinga d'an gantsaro 'kirjinta tana d'an motsa jikinta da sunan tana gyara zamanta.......Wayarshi tayi ta ringing yana ji ya kasa dauka.
Ta dago a hankali tace"Ana kiranka a waya." Dan dauke kansa yay yace."Rabu da ita." Shuru tayi tana ta'be bakinta, ta had'a tea din zata fara sha yace."Bani wannan ki had'a wani."
Mi'ka masa tayi ba tace komai ba ta had'a wani ta fara sha tana had'awa da bread, tana kallonshi ya kasa shan tea din sai auki tsaki da yake saki yana latsa wayarsa, ba tace masa komai ta gama break dinta ta mike ta bar masa gurin...........Tashinta da kamar minti biyar shima ya mike a maimakon ya fita kamar yansa ya niyyata sai ya shige dakinsa ya kwanta, zazzabi zazzabi na nema ya rufeshi.


Ita kam Wasila taji dad'in yanda taga tarkonta ya kamashi, murmushi take saki lokaci da lokacin tana jin sanyi cikin zuciyarta, tasan ko bata kai masa kanta ba to tana da tabbacin shi da kansa xai kawo kanshi..........Tunda ya shiga dakinshi bai fito ba sai lokacin sallar la'asar Hajja na kokarin shiga ta dauro alwala taga fitowarshi shima da shirin zuwa masjid tace"A'a dama kana ciki baka fita ba."?
A dan kasalance yace."Hajja ban fita ba wallahi zazzabi zazzabi nakeji a jikina."Tace."Ashsha! yana da kyau kasha magani." Yace."Yanzu idan na dawo daga massalaci zanci abinci nasha magani." Tace"Allah ya sawa'ke." Ameen yace ya fice daga gidan.


Wasila kam bayan tayi sallah wani wankan ta sakeyi ta cancad'a kwalliyarta cikin kananun kaya, riga da sket ta gyara gashinta da mayuka sai sheki yake ta daure da katon ri


bbon dankwalin abaya tayi rolling dashi, ta fito palo tana zabga kamshin turaranta mai dadi........Tana zama Hajja tace"Kinga kuwa mijinki bai da lafiya ashe bai fita yau kwata kwata yana daki a kwance sai yanzu da ya fito zai tafi massalaci yake min bayani."


Ta danji gabanta ya fad'i kadan anya kuwa wannan rashin lafiyar ta gaskiya ce? maji ma magani dai." Abinda tafada kenan cikin zuciyarta.....Ya shigo palon gabakidaya jikinsa babu kwari ko ga yanayin tafiyarshi ma zaka fahinta har yayi nufi zama a gurin cin abincin sai kuma ya fasa ya nufi dakinsa.
Hajja tace"A'a ya zaka shige kuma kaci abinci kasha magani dan Allah kada ka bari zazza'bin nan yay 'karfi a jikinka.....Ya dan Juyo yana kallon Hajjan dan ko da wasa baiyi kuskuran kallon Inda Wasila ke zaune dalili be san halin da zai shiga ba idan ya kalleta yace."Hajja bana jin zan iya zaman gurin nan Ke! Ki kawo min abincin daki." Yafad'a yana d'an hararar inda take zaune." Hajja tace"Allah y sawa'ke Wasila tashi maza ki kai masa abincin ki tsaya yaci sosai yasha magani."
Wasila ta mike ta nufi dainnig bata da wata damuwa dan ta tabbatar da cewar cutar 'karya ce ya 'kir'kirarwa kansa.












Kika futar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya ba kema keda Allah Whasap numbar
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*alliya:
'Yr Bngr Sys
*80*
Yana kwance rigingine idanunsa na kallon rufin dakin ta shiga dakin hannunta rike da karamin tire dauke da kayan abinci a kai, sallama tayi a nutse ta shiga dakin, ya amsa sallamar ba tare da ya kalleta ba, a hankali ta dan jawo wani karamin teble ta ajiye tire din abincin ta dan tsaya tana kallonshi, har yanzu guri guda yake kallo......Kamar za tayi magana kuma sai ta girgiza kanta a hankali ta juya zata tafi, Gyaran murya yay yana kokarin mikewa zaune yace."Dawo ki had'a min abincin."
Ta dawo fuskarta babu wata cikakkiyar walwala....Kasan kafet ya sauka ya tankwashe kafafunsa, yana kallonta ta dan sunkuya tana hada mishi abincin Brest dinta duk sunyo waje tamkar ma batasa breziya ba, ajiyar zuciya ya sauke idanunsa kurrr akai yana shafa gemunsa, ta hada mishi abincin ta aje gabanshi, yace." dauko min ruwa me sanyi da lemo." Ta wuce can inda fridge yake nan ma ya bita da kallo,
tana juyowa ya dauke kansa yana dan juya abincin da cokali da kyar ya kai loma guda bakinsa ya ajiye cokalin yana fad'an "Anya zan iya cin abincin nan zazzabin nan ya sanya bana jin dadin bakina."
Ta lura magana yake nema da ita a takaice tace"Ka daure kaci kasha magani zakaji sassauci."
Yace."Zan gwada ci yanzu."
Ta ajiye masa lemon da ruwa ta kama hanya tayi ficewarta tana wata irin tafiya sassan jikinta na wani irin motsawa.
Jingina jikinsa yay jikin katakon gadon ya langwabe kansa tare da lumshe idanunsa tamkar wani maraya yana sake jin wani irin feeling na taso masa.
Da kyar ya iya cin loma biyar na abincin ya mike daga gurin
Wayarsa ya dauka ya kirata lokacin suna palo suna hira, mamaki ne ya kamata ganin kiran wayarshi,
Cikin wata 'yar iskar murya tayi mishi magana, ya sake shiga tashin hankali da damuwa, murya a sanyaye yace."Kizo ki kwashe kayan abincin." A hankali tace "To." Takashe wayar, minti biyu ta mike ta nufi dakin....Idanunsa tsaye a kofar shigowa so yake kawai ta shigo ya cigaba da kallon albarkatun jikinta masu rikirkitashi, ta shigo dakin, yabi fuskarta da kallo kamar tsohon maye, dan gyara bakinta tayi ta isa inda yake zaune ya wani mi'ke kafafunshi, abincin dake gabanshi ta kalla ta ganshi da yawa dan ko rabi be ciki ba.....A hankali tace"Ai baka ci abincin ba." Ya wani lumshe jajayen idanunsa ya budesu a kanta yace."Waye ya fad'a miki.!? Ta girgiza kanta da dan ya mutsa fuska tace."Ba kowa." Daga haka bata sake cewa komai ba dan ta lura neman shiri yake da ita ita kuma bata shirya ba tukkuna.
Tana kokarin harhada kayan abincin yace."Idan zaki zauna ki bani a baki zanci kasala ce take damuna da rashin kwarin jiki shiyasa na kasa cin abincin."
Tace."Allah ya sawa'ke!." Daga haka bata sake magana ba ta dauki tiren abincin ta futa daga dakin cikin zuciyarta tana fad'in "Nasan wayo kawai ka shirya idan waya da budurwa ne ai ba zakace kasala kake ba.
Tana aje kayan abincin a cikin ta samu wani madaidaicin bokitin roba ta zuba ruwa me kyau, kaninfari ta zuba a cikin ruwan me d'an dama ta mayar ta rufe, sannan ta bud'e freezer mai dauke da kayan miya ta dauko wata madaidaiciyar kabewa ta feraye ta ta yanka dai dai misali ta zuba ruwa ta dora a wuta, tana tsaye ta dawu ta sauke ta samu ludayi ta murjeta tare da ruwanta, fridge ta bude ta sanya a ciki ta fita daga cikin din dai dai lokacin Rabe ya shigo domin ya fara aikinshi na abincin dare.




*****
Camas da Silinda sabuwar yarinyar dasu As suka samu kenan wacce ta zama makwafin Wasila dan abinda Silinda takeyi wane Wasila, tunda Silinda tazo government house suke fad'a da Camas! dan ganin komeye za'ayi sai a turata gefe guda Silinda itace a kan gaba, ko yawonsu sukaje na campaign Idan sun dawo Silinda ake bawa kudi ita kuma ta bata abinda tayi niyya shiyasa kullum suke cikin fad'a da juna, Camas! ta kare mata dan duk 'yan kud'ad'en da take samu sun 'kare 'yan damfara sun damfareta kowa ya samu rabonsa yanzu motar kanta bata da ita manya sutturunta ta kwashe ta kaisu gurin mata na kasuwar rimi ta siyar a banza a wofi dan idan ba tayi shaye shayenta ba bata jin dadi, gashi governor kwata-kwata yanzu ya daina sakin kudi kamar da suma su As din lallabawa suke domi


n governor Lawan Rabo ganin yanda jama'ar gari ke masa tawaye ta kowane fanni yasa yasha Jinin jikinsa yana ganin da wuya ya kai labari dan tuntuni ya sare da al'amarin saboda kusan kullum idan ya fita sai jama'ar gari sunyi masa ihu anyi fad'a da 'kona 'kone dan akwai wani matashi ma da yay kundumbala yayi tsale kan titi motar da yake ciki na gudu ya d'aneta sai da ya fasa gilashin motar da wata shar'bebiyar wukarsa wai sai ya kasheshi yayi masifar tsorata da al'amarin ya kuma fahimci cewar jama'ar jahar tashi a shirye suke da shirin ko ta kwana suna jiran lokacin za'be yazo yasan idan yace dole sai ya zarce to zasu iya halakashi, a take securities din da suke tare da governor din suka farwa wannan matashin da duka sai da sukayi masa jini da majina tukkuna suka daddaureshi suka kaishi suka kulle.


Silinda ta kaiwa Camas! wani bahagon mari wanda ya sanya shatin hannunta suka fito rad'au! Camas ta rike kumatunta tana wani irin huci tace"Me nayi miki kika mareni."? Silinda ta hau cusa mata ashar tana fad'in "Waike wace irin dabbace shegiya kawai wane kudi kuma zan baki jiya da muka dawo ba na baki dubu goma ba shegiya kawai wacce babu abinda ta iya sai shaye shaye."
Camas na 'kwallah tace"To ina ruwanki idan ina shaye shaye da kudinki nakeyi macuciya kawai tare fa muke tafiyar nan amma idan an bamu kudi mu raba sai dai ki bani abinda kikayi niyya jiya a gabana ina gani As ya baki dubu hamsin yace mu raba sai ki bani dubu goma saboda ke 'barauniya ce!."
Silinda na cije baki tana hura katon hancinta tace"Wallahi Camas kika sake wata magana anan gurin sai na hanaki shigowa wannan gidan kin san dai yanda kusancina yake da governor zan iya tozartaki wallahi gwarama ki lallabani ki zauna lafiya kina gani duk taurin kai irin nasu kwage da Mada sun sallama min ballanta ke banza galli ga horo." Camas ta sha'ki hanci! tana jin wani irin takaici a ranta ta girgiza kanta ta wuce ta bar gurin tamkar kububuwa."
Silinda taja tsaki tana tsartar da yawu ta wuce ta nufi inda motarta take tana karkad'a key.
Ta fito daga cikin gidan ta hangi Camas na tafiya a 'kafa takalmin 'kafarta na gurd'eta, Dariya tayi hade da buga sitiyarin motarta tazo ta wuceta fuuuuuuuu! Camas! ta tsorata da sauri ta matsa gefe tana cizar yatsa(Hausawa na cewa idan zaka gina ramin mugunta to ka gina shi dai-dai da kai dan watarana kaine zaka fada ciki)




*****
*Malam Mai allo*
Yau kusan sati guda kenan yana irin mafarki guda daya, kawai sai ya yanke shawarar yin istahra domin yana so zuciyarsa ta amince masa da abinda yake gani cikin mafarkinsa, karfe daya na dare ya tashi ya daura alwalarshi a nutse ya gabantar da istahara kamar yanda annabi ya koya mana, ya nade dadduma ya koma ya kwanta bacci, cikin iko n Allah sai dai ya sake yin irin mafarkin da yake yi dai shi da ita wannan karon ma gashinan har da albarkar haihuwa dan yaro 'karami ya gani a tsakaninsu, zuciyarsa ta aminta da abinda Allah yake nuna masa cikin mafarkinsa tsayin sati guda, tabbas jikinshi na bashi alkari ne tartare da al'amarin, kawai sai ya yanke shawarar tunkarar inda take ya cire fargaba da shakku gami da tsoron kada tayi masa rashin kunya kamar yanda ta saba.


*Allah ya tabbatar mana da Alkari*




******
Bayan ta idar da sallah isha'i ta nufi kicin, abinda ta ajiye a frdge ta dauko ta fasa madara gwangwani guda biyu ta juya kan damammiyar kabewar nan ta juya sosai ta hade jikinta sai ta zauna kan wata kujera a kicin din ta shiga sha a hankali a hankali tana lumshe idonta, za'ki za'kin kabewar da gard'in madarar na ratsata,( Macen dake yin irin wannan had'in tana sha to za tayi gard'i tayi za'ki sosai sannan gabanta zai ciko kuma zata dinga jin sha'awa a kai a kai zakiyi ni'ima wacce maigida zai dinga sakar miki ihu yana sa miki albarka)


Sai da tasha sosai sannan ta mayar da ragowar fridge ta bud'e ji'ka'kken kaninfarin data ji'ka ta sanya cup madaidaici ta d'ebo ta xauna ta shanye tas ta ajiye Cup din ta fita daga kicin d'in.


Tana 'kokarin shigewa bedroom dinta Hajja tace"Zo ki kar'beta ki bata nono tasha tin dazu take kusurkusur kin san idan ta fara tsandara ihu to ba zamuji da dad'i


ba." Tace"Hajja da wanka nakeso nayi wallahi."Hajja tace"A'a kada a shiga hakkin yarinyar nan Wasila zo dai ki fara bata nono tasha."
Sai ta zauna kusa da Hajjan tana fad'in "Gaskiya Hajja duk sanda kika tafi zanji jiki wallahi Allah yarinyar nan zata hanani komai da komai na rayuwa ita dai komai nono."
Hajja tace"Aikuwa dai tafiya ta ta zama dole dan gobe i yanzu ina gida.
Ta dan marairaice fuska tace"Yanzu Hajja da gaske dai gobe zaki tafi."? Tace"To me zan tsaya nayi gobe zan wuce insha Allah da safe zanje can gidana zanyi aikin wainar gero da za'ayi sadaka da ita, tunda Allah tasa kin yada ganye lafiya lau ai dole mugode Allah."
Tace"Hajja meye amfanin yin sadakar.''? Hajja tace"Wasu na cewa al'adace amma ni yanda na dauki al'amarin ba al'ada bace dan kayi sadaka ranar da ka yada ganye hakan na nuna cewar kana farin ciki da abinda Allah yay maka kuma duk yaron da ka bawa sadaka yaji dadi zaice Allah ya raya ya d'ayyaba."
Rashida dake danna wayar Wasila tace"Gaskiya kam ai sadaka maganin masifa ce ba laifi dan kayi sadaka lokacin da kake cikin farin ciki ko kuma ubangiji yay maka wata kyautar."
Hajja tace"Ai kowane mutum da irin fahimtarshi wasu mutanan babu ruwansu da yin irin wad'annan abubuwan."


Shigowarshi palon ce ta katse musu zance da suke, Hajja tayi mishi sannu da zuwa Rashida ma haka, ya amsa yana kokarin zama kujerar dake fuskantar Wasila, carbin dake hannunsa ya nannad'e a hannunshi Hajja tace."Jiki yay kyau kenan tunda gashi har ka iya zuwa massalaci.'' Yace."Alhamdullhi Hajja yanzu babu zazza'bin sosai sai dai ciwon kai kad'an kad'an!
Tace"Allah ya sawa'ke." Amsawa yay da "ameen.' Yana mai da hankalinsa kan Wasila dake kokarin gyara rigarta tace" Hajja kinga bacci za tayi ma." Hajja tace"To ai sai a goyata dan yanzu tunda tayi bacci da wuri kika kwantar da ita to idan ta gaji da kwanciya zata hanaki bacci da daddare."
Rashida tace"Kawo na goyata."
Tana kokarin mika mata yarinyar yace."Bani ita nan." Ta mi'ka masa ya d'orata saman kad'arshi yana shafa bayanta......Hajja tace"Aikuwa ka sabawa da yarinyar nan da haka to zaka sha wuya dan idan taji dad'i to cewa za tayi ba zatayi bacci a ko ina ba sai a kirjinka."
Yace."Hajja wannan goyon ne ni bana so sai naga kamar ana takure ta wallahi."
Hajja tace."Babu maganar takurewa, da goyo na kisa da duk baku rayu ba, dan kai d'in nan da kake gani babu irin goyon da baka sha ba a bayana."
Yace."Allah Sarki Hajja Ubangiji Allah y saka da alkairi ya kara miki nisan kwana."
Ta amsa da "amee." Tana murmushi hade da tuno lokacin kuruciyarshi sai da ta share hawaye a fakaice data tuno mahaifiyarshi Yafindo mutuniyar kirki Allah dai ya jikan musulmi."
Mikewa yay ya nufi bedroom din Wasilan da babyn a kafadarshi, shuru dakin sai Uban 'kamshin turaran wuta yakeyi
Turaran Wuta ne dana tsuguno wanda Hafsa matar Khalifa ta kawo mata kwana uku da haihuwarta bata ta'ba amfani dashi ba sai yau, mafi akasari tafi anfani da air freeshnar da tirare na tsinke koda ta haihu da irinsu ta dinga amfani yau kawai tayi sha'awar sanya na gurin Hafsa tana sanya shi kuwa dakin ya game da 'kamshi mai dadin gaske, turare ne wanda yaji kayan hadi ya kuma ji madarar turare 'yar gasken had'e ruwan ji'ko turarene da manyan mata ke amfani dashi, shi na tsugono d'in nada bala'in kyau sosai yana sanya gaban mace ya tsuke! yayi ta masifaffan 'kamshi, Allah Allah take ta fito daga wanka domin ta tsuguna kan turaran domun Hafsa tayi mata bayani dallah dallah cewar idan ta tsuguna kan turaran sai ta goga miski a gurin idan tayi kwana uku tana yin haka ita kanta zataji sauyi sosai dan gurin zai nuna alamun tamkar ba'a ta'ba haihuwa ba.
Tana fitowa kawai sai ta ganshi a zaune, gabanta ya fadi sosai gaskiya ita bata son haka to me kuma za tayi mishi da zai kama ya shigo mata daki......Ya dinga binta da kallo har ita isa gaban mirror towel din na 'bantarewa daga jikinta cinyoyinta na fitowa, rasa inda zai saka kansa yay sai kawai ya kwanta saman bed din hade da d'ora baby zahra saman cikinsa ya rintse idanunsa gam! yana sauke ajiyar zuciya yana jin yanda joystick dinshi ke wani irin harbawa......Ganin


ya juya mata baya ya sanya tayi saurin saka dunkule d'aya na turaran a cikin wutar ta tsuguna akai haya'kin na ratsa jikinta, kusan minti biyar tayi a haka sannan ta mike da sauri ta gyara towel din jikinta wanda yay dai-dai da mikewarsa zaune yana kallon inda take, da sauri ta bude wardrobe ta dauki riga da wando na bacci ta saka a jikinta ta gyara gashinta sosai ta saka hula mai wani irin ado a gabanta, turare ta fesa sosai a jikinta, ta nufi bed din,
Ta dan tsaya kansa, kamshin jikinta na fuzgarshi, kamar wani bugagge yake kallonta da lumsassun idanunsa, a hankali tace"Zan kwanta." Cigaba yay da kallonta ya kasa cewa komai." Ta sake maimaita maganarta nan ma be ce mata komai ba, sai kawai ta haye bed din tana dan turo bakinta, bargo taja ta rufe kafafunta dashi,

52 / 57