Author : Binta Umar Abbale Category : Romantic Books
fad'a masa dukanin maganganun da suka zo bankinta!!! Kokari yayi ya danne abinda ke damunsa ya dago kanshi yana kallonta tana kuka idanunta sunyi fululu! Ya zaro karamin hankici a a cikin aljihunsa, hawayen fuskarta ya shiga goge mata, tana kauda kanta hade da zumbura baki, sai da ya goge mata tas kana yace."Zanyi miki abu biyu da kika bukata amma banda na farkon....Kwanaki idan baki manta ba ni Ahamdu na tabbatar miki da cewar Ni ba zan rabu dake ba kome za'ayi kuwa, maganar na baki takardar saki ki ajeta gefe guda, Maganar mahaifiyarki da 'yar uwarki ni ban rabaki dasu ba, amma yanzu ki kwantar da hankalinki idan Allah ya kaimu gobe Ko Jibi ki shirya zan kaiki ki wuni tare dasu, maganar wayoyinki kuma, tuntuni na bayar dasu amma babu matsala idan mun fita zan siya miki wasu, maganar 'karshe da zan fada miki itace Kada na sake jin kin kira auranan namu da sunan 'kaddara idan ina kusa dake sai na fasa bakin ki! Ni wannan auran alkari nake so zama da samu kyakkyawar zuria da makoma, Saboda haka ki kiyaye kuma ki shiwa kawunki albarka a yanzu kuruciya ke damunki shiyasa kika kasa gane abinda ake so ki fahimta okey! nan gaba kadan nasan idan kinyi hankali zaki gane gaskiya." Ita dai jinsa kawai takeyi tuntuni ta shiga tunanin yanda za'ayi ta tsira a ranar da suka fita dama babban burinta ta futa daga gidan to duk hanyar da zatayi ta kubuta ta sani.....Yace."Yanzu kije ki wanke fuskarki ki sanya kwalli zakiyi bakuwa Hafsa ta kira waya tace xata zo dubaki." Simi simi ta sauka daga bed din ta nufi toilet zuciyarta wasai! Allah Allah take gari ya waye ta samu ta ku'butar da kanta...
Littafin na kudi ne.....!
Kika futar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya ba kema ke da Allah! Whasap numbar
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
[07/08, 10:55 pm] +227 98 36 59 34: 'Yr Bngr Sys
*45*
*'Dan sulaika communication center*
Nan yayi parking din motar kafin su fito sai da ya lalabi glass dinshi ya sakaye idanunshi saboda baya son sanya ido na jama'ar gari, fuskarshi dai ba 'boyayya bace tunda gashinan pastes dinshi na yawo sa'ko da luko na cikin gari da kewaye, yasan tilas ya shiga gurin nan jama'a zasu shaida shi, Handbag dinta ta gyara kafin ta sanya hannu ta bude kofar motar tana kokarin fitowa taji saukar hannunshi a bayanta, mayafinta da ya fad'i kan kafad'arta ya gyara mata ma'ana ya d'ora mata saman kanta, Ta dan juyo tana masa murmushi, Dan 'bata fuska yayi yace."Wannan gyalan naki na tuna asirin tufafin dake sanye a jikinki bashi da sirri gare ki kuma kin san da haka kika dauki riga mai faffad'an wuya kikasa bayanki duk a waje." Da sauri ta hau gyagygyarawa tana fad'in"Ai haka akayi yin d'in ki ba laifina bane." Yace."Wannan d'inki na banza ne, kyawun shi ki sanya a gidanki ba ki fita dashi ba kwata kwata ban lura ba sai yanzu dan haka ki zauna cikin mota in shiga in siyo miki wayar." Marairaice fuska tayi"Dan Allah ka bari mu shiga tare na gyara wuyan rigar ai." Tafada tana sake gyarawa.....Girgixa kanshi yayi ya dan zura jikinsa kan jikinta ya kulle motar kana ya bude bangaran da yake zaune ya fita daga motar ba tare da yace mata komai ba.....Kamar ta fashe da kuka, ta bishi da kallo tana jan tsaki! idanunta ya sauka kan wayayonshi dake aje, da sauri ta dauki daya hannu na rawa ta saka numbar As ta soma kira, As ya gane numbar dan haka da sauri ya dauka! Tace"As gamu cikin gate din *'Dan sulaika* ya shiga ciki zai siya min waya da badan ya kulleni cikin motar da tuni na fice sai dai ya dawo ya tarar bana nan."
As yace."Kar ki damu Sweetie yanzu *Mada!* yayi min waya cewar kan idanunshi kuka shiga gurin, yanzu abinda za'ayi shine! Mada da Kwage Lauje da sauran 'yan uwansu, zasu tare hanyar da kuka bi idan kin samu kin fito daga motar ki tsallaka titi ki bi hanyar ki ta dama zakiga motana a pake kawai sai na daukeki mu wuce." Murmushi tayi tace"Hakan yayi kyau Ogana naji dad'in hakan insha Allahu muke da nasara a kanshi." murmushi ya saki cike da samun nasara yace."Kada ki damu Swetie komai nayi miki banfadi ba." Tace"Allah ya bar kau.....Jin ana ta'ba motar ya sanya ta zabura! da sauri ta kashe wayar! Ya bude motar ya shigo yana dan kallonta tana rike da wayarshi tayi fi'ki fi'ki! alamun rashin gaskiya, Yace."Kirana akayi ne."? Girgiza kanta tayi tana kokarin goge numbar As d'in.....Tace"Ina duba pictures dinmu ne." Murmushi yayi ya mika mata wata leda mai she'ki da tambarin Dan sulaika jiki yace." kar'ba." Da sauri ta sanya hannu ta karba tana duba tamfatsa tamfatsan wayoyi ne guda biyu masu tsadar gaske ko wacce na cikin kwallinta, kwalayen wayar ta shiga budewa, tana murmushi a hankali tace"Nagode." Baice komai ba ya mi'ka mata wata 'yar 'karamar cover layin mtn ne da glo yace."Gashinan ko wanne nada rigstar akai sai ki sanya ko Allah ya sanya alkairi amma ki sani mutukar naga abinda ba shikkenan ba zan kwace wayoyina kamar yanda na kwace na baya." Shiru tayi mishi kokarinta ta bude wayar tasa layinkan ya karba ya sa mata, kana ya jona mata guda a charge Tace"Idan tayi ka tura min pictures din.".....Dan kallonta yayi yace."Sai mun koma gida Okey."
'Kasa tayi da kanta bata so hakaba amma dole ta hakura, motar ya kunna ya tuka suka fita daga gurin.
Can gidanta na Tishama suka nufa, sosai yayi mamakin lamarin, Governor Lawan Rabo mugu ne azzalimi yana kwashe kudin talakawa yana kyauta da bajinta dasu, Yarinya 'kankanuwa ya dauki Uban gida irin wannan ya mallaka mata Tishima Unguwace ta masu kudi kuma ginaginan dake GRA din manya ne da wuya kaga karamin gida a guraran, Ya silala motar tashi cikin gate din gidan ya samu guri yayi parking kana ya juyo yana kallonta ita kuma sai kokarin bude mota take.....Yace."Ki daina wahalar da kanki shin kin manta na kulle kofar."? Shaf ta manta ya kulle zumudi take kawai taga fita.
Yace."Juyo ki kalleni." Kallonsa tayi tana dan gyara fuskarta. Babu wasa a fuskarshi da maganarshi Yace."Shin wannan gidan da kike ciki waye ya mallaka miki shi kuma kina da takardar shaidar mallaka."? Shiru ta danyi tana kallonshi, itafa bata son neman fitina ina ruwansa da gidanta tunda ba kwabonshi ne ya siya mata ba." Zai sake magana tayi saurin cewa"Gomnati ce ta mallaka min kuma takardun gidan banki." Hararata yayi yace." Ba cewa nayi ki fada min gomnati ce ta mallaka miki gida ba cewa nayi cikin manyan 'yan siyasan da kike mu'amula dasu waye cikinsu ya siya miki gidan."? Kai tsaye tace"Mai girma governor ne." Ya sake watsa mata harara! yana naxarin maganarta dama dai sai shi d'in gaskiya magana gidan zaifi miliyan hamsin, wannan ai haukane da jahilci yanzu zarginsa ya soma tabbata kan governor lawan rabo kwakwalarshi ta lalace shiyasa yake hauka a siyasan ce ya rasa akin yi da dukiyoyin jama'a yazo yana siyan manya manyan gidaje yana ajiye wai shi me wayo idan ya sauka a mulki su zame masa kadara, aikuwa ya dauki alwashin mutukar Allah ya bashi mulki a hannunsa sai ya had'ashi da hukumar Efcc sun binkiceshi duk wasu kud'ad'e da ya sata sai ya fito dasu, idan bai fito dasu ba sai yasha d'auri!
Ya kalleta sai wani 'kif!kif take da ido irin na marasa Yace."Wane banki kike amfani dashi."!? Da sauri ta kalleshi shin wai me yasa yake cin dunduniyar ta ne? me yasa dole sai ya san sirrinta."? Ganin ya zuba mata ido babu walwala a tare dashi yasa tace."Union bank ne." Gyada kanshi yayi yace."Zamuje tare dake domin kar'bar takardar gidanan sannan ina so nayi bunkice cikin asusunki."! bata san sanda tace"Kai!!!!!!!! da mamaki tafad'i maganar.
Girarshi guda ya d'aga mata yana sakar mata wani killer smile kafin yace."Ina so in kubtar dakene! dan bana so kisha wuya a gaba, ina me tabbatar miki da cewar ni *Ahmadu* mutukar Allah ya bani wannan jagorancin to duk wani 'barawo! mugu! mazanbaci! macuci! dake fad'in jahar nan sai nasa an kamo min shi na tuhume shi, kan zalincin da yayiwa jama'a cikin wadanda zan d'aure har dake mutukar kikayi min gardama kan abinda na umarce ki, zanyi mulki ne tsakanina da Allah babu sani babu saboda zaki futo da dukanin kud'ad'an da kika 'barnatar ba tare da bin 'kaida ba."! Gabanta ya dinga faduwa tana ta kallonsa lebenta na rawa, wai shin shi wann guy ba zai kyaleta ta sarara bane? ashe tsugune bata kare mata ba koda sun rabu ita dashi zai cigaba da bibiyarta da dukanin abinda takeyi.....Tsoro ne ya kamata lokacin data tuno da cewar har yanzu fa Pose dinta na hannunsa kuma muhiman abubuwanta na ciki ciki kuwa har Atm dinta, amma kuma dole tayi gaggawar zuwa banki domin ta rufe dik wata kafa da zata tona mata asirinta gurin shi......Ganin duk alamun rashin gaskiya ya bayyana a tattare da ita ne yasa yace."Kije ku gaisa ina nan ki fito mu koma gida." Sai abun yazo mata biyu! lallaima wato shi da yana nufin ta shiga su gaisa yanzu ta fito su koma gida, Wallahi ba zai yuwuba! Kuka tasa kariris! 'bakin ciki biyu ya had'e mata, Tace"Ni wallahi bazan koma ba sai dare! kwana nawa rabona da mahaifiyata da 'yar uwata sannan kuma kace na fito yanzu." Ta dinga kuka tana shashsheka! Zuba mata idonsa yayi yana kallo, to meye abin kuka anan kuma? Kawai tace yay hakuri sai dare yazo ya dauketa sai ta hau kuka mtsss! sangarta da shagwaba na damunta......."Ya isa." Yafada cikin sanyin murya....Shiru tayi tana kallonshi, Ya ciro hankicinshi mai kamshi ya shiga goge mata fuska, yace."Shikkenan na bari sai dare okey karfe! bakwai ko shirya ana idar da sallahr isha'i zan shigo mu tafi." Daga kai tayi! Yace."Ki gaishe min da momyn tamu." Kallonsa tayi Wai Uwani yake kira da momynsa, ai ita gani take ma ya girmeta ko kunya wai momyn tamu! Tace"To." Za taji." Bude mata motar yayi yace."Shikkenan."? Daga kai tayi tayi gaggawar ficewa." Kawai sai taga Uwani da Rashida a tsaitsaye idanunsu kan motar ashe tun bayan shigowar motar tasu cikin gidan sukayo waje suka tsaitsaya suna jiran ta fito.....Shima da ya juya motar ya gansu sai dai su ba zasu ganshi ba kasancewar motar mai duhun gilashi ce (tintac) baiyi tsammanin da Uwani a cikinsu ba dan ya dauka ko 'kawayenta ko dai wasu daban! Saboda idan ka kalli Uwani a yanzu ko kusa ko alama ba zakace itace ta haifi su Wasila ba, saboda Allah yayi mata kyawun jiki sosai dan kusan ita Wasilan ta gado, zaka fi tunanin ko yayarsu ce ita..... da gudu taje suka rungume juna suna murna kana suka wuce cikin gidan cike da farin ciki haduwa da junansu.
Uwani sai kallon 'yar tata takeyi bayan shigarsu palon suka zazzauna kan kujera Wasila ta gaisheta tana tambayarsu bayan rabuwa, Rashida kuwa kallonta takeyi sosai tana mamakin yanda ta kara cika da kwarjini ta kara haske fatarta tayi luwai, abin sha'awa, ashe ba ita kadai ba har ita Uwanin mamakin sauyawar yar tata take cikin sati biyu kacal wasila ta zama wata hamsha'kiya komai na jikinta abin kallone hutu da jin dadi ya bayyana a tare da ita..........Uwani tace"Bayan rabuwa sai alkairi Wasila munanan kewa da damuwa sun dame mu amma ke kina can hankalinki a kwance kin hada 'kiba abinki ijin dai ba ciki kika bari kika dauka ba dan ni na soma zargin wannan sauyawar da kikayi.
Wasila tace"Haba Uwani wannan wace magana kike ? wane irin ciki kuma ai tunda naje gidanan d'an yatsana ban bari ya rike ba. Uwani ta sauke ajiyar zuciya tana fad'in"Alhamdullhi to yanzu me muke ciki." Wasila tace "Mun riga mun gama magana da As insha Allah komai yazo karshe zan cigaba da rayuwa tare daku aurena da wannan mutumin ya kare daga yau." Uwani tace"Naji dadin hakan! Dan na lura bashi da mutunci bai daukeni a matsayin mahaifiya yana kallona a tsaye ya tuka motarshi ya tafi, ko ya tsaya ya gaisheni to idan nice nasha wahalar haihuwarki da rainon ki sai kin rabu dashi har abada mu zuba mu gani."
Rashida tace"Wallahi anti Wasila ki kiyaye kiyiwa kanki fad......"Zanci Uwarki! kika sake min wata magana anan gurin!!!! Rashida tayi shiru tana kallonta ta cigaba da surfa mata ashar tana fad'in"Banza mara zuciya da kishin kai! a gabanki fa ya kad'a kansa ya tafi ba tare da ya gaishe da uwarki ba, kudi hauka ne! ni wallahi duk wanda zai ta'ba min martabar Uwata sai inda karfina ya kare, na lura ke din 'Yar jam'iyyarsa ce shi da wancan tsohon me allo to wallahi zaki fice min daga gida dik sanda kika sake min maganar banza." Rashida ta ta'be bakinta ta mike ta shige daki tana 'kunkuni." Tsaki taja ta maida hankalinta kan Uwani Tace"Wannan yarinyar bata da hankali wallahi." Uwani tace"Haka nake fama da ita kullum zagina ne kawai ba tayi." Wasila ta dinga zaginta tana fadin"Aikuwa mutukar tace zata goyi da bayan Ahmdu da mai allo to zata bar mata gidanta in yaso sai ta koma can garkon da zama.......Uwani tace"Wannan hukuncin da kika yanke shine dai-dai.
Nan Wasila ta shiga warware mata abubuwan da suka faru da ita gidan Ahamdu da yanda ya dinga sumar da ita yana mata kamshin mutuwa amma kuma bata fada mata cewar mu'amular aure ta shiga tsakaninta dashi, ta fada mata irin bindiddigin da yake mata da furucin sa kan gidan da suke ciki cewar idan ya kar'bi mulki sai ya tuhumeta idan ya kama ma ya daureta sai ya daureta kan kud'adan mutane." Uwani tace"To ai kema baki sukayi ba sata Kikayi ba saboda haka kada ki wani damu duk barazana ce babu abinda zai iya yi miki, Amma kuma nafi so, gobe mu kama hanya mu wuce potsikum sai 'kura ta lafa sai mu dawo mu san abinyi, sai dai kawai yaji kira daga kotu." Tace."To shikkenan yanzu dai dole zanje banki in samu na ciro kudi masu dan kwari a hannuna kafin zuwa goben."
Da misalin karfe biyar da rabi na Yamma Wasila da Camas! suka fito daga bakin union duk wasu kud'addanta ta sanya ankwashe mata su daga asusunta an maida accont din Camas kudin sun tasamma miliyan hud'u da d'aruruwa, Cikin rashin dubara da wayo ta barwa Camas! Atm din a hannunta suka wuce gida,
Sai gab da magariba suka isa, Uwani tayi musu girki mai dad'i da nama sukayi sallah tukkuna kafin su zauna zaman cin abincin, kira ya shigo Wayarta....Sabida tsabar yanda ta haddace numbarshi yasa ta gane, gabanta ya dan fadi sai dai ta dake! tayi masa sallama Ya amsa yana tambayar ta mutan gida tace"Sunanan kalau." Yace."Ina fatan kin shirya ko dan ganinan kan hanya." A kumbure tace"Abinci zanci." Murmushi ya saki wanda har sai da taji sautinsa a kunnanta, taji tsigar jikinta ta mike, yayi amfani da wata iriyar murya "Ki aje min nawa."! Ta sakejin wani bakon yanayi a jikinta jin muryar da yayi amfani da ita, Sai tayi saurin fad'in" To! ta kashe wayar dan bata so ya samu nasarar kashe mata jikinta....Uwani tace"Shine ko."? daga kai tayi kawai tana jujjuya abincin, Jin muryarshi kawai ya sanya mata kasala da mutuwar jiki!Uwani tace"Kiyi da azama yana zuwa ku tafi ni wallahi so nake inga komai ya faru na gaji da wannan abu." Wasila ta sakejin wani karfi da kuzari gami da dakiyar zuciya yazo mata, ta dan caccakali abincin ta ajiye cokalin kana ta 'kame kan kujera tana jiran zuwanshi.
Littafin na kud'i ne....!
Kika fitar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya ba kema keda Allah! Whasap numbar
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
[07/08, 10:55 pm] +227 98 36 59 34: *_Afuwa jiya nayi mistake gurin sa numbar a mai makon 46 sai na sake sanya 45 nasan dai babu matsala tinda book din na tafiya kan tsari.......VIP 'Yar Banga! sannu ku da 'kokari! ina 'kaunarku kuna fitar da book ina 'kara samun costomars😅🤝🏻 masu karantawa baku biya ba kuma sannuku da kokari 😎yawwa! guys mu cigaba da gashi!! ku d'auki abu mai amfani na cikin book d'in nan ku watsar da mara amfani......Muje zuwa_*
'Yr Bngr Sys
*47*
Kimamin mintuna goma sha biyar da kiran wayarshi, ya sake wani kiran yana sanar mata da cewar gashinan a bakin gate dan bai shigo ciki ba ma saboda yanayin akwai hadari sosai dan har an soma iska da walkiya yace maza maza ta fito su tafi. Ta mike da sauri tana gyara jakarta, Uwani tace"Kada fa kiyi da wasa kina samun kufcewa ki nemi mafaka ki 'buya idan ya bar gurin sai ki fito, Tace"Ai As ma yana gurin dan yayi min bayanin yanda zanyi." Camas dake danna wayarta tace"Ni kam inanan sai gobe ma had'u a gest house din As nasan dai can zaki kwana ko." ? Tace"E mana amma da wuri zan fito xamu wuce fataskum sai komai yayi normal kana mu dawo." Tace."To shikkenan." Rashida dai na zaune bata sanya musu baki ba cikin maganarsu duk haushi suke bata har Uwanin sam basu san inda yake musu ciwo ba, shiyasa tayi al'kawarin daina sanya musu baki a maganarsu idan ta kwa'be musu ita 'yar kalloce tinda ta fad'a musu gaskiya sun'ki ji.
Har bakin gate Camas da Uwani suka rakota, sai da ta fita tukkuna suka koma ciki.....Tana fita aka soma yayyafi da sauri ya bude mata motar ta shiga tana gyara mayafinta, ya kunna motar suka bar gurin, Sai da suka hau titi sosai ya d'anyi gyaran murya yana kallonta yace." Ya mutanan gidan ina fatan kin mi'kamin gaisuwa gurin momy kafin naje da kaina." babu yabo babu fallasa tace"Eh tace tana amsawa." Motar tayi shiru bayan maganarta ruwa ya soma yin 'karfi gabanta na cigaba da fad'uwa!
Saboda yanayin goslow din dake tsakanin tal'udu da goran dutse ya sanya yayi yanke hanya ya shiga ta wajan ma'kabarta zai bi ta 'yan rake