Author : Binta Umar Abbale Category : Romantic Books
wani dalili me karfi ba, tabbas an shiga hakkinta mutuka!! kuma irin wannan sakin shine ubangji baya so.....To amma nasan dai kai mai ilimi ne kuma kasan kaddara dai- dai gwargwado kasan cewar duk abinda Allah ya kaddara sai ya faru a kan bawanshi to sai ya faru, saboda haka ina so dukaninmu mu dauki wannan abun a matsayin kaddara wacce ta riga fata......Kuma hakika naji dad'i sosai da ya kasance cewa sakin an aikata irin wanda musulunci yake so, akwai sauran dama a halin yanzu, dan haka muke ro'ko ayi hakuri yarinyar nan ta koma d'akinta."
Mai allo ya sauke ajiyar zuciya mai 'karfi! yana kallon matar.....Hakika matar nada mutunci da kima da kuma sanin ya kamata ko ga yanayin kalamanta, baya jin zai iya wani ja'inja kan maganarta mutukar shi Ahmadu da yarjewarsa take masa bikon matarshi, zai amince da maganarta, sam baya so a zo ayi abu irin na baya ma'ana a koma gidan jiya, Ahamdu ne me aure ba Hajjah ba kuma shi ake so ya furta da bakinshi kan cewar ni wane na janye sakin da nayi wa mata wance na mayar da ita dakinta yanzu tana matsayin matata kamar yanda addinin musulunci ya tanada, to mutukar yaji wad'annan kalmomi daga bakinshi, bashi da tace addini ya riga ya halasta masa matarshi tunda dama ba tayi iddah ba." Yace."To masha Allah Hajiya, ai dukanin abinda kikaga ya faru dama da sanin Allah duniya babu wanda ya isa ya tsarawa kanshi rayuwa face wacce Allah ya tsara masa, auran Ahamdu da Wasila ya 'kare a lokacin da Allah yake so, kuma a sanda yake so zai iya sanyawa su koma su cigaba da zama mutukar rabo bai 'kare a tsakaninsu ba, Ni bani da tacewa anan gurin hakanan itama yarinya bata da magana, tunda a yanzu addinin musulunci ya bashi dama a hannunshi, zai iya yankewa kanshi hukunci, ina nufin ya d'auki aniya a zuciyarshi kancewa ya mayar da matarshi ko kuma akasin hakan duk wannan damar yanzu a hannunsa take, Yanzu ni shi nake jira ya furta min da bakinshi cewar ya amince yarinyar nan ta cigaba da zama matarshi ko A'a."? Mai allo ya 'kare maganarshi hankalinshi a kwance.
Hajjah babba tace"Eh gaskiya ne malam maganar ka na kan hanya a yanxu magana na bakinsa dani da kai duka 'yan fatan alkairi ne domin dukaninmu ba zamu haramanta abinda ya halasta ba saboda haka magana yanzu tana gurunka kai muke sauraro." Hajja ta'kare maganarta tana me zuba masa idanunta.........A nutse ya d'ago kanshi zaiyi magana kenan, Ta fito daga dakinsu, sai duk suka zuba mata ido har ta tattako a hankali ta 'karaso inda suke zaune! gaban mai allo ta dur'kusa tana hawaye da rike masa hannuwa tace"Kawu kaine fa kace ba zaka sake takurani ba! Kawu ashe ka manta al'kawarin da kayi min ranar da muka zo garinan kace ba zaka sake yi min tilas ba, zaka barni da kaina na za'bi miji wanda yayi dai-dai da rayuwata na aura." Da sauri! ya d'ago kanshi yana kallonta jin abinda take fad'a! da cikinsa za take tunanin yin aure? Kafin ya gama tunani ya juyo muryarta na shashshe'ka tana fad'in "Kawu ni daina bana son na koma gidanshi, sabida ba zan iya rayuwar da nayi dashi a baya ba, Zargina yakeyi Kawu nasan kasan aure da zargi a musulunci ya haramta ni kawai a kyaleni na haifu lafiya sai a bashi d'anshi." Cikin kuka da yanayi na damuwa take maganar gashi ta ruk'e hannun Kawunta katamau!
Dukaninsu suka bita da kallo mussaman gogon da duk jikinsa yayi sanyi ya dinga kallonta yana hango tsabagen 'kiyaysrshi a cikin kwayar idanunta......Sai yaji wani irin ba'kin ciki da takaici ya turnu'keshi! wato har wani kuka take tana nadama da fad'in ba zata koma gidanshi ba, to me yake mata da za tace ba zata koma gidanshi ta cigaba da yin rayuwar da tayi a baya ba? shin tun da suke yaushe yayi zarginta? shine zai fad'awa kowa cewa ita d'in kamila ce kuma nitsatstsiya tunda ta kawo mishi burducinta! bai ta'ba zarginta ba sai sanda wannan al'amarin ya faru!!!! 'Kwafa yay cikin ranshi, ai magana a hannunshi take ba'a hannun wani ba, malam mai allo na shirin yayi magana, Ya rigashi da gyaran murya kafin yace."Ai maganar saki tuntuni na janyeta malam yarinyar yanzu haka a matsayin matata take, wannan dalilin ne ma ya sanya ni dauko Hajja domin tazo ta baka hakuri a bisa abinda ya faru tsautsayi ne da kaddara amma insha Allah hakan ba zata sake faruwa ba." Mai allo ya sauke ajiyar zuciya a hankali yace."To madallah Alhaji naji dad'in wannan kalmar taka kuma Wasila zata koma gidanka insha Allahu amma ina so in baka shawara ko kuma in tunasar dakai duk da cewar ka sani, Allah da kanshi ya hallata saki amma kuma baya so a akaita shi, kayi kuskure a lokacin daka yanke hukunci, bance yarinyar ba tayi maka laifi ba tabbas tayi laifi wanda ya dace ka dauki ko wane irin mataki a kanta, amma banda saki, ni a ganina ba tayi abinda za'a saketa ba, saboda ita mace komai girmanta da shekarunta abar tausayi ce ballanta yarinya 'karama irin wannan!? Ka saketa tana da ciki, abinda ba'aso sannan ta amshi laifinta ta nemi afuwarka ka koreta daga gidanka, bazan 'boye maka Alhaji yarinyar nan ta wuya da wannan cikin na jiki kafin su zo nan kenan, sai bayan zuwansu, dana tsananta gurin yi mata tofi da rubutu sannan ta samu lafiya har kazo ka ganta haka, ina fad'a maka da can kwanakin baya kazo da sai ka tausaya mata mutuka dan abincin kirki bata iyaci sai yame yame irin nasu, to Alhamdullhi yanzu lafiya ta samu tana iya cin komai ta zauna lafiya, saboda haka nake baka shawara da kuma tunasarwa kan cewar duk wani abu da matarka za tayi maka na kuskure to ka dinga sanya hankali da nutsuwa kafin ka yanke hukunci akai dan saurin saki bashi ne hukunci ba, wallahi Alhaji da kazo bayan yarinyar nan ta haihu to banga dalilin da zai sanya in tilas ta mata cewar sai ta cigaba da zama da kai ba, zan dai baka dama ka shiga cikin zawarawanta idan har kana da muradin hakan."
Ya dinga kallon mai allo cike da d'umbin mamaki! wato shine ma zaibi layin zawarawa sai kace wani shashasha! tsaki yaja cikin ranshi mai allo bai ta'ba 'bata masa rai ba irin yau! amma sai ya shanye ya dake! ya hakura tunda dai magana ta'kare ai shikkenan........A nutse yace."Arrama insha Allahu hakan ba zata sake faruwa dukanin abinda ka fad'a gaskiya ne tsautsayi da 'kaddara basa wuce kan kowa, saboda haka insha Allahu magana ta wuce a gurina zan rike yarinyar nan tsakani da Allah da manzonsa, Saboda haka yanzu sai su shirya kayansu ita da 'yar uwar tata mu tafi in yaso sai ta dinga d'an d'ebe mata kewa har Allah ya sauketa lafiya"...............Da jin maganar dake fitowa daga bakinshi yasa ta mike da sauri ta shige d'akinsu tana wani irin kuka mai cin rai!!? Ta sanya hannuwanta duka ta dunga dukan katifar dake shimfid'e a tsakar d'akin.
Littafin na kudi ne.....!
Kika futar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya ba kema keda Allah! Whsap numbar
*07084653262*alliya:
'Yr Bngr Sys
*62*
Rashida ce ta shiga dakin ta tsaya kanta tana kiran sunanta, "Anti Wasila dan Allah ki daina kuka ni wallahi banga abin kuka da damuwa anan ba,Allah na yarda da nadamar mutumin nan yanzu kuma yana sonki dan da baya sonki ba zai tayar da hankalinshi a kanki ba, kawai ki hakura ki koma dakin ki shine mutuncinki damu gabakid'aya." Idanunta jaga-jaga da hawaye ta dago tana kallon 'yar uwar tata dake durkushe kusa da ita, "Rashida nifa bazan koma yanzu ba sai na haihu haka kurrum kai tsaye zaizi yace ya mai dani sai kuma na kwashi jiki na bishi babu wani shiri da da yanxu ba d'aya bane yanzu nasan ciwon kaina." Rashida tace"Eh gaskiya kuma hakane to da zai bari ki haihu shikkenan yafi sauki hakan amma yanzu ku kin koma nasan hankalinsu mai allo ba zai kwanta ba.
To a can tsakar gida kuma sai fafatawa ake tsakanin mai allo da Ahamdu da kuma Hajjah inda mai allo ya kafe kai da fata yace Wasila ba zata koma ba sai ta haihu sannan Ahamdu da Hajjah sai rarrashinsa suke da kawo masa misalai wanda suke nuni da cewar in ta koma d'in ai babu matsala insha Allah zasu kula da ita da kyau dan har hajja tayi al'kawarin zama tare da ita har sai ta haihu tayi ar'bain tukkuna sannan ta tafi gidanta, Malam mai allo yayi shiru yana nazarin maganarsu, shi dai hankalinsa yafi kwanciya da zaman yarinyar a gabanshi to amma bashi da yanda zaiyi dole ya hakura ya basu tinda yanzu suke iko da ita, Yana mutukar ganin girman hajja sabida matar tasan abinda takeyi sosai.....Yace."To shikkenan ai tunda kun rinjayeni na bar muku amma kuyi hakuri ku barmin rashida dan naji kana cewa tare zaku tafi da ita." Ahmadu ya marairaice sosai yana rarrashin mai allo kan yay hakuri ya basu har rashidan zamanta tare da 'yar uwarta zai d'ebe mata kewa sosai mai allo dai sun gama kashe mata jiki sai kawai ya amince musu amma kam zai sha kewa dan d'an zaman da sukayi dasu na watanni uku sun saba da juna sun sha'ku sosai.
Bitan na kicin ta kwalawa rashida kira ta fito da sauri ta nufi kicin......Bitan ta kammala abinci tsat tsaf ta jera kwanukan silba kan wani katon faranti shima na silba sai she'ki yake kwanuka uku ne akai d'aya lafiyayyan towon farar shinkafa ne tas dashi a nad'e cikin leda d'aya miyar taushe ce da taji gyada da alayyahu da yakuwa, d'aya kwanon kuma farfesun naman zabbi ne sai kamshi yake yayi shar shar dashi, tace"Dauki ki kai musu sai kizo ki dauki wancan jug din ki kai musu ruwa." Rashida ta dauki abincin ta fita.
Mai allo ya mi'ke ya bar gurin domin su samu sakewa suci abincin a nutse Ahamdu ya saki jikinshi yaci abincin sosai irin wanda ya Jima baici irinshi ba, hakika ya yarda da kula da tsabtar matar shiyasa ya zage sosai ya cika cikinshi
Rashida kam na daki na rarrashin Wasila suci abinci ta'ki hawaye kawai take! tarasa abinda yake damunta, mai allo ya d'aga labulen dakin yana fad'in "Ina Wasila."? Da sauri ta goge hawayen ta tace" Gani Kawu, Yace."Kiyi hakuri kinji ko kiyi hakuri ki kyautata hakuri a karo na biyu na umarce ki da kiyi biyayya kibi abinda nace miki insha Allah zaki samu alkairi a gaba, bani na fad'a ba Allah ne ya hukunta hakan! duk macen da mijinta ya saketa saki d'aya kafin ta 'kare iddah mijinta ya dawo yace ya janye sakin ma'ana ya mayar da ita ko bata so dole ta koma ta cigaba da zama dashi a matsayin mijinta, dan haka nake sake baki hakuri nake kuma ro'konki da kibi mijinki ki koma d'akin ki insha Allahu za kiji dad'i kuma kiyi alfahari anan gaba." Mai allo ya gama kashe mata jikinta da maganganunsa shiru tayi tana tsiyayar da hawaye mai allo ya saki labulen dakin zai tafi tace"Kawu ina da magana." Ya dawo da baya yana kallonta......Tace"Kafin na koma to ina so muje can pataskum gurin Uwani kaga tunda muka zo ba muje saboda yanayin rashin lafiyana ba kuma musan halin da take ciki ba."
Mai allo yayi shiru yana nazarin maganarta ta Yace.''To babu laifi sai kuje domun ki shaida mata abinda yake faruwa, yana da kyau a fita hakkinta a matsayinta na mahaifiyarki tasan halin da ake ciki, bari na sanar da Alhajin abinda ke faruwa." Labulen dakin ya saki ya nufi inda suke zaune Sun gama cin abinc
i suna hira mutumin ya saki jikinsa sosai dan har ya kira Khalifa a waya ya shaida masa abinda ke faruwa.....Mai allo ya dan jingina jikin bango a nutse yace."Anya Alhaji tafiyar nan zata yiwu yau kuwa."? Yayi saurin kallonshi yana so yaji dalilin da zai hana yiwuwar tafiyar......Mai allo yace."Yarinyar nan na bukatar ganawa da mahaifiyarta hakan nada kyau sosai mahaifiyarta tasan halin da ake ciki ta kuma sanya mata albarka, a zamantakewar auranta, dan haka nace ko zamu bari rana ita yau! insha Allah sai kadawo ka d'aukesu kafin sannan sunje sun dawo ta sake nutsuwa tukkuna.
'Dan 'bata fuska yayi yace."A'a malam ina ganin rana d'aya ma zamu iya zuwa mu dawo
Ba tare da anja dogon lokaci ba, ni da kaina zan kai su su dubata insha Allah gobe zamu dawo tare da khalifa sai su shirya muje daga can sai mu wuce kawai.'' Mai allo yace."Babu laifi hakan Allah ya kaimu lafiya." Hajjah tace "Amin amin ya rabbi mungode malam Ubangiji Allah ya kara girma da dattako." Mai allo yace."Babu komai hajiya mudai fatan anan shine Allah yasa anyi kenan Allah ya d'orar da zaman lafiya."
Ya d'an gyara zamanshi as'usel kamar ko da yaushe dai ya ciro kudi masu yawa a jikinshi ya dora saman buzun mai allo yace."Malam zamu koma Allah ya saka da alkairi." mai allo yace."Alhaji Ahmadu baka gajiya kullum cikin hidima kudin nan sunyi yawa." Yace."Babu komai malam Allah ya bamu mu bayar meye amfaninsu in ba'a badasu ba." Mai allo yace." To maddalah mungode kwarai Allah ya kara arziki da wadata." Ya amsa da "ameen." yana gyara babbar rigarshi.
Hajja ta le'ka d'akin su Wasila tana gyara lullu'binta tace"To Ina kuke zamu tafi Wasila kina ina.''? Wasila dake kwance kan kafita ta fara kokarin mikewa zaune Hajja ta shiga dakin tana fad'in "A'a yi kwanciyarki kinji ko sannu! Dan Allah kiyi hakuri karki sa damuwa cikin ranki insha Allahu abinda ya faru a baya bazai faru ba yanzu ki kwantar da hankalinki ki daina damuwa kuma ki daina kuka." Kanta a kasa tace"Insha Allah Hajja nagode ki gaida gida." Tace"Gida zaiji insha Allahu gobe inanan ina jiran zuwanku." Shiru tayi tana mayar da 'kwallar dake kokarin zubo mata......Hajja ta fito daga d'akin kawai sai ta ganshi ya 'kurawa kofar dakin ido kamar zai shiga, kai kana kallonsa kasan a dame yake daurewa kawai yake yana kokarin dauke abin daga ranshi duk dan kar girmanshi ya zube a idon yarinyar da mutanan gida.....Hajja tace"To ko zakuyi sallama ne naga kanata kallon dakin....Girgiza kanshi yace "Tunda kunyi sallama babu damuwa ai gobe zamu had'u insha Allah." Tace"To babu lefi." Bitan ce ta fito daga daki hannunta rike da wata roba mai murfi mai kamar kwanon sha robar da fulani ke zuba nono a ciki, daya hannun nata kuma ledar fura ce a cure tace"Hajjah ga wannan babu yawa, tun zuwanku naso in dama muku ayyuka sunyi yawa." Hajja ta kar'ba da walwala a tare da ita tace"To godiya muke Bitan Ubangiji Allah ya saka da alkairi kwarai naji dadin yanda kika kar'bemu hannun biyu mungode sosai." Bitan tayi murmushi kawai tana fad'in "Babu komai hajiya mune da godiya ai ku gaishe da gida Allah sauke ku lafiya." Hajja ta amsa da ameen kana tabi bayan Ahmadu da ya riga yayi gaba." Suna tsaye da mai allo suna sallama, Garba dake zaune cikin mota ya fito suka gaisa da mai allon kana ya koma ya jingina jikin motar yana ganin tawowarshi ya hude mishi mota ya shiga Hajja ma shiga ta zauna da sauri ya zauna a maxauninshi , Ahmadu ya shiga dagawa mai allo shima yana daga mishi hannu gami da yi musu fatan sauka lafiya.
Bitan ta le'ka dakin nasu sai ta tarda rashida ita kadai a zaune Wasila tayi bacci Tace"Au bacci tayi kenan."? Rashida tace"Eh tun dazu nayi nayi taci abinci ta'ki ci." Bitan tace"Kyaleta na fad'a miki tana tashi daga wannan bacci xata nemi abinci da kanta." Rashida tayi dariya tana fad'in "Aikuwa yanzu ma kawai dan tana cikin 'bacin rai ne amma anti Wasila da abinci ba dama." Bitan tasa dariya tare da fitowa daga dakin.
Aikuwa hakane ya kasance da wata masifaffiyar yunwa ta tashi da kyar taje ta wanke bakinta ta nufi kicin Bitan tace"A'a kar ki fara da abinci d'azu malam yace." Kafin kici komai kisha wann
an rubutun." Dakin bitan din ta nufa ta kar'bi rubutun ta tsuguna da bisimillah a bakinta tasha ragowar ta shafe cikinta dashi kamar yanda ta saba.....Bitan ta mike da kanta taje ta dauko mata abincin ta gyara zama sosai zauna kana tayi bisimillah ta fara cin abincin........ Sai bayan da ta kammala cin abincin ne tace "Bitan ina Rashida."? Tace" Bata jima da tafiya gidan Innar ku ba, malam yace taje ta fad'a mata abinda ke faruwa.
Ta sunkuyar da kanta kasa a hankali tace"Yanzu Bitan sai na koma gidan mutumin nan."? Bitan tace"To ya zakiyi Wasila shine alkairi don Allah kiyi hakuri ki daina wasiwasi insha Allahu babu wani abunda zai sake biyowa baya kuma insha Allahu zaki haihu lafiya." Shiru tayi tana tunanin shin idan ta koma gidan ko wane irin zama zasuyi dashi, ita yanzu ta daina jin sonsa a ranta, kawai zata koma ne ta zauna tare dashi saboda an rinjayeta.
Bayan magariba da mai allo ya shigo ya sake tabbatar mata da maganar ya kuma umarcesu da su had'a kayansu su kuma shirya da wuri don kar yazo yana jiransu.........mai allo kwana yayi yana karatun al'kurani mai girma sai da ya had'a izifi sittin kana ya tofa cikin tsabtattaccen ruwan sama, ya samu jarka mai kyau ya zuba ya rufe da murfinta ya aje a guri guda, kana ya mike a nutse ya fito ya d'aura alwala ya wuce massalaci.
Karfe tara shaura na safe sun shirya duk suna zaune a tsakar gidan har da Inna Hajara data dako sammako tazo gidan, ita da mai allo sun tasa Wasila a gaba sai fada suke mata mai tafe da nasiha irin fadan da iyaye kan yiwa 'yayansu a lokacin da za'a kaisu dakin mazajensu, Gatan da bata samu ba a farko, sosai take share hawaye tana jin wani