Author : Bilkisu Z Ya'u Category : Romantic Hausa Novels
ο»Ώππππππππππ
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
ππππππππππ
RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (π
±K)*
SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
_(Mamie)_
*πΈπ¦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```
_*DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN K'AI*_
_*ALHAMDULILLAH GODIYA TA TABBATA GA MAHALICCINMU ALLAH (S.W.A) YA ALLAH INA MAI GODIYA A GAREKA DA NI'IMAR DA KAI MIN TA BAIWA, DA ARON RAI DA LAFIYA DA KA BANI ALHAMDULILLAHI INA K'ARA GODIYA A GAREKA,π YA ALLAH KA K'ARO MIN TARE DA DUKKANIN 'YAN UWANA MUSULMAI BAKI 'DAYAπππππ*_
_*YA ALLAH KA YI SALATI GA SHUGABANMU ANNABI MUHAMMAD (S.A.W) DA IYALEN GIDANSA TSARKAKA, DA SAHABBANSA BAKI 'DAYA.π,*_
_*πΈπ¦ZAMAN AMANA WRITER'S WALLAHI HAR GA ALLAH KUMA HAR ZUCIYATA INA JIN DA'DIN ZAMA DA KU, ALLAH YA K'ARA MANA K'AUNA, HA'DIN KAI, DA FAHIMTAR JUNA.ππ*_
*AUNTYNAH AISHAN UMMA INA TAYAKI MURNAR KAMMALA DIGREE D'INKI LAFIYA, ALLAH YA KAWO AIKI NAGARTACCE DA ALBASHI ME TSOKA, AMMA FA KI SANI ALBASHINKI NA FARKO NAWA NEππ*
*ASIYA SEE-SEE SANNU BAIWAR ALLAH, ALLAH YA DORAR DA LAFIYARSA GAREKIππ°*
_*INA MIK'O GAISUWAR BAN GIRMA GA DUKKANIN MARUBUTA HA'DE DA JINJINAR K'ASAITA, GAISUWA WADDA BATA K'AREWA HAR SAI RAI YA YI HALINSA, ALLAH YA K'ARA MANA K'AUNAR JUNA DA BASIRA.ππ*_
_*WANNAN LITTAFIN GABA 'DAYAN SHI DAGA FARKO HAR K'ARSHE SADAUKARWA NE GA MA'ABOCIYAR HANKALI DA TUNANI, ILIMI DA HANGEN NESA, MA'ABOCIYAR KYAWUN HALI DA 'DABI'U ```MAMAN LABYB,,, KIN WUCE HAKA A GUNA, MATSAYINKI YAFI GABAN NAN, UBANGIJI YA 'DAGA DARAJARKI, ALLAH YA FARANTA MIKI RANKI ANAN GIDAN DUNIYA DA GIDAN LAHIRA WATO GOBE KIYAMA, TABBAS KINA AMINCI A FILI KUMA KINA AMINCI A ZUCIYA, NA FAD'A A FILI KUMA NA FA'DA A ZUCIYA, KECE MACE ME CIKE DA HALACCI A DUNIYA, IN AKWAI ABINDA YAFI SADAUKARWA DOMIN KARRAMAKI DA NUNA GIRMAN MATSAYINKI GARENI TO TABBAS ZAN YI.πππππππ*_
PAGE 1 to 5
Gidan marayu Amira ta fara zuwa matashiyar yarinya kenan ga tsananin kyawu da Allah ya bata ga kuma dukiya Allah ya hore, bayan sun gaisa da shugabar gidan sai ta bayar da taimakon kud'in da ta saba kawowa kamar koda yaushe.
Shugabar ta kalleta cike da farin ciki tace " Allah saka miki da alkhairi da irin wannan taimakon da kike yi mana."
Amira tai murmushi, sannan tace " ai dukiya ba komai bace dan ka bayar da ita ga mabuk'ata amfaninta kenan dama ka taimaki wanda baida ita sai Allah ya k'ara nunka maka mafiyinta, Addu'a kad'ai nake buk'ata daga gareku, kuma naji kuna buk'atar k'ara girman gidan za'a sake fad'ad'a wajen da yardar Allah, sannan duk abinda kuke da buk'ata dan Allah a sanar da ni, shugabar wadda Amira ta kirata da Mama tace to ba damuwa, Allah ya saka miki da alkhairi, Allah ya tsareki daga sharrin mutum ko aljan, mun gode sosai."
Daga nan suka yi sallama Amira ta fito ta shiga motar ta, ta d'auki hanyar gida.
tana cikin tafiya mota ta lalace mata a hanya, tayi - tayi ta tashi amma ina, kuma daga inda take akwai tafiya mai nisan gaske kafin ta k'arasa gida.
fitowa ta yi daga cikin motar tare da k'ura mata ido cike da takaici tana tunanin mafita a ranta.
Ta dad'e tsaye tana jiran giftawar abun hawa amma shiru kake ji, har ta ciro wayarta zata kira Dad d'inta ya turo mata da wata motar sai ta ji k'arar wata mota a bayanta, mayar da wayar tai cikin jaka sannan ta tsaya tsakiyar ti-tin ta rik'a d'agawa mai motar nan hannu, ba shiri ya ja wani irin burki a gabanta.
Wani had'ad'd'en saurayi ne ya fito daga cikin motar, sanye yake da k'ananan kaya ya sha tabarau ya fito tare da tunkaro inda Amira take tsaye.
Sai da suka yi kallon kallo wanda ke d'auke da wani sak'on da basu san ma'anar jinsa ba, sannan saurayin nan ya ja tsaki yace " mtswww ko wace mace da d'an k'aramin abu ya faru da ita sai ta fara k'ok'arin kashe kanta, wa ya sani ma ko auren dole za'ai miki kike k'ok'arin halaka kanki, to yanzu da kika tsaida ni me zan miki?"
Yana gama fad'in haka ya juya zai tafi sai tayi sauri ta sa hannu ta jawo shi, sannan tace " karka fad'a min maganar banza mana motata ce ta samu matsala shiyasa na tsayar da kai domin ka rage min hanya, kuma bana son tuk'in ganganci dan haka ka koma gefe nice zan tuk'a motar taka da kaina."
Saurayin nan ya tsaya yana kallon ta tare da mamakin k'arfin hali irin nata, se dai memakon ya ji haushi a'a saima ji yayi tana burgeshi, har taje bakin motar ta bud'e murfin motar, ta juyo inda yake tsaye tace " ka taho mu tafi mana ko in tafiyata in barka a nan," matashin nan ya rik'e k'ugu da hannu bibbiyu sannan yace " ikon Allah," a nan take ta k'arasa mishi da fad'in "sai kallo," tana gama fad'in haka ta fad'a cikin motar b'angaren driver ta zauna sannan ta tayar da motar, da yaga da gaske take zata iya tafiya ta barshi sai ya yi sauri ya k'araso ya shiga taja suka tafi.
Banda aikin kallonta babu abinda yake yi, zuciyarshi ce ke bugawa tare da jin wani bak'on yanayi a tare dashi wanda bai tab'a fuskantar kanshi a ciki ba, hakan yasa zuciyarshi ta aminta da cewa ya fad'a tafkin so duk da kuwa be tab'a yinsa ba, kuma be kula matan ma, amma halin da ya tsinci kanshi a ciki yanzu daga had'uwar farko ya tabbatar mishi da cewa ya fad'a soyayya, ita kuwa 'yar azarb'ab'i Amira banda uban surutu babu abinda take yi, a yayin da shi sam be ma san tana yi ba banda kallonta ba abinda yake, tare da zurfafa tunani kan son tantance gaskiyar abinda yake ji kuma yake zargi a halin da yake ciki yanzu.
Jin tana ta magana shiru be bata amsa ba yasa ta karkato da kanta wajen shi ta kalle shi taga ita kawai yake kallo, bud'ar bakinta sai tace " a haka dai gaka kamar wayayye ashe bak'auye ne kuma kan ta gane ne ban sani ba, dan naga alama wannan ne karo na farko da ka fara ganin mace a rayuwarka, haba wannan irin kallo haka sai kace zaka cinye ni," shi dai bai ce mata komai ba ya cigaba da kallonta, duk abinda tayi kawai burgeshi take yi.
Basu d'auki wani dogon lokaci ba suka k'araso k'ofar gidan su Amira, ta tsaida motar sannan ta fita, ta kalle shi tace " nagode sosai da rage min hanya da kayi, Allah ya saka maka da alkhairi."
Saurayin nan wanda dama idonshi yana kanta yace " kina kyau da tuk'i kin iya gudu a mota," Amira tayi murmushi, sannan tace " ai da tseren mota da na k'afa ba'a tab'a wuce ni, in kana so ka tabbatar da hakan to gobe ka shigo makarantar mu ka gani, ta fad'a mishi sunan makarantar sannan ta juya tai shigewarta gida.
Shima saurayin nan ya koma b'angaren driver ya ja motar shi yai gaba, fuskar shi na d'auke da murmushi wanda yake bayyanar da tsantsar farin cikin shi a yau.
Washe gari a wani keb'antaccen fili na makarantar aka tanada domin gudanar da tseren gasar gudun da za'ai, ko ina ka duba cike yake da mutane, a yayin da wad'anda za'a fafata dasu kuma suke ta motsa jikin su suna tirenin kafin a fara.
Ana gaf da farawa abokanan Amira su Sani da Sadeeq, da Abdul, da k'awayenta Rahma, da Suhaima, da pretty suka zo wajenta suna k'ara mata k'arfin guiwa akan tayi k'ok'ari wajen ganin ta yi nasara, duk da dama kowane lokaci nasarar a hannunta take, har sun juya zasu tafi Sadeeq ya juyo ya dawo wajenta ya ciro wani abu wanda yake kamar sark'a ya saka mata a wuyanta, sannan yace " mamata ce ta bani ni kuma na baki, na tsari ne, kar kiji fargaba ko shakka a ko'ina muddin kina tare da Allah."
Amira tai murmushi sannan ta rungume shi tare da fad'in "ina matuk'ar jin dad'in zama da kai amintacce na, ina jin dad'in kulawarka gareni, Allah ya barmu tare," sannan tayi mishi godiya,
_(wasu d'aliban bance duka ba, basu d'auki rungumar juna tsakanin mace da namiji a komai ba)_
Bayan Sadeeq ya tafi tana cikin shiri sai ta ji motsi bayanta, tana juyowa taga wannan saurayin wanda suka had'u jiya da irin kayan su na tsere alamun shima yana d'aya daga cikin masu fafatawa a gasar.
Muje zuwa
*π
±Kππ*
ππππππππππ
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
ππππππππππ
RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (π
±K)*
SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
_(Mamie)_
*πΈπ¦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```
*Mamie ina rok'on mahaliccinmu Allah mai kowa mai komai ya d'orar miki da lafiya, Allah yasa kaffara neππ*
*PAGE 5 to 10*
K'arasowa yayi inda take, sannan suka kalli juna, Amira tace " ka kyauta da kazo kallon fafatawar mu," saurayin nan yace " a'a ba kallo kad'ai zan yi ba, had'uwa dake ya sauya min ra'ayina, yasa na yanke shawarar shiga gasar tseren nima duk da yau ne ranar farkon fara shigowata makarantar ina nufin sabon d'alibi ne ni, amma na rok'i da a sakani cikin jerin masu fafatawa, farko dai sunana Amir, kuma ni sabon d'alibi ne a ajinku, ina yi miki fatan alkhairi, Allah yasa kiy nasara."
Kallon shi tai tace Allah gafarta malam Amir ya kamata fa ka gane ni d'innan ba tsararka bace, nai maka zarra ta ko'ina, kuma nan bada dad'ewa ba zaka tabbatar da hakan, ta kanne mishi ido d'aya tare da zabga mishi uban gwalo sannan ta bar wajen, alk'alan gasar ne suka fara sanar wa kan duk wani wanda yake cikin wannan gasa to ya tabbatar da ya shiga cikin fili, sannan kowa ya tsaya a layi kamar yanda aka saba yi a baya.
Bayan kowa ya shiga layi aka basu umurni da su shirya, kowanne daga cikin su ya shirya, sannan aka irga d'aya zuwa uku suka fara gudu.
Amira itace a tsakiya tana gudu cikin nuna k'warewa da k'wazo, a yayin da Amir yake a can baya, haka yaita wuce wad'anda suke gabanshi har saida yazo daf da Amira ya zamto a tare suke gudun kuma sune kan gaba, kuma kowannensu ya kafe kai da fata sai ya wuce to da yake a cikin masu yin gasar harda Abdul daya daga cikin abokan Amira, ganin da yayi wani na k'ok'arin shiga gaban Amira yasa Abdul yaita tattare wa Amir hanya, idan Amir yazo zai wuce sai ya riga shi, shi ya yarda ya fad'i indai Amirar su tai nasara, hakan yasa Amira ta k'araso wajen su cikin k'warewa, Amira suka had'a ido da Abdul yai mata nuni da kai alamun ta wuce, har ta kusa kawowa dai-dai layin da zaka tsallake ka ci gasar.
Suna gaf da shiga layin a tare duk da Amira ta d'an wuce Amir kad'an, Amir na ganin zata cinye shi yai wani irin tsalle kawai sai gashi a tsakiyar filin wajen da duk wanda ya k'araso yaci.
Ihu aka hau yi ganin yau ga wanda ya kayar da Amira a tsere, sedai wad'anda suka ji haushin ba ita taci ba sunfi yawa musamman Sadeeq d'aya daga cikin abokanta, koda yake shi ya wuce aboki dan bata da wanda take neman shawara gunsa sai shi, a tak'aice ma dai shine wanda suke kasancewa tare a koda yaushe, koda nemanta kake yi in ka tambaye shi kai tsaye zai nuna maka inda take kuma kana zuwa zaka sameta a gun, sedai hakan ma bata taba faruwa ba dan kaf cikin makarantar ko ina take to suna tare da shi.
Yaji haushi da Amira bata samu nasara ba, saida yai hawaye saboda tsabar b'acin rai.
Amir ya k'arasa wajen Amira wadda take ta mamakin irin tsallen da ya yi ya shige cikin filin, yace " haka nake da wannan baiwar duk abinda nasa a gaba to sai na yi nasara akai, idan ba zaki damu ba ina son yin magana dake a wajen shak'atawar d'alibai, ita dai Amira bata ce komai ba, ganin haka yasa Amir ya juya ya tafi.
Koda Amira ta k'arasa wajen ta riga Amir zuwa, zama tayi kan d'aya daga cikin kujerun wajen, tana duba ta inda zai b'ullo.
Daga bayanta taji maganar shi yana fad'in " gani nan ai," Amira tai murmushi sannan tace " ina tayaka murnar samun nasara, amma ya akai ka iya yin wannan tsallen da kayi lokaci guda?"
Amir yace " saboda bana tsoron mutuwa, sannan bana fargabar samun nasara ko rashinta, shiyasa nake samun sa'a akan komai," Amira tace " ai kai ba namiji bane, kuma bana maka kallon jarumi tunda har sai ka yi tsalle zaka ci gasa, kaine mutum na farko da ka kayar da ni a gasa ta hanyar cuwa-cuwa, amma ka kiyayi had'uwarmu da kai a wata gasar ta gaba, dan idan kace zakai tsalle a gasa ta gaba to tad'iyeka zan yi ka fad'i," ta k'arashe maganarta tare da murgud'a mishi baki, Amir bai san sanda ya kwashe da dariya ba, domin yanda tai maganar da fad'a tamkar ma kashedi take yi mishi.
Suna cikin magana Abdul d'aya daga cikin abokan Amira ya hango su ya taho inda suke, yana k'arasowa yace "barkan ku dai Amira," ya mik'a wa Amir hannu suka gaisa, sannan yace " kai ne d'alibin da ya zama gawurtacce a idon d'alibai a ranarka ta farkon fara zuwa makarantar nan, duk da kasancewarka sabon d'alibi."
Amir yace " nagode," suna cikin magana sai ga su Sadeeq da su preety sun k'araso wajen, nan Amira ta bisu d'aya bayan d'aya ta rungume su sannan ta fara gabatar wa da Amir su da matsayinsu gareta, har tazo kan Sadeeq wanda shine na k'arshe, bayan ta rungume shi sannan tace " wannan shine babban abokina, duk girma da fad'in makarantar nan banda kamarsa."
Shima Amir gaisawa yai da su d'aya bayan d'aya, daga nan aka kawo musu abubuwan sha harda kayan maye, wasu sun sha da yawa wasu kuma sun sha amma kad'an.
Abdul yana d'aya daga cikin wad'anda suka bugu sosai, kuma tunda ya bugu yake ta kallon Amira, tasowa yai cikin jama'a ya rungume Amira tare da fara yi mata wasu abubuwa dai kai daga gani kasan baya cikin hankalinsa, Sadeeq ne ya taso kanshi ya raba shi da Amiran sannan ya fara kai mishi bugu bayan an raba su ne Sadeeq ya nuna Abdul da yatsa, tare da fad'in " idan har ka k'ara tab'ata sai na kashe ka," cikin buguwa Abdul yace " kafin ka kashe ni ni sai na kashe ka nan fa aka janye su suka bar wajen.
Washe gari bayan an tashi daga lecture ta farko suna hutawa, sai d'aukar hotuna suke yi, bayan sun gama d'aukar hotunan sai suka zauna suna dubawa, sai ga Abdul ya k"araso wajen, yace " Amira dan Allah abinda ya faru jiya kiyi hak'uri ba da gayya nai miki ba, buguwar da na yi ce tasa haka, dan Allah kiyi hak'uri," Sadeeq da ke zaune kusa da Amira ne yake ta faman banko mishi harara.
Amira bata ce komai ba, sai da k'awayenta da abokanta suka sa baki sannan tace " shikenan ya wuce."
Da yamma Amira ce keta faman motsa jiki tana (tirenin), tana cikin motsa jikin ne taji sak'o ya shigo cikin wayarta, tana dubawa taga an yi rubutu kamar haka,
_lek'o ki d'auki sak'on zuciyata zuwa ga taki zuciyar._
Fitowa ta yi, a harabar gidan su ta ci karo da wani kwali me matuk'ar kyau, jikinshi duk an k'awata shi da flowoyi, d'auka tayi tana k'ok'arin bud'e cikin kwalin.
Babu komai a ciki sai adon fulawa, can k'asa kuma wata takarda ce a ajiye, d'auko takardar ta yi, sannan ta bud'e ta, rubutu aka yi me matuk'ar kyau da ban sha'awa, an rubuta,
_*SO MAHA'DI NE NA RAYUWA,* so babbar cuta ce ga rayuwa, lallai zuciyata ta harbu da ciwo me azabtar da ruhi, al'amuran so suna da wuya, rabuwarsa kuwa mutuwa a tare._
Sake karantawa tayi a fili, sannan tai murmushi tana k'ara duba takardar, ga dukkan alamu kalaman ciki sun yi mata dad'i, d'agowa tayi tare da d'an duddubawa ko zata ga wanda ya ajiye mata sak'on amma bata ga kowa ba, hakan yasa ta d'auki kwalin, wasik'ar kuma na rik'e a hannunta ta koma cikin gida.
*Washe gari*
Tafe suke Amira tana tsakiyar abokanta da k'awayenta, tana ta maimaita kalaman da aka rubuta mata jiya cikin wasik'a, sai Suhaima ta kalleta tace " wai ke ina kika ji wad'annan kalaman kike ta faman maimaitawa?" nan ta basu labarin duk abinda ya faru, sai Sadeeq yace " gaskiya wannan ko wanene na musamman ne," Amira tace " Sadeeq shiyasa nake sonka tun kafin na furta abunda ke zuciyata kake fahimtar sa ka rigani furtawa, kamar kasan abinda nake shirin fad'i kenan," suna cikin magana suka ji ana fad'in wad'anan kalmomin cikin ajinsu amma da wak'a ake furtasu, da saurin su suka nufi ajin Amira ce kan gaba domin ta k'osa ta gane waye yai mata wasik'ar, se dai suna shiga suka tarar da mazan ajin sunfi goma, kuma dukkan su kalaman suke maimaitawa cikin wak'ar, farko Amir ne ta tarar yana rerawa yana fad'in.
_"SO MAHAD'I NE NA RAYUWA,_ ganin shi ke rerawa har ta fara murmushi saboda dama zuciyarta shi take zargi sai kawai ta ji
Abdul shima ya d'auka yace " _so babbar cuta ce ga rayuwa, lallai zuciyata ta harbu da ciwo me azabtar da ruhi,_
Sadeeq wanda suka shigo tare da Amira shima ya je kusa