SO MAHADIN RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVELS PDF BY BILKISU Z YAU.txt

Author :  Bilkisu Z Ya'u Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   23 / 31

66K to 69K   out of 90.7K words

'yan 'kauyenmu fiye da tunaninka Amir, saboda zaka ga ka d'auki naira hamsin wadda kai a ganinka ka rainata amma in ka baiwa wani magidancin sai kaga yana godiya harda kuka, wannan dalilin yasa na d'auki alwashin taimaka musu iya iyawata, ana haka wata rana shugabana na wajen aiki ya kirani na zauna, sannan ya kalleni yace "abinda yasa na kiraka saboda dalilai biyu ne, na farko an maka 'karin girma, ka tashi daga 'karamin ma'aikaci yanzu ka zama manaja na wannan kamfanin, kuma in babu damuwa ina yi maka sha'awar auren 'yata Khadija, ba komai ya kawo duk wad'annan abubuwan ba illah kyawawan halinka, domin duk wani ma'aikaci na wannan kamfanin mukan bibiyi rayuwarsa kar muje mu d'auko wanda zai rusamu, to duk a cikinsu ka zarcesu kyawun hali da na d'abi'u ga gaskiya da ri'kon amana, babu abinda ya 'kara burgeni da kai illah tausayin wanda bashi da shi da taimako, dan haka sati me zuwa zaka fara aiki, maganar khadija kuwa kaje kayi shawara duk abinda ka yanke sai ka sanar dani daga baya," na yiwa ogana godiya sannan na tashi na koma gida, bayan iyayena da d'an uwana sun hallara waje guda sai na sanar dasu 'karin girman da akai min da kuma abinda ogana yace akan 'yarsa, sunyi murna matu'ka tare da bani goyon baya akan Khadija suka ce inje d'in in ganta in dai tayi min kawai sai in aureta, jin Sunusi shi bai ce komai ba yasa na juyo na kalleshi nace "yaya kai bakace komai ba," ba tare da nuna fara'arsa ko walwalarsa ba yace "Allah sanya alkhairi," na sake cewa "amma yaya ni nafi so sai ka fara yin aure kafin ni nayi, ko kuma muyi a rana d'aya," Sunusi yace "ai in zaka yi aurenka kayi dan ni gaskiya ba yanzu ba sai nayi arzi'ki tukun," daga haka ya tashi yace kanshi na ciwo zai shiga cikin d'aki ya kwanta, naji mamakin maganar da Yayana yake fad'a saboda albashina dubu d'ari da hamsin ake bani duk wata a lokacin, ina d'aukar saba'in da biyar in bashi saba'in da biyar, amma bansan ya yake yi da kud'i ba dan kuwa komai na gidanmu ni nake yiwa iyayenmu hatta cefane wannan kai komai ma na gidan, shi kanshi idan bu'katarshi ta tashi ni nake yi mishi, amma wai yana fad'in baida kud'i sai yayi arzi'ki, bayan sati na koma bakin aikina, daga lokacin da na fara aiki zuwa yanzu 'yan 'kauyen nan babu wanda baya 'kaunata, har gida ake bin iyayena ana yi musu godiya da yimin addu'a, ashe duk wad'annan abubuwan Sunusi ya ri'kesu a ranshi ne yana kallona dasu, naje gidansu Khadija na ganta kuma na yaba da halayenta, hakan yasa babu b'ata lokaci iyayena sukaje aka sa rana inda mahaifinta ne yai komai aka sha shagalin biki muka tare a gidan da aka bani tun ranar da na fara aiki, madaidaicin plat ne amma ya had'u, mahaifin Khadija wata guda ya bani ina shan amarci, bayan wata biyu da aurenmu na d'auki Khadija na kaita 'kauyenmu domin ta gaida iyayena da d'an uwana Sunusi, tunda sunusi yaga Khadija yake mata kallon 'kurilla tare da washe baki kamar gonar audiga, lura da hakan yasa naji kishi a raina, ada munzo muyi sati ne, amma muna yin kwana biyu nace zamu koma, muka yi sallama dasu muka juya, da yake duk 'karshen wata nake zuwa gida inga 'iyaye da 'yan uwana ina nufin talakawana na garin wad'anda na zame musu tamkar uba ko kuma wani sarkin garin, a lokacin da nazo garin sai na samu mummunan labari daga wajen Iyayenmu wai yaya sunusi ya zama d'an fashi, kuma yana shaye shaye, isowata kenan na tarar da wannan ba'kin labarin, muna cikin maganar sai ga Sunusin ya shigo da gudu wani ri'ka'k'ken d'an daba dake wani 'kauye wanda ke ma'kwabtaka da namu ya biyoshi har cikin gidan, ya d'aga wu'kar hannunshi zai yanki Sunusi da ita kenan sai nai sauri na tare ya yankeni a ciki, nai 'kara tare da zubewa 'kasa dukkansu suka yo kaina shi kuwa d'an daban nan ina jinshi yana fad'in "Allah ya 'kwaceka d'an uwanka ya ceci rayuwarka, amma ba yaawa tunda a nan 'kauyen kake kuna kusa da namu ne ai dole wata rana zamu had'e a lokacin zaka gane kurenka," ya juya suka fice shi da yaransa suna gigije girgije, iyayenmu suka d'aukeni suka kaini wani asibiti dake cikin gari aka dubani aka tsaida jinin tare da d'inkewa sanna aka samin magunguna a wajen, bayan mun dawo gida na kalli yayana wanda tun lokacin har zuwa yanzu kuka yake aikin yi, nace "yaya su waye suka biyoka kuma me kai musu?" Sunusi yace "kayi ha'kuri d'an uwana, na jawo maka an raunataka," sai nace mishi kar ya damu zan iya rasa rayuwata domin kare tashi rayuwar, nan ya fad'a min wai ciki yaiwa 'kanwar wannan d'an daban suke ta nemanshi, jin wannan maganar ba 'karamin tayar da hankalina yai ba, yayana ne shi ya kamata ace yana min fad'a in nayi kuskure ba ni ba, bayan na warke na tafi dashi Abuja yai wata shida a can sannan muka dawo na kaishi wani waje da ake d'inki nace da zama haka gwara ya koya da aikin riguna ne da kuma d'inki sukeyi nace duka a koya mishi, na biyasu a ranar ya fara koya washe gari ni kuma na koma Abuja da tunanin d'an uwana, iyayenmu duk sun rame saboda damuwar da yake jefasu ciki, ina komawa na samu sa'kon kiran gaggawa daga wajen matata Khadija ogana na nemana, haka na tafi ban ko zauna ba gabana na fad'uwa saboda be tab'a yimin irin wannan kiran bazatan ba._







Muje zuwa







*πŸ…±K CEπŸ˜˜πŸ’‹*
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜









RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (πŸ…±K)*
```(Autar marubuta)```





SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
```(Mamie)```





*πŸ‡ΈπŸ‡¦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```πŸ€œπŸ€›





*MAMAN LABYB*
(Mamie nah)
*Hajiya mamie ikon Allah, kinyi naki kinyi na me 'karamin 'karfi, hadari malafar duniya, baya goya marayu, keji ba'a yi maki 'kyaure ko an maki sai ya bud'e yasin,πŸ˜πŸ˜‰ wuhuhu ina gwanar wasu nidai ga tawa, kainuwa dashen Allah, duk mai 'kaunarki ni yaso, ma'kiyinki ni ya'ki, duk mai 'kaunata to dole ya 'kaunaceki, Allah ya cigaba da d'aga darajarki ma'kiyanki suita ganin cigabanki ba'kin ciki na halakasuπŸ˜‚πŸ˜‚, ina yinki saboda Allah.πŸ˜πŸ˜˜πŸ’‹*






*~MUMMYN - SULTANπŸ‘‘*
*Mummyn Sultan wannan shafin kyauta ne a gareki, naki ne ke kad'ai kiyi yanda kikaso dashi babu mai ce miki don meπŸ˜‰πŸ˜*








PAGE 170 to 175





_Zaune nake gaban ogana wato mahaifin matata Khadija, ina jiran 'karin bayani dangane da kiran da yai min, Alhaji ya kalleni yace "Ahmad abinda yasa na kiraka shine 'yan uwana da suke kano da Aminaina ke so in yi takarar gwamnan jihar kano, to kaga idan nace zan amince dole sai na koma can garin da zama, kuma kadarorina dake nan garin babu mai kula dasu, a ta'kaice dai gaskiya banda sha'awar yin siyasa, kuma bana so kujerar nan ta shiga hannun azzalumai, Ahmad kai na talakawa ne me burin taimaka musu a koda yaushe, wannan dama ce ka samu domin 'kara kusanto dasu zuwa gareka, amma me kace a kai, saboda sun dameni sunce su zasu yi mini komai, so nake kaje a madadina," nai shiru ina nazari kan wannan damar da na samu, sai nace mishi ya d'an bani lokaci nai tunani, bayan munyi sallama dashi na koma gida naita nazari zuciyata na bani cewa in amince dama ce wannan na samu na taimakon talakawa da jahata kanta da kuma d'an uwana shima in samar mishi da aikin yi, banyi wata-wata ba na kira iyayena a waya na sanar dasu halin da ake ciki, da farko basu amince ba amma daga baya da nai musu bayani da kyakkyawan 'kudurina akai sai sukayi na'am tare da goyamin baya akai, haka muka koma kano da zama lokacin Khadija nada tsohon cikin yayanka Ammar, mahaifin Khadija ya had'ani da aminanshi aka fara gudanar da maganar zab'e ranga-ranga, kuma cikin yardar Allah nan da nan na samu karb'uwa gurin jama'ar kano, da zab'e yazo Allah ya bani damar lashe zab'en, anan muka cigaba da zama har Allah ya sauki matata Khadija lafiya ta haifi yaronta namiji yaci sunan Ammar, ba yabon kai ba nayi wa 'kasa aiki ba kad'an ba, 'kauyenmu kuwa saida na maida shi ya dawo kamar birni, gidan iyayena ma na gyara musu shi nai musu gangariyan plat, yayana kuwa tuni na dawo dashi kusa dani a kano muna gudanar da komai tare, koda wani zab'en ya zagayo nace to gaskiya ni burina ya cika tunda Alhamdulillah dai-dai gwargwado talakawa sun amfana, na d'auko wani bawan Allah kuma abokina wanda yake takarar kansila ada sunanshi Alhaji Ahmad Tukur, shi na barwa kujerata ya hau kuma cikin ikon Allah ya samu kujerar gwamnan jahar kano, ni kuma daga lokacin na tattara na dawo gida kontagora, tarin kud'in da na mallaka da kuma kadarorina na cigaba da juya dukiyata tare da kula da kadarorinsa, duk da dai gabad'ayan kadarorina na kano na siyar ne na sake siyan wasu a Abuja da kuma kontagora sai nabar 'yan kad'an a kano irinsu gidajena na saka 'yan haya a can, lokacin da na dawo tare muka dawo da yayana ya zama kamar bashi ba yai kyau saboda kud'i sun zauna, ya tara dukiya ba kad'an ba shima, amma duk da haka be bar mummunan 'kudurinsa a kaina ba, kuma koda wasa be tab'a nuna min mugun nufinsa a kaina ba, bayan kwana biyu muna zaune da iyayena muna magana dasu nake ce musu Alhamdulillah yanzu kam burina ya cika tunda talakawan garin nan kowa yanzu yana da abun yi, bama na garin nan kad'ai ba, sannan nima kud'ina Allah ya sa musu albarka yanzu haka inada biliyoyin kud'i a account d'ina, banda kadarorin da na mallaka, nan da nan Sunusi abun ya 'kara 'kular dashi, tunani ya fara yi akan abinda ya kamata ya yi domin yaga ya mallaki dukiyar d'an uwansa ta dawo gareshi, kuma har zuwa yanzu ban daina raba dukiyata ina baiwa yayana Sunusi ba, a wannan rabin nake kula da iyayena da shi kanshi da kuma iyalina har na taimaki wasu ma a ciki, amma duk da haka dukiyata tafi tashi habbaka sosai ma kuwa, a lokacin ne kuma ya fara neman aure ba b'ata lokaci aka sha biki matarshi ta tare a kusa da gidana da na gina mana ni da shi, Sunusi fa ya samu dukiya sedai rashin godiyar Allah yasa yake hangen tawa, sedai ban tab'a sa mishi ido akan dukiyarsa ba balle insan yanda yake tafiyar da ita dan zai iya cewa saboda ni nake bashi nake yi mishi haka, dama already inada gida a kontagora nan muke zaune da iyayena, mun dawo babu dad'ewa Khadija ta sake haihuwa ta haifoka na sa maka suna Bilal, kamarku da Ammar har ta b'aci, ita kuma matar Sunusi tana da tsohon ciki a lokacin kana da wata goma sha uku a lokacin ban tab'a mantawa da wannan ranar, ranar Litinin cikin tsakar dare muna bacci yayana ya buga mana gida cikin tashin hankali muka bud'e yake shaida mana mummunan labari cewa iyayenmu sun mutu 'yan fashi ne suka shigo gidan nemana da suka 'ki nuna inda nake sai suka kashe su, mutuwar iyayenmu ya razanar da ni sosai har wasu sukaita cece kuce akan Sunusi ne ya kashe su in ba haka ba meyasa shi ko rauni ba'a ji mishi ba bayan yana cikin gidan, koda wannan furucin yaje kunnen Sunusi sai yace ai shi da yaji motsinsu be fito ba yana bacci yaji hayaniya ya tashi koda ya bud'e 'kofa har an kashe su shi yasa be fito ba, ni dai ban tab'a zargin d'an uwana ba ko kad'an, bayan wata shida da rasuwarsu wata rana muna kwance a cikin gida da dare muna bacci sai muka ji haurowar mutane cikin gidan d'aya bayan d'aya, ni na fara farkawa, koda na bud'e idanu sai na le'ka hango mutane nayi sun kai su goma sha biyar dukkaninsu ri'ke da manya manyan makamai, abinda ya bani mamaki da tsoro shine ganin Sunusi a cikinsu shima ri'ke da nashi makamin, cikin sauri na tashi Khadija nace ta tashi maza mu tafi, ta d'aukeka a hannunta tana nunamin Ammar nace taje zan d'auko shi na nuna mata wata 'kofa ta baya nace ta fita tanan, suna fita na du'ka zan d'auko d'an uwanka sai ga su Sunusi sun shigo su biyu shi da wani, Sunusi ya buga min wu'ka a hannu, a lokacin Ammar ya tashi yana ta kuka sannan Sunusi ya yanki Ammar da wu'kar nan ina gani, har gobe bazan manta da mutuwar yarona Ammar ba, ganin haka yasa nai wani 'kara tare da yin kukan kura nai kansu na daddoke su na d'auki Ammar a kafad'a na bi ta wannan 'kofar muka fice kuma na rufeta ta baya, na sami su Khadija a tsaye suna jirana nace musu muje, gudu muke, har muka 'karaso bakin mota, zamu shiga kenan muka hangosu sun kusa cin mana, sai muka yanki daji da gudu, muna cikin tafiya Khadija sai kuka take tana kallon Ammar mi'ka mata shi nayi na karb'eka daga hannunta, muna cikin gudu muka ga sun tare gabanmu da bayanmu, gefe kuma daji ne d'od'ar, jefomin wata goora sukai ta tad'iyeni na fad'i, sai na kalli Khadija nace ta shiga cikin jejin nan ita da Ammar su b'uya, Khadija tace ni kuma fa ba zata tafi ta barni anan ba, nace karta damu 'yan sanda suna hanya na kirasu kafin mu fito, ta juya da gudu ta shiga inda na nuna mata, tana tafiya suka zo suka kewaye ni ina ri'ke da Bilal, Sunusi ne ya 'karaso har inda nake ya du'ka kusa da ni, sannan yace "malam Ahmad kenan, kana tunanin duk 'kaunar da nake nuna maka ta gaske ce, to bari kaji tun muna yara na tsaneka tsana me tsanani saboda fifitaka da iyayenmu suke, kuma sai ka fini ilimi ka fini d'aukaka a rayuwa wanda abun ya dad'e yana damuna a rai, kawai nayi shiru ne saboda banda komai ko nace zan d'auki mataki ko na kawar dakai banda kud'in da zan biya masu tayani yin wannan aikin, nine babba amma maganarka ake ji ba tawa ba, na dad'e ina jin ciwon d'aukakar da ka samu a rayuwa, babban abunda baka saniba shine, 'kaunar da iyayenmu suke nuna maka da kuma rawar jikin da suke a kanka yasa suma kansu na tsanesu, abinda yasa na kawar dasu kuwa saboda sunji lokacin da nake waya ina magana da abokaina kan yanda zamu kawar da kai, yanzu kaima zan gama da kai, abinda yasa zan kasheka a yanzu shine saboda ina so dukkanin dukiyarka da kadarorinka su zama nawa kaga ka hutar dani ma tunda rabin dukiyoyin nawa duk sunana ka saka a jiki be dace in taso cikin talauci kuma in mutu ban dangwali dad'in arzi'ki ba," kasa cewa komai nayi saboda tsabar mamaki, hawaye ne kawai suke ta wanke fuskata na kalle shi nace "yanzu dama akan abin duniya kake neman rayuwarmu yaya, meyasa baka nuna min dukiyata kake so ba tun tuni da wallahi ko zan yi yawo ba ko sisi ni mai iya tattarata duka ne in baka, saboda kai shaida ne akan irin 'kaunar da nake maka ban tab'a tsammanin irin wannan sakayyar daga gareka ba Yaya, kayi ha'kuri karka kasheni, wallahi nafi 'kaunar cigaba da rayuwa tare da kai, na baka dukkanin dukiyata, bana sonta ni kai kad'ai nake so," Sunusi ko gezau be yi ba ya kalli wani wanda ke gefen damanshi yace "Makau d'auke min yaron nan daga jikinshi," Makau yayi-yayi ya 'kwaci yaron nan daga hannuna ya kasa, koda Sunusi yaga haka sai ya d'aga wu'kar hannunshi ya luma min a ciki, a lokacin ne suka samu damar 'kwaceka daga hannuna sun juya zasu bi matata su kasheta itama sai suka ji 'karar motar jami'ai, hakan yasa dukkaninsu suka gudu da kai a hannunsu, koda 'yan sandan nan suka 'karaso inda nake da'kyar na nuna musu inda Khadija ta b'uya nace "Kha di ja na can," ina gama fad'in haka na suma a hannun d'aya daga cikin 'yan sandan, saida nai sati uku a asibiti sannan na dawo cikin hayyacina, sai a lokacin ma ni na san cewa a Abuja muke, ashe tun washe garin ranar da abun ya faru Khadija tai waya da wayar d'aya daga cikin 'yan sandan ta sanar da mahaifinta komai ya turo aka kwashemu dukkanmu aka kaimu Abuja, Ammar kuwa tun kafin na farfad'o aka sallaceshi aka kaishi makwancinshi, kai kuwa bamu san inda kake ba bamu san a wane hali kake ciki ba domin da kai suka tafi a hannunsu, daga wannan lokacin ban 'kara komawa garin ba, bayan wasu shekaru abubuwa da dama sun faru ciki kuwa harda kamuwar mahaifiyarka da ciwon zuciya me tsanani sanadin b'atanka gwara ammar munsan mutuwa yayi mun rasashi kai kuwa a kullum mun kasa cire rai da ganinka, sannan na dawo da dukkanin harkokina nan garin kano ashe alkhairi ne babba dawowana nan d'in, ashe Allah kad'ai yasan abinda ya b'oye sai yanzu yai nufin bayyanuwarsa Allah mun gode maka, to kaji irin abubuwan da suka faru dani a rayuwa My Son, ashe duk kaunar da d'an uwana ke nuna min so yake ya gama samun komai daga gareni ya kasheni, na yarda da d'an uwana fiye da kowa kai fiye da kaina ma, ban tab'a tunanin ko dabba zai iya kashewa ba, nafi jin ciwon rabani da iyayena da yayi fiye da komai._



Abba ya 'karashe maganar yana kuka, shima Amir kuka yake kanshi na kife akan cinyar Abban nashi, Umma Khadija itama kuka take sosai, duk d'akin babu mai rarrashin wani.



Amir ne ya d'ago kai cikin kuka yace

23 / 31