Author : Bilkisu Z Ya'u Category : Romantic Hausa Novels
zaman lafiya da amana insha Allah)π€π€ ```
*MASOYANA INA GODIYA SOSAI DA 'DUMBIN K'AUNAR DA KUKA NUNA A GARENI, ALLAH YA SAKA MUKU DA ALKHAIRI ALLAH YA BIYAKU DA GIDAN ALJANNA FIRDAUSI, NAGODE SOSAI WALLAHI.*
*πΈπ¦Zaman amana writer's*
*Tauraronku na haskawa a ko'ina, Allah yai muku baiwa wanda ku da mak'iya se dai kallo, lallai zaman amana alkhairi ce naga nasarorinta cikin rubutu da marubuta, ni fa bance kunfi kowa ba 'yan uwana, amma fa tabbas kunfi wasu wasu kuma sun fiku, dama haka rayuwar take kafi wani wani ya fika, tabbas kuna haskawa ku ake yayi a ko'ina, Allah ya k'ara muku basirar da se dai a kwaikwaya a wajenku, d'aukakar da zata sa a daraja girman matsayinku, d'an karen zak'in hannun da zai sa mutane su mato kan k'aunar novel's d'in kuπa cigaba da basu mamakin mutanenaπ€π€πππππ*
*Har ila yau marubutan gidan sun sake kawo muku k'ayataccen labarai, RAYUWAR SAUDAT daga marubuciya RAHEENAT M. ABBAKAR, sai MARYAMA CEE daga marubuciya MARYAM KWARE, dukkanin su yanzu aka fara ba'a yi nisa ba karku sake a baku labari wallahi ku da kanku sai kun gode min da wannan albishir d'in muddin kuka karanta su.*
*Dawo masoyiya Tawan dawo wallahi na tuba, laifin da nai ki zamto yafewa wallahi na tubaππ©π°*
PAGE 50 to 55
Tun daga wannan ranar Amir da Amira so da k'auna tare da shak'uwa me k'arfi suka k'ara k'ulluwa a tsakanin su.
Yau Litinin, kuma yau ma kamar kullum tare suka shigo cikin makarantar a motar Amira wanda Amir ya tuk'o su, shi kuma tashi tana gidan Amiran sai in zai koma gida yake hawa, wata rana ma har motar canje suke yi, ya d'auki ta-ta itama ta d'auki tashi.
Suna shigowa cikin harabar makarantar sai ya yi fakin a inda ake faka motoci a makarantar, bayan ya kammala suka fito a tare rik'e da hannun juna suka jero zuwa ajin su.
Se dai a hanyar da zata sada su da ajin nasu wasu cincirindon 'yan iskan maza ne sun kai su goma suna zaune duk d'alibar da tazo wucewa sai sun tab'a jikinta, ko sun ci zarafinta da kalaman su, wasu su wuce suna kuka wasu kuma su yi musu Allah ya isa su ruga da gudu, wad'annan bayin Allahn sun yi k'aurin suna wajen rashin ji, shiyasa ma aka rasa me tanka musu suna ta iya shegen su ana kallo, kuma dukkanin su 'ya'yan manya ne ma'ana ''ya'yan masu kud'i ne.
Wata ta wuce kenan sun gama yi mata cin zarafi sannan sai ga su Amira suma sun zo wucewa, nan take suka fara fad'in "ga wata had'ad'd'iyar nan ta taho, gaskiya ta had'u," shugaban tantiran yace "ni wallahi har naji ina sonta," duk su Amir na jinsu har ya motsa hannu Amira ta k'ara rik'e shi, ya kalleta ta girgiza mishi kai, suka cigaba da tafiya, d'aya daga cikin su ya k'ara d'aga murya yace "komai ya ji gaba da baya, gashi daga ganin wannan d'an k'aramin bakin naki to haka can ma yake k'arami," habawa Amir ya fizge hannun shi daga na Amira ya nufo inda suke tare da rufe su da duka musamman ma wanda ya furta wannan kalmar.
Yanda Amir d'in ke dukan kanshi kasan a zuciye yake, dukan su yake da tokari gashi in dai k'arfi ne kam Allah ya hore mishi musamman akan Amira, dama kuma mutum ko rago ne in yaga za'a ci zarafin abinda yake so zama jarumi yake yi, hmm so kenan.
Amira taga Amir yana ta bugun wannan gayen ba ji ba gani yama dena dukan wad'ancan wanda ya furta wad'annan maganganun yake ta bugu sauran duk sun tsere yana niyyar yin kisa, gashi wajen har an cika amma an kasa janye shi daga wajen, da an jashi zai sake jawosu su dawo tare suna rike dashi d'in yana kai duka.
Wani malamin su Amiran duk ya rud'e shima ya kalli Amira dake hawaye hankalinta a tashe yace " dan Allah ki dakatar dashi ke kad'ai ce zaki iya, in ba haka ba zai yi kisa."
Amira ta kutsa cikin wajen tai mishi magana amma ina bai san tana yi ba, sai ta d'aga hannu ta daddage ta sharara mishi kyakkyawan mari lafiyayye guda d'aya, ba shiri ya d'ago rik'e da kumatun yana kallonta, yace " ni kika mara akan wad'annan 'yan iskan, to na barki da su, zanje in yi rayuwata ni kad'ai ba tare da ke ba, saboda muddin muna tare babu wanda zai tab'aki in k'yale, ya nuna wa 'yan iskan hannu wad'anda suka yi jina jina sannan yace ku kuma ku sani muddin ina numfashina kuma ko muna tare da Amira ko bama tare bazan ragawa duk wanda yai k'ok'arin ci mata mutunci ba," yana gama fad'in haka ya juya yai tafiyarsa.
Amira ta tsaya nan sakato tana hawaye ita tai marin kuma shi ta mara amma har ga Allah ita ke jin rad'ad'in a ranta, bata ji dad'in marin da tai mishi ba amma dole sai ta yi haka zata dakatar da shi, in ba haka ba zai iya yin kisa a kama su ita da shi.
Bayan malaman wajen da security's na makarantar sun yi bincike aka tabbatar musu da cewa 'yan iskan ne da laifi domin kullum haka suke yi, bayan an ja kunnen su aka tarkata su aka yi asibiti dasu domin yi musu maganin raunikan da uban soyayya yai musu.
Amira ce keta sauri ta shiga cikin aji, tana zuwa ta tarar da malamin English d'in su ya riga da ya shiga, kuma shi a k'a'idarsa in ya riga da ya shiga babu wani kuma wanda zai sake shigowa, ko ka shigo sai ka fita.
Tana shigowa malamin English ya kalleta yace ta fita, ba musu ko magiya ta juyo domin tasan ba wanda zai yi amfani, wani keb'antaccen waje ta je ta samu ta zauna inda Amir zai hangota dan ta tabbatar shima fitowa zai yi.
Bayan ta fita Amir ya tarkata i'nashi-i'nashi ya mik'e zai fito, malam ya kalle shi yace " kai kuma ina zaka je?" Amir yace " malam ko na zauna wallahi ba zan fahimci komai ba a karatun ka muddin Amira bata ciki," be jira ma yaji abinda malamin zai fad'i ba yai waje abinsa, malamin da d'aliban gaba d'aya aka bishi da kallo har ya fice.
Yana fita ya hangota, k'arasowa ya yi inda take ya zauna d'an nesa da ita tare da shan mur, Amira ta kalle shi tare da yin murmushi, ta matso kusa dashi, ya sake matsawa, ta k'ara matsowa, haka sukaita yi har suka kai k'arshen kijerar, sai ya yunk'ura zai tashi Amira ta rik'e shi ta hanashi tashi, a dai-dai wannan lokacin kuma sai ga wasu mata sunkai su Ashirin sun tunkaro wajen su, suka gaggaisa da hannu da Amiran da Amir duka, sannan suka yi mishi godiya sosai akan taimakon su da ya yi yai musu maganin wad'ancan 'yan iskan tare da jinjina mishi, Amir yace musu ba komai, haka mata da maza sukaita zuwa suna mishi godiya, shi kam abun mamaki yake bashi ya harari gefen Amira sannan a fili yace " ashe ni abinda nayi taimako ma nayi sosai haka amma nasha mari gun wata."
Amira ta kwantar da kanta a kan kafad'arsa, sannan tace " dan Allah ka yi hak'uri na san ban kyauta ba, amma hakan da nayi shi kad'ai ne mafitana saboda bana so kai kisan kai a kashe mu," Amir yai murmushi jin tace a kashe mu wato harda ita ma za'a kashe kenan.
Amira ta sake kallon shi tace " meyasa ka fito daga cikin aji?" Amir yace "hasken cikin ajin ya d'auke duhu ne kawai a ciki hasken yana nan waje."
Amira tai murmushi domin ta gane manufarshi, nan dai ta bashi hak'uri suka shirya.
Suka zauna nan suka sha hirar su har malamin English d'in ya fito, sannan suka koma tare da yin sauran karatuttukan, bayan sun kammala gaba d'aya suka koma gida.
Haka suka kasance a koda yaushe suna tare dai-dai da 'yan mintuna basa iya jure rashin juna, hakan yasa karatun su ya fara zama shiririta saboda in har fa babu d'aya a ajin to basa zama dukkanin su, sam basu damu da karatun ba yanzu soyayyar su kad'ai suka sa a gaba, yanzu ma dai gaskiya babu abinda yafi musu muhimmanci irin kasancewa da junan su.
Bayan kwana biyu ranar Juma'a ne wajen k'arfe biyu sun riga da sun yi karatu sun dawo gida, zaune suke a kujera Amira na kwance yayin da Amir ke zaune, Amir ya kalleta yace "Amira yaushe zaki kaini gidan ku neman izinin aurenki, na matsu na mallake ki matsayin mata?"
Kafin Amira ta bashi amsa wayarta tayi k'ara Dad d'inta ne ke kira, bayan ta d'aga suka gaisa sannan ya shaida mata ta shiryo ta taho gida yanzu yai mata bukin d'in jirgi ta hanyar wani abokinshi lokacin bikin sister d'inta ya zo, jiki a sanyaye ta amsa mishi da "to" Dad yace " ya naji bakya murna bayan dad'ewar da kika yi kina d'okin zuwan wannan ranar, kuma ke kikace a sanar dake in yazo kar a yi bakya nan?" Amira tace " ina murna mana sosai Dad" kuma a yayin da take fad'in haka kallon Amir take yi tana hawaye tana tausayin halinda zai shiga in ya yi nesa da ita, shi kuwa Amir ganin haka duk hankalin shi ya tashi, ya k'osa ta gama wayar ya ji meke faruwa, nan dai Amira suka yi sallama da Dad d'in nata.
Suna gama wayar Amir ya kalleta yace " daga gida ne koh, me akace miki, aure zasu yi miki, fad'amin mana."
Dafa goshinta ta yi da hannu sannan tace "Amir ka natsu mana, duk ka bi ka d'aga hankalinka wad'annan tambayoyi haka wanne zan fara amsawa," tashi ta yi ta K'araso kusa da shi, sannan ta dafa shi tace " Amir Dad yace in taho gida yanzu bikin sister na ya taso, daga gobe za'a fara gudanar da shagalin bikin, d'iyar k'anin mahaifina ce tare da ita muka taso kamar 'yan biyu, shiyasa naita jaddada musu kar a sake bikinta ya matso ba'a sanar da ni ba, a da babu labarin da yafi soyuwa a gareni irin inga lokacin bikin nan, amma a yanzu babu abinda nafi tsanar jinshi irin labarin nan, wallahi Amir duk abinda zai nisantani da kai ko na minti guda ne bana k'aunarsa."
Amir ba k'aramin razana ya yi ba jin wannan labarin, a duniya a yanzu babu abinda ke zamar mishi tashin hankali irin yin nisa da Amira.
Amma sai ya dake tare da kallonta yace " kiyi hak'uri ai ko kin tafi bamu rabu ba, tunda ga waya ga kuma Whatsapp zamu rik'a yin chat, tashi maza ki shirya," duk yanda yaso yai kuka saida ya dake ya hana k'wallar idanun shi zubowa saboda kar ta gani ta k'ara shiga damuwa, ko tace ma ta fasa.
Ganin bata da niyyar fara yin shirin tafiyar yasa ya tashi yaje bayi ya had'a mata ruwan zafi, ya fito ya ja hannunta har zuwa bayi ya turata ciki yace tayi tai wanka ta fito, sannan ya rufo mata k'ofar, ya dawo ya jawo Jakarta tare da shirya mata kaya d'aya bayan d'aya, duk kayan da yafi so in tasa yake yaba su su ya zab'ar mata, yana had'a mata kayan yana zubar da hawaye, jin k'arar bud'e k'ofar bayin yasa yai saurin share hawayen fuskarsa.
Bayan ta shirya ta saka kayan da ya ware mata sai ta kira Dad d'inta ta fad'a mishi gata nan zata taho, Dad d'in yace taje filin jirgi in taje ta sake kiran shi akwai wanda zai had'ata dashi yai mata komai.
Bayan sun gama waya suka fito suka shiga motar Amir suka d'auki hanya sai filin jirgi.
Koda isar su ta kira mahaifinta kamar yanda ya umurceta bayan sun shiga daga ciki, yace ta jira zai turo wani wajenta yanzu, bayan wasu 'yan mintuna sai ga kira da wata lamba, tana juyowa taga wanda ya kira d'in ya nufosu, nan suka tafi tare dashi aka gama mata bukin d'in komai sannan suka yi sallama da Amir har ya juya sai ta k'wala masa kira, be juyoba har sai da ita ta k'ara so wajensa ta rungume shi ta baya sannan tace " zan yi kewarka Amir," ta fashe da kuka, juyowa ya yi, sannan ya d'ago ta da hannayen shi biyu yace "nima zan yi kewarki Amira, gwara ke cikin 'yan uwanki zaki shiga zasu d'ebe miki kewata, ni kuwa yanzu zan zama kamar marayan da ya rasa kowa, dan Allah Amira karki manta da ni," yana gama fad'in haka ya zame hannunshi da ta rik'e k'am tana kuka ya tafi domin kuwa ya fara jin sanarwar cewa kowa ya shirya jirgi zai d'aga, in be tafi ba itama bazata samu yin tafiyar ba, hakan yasa ya yi tafiyarsa, har ya bud'e mota zai shiga yaji muryarta da k'arfi tana fad'in " kar kai kuka Amir, ina sonka, ka rik'e min amanar kanka," Amir ya kasa daurewa ya juyo da idanuwan shi da suke zubar da hawaye, sannan ya d'ora su a kanta, suka kalli juna sannan Amira ta juya ta shige ciki da gudu, shima ya fad'a mota ya kifa kanshi kan sitiyarin motar yana ta kuka.
Muje zuwa
*π
±K CEππ*
ππππππππππ
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
ππππππππππ
RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (π
±K)*
```(Autar marubuta)```
SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
```(Mamie) ```
*πΈπ¦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah) ```π€π€
*'YAN UWA ABOKAN AIKI πΈπ¦ZAMAN AMANA WRITER'S*
*AISHAN UMMA*
*MEELAT A.H.K (Bloodynah)*
*MUMYS FRIEND (Tawan)*
*QUEEN RUQEEY (Habibty)*
*MAIMUNA ADAM (My Memcy)*
*RAHEENAT M. ABBAKAR (My Heenat)*
*ASIYA SEE-SSE (My Friend)*
*MARYAM KWARE (My Swt Sister)*
*SOYAYYAR KU TA ZAMA JINI NA JIKINA ZUCIYA NA BAKU KYAUTA,ππ ALLAH YA BARMU TARE YA K'ARA HAD'E KAWUNANMU, A CIGABA DA BASU MAMAKI GUY'S.πππ*
*SANARWA!π£ mashahuriyar fitacciyar matashiyar nan mai suna AISHA ISA MUMMY'S FRIEND ta sake kawo muku shiryayyen labari mai suna RUUUHIN 'DANA, karku sake a baku labari, RUHIN 'DANA labari ne da yake cike da sark'ak'iya da tirka tirka kai abun dai sai wanda ya karanta, ba'a yi nisa ba shima karku sake ku zama 'yan kallo ayi babu ku, kada ku manta sunan littafin RUUHIN D'ANA!!!!*
*MY LISSA ina rok'on mahaliccina Allah ya d'orar da lafiyasa garekiππ*
PAGE 55 to 60
Amir ya dad'e zaune a cikin mota yana kuka idanun shi duk sun yi ja kamar me ciwon ido, daga k'arshe ya baiwa zuciyar sa hak'uri tare da yiwa motarshi key ya jata sai hanyar gida.
A kan hanyar Amir ta zuwa gida ya lura da wata mota a bayanshi shi kawai take bi da gudu, haka suka fara tsere kan ti-ti, can sai yaga an sha gabanshi da motar, ba shiri dole shima ya taka burki da sauri, abun mamaki Insp Yahya ne ya fito daga motar bayan shi kuma wasu 'yan sanda ne ke mara mishi baya har suka k'araso inda Amir yake.
Suna zuwa Insp Yahya ya kalli Amir yai murmushi sannan yace " malam Amir kenan, daga ina haka, ko daga gun mutuniyar kake?"
Amir yace "eh" a tak'aice.
Insp Yahya ya sake yin murmushi, sannan yace " a kwanakin baya kai da Amira ne kuke ta magana kan hujja hujja ko, to albishir nazo in yi maka nan da d'an wani lokaci zan gabatar da shedar da zata tabbatar da cewa daga Abdul har Sadeeq kashe su aka yi, kuma sai na gabatar da wanda ya kashe su duka," yana gama fad'in haka ya juya ya shige mota tare da sauran jami'an tsaron suka tayar sukai tafiyarsu.
Amir hankalin shi ya tashi matuk'a, tunani yake yi meyasa Insp zai rik'a danganta shi da kisan nan ne, haka nan dai ya ja motar shi ya k'arasa gida jiki duk a mace kuma cike da damuwa me d'auke da d'umbin tashin hankali.
Amira kuwa kuka take yi kamar ranta zai fita, duk idanunta sun kumbura, zuciyarta ce ke fad'in ashe haka masoya ke ji a duk lokacin da wani abu zai raba su, lallai ko menene mutum zai iya yi akan so musamman idan har yaga ana nema a rabashi da abinda yake k'auna, tun da suka shiga cikin jirgin Amira bata bar zubar da hawaye ba, har suka k'araso cikin garin Abuja Dad d'in nata ta kira ta sanar da shi sun iso, bata dad'e da sanar da shi ba sai ga motoci rututu an turo su d'auketa, nan da nan ta shiga suka ja suka tafi.
Amir kuwa yana k'arasawa gida wayarsa ya ciro yaga 10 missed call's d'in Amira, mamaki yake yi yanda aka yi sam be ji ringing d'in wayar ba, ya kira wayar tare da karawa a kunnensa.
A dai-dai lokacin da yake kira Amira sun k'araso gida an bud'e mata k'ofa zata fito daga cikin motar, 'yan uwanta da iyayenta duk gasu nan a tsaye harabar gidan sun fito tarbar Amira.
Ta sak'alo k'afafunta kenan zata fito daga motar kiran Amir ya shigo, ta d'aga cikin sauri tare da karawa a kunne tace " hello Amir d'ina wallahi nayi kewarka," Amir ya sauke sassanyar ajiyar zuciya sannan yace " Amira kema kinsan rashinki dole sai ya tab'a ni, bazan ma iya misalta miki adadin rad'ad'in da rashinki ya haifar a gareni ba, kin kai gida ko har yanzu kuna hanya?"
Amira tace " gani cikin gida yanzu muka k'araso ina ma cikin mota ko fitowa banyi ba naga kiranka, ya naji muryarka duk ta canza, kayi kuka ko, ba na hanaka yin kuka ba, kasan dole naji ba