SO MAHADIN RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVELS PDF BY BILKISU Z YAU.txt

Author :  Bilkisu Z Ya'u Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   18 / 31

51K to 54K   out of 90.7K words

gashi ya dawo da yake ba nisa gidanta daga station d'in nan, ya shaida min ya bata har ta bashi takarda ma ya kawo min, ta rubuta cewa sa'kona ya iso gareta kuma ta karanta Allah ya kaimu ranar, na sallami d'an sandan nan ya tafi, Amir yace "ai har yanzu baki fad'a min abinda kika rubuta mata ba," Amira tace "ro'konta nayi ta taimaka min za'a kashe min miji, na bata labari a ta'kaice, sannan nai mata bayanin shari'ar da akai a baya, nai mata kwatancen kotun farko nace taje ta samo hujjojin da suka gabata a case d'in baya domin mu yi amfani dasu wajen samun nasara a case d'in, kaji yanda akai," Amir yace "lallai Yasmeen ta taimaka sosai amma ke kin fita taimakona saboda kece kika samar da hanyar taimakon, nagode Amira ta, tabbas ni da ke amana ne, kuma rabuwarmu aiki ne, Allah ya barmu tare," Amira tai murmushi, sannan tace "ameen, kai kuwa naga zan rasa masoyi ba dole in rud'e ba, koda yake ko mutuwar ne ma 'kafata 'kafarka sedai a kashemu tare," dukkan su sukai dariya.



Yau litinin, kuma a yau ne suka sake halartar kotu a karo na uku domin zama na 'karshe.



Bayan an karanto case d'in su Amir sai aka mi'kawa Alk'ali takardun domin gudanar da cigaban shari'ar, Al'kali ya d'an jima yana rubuce-rubuce, sannan ya d'ago kanshi ya kalli lauyoyin yace "kafin mu yanke hukunci kan wannan shari'ar ko akwai lauyan da zai 'kara cewa wani abu a cikin ku?" dukkansu suka ce "babu ya mai girma me shari'a," Al'kali yace "A bisa sauraron hujjoji da bayanan kowane b'angare, a bisa shaidun da Yasmeen ta gabatar mana na ha'ki'ka muma mun 'kara yin namu binciken mun tabbatar da gaskiyar shaidunta, saboda haka kotu ta yanke hukunci kamar haka: kotu ta wanke Amir daga zargin da ake mishi na kisa domin bashi da hannu kwata-kwata a ciki, sannan kotu ta bada izinin sake shi ya cigaba da gudanar da harkokinsa na rayuwa, kuma kotu tana gargad'in Insp Yahya kan ya ri'ka yin bincike kafin ya zartar da hukunci, karya sake bada shaidar 'karya akan abinda bai tabbatar ba, kuma karya sake turo mai laifi kotu ba tare da hujjoji bayyanannu ba, in ya sake haka to za'a hukunta shi kuma zai iya rasa aikinsa ta dalilin haka, bayan haka zai biya Amir million d'aya sakamakon b'ata mishi suna da lokaci da ya yi, da wannan nake cewa a nan muka kawo 'karshen wannan shari'ar," nan da nan Kotu ta d'auki ihu da fito saboda tsabar jin dad'i, 'yan sanda suka cire wa Amir ankwar dake hannunsa aka sallameshi, an zagaye su sai bashi hannu ake ana tayasu murnar samun nasara.



Insp Yahya kuwa ya kasa motsawa daga inda yake zaune, babu abinda ranshi ke yi banda suya.



Amir kuwa har sun kai bakin 'kofa zasu fita suka hango Insp, Amira ta ja hannun Amir suka 'karasa wajenshi, Amira ta kalle shi tana dariya tace " Insp Yahya sai ha'kuri fa nasan ba haka rai yaso ba, se dai ka sani cewa duk abinda Allah ya rufe ma'ana ya sirranta to babu wanda ya isa ya tone shi ya tonu, sai a d'au ha'kuri Amira da Amir dai Allah be ce yanzu zasu mutu ba tukun, sannan abu na 'karshe shine in kana so kai ka cigaba da tsira da ranka karka 'kara shiga harkarmu, in kuma ka 'ki to tabbas kwanan nan ba'kin ciki zai zama silar ajalinka," ta sa'kala hannun Amir cikin nata suka juya sukai tafiyarsu, suka barshi nan da takaicin da suka k'ara 'kunsa mishi.



Insp Yahya ya dad'e zaune daga 'karshe wayar Dad tasa ya d'aga tare da mi'kewa ya fita daga cikin harabar kotun, sauran jami'an da ke kewaye dashi suka mara mishi baya.



Cikin mota suka shiga suka ja, hanyar station suka nufa, Insp Yahya yaiwa Dad bayanin duk yanda shari'ar ta kaya a kotu da irin hukuncin da aka zartar a kanshi, Dad ya numfasa, sannan yace ya kwantar da hankalinshi zai biya kud'in da akace ya biyasu, kuma zasu sake d'aukaka 'kara wata kotun, Insp Yahya yace "ranka ya dad'e aikina nake tsoro kar na rasa kan wannan case d'in," Dad yace "kar ka damu, muna tare ai babu me dakatar da kai, ko an dakatar da kai zansa a maida kai, ko ka manta da matsayina na shugaban 'kasa ne, ko ka rasa wannan aikin inada wad'anda suka fishi wanda zan samar maka," Insp Yahya fa hankali ya kwanta nan da nan walwalarshi ta dawo, yaiwa Dad d'in Amira godiya sannan suka yi sallama.



B'angaren su Amir kuwa suna fitowa daga kotu suka tari me keke napep suka hau sai gida, gidan Amir suka yanke shawarar tafiya da niyyar bayan kwana biyu in sun huta sai su tafi gidanta su kwaso kayanta su dawo nan gidan Amir d'in da zama gaba d'aya.



Da isar su 'kofar gidan bayan sun fito daga napep Amir ya baiwa me napep d'in ha'kuri yace bari su shiga ya d'auko mishi kud'in, me napep d'in yace "ba damuwa," suka shiga Amira ta yada zango a falo, shi kuma Amir ya wuce ciki ya d'auko dubu d'aya ya kaiwa me napep yace ya bar canjin, me napep yaita godiya.



Yana komawa ciki yaga Amira uwar tsabta an fara kaye kaye saboda 'kura da d'akin ya yi, shima ya wuce ciki ya cire kayan jikinshi ya bar gajeren wando da singileti ya fito suka ci gaba da gyaran gidan tare, saida suka gyara ko ina suka kuma wanke inda zasu wawwanke sannan Amira ta tura Amir toilet yai wanka, ita kuwa ta wuce kicin ta shiga shirya musu abinci, amma saboda ta gaji taliya ta dafa musu, cikin 'kan'kanin lokaci ta kammala ta zubo a kula ta fad'a wanka, tana jiyo Amir na fad'in "nifa yunwa nake ji zan d'ibi nawa inci kawai," Amira tace "wallahi karka tab'a min abinci, in kaci baka jirani ba wuta bal-bal," Amir yai dariya, sannan yace "Allah ya shiryeki a bayi kike magana ko, yayi kyau."



Bayan ta fito suka ci abincin su suna ci suna hira har suka kammala, dai-dai lokacin sallar Azahar yayi suka yi alwala sukai sallah, suna idarwa bayan sun yi addu'o'i da nuna godiyarsu ga Allah suka kwanta abinsu ba b'ata lokaci bacci ya d'auke su.


Bayan kwana biyu Amir suka je gidan Amira suka kwaso dukkanin kayanta da abubuwan da zata yi amfani dashi ta dawo gidan mijinta Amir da zama gaba d'aya.



Haka rayuwar su ta cigaba da tafiya cikin walwalwa da jin dad'i.


*BAYAN WATA 'DAYA*

Amir zaune yake kan doguwar kujera a yayin da Amira uwar son jiki ta lafe a jikinshi kamar mage, yanata 'ko'karin d'agata tana 'kara ma'kal'kale shi, Amir yace Allah ki d'agani ko in yar dake, bakya ganin kin zama wata 'katuwa ne hatta nauyinki ya 'karu, gaskiya ina ganin zan kai ki asibiti a duba min ko mutane biyu ke danne min jiki ban sani ba," Amira tace "me kake nufi?" Amir yace "ina nufin a duba min ko ciki gareki mana," Amira ta 'kara kwanciya jikin shi sannan tace "ba wani ciki, kawai tsabar iya kiwonka ne," Amir ya bud'e baki zai yi magana kenan sai suka ji ana knoking d'in 'kofar su, nan da nan suka gyara zama sannan Amir ya bada izinin shigowa, domin su duk a tunanin su me wanki da gugansu ne yazo.



Insp Yahya suka gani ya shigo shi da wani mutumi yana wurga musu wani irin wula'kantaccen kallo, ba shiri dukkansu suka mi'ke tsaye cikin sauri, Amira tace "malam me ya kawoka gidanmu?" Insp Yahya yace "kwantar da hankalinki 'yan mata, wannan ba zuwana bane ni d'an rakiya ne kawai, ya juya ga wannan mutumin yace yi musu bayani."



Wannan mutumin ya kalli Amir yace "kaine Amir ko?" Amir yace "eh ni ne, lafiya?" wannan mutumin yace "sa'ko aka aikoni daga babban kotu dake gwammaja kan zargin kashe Sadeeq, sai kuma 'kararka da ake yi kan guduwa da wannan yarinyar ta kusa da kai, ga takardar," ya 'karashe magana yana mi'ka wa Amir takardar dake hannunsa.



Amir yai murmushi tare da karb'ar takardar, sannan yace "ba damuwa Allah ya kaimu ranar," Insp Yahya ya dafa kafad'ar Amir, sannan yace "karfa ka ji haushina domin wannan karon ba ni na shigar da 'karar ba, me gayya me aiki ne shugaban 'kasa wato uban yarinyar da ka sace," har ya juya sai yaji Amir yai dariya, dariyar ta sakashi juyowa domin yaga me yake wa dariyar, Amir ya kalleshi yace "in kana tunanin ina tare da damuwa to wallahi ka daina, domin ni a shirye nake da ko ina za'aje domin yin wannan case d'in na dad'e da shiryawa hakan, kasan dalili? Insp yai shiru, Amir yace saboda a koda yaushe nasara a hannunmu take saboda Allah na tare da mu," Amira ta taho da gudu ta rungume Amir tare da manna mishi kiss a kumatu tace "da kyau namiji, na gode wa Allah da mijina ya zama jarumi kamar matarshi, ya daina tsayawa lusaran 'yan sanda irin wannan abun ta nuna Insp Yahya suna fad'a mishi magana son rai."



Shi d'an sa'ko dama yana mi'ka takarda ya fice ya shige mota yana jiran Insp Yahya, Insp saboda 'kunci da ba'kin cikin maganar da suka dan'kara mishi da ya juyo zai fita sai da ya bige da bango suka kuwa kwashe mishi da dariya.



Suna kan hanya yana tunani, can yana zancen zuci be san ya fito fili ba, fad'i yake "wai ni take cewa lusari, banda ina 'kaunarta da tuni na koya mata hankali wallahi."

_(topha masu karatu kunji wata sabuwa kuma, ni Bk na mato kan Insp Yahya ashe algungumin Amira yake so ba ni ba)_πŸ˜³πŸ€”πŸ˜°


Wanda aka had'osu tare da Insp d'in ya kalle shi yace "yallab'ai kai da wa kake ta magana kai kad'ai, naga kamar tunda ka fito daga gidan can ranka a b'ace yake lafiya?" Insp Yahya yace "bakomai, dama tun kafin muzo nan ina tare da damuwa kan fad'an da muka yi da wata budurwata," mutumin nan yace "ayya ashe lamari ne na so, to Allah ya dai-daita ku," Insp Yahya yace "ameen."



Haka aka sake shiga kotu nan ma su Amir ne suka yi nasara, haka sukaita d'aga 'kara daga wannan kotun zuwa waccan haka akaita korar 'karar, da suka ga ba nasara sai kawai suka ha'kura, tare da tunanin wata mafitar kuma.



Amir da Amira na zaune suna maganar komawarsu makaranta sai suka ji sallamar yaro, bayan ya shigo ya gaishe su, sannan ya mi'ka wa Amir wasi'ka yace "wai gashi inji Dadyn Amir da Amira yace a baka kuma gobe kuje Abuja yana son ganinku akwai maganar da zaku yi, dukkansu sai da gabansu ya fad'i jin wanda aka ambata, Amir ya karb'i takardar ya sallami yaron, sedai ya kasa bud'ewa ya karanta ya k'urawa wasi'kar ido sai jujjuyata kawai yake.





_Wata sabuwa inji 'yan caca, to me Dad ya rubuto kuma?πŸ€”_








Muje zuwa









*πŸ…±K CEπŸ˜˜πŸ’‹*
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜









RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (πŸ…±K)*
```(Autar marubuta)```





SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
```(Mamie)```





*πŸ‡ΈπŸ‡¦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```πŸ€œπŸ€›







PAGE 135 to 140






Dukkanin su sun ji tsoro da fargaba a ransu musamman ma Amir da takardar ke hannunsa amma ya kasa karantawa sai faman kallonta kawai yake yi.



Amira ce tai ta maza ta zare takardar daga hannunsa ta bud'e ta fara karantawa, kawai Amir ji yayi tana fad'in "tab' Allah ba inda zamu je, ni nasan akwai abinda Dad ya shirya tunda har yake neman mu," Amir wanda jikinshi yai sanyi tun d'azu ya kalleta yace "me Dad d'in yace?" Amira tace "cewa yai wai muyi ha'kuri da dukkanin abinda ya faru, shi komai ya wuce a wajen shi, amma in har muna so auren mu ya cigaba to dole sai mun zo ya yi wata muhimmiyar magana da mu, kuma gobe yake so mu taho da sassafe, gaskiya Amir kar muje ni ina jin tsoro kaga haka yai min wayau lokacin da ina 'karama aka rabani da kai, sannan lokacin da muka je 'kauye ma ranar da muka kunna wayoyinmu cewa yai komai ya wuce muna ina, ashe so suke a gano inda muke a kama mu, ni gaskiya ban yarda muje ba."



Amir ya numfasa sannan yai 'ko'karin b'oye tashi damuwar, yace "Amira ki kwantar da hankalinki, duk abinda kike bana so ki ri'ka manta matsayin su Dad a wajenki, kuma ai dama ko basu neme mu ba wata rana mu dole mu neme su, ni bansan iyayena ba tun ina yaro har na girma kuma har yanzu ina tunanin ina suke a wani hali suke ciki ban sani ba, Amira dole muje muji dalilin kiran da mahaifinki ke mana, saboda rashin zuwan ma wani 'karin laifi ne da zamu yi a wajen shi, dan haka ko da cutar da mu zaisa ayi ya zama wajibi a garemu muyi masa biyayya mu bi abinda yace, ni ba fatana ku kasance a haka ke da mahaifinki ba, fushin iyaye baya haifar da komai wallahi sai lalacewar rayuwar mutum, kuma ni ba zan so rayuwarki ta lalace ba ta sanadina, kullum tunanina dama taya zan shirya ki da mahaifinki, kiyi ha'kuri ki amince muje kinji?"



Amira ta numfasa tare da goge hawayen da ke idanunta, sannan tace "ko ada bana iya yiwa maganarka musu balle a yanzu da ka zama miji a gareni, Allah ya kaimu goben, kuma ina godiya a gareka da kyakkyawar tunatar da ni da kayi kan darajar iyayena, tabbas so kan makantar yakan sa kayi kuskure ko ka manta da komai, amma in kai sa'ar masoyi na gaske kuma nagari koda yaushe 'ko'karinsa yaga ya saka a hanya, saboda ranshi zai sosu a duk lokacin da aka nuna ka akace yau kai ne ka aikata ba dai-dai ba, wallahi ina alfahari da kai, kuma ka 'kara shiga raina fiye da ko yaushe."



Nan da nan suka saki ransu tare da cigaba da hirarsu cikin nishad'i da walwala.



*WASHE GARI*

Washe gari kamar yanda aka umurcesu da sassafe suka tashi suka shirya, sun sha ankon shadda, Amir riga da wando da malum-malum, Amira kuma doguwar riga ce a jikinta tasha aiki me d'an karen kyau da tsada, bayan sun gama shiryawa suka d'auki hanya, kuma da yake basu da wadatattun kud'i a hannunsu na tafiya a jirgi sai suka tafi a motar Amira wadda ita kad'ai ce ta rage musu a yanzu, domin sun yar da ta Amir lokacin da suke gudun cetan ransu, yanzu in za'a kashe su basu san inda motar take ba.



Sun d'auki awanni anata tafiya har Allah ya kawo su garin Abuja lafiya, da yake motar tasu ce ba ta haya ba kai tsaye gidan shugaban 'kasa wato Dad mahaifin Amira suka wuce.



Suna shigowa cikin unguwar tun daga nesa suke ganin adon furanni da busa da kad'e-kad'e kai kace gidan saraki, ana bud'e gate kuwa zasu kutsa da motarsu aka fara antayo musu fulawoyi har zuwa inda zasu faka motarsu, cikin sauri aka bud'e musu mota suka fito, sakin baki suka yi suna kallon yanda aka k'awata harabar gidan da kyawawan ado, mahaifiyar Amira da Dad d'inta da su Uncle kai har da sistern ta d'iyar Uncle d'in suna tsaye a bakin 'kofar da zata sadaka da shiga ciki, da gudu Amira ta 'karasa wajen Dad d'inta ta rungume shi tana kuka tare da fad'in "Dad dan Allah kayi ha'kuri ka ya......" kafin ta 'karasa Dad ya rufe mata baki tare da d'agota ya share mata hawaye, sannan yace " na yafe miki Doughter nah, kinsan ina sonki bana iya yin fushi dake," ya kama hannunta sannan ya yafito Amir da ya zuba musu idanu da hannu, yana zuwa shima ya ri'ke mishi hannu suka yi musu barka da zuwa sannan suka yi musu jagora har cikin babban falon gidan.



Dad kuwa in ka ganshi a wannan ranar zaka ce ba shi bane, saboda yanda yake ta bayyanar da farin cikinsa kamar wani abu bai tab'a faruwa ba.



Bayan an ci an sha, sannan suka dawo babban falo suka zauna, Dad yai gyaran murya sannan ya fara magana "abinda yasa na kira ku shine saboda in sanar da ku cewa komai ya wuce, kuma hatta aurenku mun yarda dashi, amma akwai sharad'i, saboda matsayina da kuma martabar gidan nan dole sai ka kawo mana iyayenka nan mun gansu, kuma daga yau har zuwa ranar da zaka gano inda iyayenka suke a nan gidan zaku cigaba da zama, in yaso in ka gabatar mana da su sai ka d'auki matarka ka tafi da ita ma duk inda zaka tafi da ita, rashin yin hakan zai sa da kai da wad'anda suka yi muku jagora wajen yin aure zan makaku a kotu a raba aurenka da 'yata kuma kasan tsab za'a raba d'in tunda ba mu muka d'aura ba kuma ba da yardarmu ba."



Mugun tashin hankali suka shiga daga shi har Amira, babu abinda zuciyarshi ke ayyana mishi game da wannan maganar illah anyi haka ne domin a rabashi da Amira, in ba haka ba ta ina zai fara neman iyayenshi.



Irin tunanin da yake itama Amira shi take yi, cikin sauri ta mi'ke tana fad'in "haba Dad, be kamata ka....." Dad ya d'aga mata hannu tare da fad'in "ya isa Doughter, ni mahaifinki ne, a baya mun barku kun yi yanda kuke so, a yanzu dole ku barmu muyi namu binciken a matsayinmu na iyaye, kuma na gama magana," ya mi'ke yai shigewarsa d'aki.



Uncle ya numfasa, sannan yace "gaskiya Amira ki rage yiwa mahaifinki musu a kan namiji da bashi da tabbas, kuma in kina canza halinki ta hanyar bijirewa maganar iyayenki to shi zaki jawa tsana a idanunmu, a yanzu kam ina goyon bayan maganarshi, sai kuje kuyi tunani, d'akinki shine masaukin ku an gyara ko ina, shikenan kowa ya tashi ya tafi an gama meeting d'in."



Haka kowa ya watse ya barsu a nan falon, shi kuwa Amir tunda yaji wannan maganar ya zama

18 / 31