Author : Bilkisu Z Ya'u Category : Romantic Hausa Novels
dama saboda in gwadaka ne, dan haka karka damu na yarda dakai, fatana ka nunka duk wata kulawa da kake yiwa 'yata kuma ka ri'ke amana ka kuma cika al'kawari."
Bayan sun gama magana Nura yai godiya harda hawayen drama sannan suka yi sallama ya wuce gidan Babanshi kai tsaye.
Da isarshi ya kwashe duk yanda suka yi da mahaifin Amira ya fad'awa Babanshi.
Zama suka yi suka dudduba takardun, a ciki babu na kamfanin da aka baiwa Nura, babu na mahaifinsa, sannan babu na gidan Dad wanda yake ciki da kuma na su Amira.
Nura yace "wallahi suma sai ya bada su, lallai ba zamu bar mishi komai ba sai mun yashe shi, wai harda ce mana talakwa a cikin maganarshi be san kalmar taban haushi ba, amma kwanan nan kalmar zata fara aiki a kanshi muga kuma 'karyar 'kin talaka," suka she'ke da dariya harda tafawarsu, nan suka cigaba da tsara mugayen shirinsu akan su Amira.
Washe gari Nura ya dawo daga aiki bayan sun rabu da Amir kamar kullum sai ya wuce gida.
Yana zaune wayarshi tai 'kara, yana dubawa yaga ashe mahaifinsa ne, yana d'agawa yaji mahaifinsa ya fara fad'a, "Nura ashe kai wawan yaro ne da ina cewa na haifi yaro me wayau, baka san wannan yaron da na ganku tare dashi a bakin ti-ti shine tsohon mijin Amira ba?" to in baka sani ba yanzu ka sani ai, shashasha kana nema ka rusa komai," yana gama fad'in haka ya kashe wayarsa, shi kuwa Nura wanda tun d'azu yake a tsaye, ya fara kai kawo yana nazarin wannan maganar, ganin duk wannan bazai fish she shi ba yasa ya zari makulli ya fice daga gidan.
Nura zaune yake gaban Babansa yana yi mishi tambayoyi, "Baba wanene mijin Amira da kace ka ganmu tare dashi?"
Baba yace "d'azu na ganku tare dashi," nan ya shiga koro mishi bayanin siffar Amir da kuma kayan da ya saka.
Lallai a yanzu Nura bashi da hujjar 'karyata zancen mahaifinshi ko ya musa mishi.
Nura yai murmushi sannan yace "ka kwantar da hankalinka Baba, dama na dad'e ina zargin wani abu game dashi, sannan ina sane nai saurin sabawa dashi domin in fahimci ko shi wanene saboda in d'auki mataki a kanshi da wuri, karka wani damu inada aboki d'an abokin nan naka Baba, babban d'an sanda ne shi yanzu a garin nan, ba wanda ya isa ya ja damu muddin muna tare dashi, zamu had'a hannu dashi, bari ma ka gani."
Wayarsa ya zaro yai kira har ta katse ba'a d'aga ba, sai a kira na biyu aka d'aga, bayan sun gaisa Nura yace "daga jin muryar babu tambaya Insp Yahya ne kafi 'karfin mugu?" yai maganar da sigar tambaya tare da yin shiru yana jiran amsa
Muje zuwa
*π
±K CE*ππ
ππππππππππ
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
ππππππππππ
RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (π
±K*
```(Autar marubuta)```
SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
```(Mamie)```
*πΈπ¦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```π€π€
*'YAN UWANA INA MAI TUNATAR DAMU KAN CEWA KAR MU SIYAR DA 'YANCINMU, KAR MU ZAB'I MUGAYEN SHUWAGABANNI DA ZASUITA KASHEMU, BABA BUHARI BA MUGU BANE, BA AZZALUMI BANE, KUMA BA MACI AMANAR 'KASA BANE, MUTUM NE SHI NA KWARAI ME YA'KI DA ZALUNCI DA KUMA AZZALUMAI, DUK MU FITO 'KWANMU DA 'KWAR'KWATARMU MU SAKE ZAB'ARSHI A MATSAYIN SHUGABAN 'KASA, KAR IDONMU YA RUFE MU MANTA ABUBUWAN DA SUKA FARU A SHEKARUN BAYA LOKACIN MULKIN GOOD LUCK, YANDA AKA MAIDA RAYUKAN BAYI KAMAR KIYASHI, BABU KWANCIYAR HANKALI, YARA SUKA DAINA ZUWA MAKARANTA, DUK KARMU MANTA HAKAN, DAN HAKA ZAB'I YA RAGE GAREMU, KO MU ZAB'I SHUGABA NAGARI MU RAYU CIKIN WALWALA, KO MU ZAB'I MUGAYE KUMA B'ARAYI SUITA KASHEMU KUMA SUNA KWASHE DUKIYARMU.*
PAGE 200 to 205
Insp Yahya yai dariya sannan yace "ni ne mana kana tunanin banda lambarka ne Nura, gabad'aya ka b'oye ina ka shige ne tun bayan da kuka tashi daga garinmu?"
Nura yai dariya, sannan yace "yanzu haka ina kano mun dawo nan da zama," Insp Yahya yace "nima ai ina kano, a wace unguwa kake?"
Nan dai Insp Yahya yaiwa Nura kwatancen inda yake ba tare da wani b'ata lokaci ba ya shirya ya tafi.
Nura na isa station suka sake sabuwar gaisuwa da Insp Yahya, sannan ya kwashe duk abinda ke faruwa ya fad'a mishi.
Insp Yahya ya numfasa sannan yace "kaima kayi wauta da kai saurin amince mishi, amma ba wani abu, hukuma mu a hannunmu take, amma sedai in ka yarda duk abinda kuka samu rabawa dai-dai zamu yi, ka amince?"
Nura bai yi wata-wata ba yace ya amince, Insp yace "nuna min hoton yaron in gani, kamata yayi mu fara kamashi kafin ya tona mana asiri," Nura ya d'auko wayarshi ya fito da hoton Amir sannan ya bawa Insp ya gani.
Insp Yahya na duba hoto ya mi'ke tsaye cikin sauri tare da zaro ido yace "Amir!! wannan ai Amir ne," Nura shima ya mi'ke tsaye, sannan yace ka sanshi ne?"
Insp yace " 'kwarai nasan Amir farin sani," nan dai ya bashi labarin duk abinda ya faru a tsakaninshi da su Amir, sannan ya cigaba da cewa "kuma in dai a kanshi da matarshi kake magana to ni bama sai kun bani ko si-si ba zan tayaku, saboda na dad'e ina neman hanyar da zan tozarta rayuwar Amir fiye da tunaninka, amma yanzu abinda za'ai dole tsarin ya canza saboda Amir mugun wayau ne dashi, kawo kunnenka kaji."
Nan da nan suka gama kitsa mugun 'kullin su, sannan suka tashi suka fito daga station d'in, suka shiga motar Nura yaja suka tafi.
Shi kuwa Amir tunda ya sami labarin Nura sun ganoshi ya b'uya, amma yasan gabad'ayan shirinsa ya rushe.
Amir zaune yake kan kujera yana tunanin abinda ya kamata yayi, tabbas yasan dai-dai wannan lokacin komai zai iya faruwa da Amira, cikin sauri ya d'auki wayarshi ya kira Amira tare da shaida mata tai maza ta fito daga gidan nan yanzu zai taho da mota ya d'auketa.
Amira cikin sauri ta shiga cikin d'aki domin d'auko mayafinta ta fita ta bar gidan kamar yanda masoyinta Amir yai mata umurni akai, sedai kash tana fitowa falon ta tarar da wasu samudawan 'katti sun cika mata falo, babbansu yana kan kujera hankalinsa kwance, a yayinda sauran kuma suke tsaye suna zazzare idanu, dukkansu kamanninsu bata nuna ta mutanen arzi'ki ne, kuma gaba d'ayansu ba'ka'ke 'kirin siffarsu duk babu me kyan gani, koda yake dama wanda ya rasa imani ai kalarsa da siffarsa bazatai dai-dai da ta mumini ba.
Babban ne ya kalli Amira sannan yace "sannu Amira, ashe ma kinsan da zuwanmu har kin shirya sai tafiya kawai ko?"
Amira cikin rawar murya tace "su waye ku, kuma me kuka zo yi nan?"
Babban ba tare da ya bata amsa ba ya kalli 'kattin dake tsatstsaye yai musu alama da kai da su kamata.
Cikin sauri suka kamata d'aya daga ciki ya sab'ata a wuya tana wuntsil-wuntsil a haka suka fice da ita daga gidan, har suka shiga motoci bata daina kurma ihu ba hakan yasa ogansu ya d'aga hannunsa mai kama da guduma ya mauje ta nan ta fad'a kan kafad'ar 'katon dake kusa da ita a sume.
Bayan tafiyarsu da minti goma sai ga Amir ya 'karaso da sauri ya shiga cikin gidan ya bincika ko ina amma bai ga Amira ba, dawowa falo yayi yana dube-dube can ya hango kwalin taba kuma shi iya saninshi yasan Nura baya sha, dan yasha gwadashi akan haka amma koda wasa bai tab'a gwadawa ba, shidai barshi da tantiranci da neman mata kamar d'an akuya, ganin kwalin tabar da Amir yayi ya tabbatar mishi da cewa an rigashi zuwa an tafi da Amira.
Amir ya dafe kai yana tunani, can kuma ko me ya tuno sai ya fice daga gidan cikin sauri.
Motar shi ya fad'a ya tasheta sai gidan Dad, yana zuwa kowa na cikin gidan sai kallonsa sukeyi cike da mamaki suna yi mishi tambayoyi, sai Amir yace "yanzu ba lokacin tattauna wannan maganar bane, ina Dad yake?"
Mum tace "basu dad'e da fita ba, sirikinshi Nura yazo ya d'auke shi yace akwai meeting d'in da zasu yi yanzu da wasu ba'ki da suka zo."
Amir ya saki salati tare da dafe kai yace "ba can zasu tafi ba, Nura da mahaifinsa damfarar Dad suke son yi," nan ya kwashe komai ya fad'a mata, sannan yace "bari ma kiji, wayarsa ya d'auko ya kira lambar Dad bayan minti biyu aka d'auka, Amir yace "hello Dad kana ina ne?"
Nura ya she'ke da dariya sannan yace Dad da tsohuwar matarka suna wajenmu, duk shirinka baka isa ka wargaza namu ba Amir," ana gama fad'in haka aka kashe wayar.
Amir ya kalli Mum yace "kinji ko, to yanzu duk ku fito daga gidan nan muje gidana ku zauna kar kuma su turo ai muku wani abu," saboda sanin halin mai gidan sai suka kasa yarda da abinda Amir yace, haka yaita ro'konsu amma suka 'ki binshi.
Hakan yasa yaiwa bataliyar masu tsaronshi waya kan suzo, yai musu kwatancen unguwar, cikin 'kan'kanin lokaci kuwa suka 'karaso, ya basu umurni kan su kula da mutanen gidan nan kamar yanda zasu kula da shi, sannan ya cewa su Mum da Uncle kar suji tsoro mutanenshi ne.
Amir ya juyo ya fito daga gidan, kai tsaye wucewa mtn office yai kai tsaye domin a binciko mishi daga inda aka kira lambar.
Bayan an kira lambar sai suka sake d'auka wannan karon Insp Yahya ne ya d'aga yana fad'a mishi matarshi da sirikinshi suna sume, kuma sun riga da sun saka hannu da yatsan Dad a sumen yanzu duk abinda ya mallaka a duniya ya zama ba nashi ba, kuma yanzu zasu ba'kunci lahira, sannan ya 'karashe da fad'in " idan ka isa kazo ka taimakesu."
Cikin sauri aka gama tantance inda suke Amir ya karb'i addreshin wajen ya tafi.
Gudu kawai yake a mota yana jin tsoro kar su kashe mishi Amirar shi.
Cikin minti talatin ya 'karaso wajen kuma ya shiga ciki da gudu yana 'kwalawa su Amira kira.
Cikin wani 'katon kango ne, yana shiga can ciki yaga Amira da Dad an d'aure su, cikin sauri ya nufi inda suke, lallab'owa ta baya aka yi aka buga mishi wani abu a baya, take anan ya zube 'kasa, kuma lokaci guda suka kewaye shi, bayan sun mishi dukan tsiya sannan shima aka d'aure shi.
Dad ya kalli Baban Nura yace "yanzu duk irin yardar da nai maka amma shine ka saka min da wannan abun ko, da ikon Allah 'karshenka ba zaiyi kyau ba."
Baban Nura ya she'ke da dariya sannan yace "ai kai ka jawa kanka, ka tsani talaka, sannan kana tsoron had'a komai da talaka, ai na dad'e ina jiran zuwan wannan ranar, duk 'kulawa da 'kaunar da nake maka ba taka bace ta dukiyarka ce, amma wai kai me wayau ka katange komai to muma ga irin namu wayon nan mun nuna maka, albishir biyu yanzu zanyi maka, na farko duk wasu kadarori da suke mallakinka yanzu sun zama namu ni da d'ana hatta gidan da kake ciki mun siyar, abu na biyu kuma shine yanzu zamu 'kara muku gudu zuwa lahira domin barinku a raye zai iya zama mana barazana a cikin sabuwar rayuwar da zamu yi, kuma kaga kaima mun taimaka maka shan takaicin rayuwa cikin talauci, naso dai in barka a raye kaji irin yanda rayuwar talauci take, amma na sanka farin sani sam baka yafiya akan komai."
Insp Yahya ya kalli Baba yace "ni Baba Amir d'in can nake so ku barni in kashe shi da kaina."
Baba da Nura suka she'ke da dariya, sannan suka had'a baki wajen cewa "an baka," sannan su duka ukun harda tarin 'kattan dake cike a wajen suka sake kwashewa da dariya, wurin sai amsawa yake yi.
Baba ya baiwa Nura umurnin kashe su Amiran, sedai Amir na ganin inda Nura ya tunkara hannunsa ri'ke da bindigar Insp Yahya sai yai wani irin tashi yana a d'auren yaje da gudu ya bangaji Nura suka fad'i 'kasa a tare.
Kiciniyar 'kwace bindigar Amir yakeyi daga hannun Nura cikin ikon Allah ya samu d'aurin hannunshi ya kwance ya 'kwace bindigar sannan ya kwance su Amira da Dad yana cikin kwancesu Insp Yahya ya ciro bindigar jami'in dake kusa dashi ya saita Amir da ita tare da harbin Amir d'in a hannu, Amir yai wani irin razanannen 'kara, tare da dafe wajen ya kalli su Dad yace su gudu zai biyosu daga baya, Amira taja ta tsaya tana ri'ke da hannunshi mai ciwon tana kuka tana fad'in "taya zan tafi in barka a irin wannan halin, ni ba inda zanje ko mutuwar ne ma gwara a kashemu tare," Amir ya dafata, sannan yace "ki kwantar da hankalinki Amira Insha Allah rabuwarmu ba yanzu ba, zan dawo gareki nai miki al'kawari."
Cikin sauri kuwa Dad ya jata da gudu suka fice daga wurin nace ashe Dad ansan darajar rai hahaha,π a yayin da su Nura sukace a kamosu, duk wanda ya taho da niyyar fita daga wajen zuwa kamosu Amira sai Amir ya barshi kwance, haka akai ta d'auki ba dad'i.
Sai da ya kashe rabinsu duk yabi ya gaji li'kis, sannan Allah ya basu sa'a a kanshi suka far mishi, saida suka tabbatar da baya numfashi sannan suka fice sukai tafiyarsu suka barshi a nan wajen.
Tunkarar gidan Dad suka yi, a haukarsu wai shine su bisu har gida su kashe su, sedai daga nesa suka hango security's ta ko'ina, hakan ya tabbatar musu da cewa in suka 'karasa lallai za'a kamasu, ba shiri suka juya.
Amira ce ta kalli mahaifinta sannan tace "gaskiya Dad be kamata ba ace Amir ya shiga irin wannan halin ta dalilinmu kuma mu taho mu 'kyale shi, ya kamata mu kai mishi taimako koda da jami'an tsaro ne su taimaka mishi."
Uncle yace "gaskiyarki Amira, bawan Allahn nan ya jefa rayuwarshi cikin had'ari domin kawai ya bamu kulawa da kariya ta ko'ina, be kamata mu 'kyaleshi a haka ba, ya kamata mu sanar da 'yan sanda."
Dad ya kasa magana saboda tsabar firgici da mamaki dake tare dashi har yanzu, ishara kawai yai musu da hannu akan Uncle d'in shi da Amira suje.
Cikin sauri kuwa Amira da Uncle suka shiga mota suka fice harda wasu daga cikin securityn cikin gidan.
Muje zuwa
*π
±K CE*
ππππππππππ
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
ππππππππππ
RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (π
±K*
```(Autar marubuta)```
SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
```(Mamie)```
*πΈπ¦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```π€π€
*INA 'KARA TUNATAR DA MU CEWA BABU FA WANDA ALLAH ZAI HALITTA YACE BAZAI FUSKANCI JARABAWAR UBANGIJI BA, KARMU MANTA ALLAH MUKA RO'KA DA YA ZAB'AR MANA SHUGABA NA GARI A WANCAN SHEKARUN, SAI ALLAH YA ZAB'A MANA BABA BUHARI, TO KO DA ALLAH YA BAMU SHI A TUNANINMU ALLAH BA ZAI JARABCEMU BA TA WANI B'ANGAREN? WALLAHI ALLAH KO DA TSAYAR DA BAMA BAMAI KAD'AI DA BABA BUHARI YAI 'KO'KARIN YI KAD'AI MUKA TUNA YA ISA MU GODEWA ALLAH KUMA MUSAN CEWA LALLAI BA ZALUNCI NE YA KAWO BABA BUHARI CIKIN RAYUWARMU BA, KARMU MANTA KAFIN BUHARI YACI ZAB'E A BAYA A LOKACIN DA GOODLUCK KE MULKARMU BABA BUHARI YASHA ZUBAR DA HAWAYENSA YASHA YIN KUKA KAN HALIN DA 'YAN 'KASA KE CIKI, KAFIN YACI MA KENAN DA YACI KUMA BURINSHI YAGA MUN SAMU CIGABA A RAYUWARMU, KAR MU ZAMA BUTULU A RAYUWA ANATA MAGANAR ABINCI YAI TSADA BAFA RASAWA MUKAI GABA D'AYA BA, KUMA KOWANE TSANANI YANADA IYAKA NA D'AN LOKACI NE KUMA SAI ANSHA WUYA AKE SHAN DAD'I, INACE A BAYA MULKIN GOOD LUCK GA KUD'IN AKWAI GA ABINCIN AMMA BAYA CIYUWA, NA CEFANE MA BASA SAMUWA SABODA FARGABAR KA FITA WAJEN NEMA A HARBEKA KO ASA BOM YA TAYAR DAKAI, KARMU MANTA CEWA ANSHA SAKA BOM A MASALLATAI MUSAN CEWA TABBAS IN MUNA CIGABA DA BARI SHUGABANNI AZZALUMAI NA MULKARMU TO ZA'A WAYI GARI BABU RABINMU SUN KASHE, MUYI TUNANI SOSAI WALLAHI KAR MU BARI 'YAN CANJI NA WANI LOKACI DA ZASU 'KARE SU BARMU DA SHAN WAHALAR SHEKARU SU RUD'EMU, MUYI TUNANI DUK MAI SHIRYA GASKIYA BAZAI BAKA CIN HANCI DAN KA ZABESHI BA, HALIN MUTUM JARINSA HALIN MUTUM KE BAYYANAR DA CANCANTARSA WAJEN JAMA'A, NIDAI NACE INSHA ALLAH 4+4 SAI MAI GASKIYA.*
PAGE 205 to 210
Kai tsaye su Amira wucewa can wajen da abun ya faru sukayi, saboda Uncle yace ba sai sun kira jami'an tsaro ba tunda suna tare da security sun wadatar, kuma jami'an tsaron ma da akwai mugaye da munafukai a ciki wad'anda zasu iya tseguntawa Insp Yahya in sukaji bai mutu ba suzo su 'karasashi, da wannan shawarar ta Uncle sukai amfani sukayi watsi da maganar neman 'yan sanda, cikin 'kan'kanin lokaci Allah ya kaisu wajen, basu tarar da kowa ba a wajen sai Amir yashe a wajen kwance cikin jini, babu b'ata lokaci suka d'aukeshi suka yi asibitin da ake duba iyalen Dad da shi.
Suna zuwa babu wani b'ata lokaci aka shiga dashi emergency cikin sauri saboda ganin harda harbi.
Sai da aka kammala mishi komai aka kuma tabbatar musu da yana raye kuma insha Allah nan da wasu lokuta zai farfad'o sannan hankalinsu