SO MAHADIN RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVELS PDF BY BILKISU Z YAU.txt

Author :  Bilkisu Z Ya'u Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   2 / 31

3K to 6K   out of 90.7K words

da su Amir ya zauna, ya d'ora da fad'in _"al'amuran so suna da wuya, rabuwar sa kuwa mutuwa a tare._"



Gaba d'aya duk sun raba mata hankali ta kasa tantance wanda yake da mallakin kalmomin, ta rasa ina dukkansu suka sami wad'annan kalaman suka ji shi, dan tasan cikin abokanta na skul d'in Sadeeq ne a tare da su lokacin da take fad'a, sai Sani, sauran kuma k'awayenta ne mata, babu Abdul da Amir, ta juya zata fita kenan ganin bata da amsar tambayoyin da take wa zuciyarta, tana kallon allon ajin taga an rubuta kalaman da suke ta maimaitawa, sai a lokacin ta gano wato duk a nan suka gani kenan suke maimaitawa, to waye ya rubuta?











Muje zuwa







*πŸ…±K CEπŸ˜˜πŸ’‹*
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜






RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (πŸ…±K)*
```(Autar marubuta)```






SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
_(Mamie)_






*πŸ‡ΈπŸ‡¦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```{Gidan zaman lafiya da amana insha Allah}```






_*FAUZIYYA AMMANI* zama tare da ke alkhairi ne, kuma babbar nasara ce, samun k'awa kuma 'yar uwa ta gari irinki abun alfahari ne, ina rok'on Allah dare da rana Allah ya faranta miki, ina sonki, iya wuya kuma ana tareπŸ˜πŸ˜˜πŸ’‹._






_*TAWAN* ina rok'on mahaliccinmu Allah ya yaye miki dukkan damuwarki, ya bayyanar da farin ciki da walwala a gareki, ya k'ara miki lafiya mai d'orewa._






_dan girman Allah muna cigiyar *BAHAGON TUNANI* daga farko zuwa inda aka tsaya,πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ˜­πŸ˜­πŸ˜­πŸ˜­πŸ˜­ duk wanda yake da shi ya hana ni *wuta bal bal*😑😏_






PAGE 10 to 15






Yau ta kama Asabar ba makaranta, Amira ce kwance kan k'ayataccen gadonta tana karatu domin gaskiya yarinyar akwai k'ok'ari, sam bata wasa da karatun ta.



k'arar message ne ya shigo cikin wayarta, ta d'auki wayar tare da dubawa, rubutu taga an yi kamar haka.


_Dan Allah Amira ki bud'e zuciyarki ki sakani a ciki, ki tausayawa rayuwata._


Tana gama karantawa tayi k'ok'arin bin lambar da aka turo sak'on da ita, amma tana kira akace a kashe take.



Tunani ta shiga yi wai wanene wannan yake turo mata irin wad'annan sak'onnin, amma koma wanene zan ganoshi kwanan nan da yardar Allah, ta d'auki littafinta ta ci gaba da karatunta.



Washe gari Lahadi kenan Amira ce ita da Sadeeq suke ta faman tsere, a filin wasanni da motsa jiki na makarantar, a yayin da Amir ke zaune kan kujera yana kallon su.



Sun dad'e suna zuba uban tsere da Sadeeq da Amira, Amira sai wuce Sadeeq take yi tana jin dad'i a ranta, can kamar ance ta d'aga kai ta hango Amir zaune babu wanda yake kallo sai ita, idonshi yana kanta ko k'yaftawa baya yi.



Kallon Sadeeq Amira tayi tace tana zuwa bari ta kira Amir ayi wasan tare dashi.




Tana k'arasowa ta rik'e k'ugu sannan tace " aboki ya akayi ne, taso muje mu yi wasan tare," Amir yai murmushi sannan yace " a'a kuje kuyi wasanku, bana sha'awar yin komai yau," Amira ta kalle shi sannan tace " na rantse da Allah sai ka yi, ta kama hanunshi tana ja, tashi yayi ya bita, suna tafe tana mita tana fad'in " in zaka sani ka sani tunda Allah ya had'amu kwanakin baya a hanya ka zama abokina, kuma duk wanda ke tare da Amira baya zaman zuru kamar wani marayan da ya rasa kowa, koda yaushe kana zaune ba um ba um-um, ba abinda ka iya sai kallo, a wajen kallo ne kafi auki in ka fara kallona sai kace zaka cinye ni, tun kallonka na tsorata ni har ya fara bani haushi, haba kallo sai kace bak'auye," shi dai ba abinda yace mata banda binta a baya da yake tana rik'e da hannun nashi, kuma bai fasa kallonta ba, in ya kalleta sai ya kalli hannun shi da ta rik'e, juyowa tayi tana kallon shi nan take suka had'a ido tace " ahaf aikin kenan juyowa d'ari ni kake kallo ba canji, to ko maye ne kai sai dai kayi ka gama ka k'yaleni wallahi, dan nama na yafi k'arfinka," ta k'arashe maganar tare da murgud'a mishi baki, Amir yai murmushi, shi har ga Allah tsiwar Amira burgeshi take.



A haka tana mitar ta shi kuma yana dariya tare da cigaba da kallon nata har suka k'araso tsakiyar filin, hakanan dole Amir ya zage suka yi wasan tare su uku, se dai wannan karon da yake babu abun a ranshi ko kuwa kallon Amira ne ya shagaltar da shi oho Amira taita cinye su dukkansu, gwara ma Sadeeq ya ci d'aya, shi kuwa Amir ko d'ayan ma be samu ba.



Amira ce ta samu waje ta zauna tace " gaskiya na gaji tunda dai na ci ku har sau biyar kuma ba wanda yai nasara a kaina to Allah amfana wasa ya tashi hakanan."



Suma zama suka yi kusa da ita suna yi mata dariya, Amir yana gefen damanta, a yayin da Sadeeq shi kuma ke gefen hagunta.



Ruwa me sanyi suka sha, sannan Amira ta had'a komatsanta tace musu zata tafi gida, tai sallama da su ta juya, har ta fara tafiya Sadeeq ya kira sunanta.




Amira ta tsaya cak tare da juyowa, Sadeeq yace " gobe in kin shigo makaranta akwai maganar da nake so mu yi da ke, maganar ta shafemu ni da ke, kuma ta shafi zuciyata," Amira tai shiru tana tunani kodai Sadeeq ne ke turo mata sak'onnin nan, nan da nan zuciyarta ta kwab'eta kai gaskiya ba shi bane, wata zuciyar kuma tace to ki bari mana ki jira kiji me zaice miki goben mana sai ki tabbatar da abinda kike zargi hakanne ko akasin haka, a fili kuwa Amira tace " to me zai hana muyi maganar yanzu?" Sadeeq yace " a'a ki dai bari sai goben in Allah ya kaimu," Amira tace to shikenan Allah ya kaimu," ta juya ta kama hanyar gida, su kuma Sadeeq da Amir da yake Sadeeq da Sani a hostel suke na makarantar, shi kuma Amir ba a hostel yake ba zuwa yake yi ya koma, nan dai suka yi sallama suma kowa ya kama gabanshi.




Bayan Amira ta koma gida tayi wanka tai Alwala tai sallah, sannan ta kwanta bacci, gaf da la'asar ta tashi, tana tashi ta sake shek'a wanka sannan ta canza kaya ta yi sallar asri, (la'asar) bayan ta idar ta zauna kenan ta d'auko wayarta zata kira Dad d'inta da Mum sai ta ji sallama a k'ofar d'akinta.




Amsawa tayi, tare da bada izinin shigowa, wani yaro ne ya shigo hannun shi d'auke da farar takarda.



Mik'a mata wannan wasik'ar ya yi, sannan yace " wani mutumi ne ya bani yace in kawo miki, " Amira ta karb'a sannan tace " yanzu ina mutumin yake?" yaro yace " ya tafi, cewa ma ya yi kar na shigo sai ya sha kwanar layin, sannan sai in shigo in kawo miki," Amira tace " kasan mutumin?" yaro yace a'a banma tab'a ganinshi ba sai yau," Amira tace " shikenan jeka nagode."



Yaron na fita Amira ta bud'e takardar nan ta fara karantawa.



_Amincin Allah ya cigaba da tabbata ga kyakkyawar sarauniyar zuciyata, idan ba zaki damu ba zan so na kasance farin cikin ki a rayuwa, ina sonki so na hak'ik'a, so na gaskiya, so na har abada, zuciyata ta yarda dake, da soyayyarki nake alfahari, kuma a ko'ina nai miki alk'awari idan har kina tare da ni ba zaki tab'a zubar da hawaye ba, soyayyarki itace abun yi cikin dare har zuwa safiya, ke kad'ai ce fatana, tunanina, mafarkina, da walwalata, wallahi ina matuk'ar sonki, idan kika gujeni bazan iya aikata komai ba, ki tausayawa rayuwata ki amince da ni da soyayyata, ina jiran amsarki idan kin rubuta amsar ki ajiye a wajen zamanki cikin aji zan zo in d'auka, kuma ina ganin amsarki zan bayyana gareki, na barki lafiya._



Bayan ta gama karantawa taja doguwar ajiyar zuciya, sannan a fili tace " koma wanene koda ace na ganka ka yimin ina sonka, idan ka shigo hannuna wahalar da zan baka zaka sha mamakinta, Allah ya kaimu goben.



Washe gari da wuri Amira tai shiri ta fita makaranta saboda zumud'in abu biyu, yau ta k'udurta a ranta sai ta gano wanene wannan yake turo mata sak'onni, sai kuma son jin maganar da Sadeeq yace zasu yi da ita.



Tsayawa ta yi ganin cincirindon d'alibai da malamai har da police cikin harabar makarantar tasu, nan da nan gabanta ya fara fad'uwa tana tunanin menene ya faru a makarantar su haka da sassafen nan, hango abokanta su Suhaima da Abdul ne yasa ta tunkari wajen su da sauri, ta yi tambayar duniyar nan su fad'a mata abinda ke faruwa amma abin mamaki sai kuka suke yi, kuma kamar ma ganinta shi ya k'ara sa su yin kukan.



Nan hankalinta ya k'ara tashi, barin wajen su tayi tunda sun k'i yi mata magana, abinda yafi d'aure mata kai shine duk wanda ta tare ta tambayeshi abinda yake faruwa sai su kasa bata amsa se ma kuka ko hawaye da suke k'ara zubarwa, hakan yasa ta tunkari wajen da mutanen suka taru, ta kutsa cikin su har ta samu ta shigo gaba, se dai abinda idanunta suka gani ya yi matuk'ar razanar da ita.







Muje zuwa







*πŸ…±K CEπŸ˜˜πŸ’‹*
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜






RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (πŸ…±K)*
```(Autar marubuta)```






SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
_(Mamie)_






*πŸ‡ΈπŸ‡¦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```{Gidan zaman lafiya da amana insha Allah}```






PAGE 15 to 20






Gawar Sadeeq ne a wajen babu alamar rai a tare da shi.



Zaro idanu ta yi tare da kiran sunan shi cikin wata irin razananniyar k'ara, k'arasawa tai kusa da shi, ta tsugunna sannan ta saki wani irin kuka tare da jijjigashi tana fad'in " Sadeeq bana son irin wannan wasan, dan Allah ka tashi," ganin ko motsi baya yi yasa ta tashi ta fita daga wajen duk kallo kuma sai ya koma wajenta suna tayata kokawa rashin da tayi, domin kowa yasan irin muguwar shak'uwar dake tsakanin su da Sadeeq d'in.



Amira ta doshi wajen su Abdul da gudu, tana k'arasawa ta kalli Sani tace " Sani dan Allah fad'amin a mafarki nake ganin komai ko, ai ba gaskiya bane ko?" Sani yai shiru tare da duk'ar da kai yana cigaba da kuka.



Matsawa tai kusa da Abdul ta kalle shi cikin kuka tare da nuna inda gawar take tace " jiya fa muna tare dashi, mun dad'e tare muna wasan gudu yau kuma ace ya mutu," Preety ce tazo ta rik'eta tare da fad'in Amira dan Allah kiyi shiru kar kije kiy sab'o," Amira ta juyo da kallonta gun Preety tace " yace yau zai fad'a min wata magana shine zai mutu kafin ya fad'a min ko," k'arasawa tai wajen Suhaima wadda babu abinda take yi sai kuka kamar ranta zai fita, saboda itama taji mutuwar Sadeeq domin ta dad'e tana k'aunarshi.



Amira ta kalli Suhaima tace " kema kin yarda ya mutu kenan ko, ni wallahi ban yarda ba wasa yake mana kuma zai tashi bari kiga, tashi ta yi ta nufi kan gawar tana jijjiga shi tana fad'in Sadeeq dan Allah ka tashi, kar kai min haka duk duniya banda amini sama da kai ka tashi ta kwanta a jikinshi tare da cigaba da kuka.



Amir wanda shigowar shi kenan cikin makarantar ake fad'a mishi abinda ke faruwa, k'arasawa yai inda gawar take jikin shi a sanyaye ya dafata, d'agowa ta yi, tana ganin Amir ne sai ta mik'e ta fad'a jikinshi tare da cigaba da kuka me ban tausayi, shima hawaye kawai yake ta faman zubarwa, k'ok'arin janta yake su bar cikin taron jama'an ya samu ya maidata gida, se dai luuuuu tayi zata zame daga jikin shi tai k'asa.



Da sauri ya tare ta, sannan aka samo ruwa tana kan jikin shi aka yarfa mata, cikin ikon Allah kuwa ta farfad'o da sunan Sadeeq a bakinta, kuka take yi musu tana fad'in a kaita wajen Sadeeq.



Abdul ne ya kalli Amir yace "gaskiya ya kamata ka kaita gida Amir," 'yan sanda da malaman makarantar ma abinda suka ce kenan a kaita gida.



Hakan kuwa aka yi, ya d'auketa ya saka ta cikin motar ta da tazo da ita suka tafi.



Iyayen Sadeeq ne suka k'araso cike da rud'u, firgici, da tashin hankali, sunyi kuka kamar me, amma ya zasu yi Allah ya basu shi kuma ya karb'i abinsa.



Bayan 'yan sanda sun gama binciken su da suke yi shima likita ya gama aune aunen sa, sannan babban jami'in 'yan sandan ya bawa iyayen Sadeeq umurni kan su tafi da shi ai mishi sallah, kuma insha Allah zasu ji sakamakon bincike akan gawar da suka yi, sannan dole a cikin d'aliban makarantar nan suma akwai yiwuwar a tattauna da su.



Iyayen Sadeeq suka ce ba inda zasu matsa daga nan sai an fad'a musu abinda yai silar mutuwar d'an su.



Babban jami'in nan ya kalle su yace " alamu sun nuna kashe shi aka yi, saboda wuk'a aka caka mishi, kuma d'akin a hargitse, hakan na nuna ya yi k'ok'arin ceton ranshi kafin a far mishi, amma muna dai kan bincike tukun har sai mun gano gaskiya."



Amira kuwa bayan har suka k'araso gida kuka take yi, Amir ya kalleta sannan yace " Amira dukkan mai rai fa mamaci ne, kuma a koda yaushe idan tazo baka isa ka k'ara koda sakwanni ba a duniya, ki sa wa ranki hak'uri, tabbas Amira kinyi rashin babban amini, hakan yasa muma abokan ki muke tayaki kuka saboda tausayinki, da kuma shak'uwar da mu kanmu muka yi da shi, kiyi hak'uri a yanzu yafi buk'atar addu'arki fiye da komai a duniya."



Bata ce mishi komai ba amma ta rage kukan da take ta faman yi, kwantar da ita ya yi, sannan ya tashi ya shiga shiga toilet ya had'a mata ruwan zafi ya kaita sannan ya fito ya jawo toilet d'in, kicin ya shiga kafin ta fito ya had'a mata tea me kauri sannan ya soya mata dankalin turawa, ya fito hannun shi rik'e da k'aton faranti ya d'ora plet d'in dankalin da kuma tea d'in da ya had'a mata, koda ya fito har ta shirya ta koma ta kwanta amma har yanzu hawaye bai tsaya da kwararowa ba a fuskarta.



Bayan ya ajiye kayan yace ta taso ta karya yasan yanda aka wayi garin yau na firgicin rashin da aka yi ba lallai bane ta tsaya karyawa.



Girgiza mishi kai tayi alamun ba zata ci ba.



Amir yace " dan girman Allah ki tashi ki karya," bata son yin musu in tana cikin tashin hankali irin wannan, hakan yasa ta tashi ta d'an ci ta sha tea d'in sannan ta koma ta kwanta.



Bayan wasu lokuta zazzab'i ya rufeta ta fara rawar sanyi, nan da nan jikinta ya gashe da zafi, hankalin Amir ya tashi ya rasa ya zai yi.


Hakanan ya sake d'aukarta suka yi Asibiti aka basu gado ganin yanda jikin nata yake a rikice har takai ga tana suma.



Bayan kwana d'aya washe garin ranar kenan b'angaren makaranta mamaci dai an birneshi, se dai fatan Allah yai mishi rahma, amma kowa ka gani cikin makarantar baya tare da farin ciki, duk mutuwar Sadeeq ta tab'a su, saboda mutum ne shi mai faran-faran da jama'a shiyasa suke kukan rashinsa.



An so bada hutun makarantar 'yan sanda suka ce kar a bayar suna so su gano wanda ya aikata wannan laifin, hakan ne yasa aka ci gaba da zuwa.



Su Abdul ne da su sani dukkanin abokan Amira dai suna harabar makarantar zaune suna jajantawa juna, suna cikin tattaunawa a kan idan an tashi zasu lek'a Amira su ga ya take daga nan su k'ara bata baki, kawai sai suka ji sallama a kansu, suna d'agowa suka ga 'yan sanda.



Babban nasu yace " waye Abdul a cikin ku?" Abdul yace " ni ne yallab'ai Allah yasa dai lafiya?"



'Dan sandan nan yace " munzo ne mu tafi da kai caji office domin yi maka wasu tambayoyi, sannan kuma ya nuna sauran yace duk zamu gayyace ku d'aya bayan d'aya domin jin bayanai daga bakunan ku," haka suna ji suna gani 'yan sandan nan suka tasa k'eyar Abdul suka tafi dashi caji office.






Muje zuwa






*πŸ…±K CEπŸ˜˜πŸ’‹*
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜






RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (πŸ…±K)*
```(Autar marubuta)```






SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
_(Mamie)_






*πŸ‡ΈπŸ‡¦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```{Gidan zaman lafiya da amana insha Allah}```




WOHOHO HABIBTY
πŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ
*Zo mu zauna dake masoyiya na amince dake har zuciya, tunda kin mini so da gaskiya, zana kula dake zinariyaπŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹*
_*Ya ilahi HABIBTY NAH QUEEN RUQEEY, yasin har na gama typing zan turo naga gagarumin yabo had'e da kirarin da kika rangad'amin a page d'inki na yau cikin littafin sharrin ashqeey, hak'ik'a so baya tab'a tsufa, nagode nagode nagode Allah ya k'ara mana aminci da k'aunar juna, yanda kike farantamin kema Allah ya dauwamar da ruhinki cikin farin ciki har k'arshen rayuwa, daga k'arshe nake cewa ki rik'e karki manta har abada πŸ…±K tana yinkiπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹*_









2 / 31