SO MAHADIN RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVELS PDF BY BILKISU Z YAU.txt

Author :  Bilkisu Z Ya'u Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   16 / 31

45K to 48K   out of 90.7K words

๏ผˆMamien๏ผ‰






*๐Ÿ‡ธ๐Ÿ‡ฆZAMAN AMANA WRITER'S*
๏ผˆGidan zaman lafiya da amana in sha Allah๏ผ‰๐Ÿคœ๐Ÿค›






*MAMAN LABYB ๏ผˆMAMIE๏ผ‰da AUNTY LIPSON (Maman Saleem) ina ro'kon Allah mahaliccina ya d'orar da lafiyarsa gareku๐Ÿ‘๐Ÿ˜ฉ*








PAGE 115 to 120






Washe gari Amir da Amira ne zaune gaban su Umma, Amir har ya bud'e baki zai fara magana Amira tai karaf ta fara magana da fad'in "Baba, Umma, iyayena auren dole suke so su yi min ni kuma bana so, saboda yaron da zasu had'amu beda tarbiyya su kuma basa son talaka wannan dalilin yasa suka tsani had'a aurena da Amir," tana kaiwa nan a zancenta sai ta fashe da kuka, d'akin yai tsit banda sautin kukan Amira dake tashi, can sai Amir ya d'ago kai ya kalli Baba yace "Baba dan Allah ka d'aura mana aure dan girman Allah, shima ya fashe da kuka yana ci gaba da yiwa Baba magiya, daga Baba har Umma shiru suka yi, a yayin da tausayin yaran ya gama lullub'esu, kuma tabbas yanda suka sha'kun nan in akace za'a raba su to zasu cutu, dukkanin su sun yi Allah wadai da wannan muguwar d'abi'a ta iyayen Amira kan dole sai sun aurar da ita ga mai kud'i sai kace talaka shi ba Allah ne ya yishi ba, duk wannan tunanin Umma da Baba cikin zuciyarsu suke yinsa.



Baba ya kalle su har yanzu kukan suke ta yi, sai yace "ya isa kukan, bayan sun yi shiru ya cigaba da fad'in kuje cikin d'akin ku ku shirya kafin nan zamu yi shawara da Mamanku, kuma a yanda kuka bamu labari kunce sun biyoku har cikin rugar nan, to tabbas nasan zasu sake dawowa, saboda haka kuje kuyi shiri in mun gama shawara da Ummanku to ko za'a d'aura muku auren ba a nan ba zan tura ku wani 'kauye nan wanda ke ma'kwabtaka da namu wajen yayana sai a d'aura muku auren a can in yaso ma sai ku zauna a can d'in kawai."



Cikin sauri kuma cike da farin ciki suka tashi suka shiga cikin d'aki, can bada dad'ewa ba sai ga Baba yai sallama tare da le'kowa yace su fito su tafi, har sun bar wayar su Baba yace su d'auka in yaso sai su canza sim su karya wancan, Baba da kanshi yai musu jagora suka yi sallama da Umma suka fice daga gidan suka d'auki 'kauyen gidan d'ango, daga 'kauyen damari zuwa 'kauyen gidan d'ango da tazara sosai shiyasa suka jima suna tafe kafin su iso cikin 'kauyen.



Bayan sun 'karasa gidan suka gaggaisa aka kawo musu fura da nono da ruwa mai sanyi suka sha, bayan sun gama Baba ya kora wa yayansa bayanin duk abinda ke faruwa da kuma dalilin zuwan su a yanzu da ro'kon yayan nasa alfarma kan su zauna a 'kauyen har sai Allah ya kawo dai-daituwar komai.



Yayan Baba wanda yaransa ke kiransa da Baffa yace "ba wani abu Allah ya shige mana gaba, yanzu abinda za'ai shine malam Amir in har kana da kud'i a jikinka ka kawo a d'aura yanzu, bari nasa a kira ma'kwabta da 'yan uwa da abokan arzi'ki, Baffa yasa aka kira su wad'anda suke nan nan da nan suka had'u, Baba ya ciro dubu biyar yace "ga sadakin Amir kuma ni ne waliyyinsa," Baffa yace "masha Allah nine waliyyin Amira," wani liman dake unguwar yace " to Alhamdulillah, nan fa babu b'ata lokaci aka gabatar da dukkanin abubuwan da suka kamata, aka d'aura aure sannan aka yi addu'a tare da yi masu fatan zaman lafiya kowa ya watse.



'Daki guda aka samar musu a cikin gidan Baffa, sai da aka gama komai sannan Baba yai sallama dasu su Amir suka rakoshi hanya cike da farin cikin kasancewarsu ma'aurata.



Suna tafe Baba yana k'ara yi musu nasihar zaman lafiya a zamantakewar aurensu, sun d'an fara yin nisa da unguwar Baba ya tsaya yace "to rakiyar taku ta isheni daga nan, ku koma nagode Allah muku albarka."



Amir ya bud'e baki kenan zai yi magana sai ga motoci sun zagayesu ta ko'ina kuma motocin na tsayawa suka shiga fitowa d'aya bayan d'aya, su Insp Yahya ne sojoji da 'yan sanda gaba d'aya suka zagaye su Amira suka saka su a tsakiya, can kuma sai ga Umma matar Baba itama an fito harda ita a cikin motar, Baba ya kalleta yace " meyasa zaki nuna inda bayin Allahn nan suke, yanzu abinda kikai kin kyauta kenan๏ผŸ"



Insp Yahya yai tattaki ya 'karasa har kusa da Baba sannan yace "Baba hala baka san abinda wad'annan suka aikata ba shiyasa kake b'oye masu laifi a gidanka ko, to bari kaji kisa Amir yayi ya kuma sace 'yar shugaban 'kasa ya gudu da ita, idan har da baka san laifin da ya aikata ba to yanzu ka sani, muddin ka 'kara b'oye shi ko kasa aka b'oyeshi to kuma sai mun hukunta ku."



Insp Yahya ya sake yin tattaki ya 'karasa har gaban Amir, sun dad'e suna yiwa juna kallon kallo sannan Insp yai murmushi yace " Amir karka manta da sunana Insp Yahya kafi 'karfin mugu, babu inda zaka shiga ka guje mini in dai kana cikin Nigeria ne, dan haka ku kama shi muje."



Amir ya kalli Amira wadda itama shi take kallo suka yiwa juna murmushi, sannan ya maida kallon shi ga su Baba yace "Baba, Umma, wallahi bazamu tab'a mantawa daku ba har abada, saboda kun d'aukemu tamkar yaran da kuka haifa," Amira tai karaf tace "kuma kuka yi mana abinda iyayenmu da 'yan uwa suka kasa yi mana, wallahi har mu mutu ba zamu daina 'kaunarku ba da kallonku a matsayin iyaye wad'anda suka haife mu, idan mun yi muku laifi a zaman mu daku ku yafe mana, in Allah ya yi da sauran ranmu zamu dawo gareku, in kuma an kashemu to ku tuna damu cikin addu'armu."



Insp Yahya ya kalli Amira yace " wai ke Amira meyasa kike son sa kanki cikin laifin da babu ke a cikinsa ne๏ผŸ"



Amira ta balla mishi harara sannan tace " ina ciki nice babbar me ruwa da tsaki ma kuwa tunda kuke bibiyar burin raina Amir d'ina da mugun sharrin ku, kuma a kanku zai 'kare," ta 'karashe maganar tare da murgud'a mishi baki.



Insp ya kalli bataliyar jami'an nan yace a saka su a mota, kamar jira suke suka nufi su Amir, sai da suka je daf da su Amira ta daka musu tsawa tare da d'aga hannu tana fad'in "ku dakata ba sai kun kama mu ba, zamu shiga da kanmu ku kaimu duk inda zaku kaimu, ni dai nasan duk hukuncin ku baku iya canza 'kaddarar ubangiji, ta kalli Amir sukaiwa juna murmushi a karo na biyu suna ri'ke da hannun juna, sannan ta cigaba da fad'in " Amir d'ina tunda Allah ya cika mana burin mu na zama ma'aurata to mu bisu su dafa mu a babbar tukunya in zasu iya, muje koh๏ผŸ" Amir yai murmushi sannan yace "eh mana me muke jira."



Har suka shiga mota Insp Yahya na tsaye yana kallon ikon Allah yanda gaba d'ayansu suka nuna rashin tsoro ko damuwa a tattare dasu, ga kuma wata magana da yaji wai sun zama ma'aurata.



Aikuwa Allah Allah yake su isa station ya sanar da Dad, saboda gun sauri ya manta da wayarsa a office jin an gano inda su Amiran suka gudu.



Suna cikin tafiya tayar motar su tai faci, sai aka faka ana tsayawa Amir ya fara 'ko'karin guduwa shi da Amira, Amir ya bubbuge wad'anda ke kusa da su, ya ja Amira suka runtuma a guje, sun fara gudu kenan sai Insp Yahya ya saita Amir da bindiga ya harbeshi a gefen ciki ta baya, nan Amir ya saki wani irin 'kara Amira ta juyo itama sannan ta ankara da harbin da aka yi mishi, hakan yasa dole Amir ya zube a nan, nan da nan 'yan sanda suka kewaye su, aka maida su cikin mota aka nufi asibiti, cikin emergency aka nufa dashi cikin Saudi, kuma duk abin su Amira sai da ta shiga, aka cire mishi riga domin suga sun yi 'ko'kari sun cire mishi bullet d'in, ana cire rigar sunan Amira ya fito rad'o-rad'o a 'kirjin shi, kuma daga gani tsaga jikinshi aka yi aka rubuta a fatar jikin nashi irin wanda ba zai tab'a gogewa ba ko ya b'ace har abada.



Amira na ganin sunanta a 'kirjin Amir taji 'kaunarsa ta dawo mata sabuwa tare da jin matsanancin tausayin shi, tabbas tayi imani cewa ba zata tab'a samun masoyi kamar Amir ba.



Bayan kwana biyu Amir ya warke sarai aka sallame su, kai tsaye station aka wuce dasu.



Ko da isar su suka tarar da mahaifin Amira ya zo, cikin 'karaji da fusata Dad yace "ku saka shi cikin cell, ita kuma Amira ku kai min ita mota, sannan ku gaggauta had'a duk wasu bayanai da hujjoji ku tura shi kotu tunda kun kasa tsareshi har ku tuhume shi sosai ya amsa laifin sa, ku tabbatar kun mik'a shi kotu."



Amira jin ance za'a tafi da ita yasa hankalinta yai mugun tashi, tunanin mafita ta fara yi cikin ranta, can sai ta hango bindigar Insp Yahya a kan tebur tai wuf ta d'auka hakan ya yi dai-dai da jefa Amir cikin cell da aka yi, aka rufo wajen.



Cikin sauri Amira ta nuna d'an sandan dake k'ok'arin rufe 'kofar da bindiga, sannan ta umurceshi da ya bud'e 'kofar, cikin sauri ya bud'e ta shige ciki itama sannan ta sake nuna shi da bindiga sannan tace " rufe mu," aka rufe su ita da Amir a ciki sannan ta kalli mahaifinta wanda shima ita yake kallo yana mamakinta tace "Dad zuwa yanzu yaci ace kun ha'kura, a yanzu Amir mijina ne domin an d'aura mana aure ni da shi, muddin za'a cigaba da tsareshi to wallahi se dai a tsare mu dukkan mu ni da shi, Dad babu shaidar da zata nuna Amir shi yai kisan, kuma in dai za'a cigaba da tsareshi da tuhuma to tabbas zan cigaba da bashi kariya ta hanyar maida laifin kaina."




Amira cikin kuka ta cigaba da cewa " Dad wallahi in na rasa Amir nima zaka rasani, ka yi ha'kuri ka barmu mu tafi."



Amir shima cikin kuka ya kalli Dad d'in yace " dan Allah Dad ka tausaya wa rayuwata, wallahi zan iya rabuwa da komai in ha'kura amma banda Amira saboda itace *MAHA'DIN RAYUWATA* dan Allah Dad," Dad be ce komai ba ya juya zai tafi, sai da ya kai bakin k'ofar fita sannan yai magana ba tare da ya juyo ba, yace" tunda kin zab'i zama dashi a kanmu zan d'auki matakin k'arshe, kai kuma Insp ka aiwatar da abinda nace maka," yana kai nan a zancen shi ya fice yai tafiyarsa.









Muje zuwa







*๐Ÿ…ฑK CE๐Ÿ˜˜๐Ÿ’‹*
๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜









RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (๐Ÿ…ฑK)*
```(Autar marubuta)```





SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
```(Mamie Nah)```





*๐Ÿ‡ธ๐Ÿ‡ฆZAMAN AMANA WRITER'S*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```๐Ÿคœ๐Ÿค›





*ALLAH SARKI RAYUWA! SHEKARAR DUBU BIYU DA SHA TAKWAS TA WUCE KUMA BAZATA TAB'A DAWOWA BA, MU ZAUNA MUYI NAZARI ME MUKA AIKATA A CIKINTA, SHIN AIYUKAN ALKHAIRINMU YA RINJAYI NA SHARRIN KO KUWA A'A AIYUKAN SHARRIN NE SUKA RINJAYI NA ALKHAIRIN, MU ZAUNA MUYI NAZARI DA TUNANI, WUCEWAR LOKUTA DA SHEKARU BA ABUN MURNA BANE ABABEN TUNATAR DA BAYIN ALLAH NE SU GANE CEWA LOKUTANSU FA NATA TAFIYA, MU RIBACI RAYUWARMU DA AIKATA ALKHAIRI KAFIN MUTUWARMU, MUYI TUNANI ME MUKA AIKATA A BAYA, KUMA ME ZAMU AIKATA A GABA NA ALKHAIRI, YA UBANGIJINMU KA YAFE KURAKURENMU NA BAYA KA BAMU IKON AIKATA ALKHAIRAI CIKIN WANNAN SHEKARAR WADANDA ZASU ZAMA SILAR SHIGARMU ALJANNA๐Ÿ‘๐Ÿ‘๐Ÿ‘๐Ÿ‘๐Ÿ‘๐Ÿ˜ญ*





```INA MIK'A SAK'ON GODIYATA GA 'DUMBIN MASOYANA DA SUKA KIRANI DOMIN TAYANI TA'AZIYYAR RASHIN UNCLE 'DINA SULAIMAN DA NAYI, DA WA'DANDA SUKA KIRA DOMIN GAISHENI DA JIKI DOMIN RASHIN LAFIYA DA ALLAH YA JARABCENI DA ITA, KA'DAN DAGA CIKI SUNE```


*MAMAN LABYB*
(Mamie Nah)
```KODA YAKE KE AI MAMIE JIGO CE TA RAYUWAR BK๐Ÿ˜‰๐Ÿ˜Š IDAN NACE JIGO INA NUFIN KECE KOMAI NAWA, AMMA DUK DA HAKA WAJIBI NE IN GODE MIKI DOMIN TABBAS KIN DAMU DANI FIYE DA KOWA, K'AUNA BATA IRGUWA SONDA NAKE MIKI BAI MISALTUWA๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ’‹.```

SAI *AISHAN UMMA*
(Auntynah)
*MEELAT A.H.K*
(Bloodynah)
*QUEEN RUQEEY*
(Habibty nah)
*MUMMYS FRIEND*
(Tawan)
*RAHEENAT M. ABBAKAR*
(My heenat)
*HAUWA JAMIL*
*MARYAM M. HASSAN MEEMAH* (Hearty nah)

```Dukkaninku da na lissafo gaskiya bana kallonku matsayin friend kawai, kallonku nake matsayin 'yan uwa, 'yan uwan ma na jini, dalili kuwa shine kun damu dani fiye da kowa, ko na yini d'aya tak in baku ganni ba online sai kun binciki dalili, Allah ya saka muku da alkhairi tabbas irinku ake so, ina da tabbas akan ko bayan babu ni zaku ri'ka tunawa dani har in samu addu'a daga gareku, shiyasa bana had'a matsayinku da na kowa gaskiya, Allah ya saka muku da alkhairi.```




*MASOYANA*
```bazan manta da ku ba masoyana wad'anda suka kwararo min tasu addu'ar ta cikin whatsapp irin su```

*REAL KHADY*
(Princess)
*~HAJARAH GHANDHI*
(Hajjona)
*~MOMYN KHADEEJA๐Ÿง•*
*~UMMUZAID*
~*MAMAN ARFAT*
~*MUMMYN-SULTAN*
*ASIYA SEE SEE*
*MY LISSA*
*MARYAM KWARE*
*QUEEN BK*
*HAJ CEEYMER UMMEETA*
*MARYAM*
*HAPSY MK*

```Kuna farko farko a zuciyata kun nuna mini so da kulawa nagode 'kwarai da nuna kulawarku kaina, Allah ya saka muku da mafificin Alkhairinsa, duk wad'anda suka tayani addu'ar samun lafiya da masu yimin ta'aziyya duk na gani gaba d'aya Allah ya saka muku da alkhairi ya biyaku, wadanda suka ga ban ambaci sunansu ba suyi hakuri ban gani bane saboda yawancin maessage dina duk waiting suka sa min amma ina godiya Allah ya saka muku da alkhairi gaba d'aya, iya wuya fa ana mugun tare.```




*๐Ÿ‡ธ๐Ÿ‡ฆZAMAN AMANA WRITER'S*
```Ina godiya da tarin addu'ar da nake sha kullum a wajenku babu dare ba rana, wallahi kunci sunanku 'yan amana, domin d'an amana ne kad'ai yasan mecece amana kuma ya kiyayeta, kuna burgeni ina yinku har abada, kawai a cigaba da basu maamaaki mutanena๐Ÿคœ๐Ÿค›๐Ÿ˜‰๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜๐Ÿ‘ฏโ€โ™€```




PAGE 120 to 125




Dad ya bada umurni a cigaba da tsare su Amir cikin cell d'in tare da 'yarsa Amira a cewarsa tunda haka ta zab'a kuma taga yafi mata, har zuwa ranar da za a shiga kotu.


Insp Yahya kuwa Allah Allah yake a yanke wa Amir hukuncin kisa ba dan tsanar da yai mishi kad'ai ba ma, ko dan wahalar da suka sha a kanshi, hakan yasa cikin 'kan'kanin lokaci ya had'a dukkanin takardu d'auke da bayanan 'karya aka mi'ka su kotu, wanda za'a halarci kotun ranar Litinin.


Yau litinin, kuma a yau ne kotu ta cika ma'kil domin gudanar da shari'ar su Amir, inda Amira ta 'kara ja mishi kunne kan karya sake duk tsananin wuya ya amsa laifin, sannan ta k'ara 'karfafa mishi guiwa ta hanyar tabbatar mishi da cewa su ne da nasara in Allah ya yarda.


Shigowar Al'kali kenan kowa ya mi'ke, sai da Al'kali ya zauna sannan kowa ya koma mazaunin shi ya zauna.


Kotu tai tsit kowa ya baza kunne da idanu domin bada muhimmanci wajen ganin yanda wannan shari'ar zata kasance.


Da yake shari'ar su Amir itace aka sa a farko shi yasa aka fara karantota, sannan aka umurci gabatar da Amir inda Amira ke biye da shi, can d'aya b'angaren kuma iyayen Sadeeq ne.


Bayan shiru na wasu lokuta saboda nazartar takardun da aka mi'kawa Al'kali da yake yi, can sai Alk'ali ya d'ago ya kalli Amir, sannan ya maida kallon shi kan Amira yace "malama ki koma ki zauna har sai an kira ki," Amira tace " ranka ya dad'e zargin da ake wa Amir mu biyu ake zarga, shiyasa ma na biyo shi muka fito gabanka muka tsaya a tare."


Al'kali yace "duk da haka ki koma ki zauna sai an nemeki," Amira ta kalli Amir shima Amir ya kalleta idonta har ya ciko da 'kwalla, sai ya d'aga mata kai alamar taje ta zauna, Amira taje ta samu waje ta zauna.


Al'kali ya kalli Amir yace "malam Amir kaji irin tuhumar da ake yi maka na kashe Sadeeq, shin ka amince kai kayi kisan ko baka amince da hakan ba?


Amir yace " ba ni na kashe shi ba Allah gafarta malam, ni lokacin da aka yi kisan ma bana wajen, washe gari da na shigo ne naga gawarshi cikin school mutane sun kewayeta.


Al'kali ya d'an yi rubutu sannan ya d'ago yace a gabatar mishi da 'yan sandan da suka yi bincike kan case d'in.


Insp Yahya yazo gaban kotu ya tsaya, Al'kali yace yana son yaiwa kotu bayanin yanda suka gudanar da binciken su har suka tabbatar da Amir shi ya kashe Sadeeq.


Nan Insp Yahya ya fara kwakuso bayani tun daga kan soyayyar da Abdul da Sadeeq suke mata harma da Amir d'in, amma shi sai ya b'oye nashi saboda wani manufarsa da ya barwa kanshi sani a lokacin, sai daga baya yai amfani da damar da ya samu na fad'an da Abdul da Amir suka yi har da ikirarin kashe junansu, Insp ya cigaba da cewa " da wannan damar yai amfani ya kashe Sadeeq tare da barin shaidun da zasu sa a yarda cewa Abdul ne ya kashe Sadeeq, bayan faruwar haka sai na fara bincike kan Amir d'in da Amira, anan na gano ashe shima Amir d'in yana son Amira, amma be nuna mata ba sai da ya kawar da masoyanta Sadeeq da Abdul, sannan na jiyo da kunnena yana baiwa Amira labari cewa shine ya kashe Sadeeq saboda ita."


Al'kali ya rubuta bayanan da ya samu daga Insp Yahya, sannan yace wa Insp ya koma ya zauna, Al'kali ya kalli Amir yace "malam Amir kaji abinda Insp Yahya yace?" Amir yace "eh ya me shari'a," Al'kali yace "kana da ja ko babu?" Amir yace "eh ya me girma me shari'a ina da ja, domin ban tab'a kashe kowa ba."


Al'kali yace "wanene shaidanka?" Amir yace " Allah ne kad'ai shaida ta, sannan kuma ni banac cikin makarantar ranar da akai kisan, washe gari ne da na shigo makaranta na tarar da gawar, in kuma su sunada shaida akan haka to su gabatar, sannan ni da mamatan dukkaninsu muna da kyakkyawar alak'a ko musayar yawu be tab'a had'ani dasu ba."


Al'kali yayi rubuce-rubuce, sannan ya sake kiran Insp Yahya domin ya gabatar da

16 / 31