Author : Bilkisu Z Ya'u Category : Romantic Hausa Novels
kamar gunki ya kasa motsi, babu abinda ke mishi yawo sai maganar Dad.
Amira ta matso inda yake zaune a 'kasan kafet, ta share mishi Hawayen da ke zubowa kan fuskarshi, sannan ta mi'ke tare da kama hannunshi ta jashi suka hau sama haka yaita binta kamar ra'kumi har suka shiga d'aki.
Amira ta zaunar da shi sannan ta fad'a jikinshi ta fashe da wani irin kuka, shima kukan yake tare da 'kara rungumeta yana fad'in "wallahi Amira banso na rasaki, a ina zanga iyayena in kawosu kar a rabani da ke," ya sake fashewa da kuka kamar 'karamin yaro.
Amira tana rungume dashi itama tace "abinda na gudar mana kenan tun farko Amir d'ina shiyasa nace kar mu zo, ni nasan so ake kawai a rabamu shiyasa aka b'ullo da wannan maganar.
Amir ya sake 'kan'kameta kai kace saceta za'ai, yace "Amira 'kaunarki itace bugun numfashina, sonki shine *Mahad'in rayuwata* ana rabamu numfashina zai tsaya ya daina aiki, dan Allah karki yarda a rabamu, Amira bansan iyayena ba ta ina zan fara."
Amira cikin kuka itama tace "Amir d'ina babu mai rabamu sai Allah, shi kad'ai zai iya rabamu domin shi ya nufemu da had'uwa, to me zaisa ka damu tunda muna da tabbas akan yana tare da mu."
A ranar dai haka suka kwana ba bacci musamman Amir, gwara Amira rashin baccin Amir d'in shi ya dakatar da nata, dan har ta fara baccin, minti biyar da farawarta ta farka ta ganshi a kan dadduma yana addu'a yana rusa kuka, dole ta ha'kura da baccin, kuma tai 'ko'karin danne nata damuwar domin kwantar mishi da hankali.
haka Amira ta kwantar da Amir a jikinta kan cinyarta taita rarrashinsa, har Allah yasa bacci yai awon gaba da shi, Amira ta 'kura mishi ido, wani irin tausayinshi yana 'kara ratsa zuciyarta, tunani take yi, ita kanta ta san Amir na yi mata so na ban mamaki, tasan a yanzu tashin hankalinsa da kuma damuwarsa da dalilin kukansa shine ina zaiga iyayensa kar a rabamu, duk duniya babu abinda yake tsoro sama da duk wani abinda zai rabamu, hawayen idanunta ta share tana cigaba da kallonsa, 'kaunarsa na 'kara ratsa ko'ina na jikinta.
Haka Amira ta kwana a zaune bata runtsa ba, ta kasa koda 'kwa'k'kwaran motsi saboda kar baccin Amir d'inta ya yanke.
Sai da Asuba ta tashe shi suka yi Alwala sukai sallah a tare, bayan sun idar tare da yin doguwar addu'a, sannan Amira ta kwanta, Amir kuwa yana zaune kan dadduma zai fara sana'ar tasa wato tunani sai tai sauri ta sa hannunta ta jawoshi ya kwanta kusa da ita, fuskarsu tana fuskantar juna, Amira tace kai bacci karna sake ganinka kayi tunani banso, yanda ta b'ata rai da yanayin yanda tai maganar yasa Amir yin murmushi, Amira tace "yauwa ko kai fa, nafi so fara'arka ta dawo dan baka kyau sam in ba walwala a fuskarka," suka koma bacci abinsu.
Washe gari wajen 'karfe goma suka tashi, suka tarar har an shigo musu da abin karyawa, Wanka suka yi da wanke baki, sai da suka shirya tsaf sannan suka zauna karyawa.
Bayan sun gama karyawa Amir yace su sauka suje su gaishe da su Dad, tace "to," suka mi'ke lokaci d'aya a tare, Amira taji dad'i a ranta yanda taga Amir na daraja iyayenta duk da kora da halin da suka yi mishi jiya, kuma taji dad'i yanda taga ya fara sakin ranshi.
Sun taki sa'a kuwa suna falo dukkansu, suka bisu d'aya bayan d'aya suka gaishe da su.
Bayan sun gama gaisawa Dad yai gyaran murya sannan yace "Amir kayi ha'kuri kar kaji haushina kan hukuncin da na yanke a kanka, matsayinmu na iyaye wajibi ne muyi bincike kanka kuma mu san wani naka, in kayi tunani kai kanka gata nai maka, kuma kaga nima mutuncina be zube ba matsayina na shugaban 'kasa, kasan zab'e ya kusa 'yan adawa kad'an suke jira su b'ataka a idon jama'a."
Amir yace "wallahi ko kad'an banga laifinka ba Dad, kowane uba hukuncin da ka yanke shi zai yanke, kuma muna 'kara baka ha'kuri kan abinda suka faru a baya dan Allah ka yafe mana, kuma nagode da damar da ka bani, kuma daga yanzu ma zan fara 'ko'karin nemansu insha Allah."
Dad yace "ai tuni na yafe muku yarona, Allah ya taimakeka, duk taimakon da kake nema kar kaji nauyin tambayata ko ka sanar da Amira ta fad'a min, Allah yai muku albarka," dukkansu suka ce "Ameen."
Muje zuwa
*π
±K CEππ*
ππππππππππ
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
ππππππππππ
RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (π
±K)*
```(Autar marubuta)```
SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
```(Mamie)```
*πΈπ¦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```π€π€
PAGE 140 to 145
Suna gama magana yai sallama da su kan zai tafi ya fara bincike akan asalin nashi, Amira ce ta d'ago kai cikin sauri ta kalle shi tana mamaki, domin ta san ita basu yi wannan maganar ba a d'aki, yanzu ya 'kir'kiro da ita, suna had'a idanu ya fakaici idanun mutane yai mata murmushi tare da gwalo a lokaci d'aya.
Tashi yai dukkansu suka yi mishi fatan alkhairi, ya kama hanya ya fice daga gidan.
Yana fita ya d'auki hanya Amira itama ta haye sama ta d'auki wayarta tare da antaya wa lambarsa kira, har ya fita daga gidan gaba d'aya ya fara tafiya yana tunani da mamakin bataliyar security da aka 'karo, yasan ba akan komai bane sai a kansu shi da Amira, yana cikin wannan tunanin ne yaji wayarsa tana bada sautin 'kara me d'an karen dad'i, murmushi yayi domin yasan me kiran tunda ita kad'ai ya sakawa wannan ringing tone d'in, ciro wayar yayi, sannan ya d'aga tare da karata a kunne.
Kafin yai magana ta balbale shi da fad'a, " yaushe muka yi maganar zaka fita daga zuwan mu zaka fita wani yawonka da sunan yin bincike, in ba yawo ba ina zaka je wa zaka tambaya, to wallahi kar kaga kai mijina ne zan iya hukuntaka, kuma ko yanzu ba 'kyaleka zanyi ba, ba zaka ci abincina ba, kuma ba zaka ga walwalata ba, kuma sai kayi tsallen kwad'o," tana gama fad'in haka ta katse wayar, Amir ya kwashe da dariya domin shi maganarta dariya suka bashi, ya maida wayarsa aljihu ya cigaba da tafiyar shi.
Yana cikin tafiya yaji message ya shigo, yana dubawa yaga Amira ce, cikin sauri ya duba.
_Na duba harabar gidan naga motata tana nan baka fita da ita ba, ka dawo ka d'auka banson tafiyar 'kasa malam ko cemaka aka yi bana kishinka, kuma wallahi ka ri'ke min amanar kanka, duk macen da ta kalleka ka mareta ni na saka._
Amir ya ci dariya kamar me, sannan ya dawo dolen shi tunda basa musa wa junan su, ya d'auki motar ya tafi, yana cikin tafiya yana tuno da diramar matarshi shi kad'ai yana dariya.
A haka ya kasance cikin walwala da farin ciki har Allah ya kawo shi inda zai zo.
Ya bud'e 'kofa zai fito ya sake jin wani 'karar message d'in, ya fito da wayar ya duba
_Duk da ina fushi da kai ban isa hana zuciyata kewa da tunaninka ba, nayi kewarka mijina._
_'Kalubalenku mata ma'aurata, ni abinda ke d'auremin kai da wasu matan auren shine dan girman Allah in baki samar wa da mijinki farin ciki ba a lokacin da yake cikin gida da kuma idan ya fito wa kike so ta bashi? anya kina iya nunawa mijinki kin damu dashi, kina gwada mishi so da 'kauna kuwa koda ace kina fushi dashi ne? to ai bari kuji hikimar yin hakan shine in har kina yin hakan to wallahi tunaninki a ransa ba zai tab'a barinsa ba, ko mata dubu ya aura sai kin fita daban a cikinsu, saboda kulawarki takice ke d'aya babu kishiyar da zata kama 'kafarki, ga dai Amir nan ya fito kamar zararre a mota sai dariya yake, wacece sanadi? matarsa, to da a 'kasa ya taho yasin d'auka za'ai mahaukaci ne, haka ya kamata ki zauta shi ya zama baida wani sauran tunani sai naki, Allah yasa mu dace._
Amir ya dakata da fitowa daga motar ya fara bata amsa kamar haka.
_Amanarki na ri'ke Amirata, kuma kema kinsan duk halin da kike ciki dole nima in tsinci kaina a ciki, domin kuwa zuciyoyin mu a had'e suke, gangar jikina ne kawai bata tare dake, amma zuciyata tana wajenki, domin kuwa tunaninki take, ki kular min da kanki kinji, bazan dad'e ba zan dawo gareki ko zuciyata ta huta daga tunani da kuma kewarki, ina sonki,_
_daga mijinki AMIR._
Yana gama rubutawa ya tura mata, sannan ya fito daga motar, unguwar yake kallo, tare da 'karewa gidan da ya taso rayuwa a cikinsa, ba ko wane gida bane illah gidan da wannan mutumin ya ri'ke shi, yasan Allah yai mishi rasuwa, amma yazo tambayar ma'kwabtansa ne da abokansa ko Allah zaisa ya samu wanda ya san daga inda ya fito.
Amir ya fara da wani shago dake kusa da gidan, da sallamarsa ya 'karasa shagon, me shagon wani dattijo ne ya amsa mishi, dattijon nan abokin mari'kinshi ne, shiyasa yazo wajen shi ko yana da wani labari a kansa.
Bayan sun gaisa Amir yace "Baba ka gane ni kuwa?" Baba yace "a'a yaro, ban shaida ka ba," Amir yace "Amir ne yaron marigayi me can gidan," ya nuna mishi gidan da hannu.
'Dan tsohon nan ya zaro idanu, sannan yace "wai kana nufin Ameeru ne wannan a gabana?"
Amir yai murmushi, shi sam yama manta sunan shi Ameeru a da, yace " eh ni ne Baba," Baba yace "Allah mai iko, Ameeru kai ne ka zama kyakkyawan bature haka," Amir yai dariya, nan suka sake sabuwar gaisuwa, sannan Amir yai gyaran murya yace "Baba akwai abinda ke tafe dani wajenka," Baba yace "to ina jinka Ameeru, Amir yace "zuwa nayi inji ko kasan wani abu game da labarina, ina nufin inda mari'kina ya sameni, ko kuma ajiyata aka kawo mishi?"
Baba yai shiru yana tunani, can sai yace "eh to gaskiya ni a yanda yace min lokacin da na ganshi da kai a hannu na tambayeshi, cemin yai tsintarka ya yi, se dai har ga Allah ban san a ina ya tsinceka ba," iya abinda ya samu kenan wajen Baba, haka ya gama binciken shi a unguwar nan amma babu wani abu da ya 'kara samu, hakan yasa ya wuce station ya shigar da 'korafi kan ya rasa iyayensa tun be san kanshi ba, yanzu shekaru talatin kenan, koda wasu sun zo neman d'ansu a kirashi ya gansu, duk wata station da take wannan garin sai da yaje ya shigar da wannan bayani, tare da rarraba lambobinsa koda za'a nemeshi, sannan ya juyo kan motarshi zuwa gida jiki a sanyaye.
Yana zuwa bakin 'kofar gidan yai hon aka bud'e mishi ya shiga, kai tsaye wajen fakin ya wuce ya faka motar sannan ya kasheta ya fito ya shiga cikin gida.
Be tarar da kowa ba a babban falo, hakan yasa kai tsaye ya haye sama, ba kowa a d'akin nasu, ko'ina ya duba Amma Amira bata ciki.
Wayarshi ya ciro ya kira wayarta yaji tana ina, Amira kuwa tana sashen mahaifiyarta tana zuba mata shagwab'a, wayarta taji tana 'kara kuma tasan wanda ke kira, saboda itama ringing d'in kiran shi daban ta saka, bata d'aga ba mi'kewa kawai tayi tace wa Mummyn ta hira ya 'kare bari ta koma d'aki.
Mummy tace "oh Allah ya kawomu zamani mijinki ya dawo ya kiraki a waya kin tashi da rawar jiki zaki tafi," Amira ta turo baki sannan tace "ya akai kika gane shi ya kira?" Mummy tace "yanayin zumud'in da kika nuna yanzu mana," Amira tayi dariya sannan tace "kaji Mum dai kema fa tunda nai wayau ban tab'a ganin Dad ya shigo ya wuce d'akinshi kuma ki cigaba da zama wajenmu ba, in dai yana gida to kema a koda yaushe kina wajenshi, idan mun ganki to baya nan ne, nima yasin dan bayanan ne yasa kuka ganni," tana kai nan a maganarta ta danna a guje ta fice daga d'akin.
Mahaifiyarta kuwa salati ta hau yi, tace kaga ja'irar yarinya ta samin ido ni da mijina," matar Uncle d'insu kuwa dake zaune tana jin duk abinda Amiran tace dariya take ta yi.
Amira da d'aurewarta ta shiga d'akin tana cin magani ita a dole tai fushi, kuma tana shigowa kusa dashi ta samu waje ta zauna, jin yai shiru be ce mata komai ba yasa ta d'ago ta fara satar kallonshi, tunani yake sosai idan ma ance be san ta shigo ba ba musu.
Nan da nan Amira ta warware ta nemi fushinta ta rasa, fuskarta ta koma bayyanar da yanayi na damuwa, 'kara matsowa kusa da shi tayi, tare da dafa kafad'arshi tana jijjiga shi cikin damuwa tace "Amir d'ina lafiya, meke faruwa na ganka cikin wannan yanayin, dan Allah ka fad'amin meyafaru?"
Amir yai firgigit, sannan ya numfasa, ya kalleta yace "Amirata kin shigo ashe, wallahi Amira nayi yawon amma ba nasara," ya kwashe komai ya fad'a mata har yanda suka yi da tsohon nan.
Amira ta numfasa sannan tace "shine kabi duk ka d'aga hankalinka, bayan kuma kasan idan ka shiga damuwa ina finka shiga tashin hankali, haba Amir d'ina dan baka ga iyayenka ba sai akace maka mun rabu kenan, ina lura da kai tunda Dad yai wannan maganar ka shiga damuwa, ni nace maka zan barka ne, fad'in Dad ne kawai kaima ka sani, amma duk wuya duk rintsi ina tare da kai, babu abinda zai rabamu insha Allah, ka kwantar da hankalinka ko me za'a yi, kuma ko menene zai faru se dai ya faru amma ban tab'a rabuwa dakai, ban tab'a juyawa soyayyarka baya.
Cikin 'kan'kanin lokaci sai da taga ya dawo asalin Amir d'inta sannan hankalinshi ya kwanta itama ta samu natsuwa, ta had'a mishi ruwa yai wanka sannan ta shirya mishi abinci a gabanshi ya zauna zai fara ci, ya Kalleta yace "wai ina fushin da kike yi dani ya tafi, har abinci fa akace baza'a bani ba," Amira ta turo baki sannan tace "ya za'ai in kula wani fushi na ganka cikin yanayi na damuwa, ni nama manta," haka sukaita hirar su cikin jin dad'i.
Haka Amir yaita sintiri kullum amma ba wani labari, har cikin 'kauyukan garin ya shiga yana bincike amma shiru har yanzu, har wajen wata uku yana zirga-zirgar neman bayani akai amma shiru.
Yau lahadi, kamar kullum yau ma Amir ya shirya tsab domin fita cigaba da neman 'karin bayani kan wanene shi kamar yanda ya saba, bayan ya shirya tsab ya kalli Amira yaga yanda ta had'e rai, yai murmushi sannan yace "wai ke dan Allah meyasa duk in zan fita sai kin b'ata rai ne," Amira ta 'kara turo baki sannan tace "saboda rashin sabo mana," Amir yace ai kuwa ya ci ace kin saba mun shiga wata na uku ina fita fa," Amira ta 'kara turo baki sannan tace ni bazan saba ba, ni yasin yau binka ma zanyi," Amir yace "kiyi ha'kuri yau waje d'aya zanje in dawo bazan dad'e ba insha Allah."
Da 'kyar ta barshi ya fito ya shiga mota ya fice daga gidan, cikin 'kauye ya nufa, yana cikin tafiya wata babbar mota ta taho da gudu, duk yanda yaso ya kauce mata ya yi amma ya kasa, sai da tabi ta kanshi motar Amir ta hantsila can gefen ti-ti, cikin sauri masu babbar motar suka fito suka ga sam ba alamun numfashi a tare da Amir, d'aya daga cikin su yace "baya numfashi wallahi mui ta kanmu," ai kuwa su duka ukun suka fad'a mota suka jata da gudu suka bar wajen.
Muje zuwa
*π
±K CEππ*
ππππππππππ
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
ππππππππππ
RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (π
±K)*
```(Autar marubuta)```
SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
```(Mamie)```
*πΈπ¦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```π€π€
PAGE 145 to 150
Da yake ba cikin gari bane motoci d'ad'd'aiku ne suke wucewa kan hanyar, kuma ikon Allah duk wanda yazo kai tsaye yake wucewa babu wanda ya tsaya saboda ba wanda ya kawo akwai mutum a ciki, sedai in zasu wuce daga cikin motar kaji ana cewa kai amma an gwabza hatsari anan Allah ya kiyaye gaba, sai su wuce abinsu.
β¦β¦β¦β¦β¦β¦β¦β¦β¦β¦β¦β¦β¦
Ahmad da matarsa Khadija tafe suke a kan hanya, Ahmad yana tu'ki yana yiwa matarshi fad'a yace "wai Hauwa sai yaushe ne zaki cire tunani ne daga ranki, kinsani fa sarai abinda tunani ke haifarwa ko so kike nai rashinki? dan Allah ki daina tunanin nan zuwa yanzu yaci ace kin.........." kasa 'karasawa yayi sakamakon ganin mota a tuntsire, kuma daga gani wannan had'arin be dad'e ba dan ba alamun hakan, ya kalli matarshi yace "kin kuwa hango abinda nake gani a gabanmu? hatsari aka yi, kuma ni kamar ma hannun mutum nake hangowa bari inje in duba," cikin sauri matarsa Hauwa ta ri'ke shi, tace "nifa tsoro nake ji, kasan yanda duniyar nan ta zama, ba mamaki ma 'yan fashi ne," Ahmad yace "kai bana tunanin haka gaskiya, koma dai menene zanje in duba, Allah yaga zuciyata, ba zai bari su cutar da ni ba."
Yana gama fad'in haka ya fita daga motar ya tunkari wajen wannan motar da suka gani, yana zuwa ya le'ka ciki ai kuwa mutum ne ya gani a ciki yaro matashi kanshi na fitar da jini, duk yaji ciwo a jiki, kuma babu alamar numfashi ko kad'an a tare dashi.
Cikin sauri ya fara 'ko'karin neman hanyar da zai fito da shi, da 'kyar Allah ya bashi sa'a ya fito dashi daga ciki.
Matarshi kuwa koda ta hango abinda ke faruwa ta glass d'in motar ta fito cikin sauri ta tunkaro wajen, 'kokarin kamashi suka yi suka sa a mota sannan suka tafi asibiti, a hanya matarshi 'korafi take ta yi tana fad'in kaga amfanin securitys da jami'ai ko, amma kai in za'a fita sai kace baka so suna binka,