Author : Bilkisu Z Ya'u Category : Romantic Hausa Novels
ikon watsi da kura kuren cikinsa, abinda kikai dai-dai Allah ya baki ladan, kuskuren dake ciki kuwa Allah ya yafe miki, Allah ya 'kara miki basira, d'aukaka, da d'an karen za'kin hannu, sai mun jiki cikin sabon novel d'inki.😍😘💋*
PAGE 100 to 105
Bayan d'an wani lokaci sai ga kiran kwamishina cikin sauri Dad ya d'aga yace ‘’ya ake ciki tana nan kuma kun ganta da idanunku?‘’ kwamishina yace ‘’gaskiya bata cikin makarantar nan domin ta ma dad'e bata shigowa ciki, ance tana tare da wani yaro wai saurayinta ne, se dai ba'a san inda suke ba.‘’
Dad yace ‘’ku baza yaranku a fita neman su nan ma zansa a bincike su, duk yanda ake ciki zamu yi waya,‘’ suna gama waya Dad ya sake kiran shugaban 'yan sanda na nan Abuja yai mishi bayanin komai tare da bashi umurnin a bincika ko ina duk wanda aka gani cikinsu a kamo shi a kawo su gareshi, bayan ya gama wayar yaita gwada ta Amira amma sam tak'i shiga, wurgi ya yi da wayar kan tiles d'in falon ai kuwa ta tararratse, yana fad'in ‘’ta kashe wayarta balle insa a gano inda take, wallahi na kama Amira sai ta raina kanta, sai na ajiye tsananin k'aunar da nake yi mata a raina na hukuntata dai-dai da abinda ta aikata a gareni, na saki jiki tana karatu ashe ta maida mu wawaye tana can tabi d'an iska, haka yaita surutu shi kad'ai cikin tsantsar b'acin rai idanunshi sunyi mugun ja saboda b'acin rai, ya kalli 'kaninshi ya cigaba da fad'in Amira na so ta zubar mana da mutuncin gida, wai ta rasa wanda zata so sai makashi mai yin kisa kuma har ta bishi su gudu, ita da na tura tai karatu itace da bin d'an iska makashin mutane har rayuka biyu, to wallahi idona idon saurayin nan nata koh, wallahi sai na b'atar dashi, sai na wulak'anta rayuwarshi kamar yanda ya hure wa 'yata kunne, ita kuma koh hmmmm,‘’ ya juya cikin tsananin fushi ya shiga d'akin shi.
Ko'ina an baza yara neman su Amir amma sam ba labarinsu, hakan ya k'ara wa Dad shiga cikin damuwa, kuma kullum cikin gwada lambar wayar Amira yake yi ko Allah zai sa a dace wata rana a samu, a haka har aka kai wajen wata d'aya ana bincike amma sam babu su ba labarin su, hakan yasa Dad yasa aka turo mishi Insp Yahya har gida domin yai ganawa ta musamman da shi.
……………………… ……………………
Bangaren su Amira da Amir kuwa hankalinsu kwance yake a k'auyen nan ba abinda ke damun su, soyayyar su kuwa kullum dad'a nunkuwa take, kullum suka gama taya iyayen gidan su aiki zama suke cikin gida ko a waje jikin bishiya suita hirar su, abu d'aya ne kad'ai ya fara damun Amira, yanda ta lura da 'yan matan k'auyen ke nuna soyayyar su a kan Amir, har cincirindo wasu suke yi kawai dan su ganshi.
Yau ma zaune suke a waje da yamma suna hirar su me dad'i, Amira ta kalli Amir tace " son da nake maka abu ne me matu'kar muhimmanci a rayuwata, rasaka kuma tamkar rasa rayuwata ne, shin kana jin shau'kin son da nake maka kuwa Amir d'ina, tunda nake ban tab'a son wani d'a namiji ba sai kai, kuma zuciyata ba zata tab'a d'aukar wani ba bayan kai."
Amir ya ce "Amira ki kwantar da hankalinki ni naki ne har abada haka kema tawa ce har k'arshen numfashi, gamu kuma a tare muna rayuwa waje d'aya, kawai addu'a zamui ta yi Allah ya bamu ikon mallakar juna matsayin ma'aurata."
Amira tayi murmushi sannan ta amsa da "ameen. "
To da yake 'kauyen da suke ciki suna dad'ewa kafin su samu wuta shiyasa wayoyinsu kwata kwata babu caji, suna,cikin wannan hirar cikin ikon Allah sai ga wuta an kawo gaba d'aya 'kauyen ya kaure da 'kara kasancewar sun dad' basu ga k'yallowarta ba, hakan yasa su Amir ma suka katse hirar da suke yi suka shiga ciki domin su saka caji.
Suna saka caji Amira ta kunna ta-ta wayar, tana kunnawa ta koma kusa da Amir ta zauna suka ci gaba da hira, sedai bata dad'e da zama ba wayarta ta fara ringing, tashi ta yi domin zuwa ta duba taga ko waye ya kira ta, Dad d'inta ne ke kira, cikin sauri ta d'aga tare da karawa a kunne se dai ta kasa cewa komai, ji tayi yace " My Daughter karki damu nasan duk abinda ke faruwa, saboda haka ki kwantar da hankalinki yanzu kina ina ne?"
Amira cikin murna da farin cikin mahaifinta be d'auki zafi ba kan lamarin tace "Dad muna…………" Amir ne yai saurin karb'e wayar daga hannunta tare da kashewa gaba d'aya.
Amira ta kalle shi tace " Amir Dad d'ina ne fa," Amir yace "haba Amira so kike azo a kama mu, ko kin dena sona ne yanzu kin amince a kasheni?"
Amira tace "no babu wannan ranar har abada, kawai dai tunani nayi akan b'oyon da muke ta yi sam bashi da amfani," Amir yace "amma Amira ki gane mana kuma kiyi tunani kinsan Dad yana da zafi sosai in har ba abinda suka shirya a kanmu be kamata ace yai saurin saukowa ba haka har yana neman inda muke, kuma be yi miki fad'a ba fa sai tambaya da yake yi wai kina ina, in kika fad' inda muke Amira kama ni za'ai kuma nasan daga ranar ba zamu sake ganin juna ba dan kasheni zasu yi."
Amira tace " Amir ka kwantar da hankalinka, Dad yana 'kaunata sosai, kuma na tabbatar 'kaunar da yake min zaisa ya amince in auri wanda nake so, ka kwantar da hankalinka a yanayin da na jishi ba zai bamu matsala ba insha Allah."
Amir kam ba don ya gamsu da bayananta ba ya amince dasu, domin shi ya tabbatar suna zuwa zasu raba su, amma saboda baya so ya cigaba da jayayya da ita a kan magana da mahaifinta sai ya amince da abinda tace tare da mi'ka mata wayar ya koma inda yake zaune da ya zauna tare da zuba mata idanu.
Amira ta karb'i wayar ta kunna, tana 'ko'karin kiran Dadyn sai ga kiransa ya sake shigowa, Amira ta d'aga sannan cikin sanyin murya wadda take bayyanar da aji tausayin mutum tace "Dad muna magana d'azu ta yanke," Dad yace ba damuwa fad'a min kuna ina ne gobe zan turo a d'auke ku?"
Amira tace " muna zaria cikin 'kauyen…………" da yake wayar da suke yi ba caji tayi ba suka sake d'auke wutar su, Amira tace " wayyo Allah Amir sun sake d'aukewa kuma, ko taka ta yi caji ka d'an ara min in kira Dad?" Amir wanda yai mugun jin dad'in d'aukewar wutar yace " ai ni tawa wayar ma ta'ki kawowa kwata kwata, 'kila saboda dad'ewar da tayi ba caji ne."
Amira tace " to Allah sa su dawo da ita, sai yanzu hankalina ya fara kwanciya nake jin k'arfin guiwar yiwuwar aurenmu da kai Amir," Amir yai murmushi sannan yace " Allah ya tabbatar mana da alkhairi," Amira tace " Ameen, amma ya naga yanayinka ya canza?"
Amir yace "ka jita, to na canza da me, bakomai fa," nan dai suka ci gaba da hira har lokacin sallar magrib ya yi, suka tashi suka fita tsakar gida domin yin alwala su gabatar da sallar su.
Da dare Amira ta kasa bacci zuciyarta na nazarin maganar Amir, har Amir yai bacci ma amma ita idanunta biyu, tunani take yi itama yanda mahaifint ke 'kaunar karatun ta yaji bata makaranta kuma yai saurin saukowa haka, lallai akwai wata a k'asa, ta sake tuno abinda aka yi mata kan Amir tun suna 'kanana, hakan yasa tai amanna da zancen Amir cikin zuciyarta.
*BAYAN KWANA BIYU*
Dad ne zaune shi da Insp Yahya a d'aki na musamman suna tattaunawa kan maganar su Amira, bayan sun gama magana Dad ya bashi lambar Amir da Amira tare da bada umurnin suita kira duk ranar da suka yi sa'a suka samu lambar d'aya daga ciki to kawai suyi 'ko'karin binciko inda suke.
Insp Yahya yace " ai yanzu da wuya su d'aga kowace lamba musamman lambar da babu suna, ni a tunanina kamata yai a cikin wad'anda suke shiri kuma suke waya cikin d'alibai mu samu d'aya daga cikin su a sashi yaita kira har a samu su d'aga koda mutum uku ne dole za'a samu mutum d'aya a cikinsu wanda zasu d'aga wayar shi."
Dad yace " lallai na yarda da maganar da kwamishina ya yi a kanka, kaje ka aiwatar da duk abinda ya kamata daga yau, da zarar kun samu wayar ta shiga kafin ku binciko inda suke ku sanar dani a gabana nake so a kama su domin inga mai k'arfin halin iya d'auke min 'ya."
Nan dai suka yi sallama Dad ya bashi ma'kudan kud'i, Insp Yahya ya fito ya tafi.
Yau Alhamis, 'karfe takwas dai-dai na safe Amir da Amira suna zaune cikin d'aki, gama karyawarsu kenan, sun fitar da kayan abincin Amira ta wanke ta dawo suka zauna suna hira, suna cikin hirar ne aka kawo wuta, suka sa caji sannan suka tashi suka tafi d'ebo ruwa.
kasancewar sun tarar da layi yasa suka dad'e a wajen sai da suka yi wajen kusan awa guda sannan layi yazo kansu suka d'iba suka juyo zuwa gida, se dai suna shawo kwanar gidan suka hango su Umma a 'kofar gida, cikin sauri suka k'araso wajen su suna tambayar su me suke yi a tsaye a 'kofar gida, Umma cikin farin ciki tace " albishirinku yarana bayan fitarku aka kira wayar Amira naji k'aran ya'ki 'karewa nazo naita daddangwalawa sai in na kara kuma inji shiru ban sani ba ko kashewa nai ko d'auka har Allah ya bani sa'a aka jini sai na fad'a musu bakwa nan kun fita, sai suka fad'amin cewa kun b'ace ne suna nemanku, , ina jin haka na gane 'yan uwanku ne, shiyasa nai musu kwatancen nan suka taho, a ta'kaice dai yau Allah ya kawo iyayenku."
Amira ta d'ora hannaye a kai tare da runtuma kuka tana fad'in shikenan mun shiga uku," Amir yace " Amira tunda sun gane inda muke zo mu gudu tun kafin su zo su iskemu anan," Baba da Umma suna ta fad'in me yafaru meyasa bakwa farin ciki, ina sam basu sauraresu ba Amir ya kama hannun Amira ya jata zasu gudu amma se dai sun makaro, suna juyowa suka ga Dad da rundunar sojoji da 'yan sanda kewaye dasu kamar wad'anda zasu tafi ya'kar miliyoyin mutane.
Dukkanin su sun saita su da bindiga, Amira kuwa cikin sauri da tsoro ta tsaya gaban Amir tare da kareshi kar a harbeshi, Dad kuwa cikin tsananin b'acin rai yake kallon Amir, cikin d'aga murya kuma ya bada umurni kamar haka "ai mishi shegen dukan da zai kasa tashi tun a nan kafin mu tafi dasu."
_wayyo ina cikin firgicin ganin za'a raba masoya ta k'arfi da yaji shiyasa kuka yaci k'arfina baran iya cigaba da typing ba,😭 kunji dai gaskiya na gaji da typing ne yasin😂 sai kuma gobe😜_
Muje zuwa
*🅱K CE😘💋*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (🅱K)*
(Autar marubuta)
SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
(Mamie)
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛
*DARLING INSPECTOR YACE A FAD'AWA 'YAN TEAM D'IN AMIR YANA GAMAWA DASHI TO KANKU ZAI DAWO DUK SAI YA GARK'AME KU D'AYA BAYAN D'AYA, INA TAUSAYA MUKU KUKA SHIGO HANNUN DARLING INSP KAFI 'KARFIN MUGU BA SASSAUCI😂😂😂😂😂 SAURA SU O'O ACE NI BK NICE NA FAD'A MISHI😏😏*
*SA'KO ZUWA GA MASOYANA💌*
*Amincin Allah su tabbata ga masoyana ma'abota aminci,🙏😊 wasu daga cikin masoya sun kirani wasu sun yo min test message wasu sun tambayeni ta watsapp wai sun sami labari ni 🅱K nima na maida littafina na kud'i, ma'ana sai an biya kud'i zan tura wai shiyasa na daina typing kwana biyu, wasu kuma rok'ona suke yi dan Allah kar nima ince zan maida novel d'ina na kud'i, to maganar gaskiya bansan da wannan zancen ba, hasali ma rashin lafiya nake shiyasa kuka jini shiru kwana biyu, duk wainar da ake toyawa bansan da ita ba sai da sak'onnin masoyana ya iso gareni, to masoyana ku kwantar da hankalin ku novels d'ina duka kyauta ne babu kud'in da zansa akai ince ku biyani, abu d'aya nakeso kuyi ku biyani dashi shine dan Allah kar ku manta dani cikin addu'arku a yanzu da nake a raye da kuma bayan na mutu, addu'arku gareni itace zata tabbatar min da cewa kuna k'aunata k'auna ta gaskiya, Allah ya barmu tare, wallahi na matuk'ar jin dad'in k'aunar da kuke gwada min yanda kuka nuna damuwarku kan lamurana da kuma abinda ya shafi novel d'ina, kamar yanda nake jin farin ciki mara misaltuwa a duk lokacin da naci karo da masoyana ko kuma nai magana dasu kai tsaye*
*NAGODE! NAGODE!! NAGODE!!!*
PAGE 105 to 110
Insp Yahya shi da wasu murd'a murd'an 'yan sanda suka yo kan Amir, Amira ta tsaya gaban Amir tare da 'kan'kame shi tana girgiza kai tare da kallon bataliyar 'yan sandan da suka yo kansu domin jibgar mutum d'aya tak, tace "karku sake ku tab'ashi ba shi bane yai kisan fa Dad ni na kashe shi da hannuna," Amir da ke shirin yin magana ta ri'ke hannun shi sannan cikin rad'a tace " kar kace komai Amir muddin kana son mu cigaba da rayuwa a tare."
Dad da kanshi ya tako har inda Amira take ya sharara mata kyakkyawan mari jin abinda take fad'a, sannan ya kama hannunta ya jata har cikin mota ya sakata ciki sannan ya rufo ya dawo ya bada umurnin aiwa Amir wanda ke ta faman kwad'a wa Amira kira yana kuka tunda aka b'anb'areta daga jikin shi duka, Insp Yahya shine kan gaba, kafin ya fara dukansa ma bayan sun k'araso gabansa sai da ya kalli Amir yai mishi wata irin dariyar da ke d'auke da ma'anar yau gaka a hannu na me 'kwatarka sai Allah, haka sukaita dukansa ba ji ba gani kuma Insp Yahya yafi kowa jibgar Amir.
Nan fa suka rufar mishi da duka ta ko'ina tun yana iya yin 'kara har muryarsa ta disashe kuma duk da haka Dad be bada umurnin a daina dukansa ba, Amira ce ta fito daga mota da gudu Allah ya bata sa'a ta warce wata bindiga dake hannun wani d'an sanda cikin sauri kuma ta saita kanta da bindigar tare da fad'awa kan Amir tana saite da bindigar, Dad ne ya k'wala mata kira da k'arfi, Amira tana kuka tace "wallahi Dad nice na kashe shi, Amir ya yi hakan ne kawai domin ya kub'utar dani daga fad'awa hannun 'yan sanda, sannan yai haka ne saboda soyayyar da yake min shiyasa ya d'ora laifin kansa, Dad kama kuwa gane wanda ke tare da 'yarka har yanzu? to yaron nan ne dai da ka rabamu tun muna 'kanana, zuwa yanzu ya kamata ace ka gane cewa had'uwarmu daga Allah ne, kuma duk abinda Allah yaso faruwarsa babu mai iya canza shi ko wanene, Dad kasan tun ina yarinya ban saba yi maka 'karya ba ko laifi nayi na gwammace in fad'i gaskiya ka hukunta ni, to yanzu ma gaskiyar zan sake fad'a maka duk duniya babu wanda nake so nake 'kauna sai Amir kuma babu wanda zan iya aura in ba shi ba, dan Allah Dad ina ro'konka ka 'kyalemu mu tafi, in kuma ba haka ba zaka rasani na gwammace mutuwa da inga ranar da zaku rabani da Amir domin Amir shine *MAHA'DIN RAYUWATA* " har ta gama magana tana saite da bindigar bata sauke ba, kuma bata daina magiya ba, shima Amir kuka yake suna ri'ke da juna gam kamar wad'anda za'a raba, af ashe fa rabasun za'ai ko😰 jin abinda Amira ta fad'i babu abinda ya 'karawa Dad banda tsananin tsanar Amir, dama shine yaron da sanadin shi ne ya dawo da karatun Amira kacokam garin kano amma duk da haka saida ya biyota nan d'in ma, zuciyar shi fad'i take ashe d'an iskan nan shi ya ruguza min mafarkina a kan Amira, ji ya yi tsanar Amir ta dad'a nunkuwa, cikin fushi yace " ku cigaba da dukansa har sai nace ku daina," Amira ta sake kare shi tare da saita bindigar a kanta tace " wallahi Dad duk suka 'kara dukan Amir sai na kashe kaina da wannan bindigar," Dad ya dakatar da su cikin sauri domin yasan tabbas abinda Amira ta fad'i zata iya aikatawa, tunani ya yi kan dole sai an biyo musu ta siyasa kafin su sami damar tafiya da su.
Umma da Baba kuwa babu abinda suke yi banda kuka, duk da basu san meke faruwa ba amma sun tausayawa yaran dan jinsu suke yi kamar yaran da suka haifa a cikin su.
Dad ya kalli Amira yace " yanzu me kike so ayi?" Amira tace " so nake ka yi ha'kuri Dad ka barmu mu tafi," Dad ya kalleta yace " a'a bazai yiwu ba in barku ku tafi Daughter, kece 'ya d'aya tilo a wajena, kuma kinsan tunda nemanku ake a ko'ina koda kun tafi k'ara kamaku za'ai a wani wajen, kinga kuwa tafiyarku sam bata da amfani muddin ba'a kashe case d'in ba, yanzu abinda za'ai shine ki bari muje station a kashe magana kuma ku saka hannu tukun," sai a lokacin hankalin su ya d'an kwanta, amma ganin irin kallon da Dad ke wa Amir yasa jikin Amir d'in yai sanyi kuma zuciyarshi na kokwanto kan zancen da yai musu.
Anyi - Anyi da Amira ta ajiye bindigar hannunta amma ta'ki ajiyewa, tama 'ki yarda a matso kusa da ita balle su 'kwace, dole a haka suka d'auki hanya sai station, ko da isarsu suka tarar da rundunar 'yan sanda da sojoji suna jiran zuwan su, nan jikin su Amir da Amira ya 'kara yin sanyi