SO MAHADIN RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVELS PDF BY BILKISU Z YAU.txt

Author :  Bilkisu Z Ya'u Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   29 / 31

84K to 87K   out of 90.7K words

kuka yake da idanunshi, wai yau shi ake yiwa haka a rayuwa.



Suna cikin wannan yanayin su Abba suka yi sallama suka shigo, Dad ya d'aga kai ya kalli Abba ya zaro idanu tare da fad'in "Ahmad!!!! yau kaine a gidana, ya kalli gefen Abba inda Amir ke tsaye hannunshi cikin na Abban ya sake cewa "kar dai Amir d'anka ne?"



Abba yai Murmushi, sannan yace "Amir d'ana ne na cikina, ashe kaine mahaifin Amira, ikon Allah kenan," Dad ya fad'i 'kasa dab'as kan kafet, tare da dafe kai yace "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un!! na cuci kaina," yana gama fad'in haka ya cigaba da kuka cike da jin kunya me yawa da takaici, had'e da nadama.







Muje zuwa








*πŸ…±K CE*πŸ˜˜πŸ’‹
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜





RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (πŸ…±K*
```(Autar marubuta)```






SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
```(Mamie)```






*πŸ‡ΈπŸ‡¦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```πŸ€œπŸ€›







PAGE 215 to 220






Sam Dad ya kasa d'ago idanu ya kalli Abba balle Amir da 'yarshi Amira.



Amir ne ya kalli mahaifinsa yace "Abba kasan Dad ne dama?"



Abba ya kalli Amir yace "na sanshi abokina ne wanda acikin labarina da na baka na baka labari ni nai mishi jagora ya samu damar d'anewa kujerar shugaban 'kasa, saboda mutane suna sona kuma sunji dad'in mulkina shiyasa da sukaga dani a wajen tsayar da mahaifin Amira yasa shima ya samu karb'uwa sosai a wajen mutane, daga nan ni kuma na koma garinmu da zama ni da iyalina domin bana bu'katar cigaba da mulkin a lokacin."



Abba ya dakatar da wad'annan mutanen da suke yiwa su Dad watsi da kaya, yasa mutanenshi suka kwashe dukkanin kayan yace su kai sabon gidan da ya gina kwanan nan, wanda yake kusa da nashi da yake ciki a yanzu.



Bayan an gama kwashewa sun sanar dashi yai waya aje a shirya musu gidan a shirya komai yanda ya dace, su kuma yace su tashi gaba d'ayansu su tafi gidanshi idan sunje can a tattauna.



Dad tunda ya zauna a 'kasa ya kasa d'agowa, kanshi na sunkuye har yanzu, banda kuka da nadama babu abinda yake.



Abba ne ya taka yaje har inda Dad yake ya tsugunna, sannan ya kalleshi yace "abokina dan Allah ba dan ni ba ina ro'konka ka manta da komai, karka sashi a ranka, ka tashi muje, tashi," Abba ya kama mishi hannu Dad ya mi'ke suka fito daga gidan suka shisshiga motoci suka tayar suka d'auki hanyar gidan.



Kai tsaye gidan Abba suka wuce domin har yanzu basu 'karasa shiryawa su Dad kayansu ba a d'ayan gidan.



Kowa ya samu waje aka zazzauna a kujeru, aka ci aka sha amma banda Dad domin shi har yanzu kuka yake.



Abba ne ya kalli Dad yace "abokina ya bayan saduwa?" shiru ba amsa kuka kawai yake yi, Abba yai murmushi tare da girgiza kai, sannan yace "wallahi duk wad'annan abubuwan da suka faru ban ri'kesu a raina ba, illah dai abu biyu da kayi a lokacin da kake mulkar 'kasa wanda banji dad'insa ba, kuma shine ma zan iya cewa dalilin da yasa na sake tsayawa zab'e a karo na biyu kuma Allah ya sake bani nasara na sake zama matsayin shugaban 'kasan da nake kai a yanzu, saboda mutane sun koka lokacin mulkinka wanda ni sam banyi tsammanin hakan daga gareka ba, shugabanci fa bawai kaci kasha bane kuma ka gina kanka da iyalenka, a'a amana ne ake d'auka a baka na kula da dukiyar talakawa tare da bincikar matsalolinsu da magance musu, amma yanzu shugabbani ba abinda suka sani sai gina kansu da 'yan'uwansu da iyalensu, wanda su basu sani ba yin hakan da suke kashe kansu suke domin mulki babban abune wanda ya tafiyar dashi dai-dai ya dace, wanda yayi son ranshi ya cuci al'umma kuma ya cuci kanshi kuma ya tab'e duniya da lahira, sannan bayan haka kana 'kyamar talaka tare da guje musu kuma a matsayinka na wakilinsu, to tayaya zaka san damuwoyinsu balle har kai musu maganinta, wad'annan dalilan biyu su suka b'atamin rai har kaga na fita harkarka, domin ni a rayuwa banaso inga ana zaluntar talaka, kuma kai shaida ne ka sani sanadina suka zab'eka, amma komai ya wuce tunda gashi ma har nazo gidanka."



Uncle yai gyaran murya sannan ya kalli Dad yace "d'an'uwa kaga abinda nake fad'a maka ko, kaga irin ranar da nake guje maka zuwanta ko, ranar nadama da jin kunya mara iyaka, ba kai kad'ai ba wallahi mu kanmu kasa kunyar bawan Allahn nan mukeji, kaga illar wula'kanta d'an adam ko, gashi ya jawo maka kaje ka tozarta d'an wanda yai maka rana a rayuwa, d'an wanda yai maka halaccin da kai ka kasa rama mishi, shiyasa ba'a so ka wula'kanta mutum a rayuwa saboda komai talaucinsa to yana da darajarsa, kuma Allah ya karrama duk wani d'an adam sannan ya fifita matsayin mu fiye da halittun duniya."



Abba yace "duk kubar wannan maganar, duk abinda ya faru ni sai jiya ma nake ji, wallahi ni ya wuce a wajena, kuma ban ri'keshi akan wannan maganar ba."



Mahaifiyar Amira ha'kurarrar baiwar Allah, sai yanzu ta bud'a baki tai magana, tace "zafin zuciyarka da tsananta abinda be kai ya kawo ba da 'kin d'aukar shawara duk shi ya kawomu ga kaiwa wannan matakin, duk abinda ya faru ba kowa bane ya jawo sai kai da kanka, kuma ba komai bane sila illah alhakin bawan Allahn nan Amir da ka d'auka."




Amira cikin kuka itama ta amshe tana cewa "Dad kaga ikon Allah ko, yau gamu a 'kar'kashin wad'anda ka zalunci d'ansu ka tozarta rayuwarsa tare da nuna mishi tsana me tsanani, ashema d'an abokinka ne, amma da Allah ya tashi nuna maka aya da ishara sai ya turo mutanen da ka yarda dasu wato su Nura da mahaifinsa suka yashe maka komai da ka mallaka suka talautaka gashi yau har wajen zama yana nema ya gagaremu sai da Allah ya kawomu gidan iyayen talakan nan kuma matsiyaci sun taimaka maka da wajen zama kai da iyalinka, yanzu wa gari ya waya tsakanin kai da shi, Dad kud'i sunsa ka shagalta da duniya har ka manta cewa wata rana ranka ma zaka iya rasashi a binneka ba tare da dukiyar da kake wula'kanta mutane dominta ba, kuma ka manta cewa da ranka ma in Allah yaso zai iya 'kwace duk abinda ya mallaka maka, dama ai komai na Allah ne, baka yayi domin yaga yanda zaka tafiyar da ita, sai gashi lokaci guda wanda in na rantse ko kaffara bazanyi ba idan nace kwata-kwata baka tab'a sawa ranka akwai kwatan-kwacin hakan zai faru dakai a rayuwarka ba, yanzu baka ji kunya ba, wanda ka d'auka 'kas'kantacce ashe mahaifinshi ya fika matsayi da dukiyar da kake gadara da ita, hasali ma shine silar duk wani arzi'ki da kake tin'kaho dashi, tana kai nan a zancenta ta sake fashewa da kuka.



Abba ya d'ago kai ya kallesu dukkansu sannan yace "banji dad'in jin irin wad'annan maganganun ba daga bakinku, musamman ma ke Amira, uba ubane fa ko me ya zama kuwa wannan sunanshi na uba a gareki bai tab'a canzawa, akwai hanyoyi da sigar da addini ya warewa 'ya'ya suyi magana da iyayensu, ba irin wanda kikai magana da mahaifinki ba a yanzu saboda haka ki bawa mahaifinki ha'kuri."



Amira ta bawa mahaifinta ha'kuri cikin kuka.



Amir ya tashi ya taka har gaban Dad ya tsugunna, tare da dafa hannun Dad d'in yace "Dad ka umurceni da in nemo iyayena in na kawosu zaka yarda da aurena da Amira, kuma gasu a gabanka a yanzu na kawosu, ashema kunsan juna, Dad dole zan gode maka akan abu d'aya in kuma ro'keka abu guda, na farko ina godiya ga Allah da ya bayyana min iyayena, sannan ina gode maka kaima domin kaine silar jajircewata wajen fita nemansu wanda ta sanadin hakan ne har Allah ya had'ani dasu, sai abu na biyu shine dan Allah Dad ina ro'konka ko sau d'aya ka soni kuma ka karb'eni a matsayin sirikinka kuma ka sa wa aurenmu albarka," ya 'karasa maganar yana mai had'a hannayenshi biyu tare da cigaba da ro'konsa.



Cikin sauri Dad ya d'ago kai tare da ri'ke hannayen Amir, yana cigaba da kuka mai matu'kar sauti, yana fad'in "kai ba siriki bane kad'ai a wajena kai d'ana ne, dan Allah Amir ku yafe min, tabbas na zalunceku na zalunci kaina, gashi yau ina cike da nadama da kuma jin kunya wanda bazan tab'a mantawa dashi ba, kuma bazai goge a raina ba" kuka ya cigaba da yi sosai yana kuma cigaba da magiya akan a yafe mishi.



Shi kuwa Amir wani irin farin ciki yaji wai yau gashi ga mahaifin Amira kuma har yana ri'ke mishi hannaye, itama haka Amira hakan ya tabbatar mata da mahaifinta yai nadama.



Dad ya kalli iyayen Amir yace "kun ganshi nan ya nuna Amir da hannu yace kullum burinshi ya kare rayuwar iyalaina da na 'yata Amira, akan hakan be damu ba ya rayu ko ya rasa ranshi, amma ni kullum burina bai wuce naga na rabashi da 'yata kuma in nisantashi da duniyar ba," ya sake fashewa da kuka me matu'kar ban tausayi.



Abba yai gyaran murya sannan yace "abokina dan girman Allah kai shiru haka nan, damuwar nan zata iya jefaka cikin wani hali, ni wallahi ban ri'keka ba, ka sanni ka san halina bani da ri'ko, mu munzo ne mu gaisheku muka tarar da wannan al'amari ba nufinmu azo aita tayarda abinda ya riga da ya wuce ba, dan haka abar maganar daga yanzu ta wuce kar wanda ya sake tayar da ita."




Abba ya cigaba da fad'in "ga gida nan da ke kusa da wannan, yafi wannan da nake zaune kyau da girma ka zauna kai da iyalinka, kuma na baka shi duniya da lahira takardun na wajen 'kaninmu na bashi ya baka, makullan gidan kuma duk suna wajen masu shirya gidan, kuma nasan yanzu haka sun kammala komai kuna iya zuwa ku duba in be yiba a canza wani."



Nan ma Dad kuka yasa yana godiya yana kuka matarshi da Uncle suna tayashi godiyar.



Bayan sun gama godiyar sukai musu sallama sannan suka tafi nasu sabon gidan da ya zama mallakinsu.



Washe gari wajen 'karfe d'aya su Dad suka 'kara shigowa cikin gidan Abba, bayan sun gaisa suka sake yi musu godiya, Abba yace "bakomai yiwa kaine."



Dad yace "ina d'ana Amir yake?" Abba yace "suna can shi da matarshi suna had'a mana kaya gobe zamu koma Abuja gabad'ayanmu harda su."



Ana cikin maganarsu sai gasu sun fito da gudu Amira ce ke gudun neman wajen b'uya Amir na biye da ita yana fad'in "wallahi ki tsaya in rama".



Amira ta b'oye bayan Umma tana cewa "Umma kinga Amir ko ya lakuce min hanci ni kuma na murd'e mishi kunne shine wai sai ya rama."



Umma tace "shi ya isa ma ya tab'a min ke."



Dad yana dariya yace "zo nan kaji Yarona barta zatazo hannunmu ne mu rama wata rana."



Amir jin abun yayi banbarakwai, to be saba ba, ya 'karasa wajen Dad ya zauna a 'kasa ya gaishe da Dad, Dad ya amsa tare da d'agashi ya zaunar dashi a kusa da shi, sannan ya kalli Abba yace "ina ro'kon alfarma ka barmin yarannan a nan su zauna a gidanmu su saba da ni nima."



Abba yace "haba abokina menene na neman alfarma kuma kai da 'ya'yanka, ai ba wani abu su zauna d'in, dama naga kamar sunfi son zaman kanon," Amir ya mi'ke cikin sauri yace "yauwa to tunda mu mun fasa tafiya bari inje in cire kayanmu cikin naku," ya juya ya tafi," Amira ma ta mi'ke tana fad'in "eh wallahi muje na tayaka," dukkansu iyayen nasu suka bisu da idanu suna dariya, Abba yace "dama na fad'a maka sunfi son zaman nan."



Washe gari Abba ya kira Uncle ya bashi kyautar gidan da suke ciki, yace in su Amira sun koma gidan Dad da zama ya dawo nan ya zauna da iyalansa ya bashi halak malak, nan Uncle yaita godiya yana kuka yana fad'in "yau ka yimin abinda d'an uwana na jini ma ya kasa yimin."



Abba yace "ka daina fad'in haka, ai nima d'an uwanka ne na jini, d'an uwa ba sai wanda kuka fito ciki d'aya ba kad'ai yake zama d'an uwa, bare ma yana zama d'an uwa na jini wallahi, to ni haka nake kallonku, ina fatan kuma zaku d'aukeni a haka."



Uncle yai murmushi, sannan yace "wallahi d'an uwa kai na musamman ne, samun irinka sai an tona."




A tare suka shiga gidan Dad Uncle ya fad'a musu abin arzi'kin da akai mishi suka tayashi yin godiya, sannan suka yi musu sallama suka tafi, su Amira sune 'yan rakiyar filin jirgi.








Muje zuwa









*πŸ…±K CE*πŸ˜˜πŸ’‹
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜





RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (πŸ…±K*
```(Autar marubuta)```






SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
```(Mamie)```






*πŸ‡ΈπŸ‡¦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```πŸ€œπŸ€›







PAGE 220 to 225







Bayan su Amir sun koma gidan su Dad da zama shi kuma Uncle ya d'auko matarshi da yaranshi suka dawo gidan da Abba ya basu halak malak, basu ri'ko komai ba kansu kawai suka kai, domin yace ya basu harda komai na gidan duk ya zama mallakinsu, a ranar da suka koma gidan ma saida Uncle yai kuka, tunani yake wai shine yau da wannan tafkeken gidan da kaya na alfarma ga kuma masu aiki da masu gadi, abinda ya kamata ace d'an uwanshi yayi mishi tun lokacin da yake da d'aukakar da kuma tarin dukiyar, gashi nan yanzu be ciba be bari sun mora ba wasu 'kattin banza sunzo sun yashe, ya dad'e yana takaicin wannan abu wai ace d'an uwanka yana da abu amma bazai iya taimakonka ba se wani bare can wanda basu had'a komai ba, nan dai yaci kukanshi matarsa na rarrashi sannan ya 'kara yiwa Allah godiya tare da zubawa Abba Ahmad addu'o'i.




Bayan komawar su Abba da sati d'aya, yau juma'a dawowar su Dad da Uncle da Amir kenan daga masallacin juma'a.



Yanzu kam halayen Dad gaba d'aya sun sauya, wani irin sabon tattali da 'kauna yake nunawa Amir, domin a yanzu ya tabbatar babu wanda yake 'kaunarsu da gaskiya sama dashi, kuma ya fahimci cewa ba'a sakaci da samun masoya na 'kwarai saboda ko ba komai duk halin da ka shiga sune basu gudunka, kuma irinsu ne suka yi 'karanci yanzu a duniya.



Shi kanshi Dad d'in a yanzu yafi jin dad'in rayuwarshi fiye da da.



Tun Amir yana d'ari-d'ari dashi har yazo ya saki jiki domin duk inda zasu tare suke zuwa hatta wajen motsa jiki, sha'kuwa sukai ta ban mamaki a tsakaninsu.




Yau ma bayan sallar la'asar Dad ne da Amir a wani fili na cikin gidan sunata buga 'kwallo.



Amira ce ta fito daga cikin gidan itama tana neman su Amir d'in, hangosu tayi sunata faman buga 'kwallo cikin nishad'i da kwanciyar hankali, tsayawa tayi tana kallonsu, fuskarta d'auke da murmushin dake bayyanar da farin cikinta.



'Karasawa cikin wajen tayi, saida ta shiga tsakiyar filin sannan taja ta tsaya tana kallonsu.



Dad yace "Doughter matsa mana," Amir shima yai magana "matsa mana ko so kike kija Dad ya cinyeni?"



Amira tace "Allah nima dani za'ayi 'kwallon," Amir ya kalli Dad, shima Dad ya kalli Amir suka kece da dariya suna yi suna nunata.



Amira tazo iya wuya, sai ta zauna ma a tsakiyar filin tare da sake murtuke fuska, su san cewa lallai da gaske take, tace "wallahi in dai bakuyi dani ba to kun gama wasan daga yanzu."



Dad ya 'karaso inda take tare da 'kunshe dariyarsa, yana 'karasowa ya dafata yace "kwantar da hankalinki, jeki ki kirawo Mum d'inki tazo ayi da ita, saboda ban yarda ku had'e min kai ba kuita yi ku biyu kuna cinyeni, gwara matana tazo ku biyu mu biyu."



Amira kuwa da gudunta ta shiga cikin gida Amir shima ya biyota ta jawo Mum d'inta tana fad'in "Mum zo muje," Mum tace "ke sakeni, ina zamuje kuma, ina zaki kaini?"



Amira bata fasa janta ba tace " kedai kizo muje kawai koma menene zaki gani, saida sukaje filin sannan Amira tace "'kwallo zamuyi kina b'angaren Dad, ni ina b'angaren Amir."



Mum kuwa ta biye mata, 'yan gidan gabada'aya da security's da masu aiki sukazo suka zagayesu suna kallo domin suga yanda za'a 'kare, aka karkasu, Dad da Mum, Amir da Amira.



Nan aka fara buga wasa duk wanda yaci sai tsalle da murna, idan su Amir sukaci sai su rungume juna shi da Amira suna murna, idan su Dad ne sukaci suma haka sukeyi, rungume juna sukeyi suna murna.



Haka sukaita yi gwanin ban sha'awa sai burge jama'ar gidan suke yi, bama su kad'ai ba kowa ji yake yi inama shine yake tare da iyalanshi haka.



Haka sukaita yi har sukayi lilis, kuma a lokacin Amir da Amira sunci su Dad wajen sau takwas su kuma Dad d'in suna da uku, su Amira sun fisu da biyar kenan, a haka aka tashi su Dad suna fad'in Allah ya kaimu na gaba zamu rama, su Amir na yi musu gwalo suna fad'in zasu rame dai.



Haka rayuwarsu ta cigaba da kasancewa gwanin ban

29 / 31