Author : Bilkisu Z Ya'u Category : Romantic Hausa Novels
ya kwanta musamman ma Amira wadda ta kasa zaune ta kasa tsaye, banda kuka babu abinda takeyi, ita zuciyarta kawai bata takeyi Amir d'inta ya rasu, saida taji bayanin Doctor d'in sannan hankalinta ya kwanta.
Amira cikin sauri ta fad'a d'akin da aka maida Amir, Uncle da Doctor suka bita da ido, Doctor yace "hala wancan majinyacin mijinta ne?" Uncle yace "eh Doctor," Doctor yace "haba shiyasa naga gabad'aya bata cikin hayyacinta," dukkansu sukayi murmushi, sannan ya umurci Uncle da ya bishi office akwai magungunan da za'a nemo da ya tashi a bashi koda ruwan tea ne sai a bashi magungunan yasha, Amira na shiga d'akin ta 'karasa kusa da bakin gadon da yake kwance, kara kanta tayi dai-dai saitin 'kirjinsa ta tabbatar da abinda likita ya fad'a musu sannan ta numfasa kuma ta yarda da ranshi, sai ta samu waje ta zauna.
Ta ri'ko hannunshi ta had'a da nata tana zubar da hawaye ta fara magana ita kad'ai, "Amir d'ina kayi ha'kuri ka yafe min, tunda ka had'u dani kake fuskantar barazana a kaina na rasa rayuwarka, amma koda wasa hakan baisa ka 'kini ba saima 'kara 'kaunata da kake, kuma har kullum burinka ka tseratar da tawa rayuwar daga fad'awa cikin halaka, ba dan komai ba sai dan saboda in ka rasani kaima bazaka iya cigaba da rayuwa ba, wallahi ko a tarihin masoya banga kamarka ba Amir wanda zai yarda ya mutu domin ceto ran wanda yake so," tana kai nan a zancenta ta sake fashewa da kuka matsananci.
Turo 'kofa aka yi aka shigo, Uncle ne shi da likita, Uncle ne ya kalleta ya fara fad'a yana fad'in "haba Amira ke da zakiy wa Allah godiya Amir d'inki yana raye sai ki zauna kina ta faman kuka," sannan ya cigaba da rarrashinta likita yana tayashi har tayi shiru, sannan likita ya kalli Amira yana murmushi yace "ranki ya dad'e kema ina ganin baki gado zamuyi mui jinyarku a tare," gaba d'aya dariya suka sa harda Amiran, haka likitan nan yaita sa Amira dariya da yake mutum ne shi me barkwanci.
Bayan 'yan awanni sai Amir ya farfad'o, wayyo masu karatu kar kuso kuga farin ciki gun Amira, sai nan nan take dashi, ko yaya taga ya yamutsa fuska itama sai ta canza ta-ta fuskar, nan da nan ta had'a mishi tea ta bashi yasha, sannan yasha magungunanshi, akai mishi allura cikin 'kan'kanin lokaci ya koma bacci.
Bayan komawar Amir bacci Uncle yacewa Amira zai tafi gida domin sanar dasu halin da ake ciki, suka yi sallama da Amira ta fad'a mishi abubuwan da take so a taho mata dasu in zasu dawo.
Ko da Uncle ya koma gida ya tarar da Dad ba lafiya shima jikinshi har yai zafi, kuma anyi anyi dashi ya bari a kaishi asibiti ya'ki yarda.
Dole haka nan Uncle ya kira Doctor yazo har gida ya dudduba shi, anan ne ya tabbatar musu da cewa jininshi ya hau, ya kamata ya rage damuwa da tunani da sauransu.
Ko da Doctor ya tafi Uncle ya je rakashi, ko da ya dawo ya tarar Dad ya samu bacci.
Mum d'in Amira ta kalli Uncle tace "sannu da 'ko'kari, Allah dai ya biyaka, ya kamata dai kaje ka huta," nan ya fad'a mata Amir ya farfad'o, ya kuma sanar da ita asibitin da yake, sannan ya fad'a mata sa'konnin da Amira tace akai mata.
Mum ta tashi ta haye sama d'akin Amira ta dubo sa'konnin ta kawo aka baiwa driver yaje ya kai mata, Mum kenan ha'kurarriyar mata, Allah ya sa mata ha'kuri da juriya dan da bata da su miji irin Dad kam da tuni ta fece.
Bayan kwana biyu jikin Dad yai sau'ki har Amira ma ta samu labari tazo ta dubashi ta koma.
Dad ne zaune a d'akinsa gefenshi kuma Uncle ne, sai d'aya b'angaren matarshi ce Mum d'in Amira.
Dad ya kallesu d'aya bayan d'aya sannan yace "abinda yasa nace kuzo shine kan maganar wad'annan yaran ne, ni bazan hana Amira komawa gidan Amir ba, amma ku shaida musu da ita da shi kanshi mijin nata kar su sake takowa inda nake, duk wannan halin da nake ciki ba komai bane ya jawo min illah wannan talakan yaron Amir me 'kashin arzi'ki, dan haka ku fad'a mishi karsu sake takowa inda nake."
Mum cikin zubar da hawaye tace "wai dan Allah sai yaushe zaka sauya ne, wannan ba'kar a'kidar da canfe-canfen marasa tushe ba zaka barsu ba ko, yanzu duk abinda ya faru dakai bai zame maka ishara ba."
Uncle shima ya d'auka yace "maganar gaskiya banji dad'in maganganunka ba wallahi, nai tunanin wad'annan abubuwan da suka faru zasu zama ishara a gareka, meyasa kake wa yaron nan irin wannan tsanar ne haka, wallahi yaron nan ba ma'kiyinmu bane masoyinmu ne, hasalima alkhairi ne a garemu tunda shine sanadin kub'utarku daga hannun wad'ancan azzaluman, su ya kamata ka tsana kuma kaji haushi ba wanda ya sadaukar da ranshi saboda kai da 'yarka ba," Dad cikin tsawa yace "sadaukar da ranshi na banza, ya barni su kasheni mana, ko menene indai daga gareshi ne bana 'kaunarsa, kuma na gama yanke hukunci."
Uncle ya mi'ke tsaye dan har ga Allah halin d'an uwan nashi ya fara bashi haushi, sannan yace "Allah ya kyauta, kadai yi tunani kar gaba kaji kunya da nadama mara iyaka," Dad yace "ba wata nadama da zanyi hukunci kuma babu sauyi."
Uncle bai sake waiwayowa ba kuma bai sake cewa komai ba ya fice daga d'akin, zama yayi a falo yana 'kara jin takaicin hali irin na d'an uwan nasa.
Mum ce ta fito daga cikin d'akin itama tana share hawaye, zata wuce Uncle ya kalleta yace "ki cigaba da ha'kuri da halin d'an uwana, wata rana sai labari, yanzu ma zanje can wajen su Amiran in dubo halin da suke ciki."
Mum tace "to bakomai nagode, in kaje ka gaishe su," sannan ta wuce sashenta.
Daga nan Uncle asibiti ya nufa, kuma sai yaje a dai-dai an basu sallama Amira nata faman had'a kayansu waje guda.
Bayan sun gaishe da Uncle yaiwa Amir ya jiki sannan suka shaida mishi maganar sallamar.
Uncle yai shiru yana nazarin yanda zai fad'a musu maganar Dad, amma ba yanda ya iya tunda baida muhalli nashi na kanshi da zai kaisu, haka nan ya daure ya sanar dasu sa'kon Dad amma be fad'a musu cewan da yayi shigowar Amir rayuwarsu shine sanadin faruwar komai, sannan ya kalli Amir yace "ka cigaba da ha'kuri da halin sirikinka Amir wata rana komai zai wuce, yanzu ka kaita mazauninka gidan da kake zaune nima zan biku inga wajen, gobe in Allah ya kaimu zanzo muje wata kotu da take nan kusa damu muga wani malami kuma al'kali domin jin abinda ya kamata dangane da hanyoyin da za'a bi domin komawar aurenku.
Jin wannan kyakkyawan labarin na komawar aurensu shi ya wanke damuwar da suka shiga na maganar Dad, sunyi farin ciki sosai daga 'karshe suka yi mishi godiya.
Da yake a motarshi yazo sai suka shiga tasu shima ya shiga tashi suka tafi har gidan su Amir.
Ganin 'kerarre kuma katafaren gidan da ya kutsa dasu ya d'aure musu kai.
Suna fitowa ma'aikata da masu tsaro birjik ta ko'ina sai kwasar gaisuwa suke yi.
Saida suka d'an yi tafiya mai tsawo sannan suka isa babban falon gidan.
Bayan sun zauna aka cika gabansu da kayan ciye-ciye kala-kala, Uncle dai kasa ha'kuri yayi yace "wai ni kam Amir gidan su wa ka kawomu ne?"
Amir yai murmushi, sannan yace "wannan d'aya daga cikin gidajen mahaifina ne, mahaifina shine shugaban 'kasar nan na yanzu."
Uncle ya jinjina kai yana 'kara jin hukunci irin na mahalicci, a yayin da ita kuma Amira ta zazzaro idanu amma bata ce komai ba.
Uncle ya tayashi murnar ganin iyayenshi sannan ya mi'ke yace shi zai tafi gobe su shirya da wuri, suka yi mishi godiya sannan suka rakashi har bakin motarshi, saida ya tafi suka dawo cikin falon suka zauna suna hira.
Muje zuwa
*π
±K CE*ππ
ππππππππππ
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
ππππππππππ
RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (π
±K*
```(Autar marubuta)```
SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
```(Mamie)```
*πΈπ¦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```π€π€
PAGE 210 to 215
Bayan sun raka Uncle bakin motarshi ya tafi sai suka dawo cikin falo Amir ya zauna kan kujera, Amira ta fad'a kan jikin Amir tana fad'in "Amir d'ina ka yimin laifi, baka fad'amin Daddynmu shugaban 'kasa bane, kuma baka tab'a had'amu koda a waya ba mun gaisa."
Amir ya d'agata daga jikinshi yana kallonta itama shi take kallo tana neman 'karin bayani akan d'agata daga jikinshi da yayi, ya harareta, sannan yace "dallah d'agani bakisan ke yanzu matar maza biyu bace," ya 'karashe maganar tare da murgud'a mata baki.
Amira ta 'kyal'kyace da dariya, yanda taga yayi maganar cikin turo da baki harda su harara da murgud'a baki, ta sake fad'awa jikinshi sannan tace "wallahi ni mijina d'aya ne tak a duniya har lahira ma insha Allah kuma gashi nan a tare dani."
ya sake turota tare da sake cewa "dallah d'agani," itama turo baki tayi tace "ni wallahi ka daina tureni daga kan jikinka," dariya yai mata tare da yi mata gwalo ta mi'ke zata kai mishi duka, ya tashi ya gudu cikin d'aki itama ta bishi suna tsere.
*WASHE GARI*
Washe gari Uncle yazo dama su tuni sun shirya shi suke jira, babu b'ata lokaci suka tafi.
To dama a addinance mun sani idan irin haka ta faru mata ake baiwa zab'i ta zab'a a cikinsu wanda tafi 'kaunar zama tare dashi, kuma ba wanda ta zab'a sai Amir, dan haka aka 'karashe duk wasu abubuwa da addini ya tanadar cikin lokaci 'kan'kani aka maida auren Amira kan Amir.
Suka cigaba da zamansu cikin jin dad'i da kwanciyar hankali.
Zaune suke a falo suna hira Amira ta kalli Amir tace "wallahi Uncle yanada kirki, ina ma shine mahaifina ba Dad ba."
Amir ya rufe mata baki, sannan yace "ki daina fad'in haka, Dad ne Allah ya hukunta matsayin mahaifinki, kuma bai tab'a canzawa daga wannan matsayin a wajenki, kuma shima Uncle ai matsayin uba yake a garemu, dan haka dukkaninsu iyayenmu ne."
Amira ta kalli Amir tace "Amir d'ina dan Allah kayi ha'kuri akan irin abinda mahaifina yake maka, kuma ina 'kara godiya a gareka da sadaukar da rayuwarka da kayi wajen ceto tawa rayuwar da ta 'yan'uwana."
Amir yace "Amirata karki damu da duk abinda Dad yake a kaina, ai nima wallahi Dad mahaifine a gareni, kuma mahaifi yanada damar yin komai akan yaranshi, kuma ni inhar za'a barni na rayu dake to komaima ai mini wallahi bazai dameni ba zan jure tunda ina tare dake, dan haka karki damu, sannan kuma ki daina godemin, idan na ceto ranki rayuwata na ceta domin ban iya cigaba da numfashi in babu ke a tare dani, dan haka a shirye nake da in cigaba da sadaukar da tawa rayuwar domin ceto rayuwarki, karki manta raina fansa ne a gareki Amirata."
Sun dad'e suna hirarsu cikin nishad'i da walwala.
Haka rayuwarsu ta cigaba da kasancewa gwanin ban sha'awa, koda yaushe Amir suna waya da iyayenshi, kuma tun a waya ya basu kyakkyawan labari game da bayyanar Amira gareshi da kuma maida aurensu, hakan yasa sukace suma suna nan tafe kwanan nan zasu zo suga surikarsu daga nan su koma tare dasu Abuja gabad'aya.
Bayan sati d'aya da dawowar auren su Amir suka shirya domin suje su gaishe da su Dad, sedai sunyi dana sanin zuwansu gidan, domin Dad korar kare yai musu tare da kashedin kar su sake zuwar mishi gida yai musu kaca-kaca, yace Amir shine sanadin duk wani halin da yake ciki, da be rab'eshi ba da duk hakan be faru dashi ba, wanda yasa har suka koma gida Amira na kuka, shi kuwa Amir idanunshi sunyi ja kamar me ciwon ido saboda tsananin b'acin rai.
Amira taso ta fad'awa Dad d'inta ko Amir d'an waye, Amir shi ya kwab'eta tare da hanata.
Bayan sun koma gida Amira taci kuka kamar me, shi kuwa Amir ba kukan sai tsabar jan ido da zafi da zuciyarshi ke mishi.
Komawa kusa da ita yayi ya fara rarrashinta, da 'kyar ya samu tai shiru sai ajiyar zuciya take yi.
Tun daga wannan ranar su Amir suka fita harkar su Dad d'in suma, basu sake bi ta kansu ba.
*BAYAN WATA UKU*
Amir ne zaune yana chat a waya, sai ga Amira ta fito daga cikin d'aki itama ta zauna kusa dashi takai hannunta tana 'ko'karin le'ka wayar taga me yake yi, sai yai sauri ya kawar da wayar tare da cewa "matsa karki gane min sirri," ai kuwa Amira ta dage tana 'ko'karin saita 'kwace wayar daga hannunshi tana fad'in "bani wayar nan in gani da waye kake chat?"
Amir ya tashi yana b'ob'b'oyewa suka fara zagaye d'akin Amira ta dage sai ta 'kwaci waya daga hannunshi suna cikin wannan yanayin suka ji sallamar su Abba da Umma, bayansu kuma wasu daga cikin masu tsaron lafiyarsu ne ke take musu baya.
Amira ce ta kwasa da gudu taje ta rungume Umma tana masu oyoyo, shi kuma Amir yaje ya rungume Abban shi, sannan suka je suka zazzauna kan kujeru.
Nan suka gaggaisa, sannan aka cika musu gabansu da kayan ciye-ciye kala-kala.
Amir dake lafe cikin jikin Abba yace "Abba yanzu ashe kun taho shine ko ku fad'a mana muje mu taroku."
Umma tace "to in banda kai da abunka yaron kirki ba gashi yanzu kaji dad'in ganinmu ba, dama so muke muyi muku bazata shiyasa muka zo ba tare da mun sanar daku ba."
Amir ya kalli Umma sannan ya kalli Amira dake lafe itama a jikin Umma, sai ya tashi yaje kusa da Umman yana 'ko'karin d'aga Amira daga jikin Umma yana cewa "dallah tashi nima in kwanta ai ba Ummanki bace ke kad'ai."
Amira ta 'kara ri'ke Umma tamau tana fad'in "wallahi bazan d'agata ba ai ba Ummanka bace kai kad'ai."
Abba da Umma sai dariya sukeyi, can sai Abba ya taso yace "ku tsaya wallahi in kuka b'allamin mata ba 'kyaleku zanyi ba duk sai na kulleku," dukkansu suka sa dariya.
Abba ya zauna gefen matarshi sannan yace wa Amir ya 'kyalesu yazo wajenshi ya zauna, haka kuwa akayi ya tafi kusa da Dad d'inshi ya zauna, suka cigaba da hira abinsu cikin jin dad'i, iyayen Amir sunyi farin ciki sosai da ganin yaran nasu cikin kwanciyar hankali, da kuma samun suruka me kirki, haka itama Amira da ka kalleta kasan tana cikin farin cikin samun iyayen miji nagartattu, kuma masu kirki da sau'kin kai.
*BAYAN SATI 'DAYA*
Su Abba ne zaune gabad'ayansu suna hira.
Abba ya kalli su Amira da Amir yace "ya kamata fa ku kaimu wajen iyayen Amira domin muyi musu godiya."
Amira da Amir nan take suka canza fuska, Umma ta kallesu tace "ya haka daga yi muku maganar zuwa gaisawa da iyayenku na nan kano duk kun canza fuska?"
Amira ta mi'ke tsaye sannan tace "gaskiya ni Abba ba inda zanje, tunda su suka zab'i barinmu me zamu je muyi musu," tana gama fad'in haka ta juya ta shige cikin d'aki abinta, su Abba da Umma kuwa suka bita da idanu suna mamakin abubuwan da take fad'i.
Abba ya juyo da kallonshi kan Amir yace "Amir wai meke faruwa ne, kai mana bayani, wani abun ya faru ne tsakaninka da surukanka?"
Amir ya gyara zama sannan yai murmushi, yace "Abba bafa wani abu bane Amira ta zafafa shi haka," nan Amir ya kwashe duk abubuwan da suka faru tun daga farko har 'karshe ya fad'a musu.
Sun dad'e suna jinjina wannan lamari sosai, suna kuma mamakin irin tsanar da Dad ke gwada wa Amir haka, sannan sun jinjina tsananin ha'kuri da Amir yayi.
Umma cikin fushi tace " wannan wane irin mutum ne haka, gaskiya baida imani, kuma babu inda zamuje saboda zuwa wajenshi baida amfani, me zai kaimu gun mutumin da yaci zarafin d'anmu haka, an fad'a mishi kai d'in 'kas'kantaccen mutum ne, dama ance rashin sani yafi dare duhu, wallahi da yasan kai waye da ko da kud'i akace kallon banza wannan yai maka bazai yi maka ba."
Abba ya kalleta yai murmushi, sannan yace "yi ha'kuri my love, ya kamata kiyi tunani kiy nazari ki gani koma menene mahaifin Amira yai mana ya kula da d'anmu a baya, kuma bayan haka Allah ya riga da ya had'amu tunda ga 'yarsu tana auren d'anmu, kinga kuwa an had'u had'uwar da babu ranar rabuwa, ni kaina abinda aka yiwa Amir naji ciwonshi a raina fiye da tunaninki, amma dole in muna so Allah ya yafe mana muma mu zamto masu afuwa akoda yaushe, kuma karmu ri'ka manta alkhairin mutum komai 'kan'kantarsa."
Abba ya numfasa sannan ya cigaba da cewa "Amir kiramin matarka," Amir ya tashi yaje ya kira Amira suka dawo cikin falon tare.
Abba ya kalli Amira yace "Daughter kiyi ha'kuri kinji akan d'an wannan abun banaso ki 'kara tayar da hankalinki balle har ki furta makamancin haka, gobe in Allah ya kaimu zamu je gidanku insha Allah domin mu gaisa da iyayenki."
Da ace Amira zata iya yiwa Abba musu to tabbas akan wannan maganar yau da tayi mishi, amma bata tab'a iya jayayya dashi saboda darajarshi da kimarshi a idanunta, shiyasa ba yanda ta iya, kanta na sunkuye tace "to Abba Allah ya kaimu."
Amir yai wani dogon numfashi sannan yace "lallai mun gode Allah Abba kaci sa'a," Amira ta harari Amir, shi kuma ya kwashe mata da dariya.
Washe gari dukkansu suka shirya suka tafi gidan su Dad.
Suna isowa suka tarar da kayan su Dad birjik a 'kofar gida ana watso musu, koda su Abba suka tambaya aka shaida musu wad'anda su Nura suka siyarwa da gidan ne suka gaji da d'aga musu 'kafa yau sukazo suke musu watsi da kaya.
Cikin gidan suka 'karasa dukkanin 'yan gidan suna tsaye a falo suna kallon sarautar Allah, Dad kuwa