SO MAHADIN RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVELS PDF BY BILKISU Z YAU.txt

Author :  Bilkisu Z Ya'u Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   31 / 31

90K to 90.7K   out of 90.7K words

lafiyar matarshi sannan ya karb'i Baby, shima saida aka sake biyoshi da su, sannan yai musu Addu'a tare da rad'a musu suna, inda jaririyar taci sunan mahaifiyar Amira. Jaririn kuma yaci sunan Dad mahaifin Amira








Haka rayuwar bayin Allahn nan ta cigaba da kasancewa cikin jin dad'i da kwanciyar hankali.




Amir ne kwance akan gado yana fuskantar inda Amira take kwance, kallonshi itama Amiran take, tayi murmushi sannan tace " menene kake kallona?" 'kaunarki nakeyi Amirata, wallahi 'kaunarki kullum 'kara zama sabuwa take cikin raina, akoda yaushe dare da rana safe da yamma ina ro'kon Allah yasa in rayu kuma in mutu da 'kaunarki cikin raina."



Amira tai murmushi, sannan tace "wallahi na dad'e da yarda da 'kaunar da kake yimin Amir, shiyasa nake jina kamar wata basarakiya, saboda gani nake nafi matan duniya dace da sadaukin maza me yin 'kauna ta gaske, shiyasa nake kaf kaf dakai saboda darajarka gareni," Amir yai murmushi sannan yace "to saki ranki daina kaffa kaffa duk duniya bayan ke babu 'yar da zata burgeni har in sata a raina bayan ke."



Amira tace "Alhamdulillah, nagodewa Allah da ya had'a zuciyarmu da rayuwarmu waje guda."



Haka suka cigaba da fad'awa juna zantukan soyayya har bacci ya d'aukesu.







ALHAMDULILLAHI RABBIL ALAMEEN👏



*Dama haka rayuwa take ma'kiyinka sai ya dawo masoyinka na kusa kusa ma, shiyasa akace ka'ki mutum 'ki kadan saboda wata rana zai zama masoyinka kamar yanda Dad da Insp Yahya suka zama masoyan Amir, haka kuma in zaka so mutum ka soshu kad'an domin zai iya zama ma'kiyinka na ha'ki'ka kamar yanda Baban Nura da Nura suka yiwa Dad, da kuma abinda Salisu yaiwa Abba duk da irin 'kaunar da ya nuna mishi a rayuwa.*




*Nan na kawo 'karshen wannan labarin mai suna SO MAHA'DIN RAYUWA!,*



*KA'DAN DAGA CIKIN ABINDA LABARIN YA 'KUNSA SHINE:*



1- *DARASI AKAN SOYAYYAR GASKIYA, MUN DAI GA DUK HALIN DA AMIR YA SHIGA AKAN AMIRA AMMA DA YAKE SO NA GASKIYA SUKEWA JUNA BASU RABU BA BABU ABINDA YA CANZA MA A SOYAYYARSU SAI 'KARUWAR 'KAUNAR JUNA DA KULAWA.*



2- *DOLE MU SANI SOYAYYA TANA MAKANTAR DA MUTUM NE TA YANDA TAKESA MUTUM YAGA KOME YA AIKATA DAI-DAINE ME KYAU KO MARA KYAU INDAI AKAN MASOYINSA NE, SHIYASA DA DAMA TAKE SA MUTUM YA KARKACE, IDAN KAI SA'A DA MASOYI B'ATACCE TO BURINSHI KAIMA YA B'ATAKA, KUMA TANA ZAMA SILAR DAWO DASHI HANYA, KAMAR YANDA AMIRA TAI SA'A DA MASOYI NA 'KWARAI, DUK DA TA MAKANTAR DA ITA GANI TAKE DUK DUNIYA BABU KAMAR AMIR GUNTA TANA NEMAN BIJIREWA IYAYENTA, SAIDA YA TSAYA TSAYIN DAKA WAJEN TUNATAR DA ITA MUHIMMANCIN IYAYE, TO DARASIN ANAN SHINE YIN SOYAYYA DOMIN ALLAH DA KUMA 'DORA MASOYANMU KAN HANYAR 'KWARAI WALLAHI WANNAN KE KAWO 'DOREWAR SOYAYYA IN BAMU SANIBA MU SANI.*



3- *MUNGA MUHIMMANCIN HA'KURI DA NASARAR DA YAKE HAIFARWA, MUNGA KUMA SAKAMAKON MAI KYAUTATAWA DUK WANDA YAI ZALUNCI, BA FAD'UWA BANE DAN KA KYAUTATAWA WANDA YA ZALUNCEKA, SAI KAGA ALLAH YAI MAKA AFIWA TARE DA KAWO MAKA KYAKKYAWAR MAFITA A RAYUWA SAKAMAKON AIKATA HAKAN DA KAYI.*




4- *MUNGA 'KARSHEN ZALUNCI DA AZZALUMAI DAMA DAI 'KARSHEN BAYA YIN KYAU.*


5- *NASHA FAD'I CEWA MASU KUD'I SUNA BANI TAUSAYI, SABODA YAWANCINSU BA DAN ALLAH AKE KAUNARSU BA, DAN ABINDA ZASU MIKO SHI AKE YI MAWA, SHIYASA GANE MASOYI NA GASKE KE YI MUSU WAHALA, BABBAN MATAKI SHINE ADDU'A DA KUMA BOYE MATSAYINKA HAR SAI KA TABBATAR DA IRIN K'AUNAR DA AKE MAKA, KAR YAZO ANA CE MAKA I LOVE YOU ASHE I LOVE YOU MONEY NE BAKA SANI BA😂.*




*MUNGA KUMA YANDA WASU AKAN DUKIYA SUKE 'KO'KARIN NISANTAKA DA MASOYIN GASKE*




*MUNGA 'KAUNA TA GASKIYA, DAMA ANCE SO HANA GANIN LAIFI, AMIRA FA TASAN AMIR SHI YA AIKATA KISAN NAN AMMA KODA YAUSHE 'KO'KARI TAKE TAGA TA KARESHI, KAI SOMA TAKE TAGA TA 'DORA LAIFIN A KANTA, TO WANNAN SHINE MASOYIN GASKE WANDA ZAI 'BOYE AIBUNKA YA BAYYANA ALKHAIRINKA, KUMA DUK WUYA DUK RINTSI KOWANE HALI KA SHIGA BAI TAB'A GUJE MAKA.*




*KAI DARUSSAN SUNADA YAWA, AMMA KA'DAN DAGA CIKI NA KAWO MUKU, SAURAN KUMA INA JIRAN NAJI DAGA BAKINKU ABINDA KUKA 'KARU DASHI A WANNAN LABARIN CIKIN TATTAUNAWAR DA ZA'AI DANI INSHA ALLAH.*

*ALHAMDULILLAH, ALHAMDULILLAH, ALHAMDULILLAH, INA GODIYA GA ALLAH DA YA NUNA MINI WANNAN RANA DA NA KAWO 'KARSHEN WANNAN LABARIN.*



*YA UBANGIJINA KA YAFEMIN DUKKANIN KURA KURAN DA NAYI A CIKI, YA ALLAH KA BANI LADAN ABINDA NAYI DAI DAI A CIKINSA, MAKARANTAN DA SUKA KARANTA KUMA SUKA 'KARU SUMA ALLAH YA BASU LADA DA IKON AMFANA DA DARUSSAN CIKI.*




*SAI MUN SAKE HA'DUWA A SABON LITTAFI NA WANDA ZAIZO NAN BADA DA'DEWA BA INSHA ALLAH.*






*🅱K CE*😘💋

31 / 31