SO MAHADIN RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVELS PDF BY BILKISU Z YAU.txt

Author :  Bilkisu Z Ya'u Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   13 / 31

36K to 39K   out of 90.7K words

kawota wani k'aramin gari a nan ta tambaya inda zasu sami asibiti ko kemis, aka raka su wani asibiti wanda aka k'i karb'ar Amir ganin harbi ne kuma ba d'an sanda kuma shi kanshi Amir d'in ya wahala.




sai da k'yar suka amince suka karb'e shi, amma Doctor d'in da zai duba Amir ya kafe ya dage kan ba zai yi mishi komai ba sai taje ta taho da d'an sanda sannan zasu duba shi.



Ba tare da b'ata lokaci ba aka raka Amira station tai musu bayani akan mijinta ne 'yan fashi ne suka shigar musu gida suka kwashe musu kud'i sannan suka harbi mijinta a hannu, shine akace sai tazo da d'an sanda.




Babu b'ata lokaci aka had'ata da mutum d'aya cikin jami'an suka koma asibitin.



Koda isar su taga yanda Amir d'inta ya k'ara galabaita gashi har yanzu basu tab'a shi ba.



Amira ta haukace musu a asibitin tana kuka tana fad'in su yi k'ok'ari su ceto ranshi, zata basu ko nawa suke buk'ata, in kuwa ya mutu to sai ta k'arar da kowa dake cikin asibitin.



'Dan sandan da aka had'a su tare shine yake rarrashinta tare da bata baki, babu b'ata lokaci jami'in nan ya saka hannu aka fara duba Amir cikin gaggawa, aka cire bulet d'in tare da yi mishi duk wani taimakon da ya dace.



Alhamdulillah Amir ya samu sauk'i, amma Amira sam bata so ma suka kwana a garin ba saboda hankalinta bai kwanta da wurin ba gani take kamar za'a zo a rabata da Amir d'inta.



Bayan kwana biyu Amira ta matsa aka sallame su, Amira ce ke tuk'a motar a yayin da Amir ke zaune gefe kuma ta rasa ma ina zata nufa da su, har sun fara tafiya sai kuma ta faka motar tare da kallon Amir tace " yanzu Amir ina zamu je kaga shiga cikin gari be kama mu ba saboda duk muka shiga nasan a yanzu kuma a ko'ina neman mu ake yi."



Amir wanda ke zubar da hawayen nadamar halin da ya jefa su a ciki, gashi wadda ya yi dominta yana neman rasata, lallai ya yarda so makaho ne, lokuta da yawa yakan makantar da kai ka aikata komai wanda koda zaka yi nadama ne daga baya sai kayi, Amir yace " Amira dan Allah kiyi hak'uri ki yafe min, bana yin nadamar duk abinda na aikata a kanki koda kuwa abinda nayi zaisa a rabani da raina ne, damuwata d'aya ne a yanzu na jefaki cikin damuwa da nayi, ni kuma duk duniya babu abinda na tsana wanda ya wuce shigarki wani hali balle kuma ace ta sanadina, ina rok'onki Amira muyi hak'uri mu yi nesa da juna har sai na fita daga cikin wannan halin saboda bana so kema ki shiga ciki."



Kuka suke yi sosai kamar ransu zai fita, can sai Amira ta tsagaita da nata kukan sannan ta kalleshi tace " dan Allah Amir kukan nan ya isa haka ba shi bane mafita a garemu, hanyar da zamu ceci soyayyarmu daga rushewa ya kamata mu nema, Amir ban tab'a yin so ba sai a kanka, kuma gaskiya ban shirya rabuwa dakai ba, so nake mu rayu tare ya zama mutuwa ce kad'ai zata rabamu, itama da da hali zanso mu mutu a tare, saboda haka kama daina zancen yin nesa da juna kasan ni da kai duk bazamu iya jure faruwar hakan ba, in har kana k'aunata kuma da gaske baka son rabuwarmu to ka zuba min idanu kan dukkanin wani hukunci da zan yanke."



Amir ya share hawayen shi, sannan yace "Amira gaba d'ayan rayuwata tana gurinki, na gwammace ace na mutu na barki da ace yau ina raye amma na rasaki," Amira ta katse shi cikin sauri tare da fad'in " Amir nima a wannan duniyar muddin babu kai tabbas bak'in cikin rashinka zaisa in bar cikinta, nasha fad'a maka cewa banda rayuwa a cikin rayuwar da babu kai, da kai na saba taya rabuwa zata zama abu mafi sauk'i a garemu, kama bar wannan maganar tana d'aga hankalina, insha Allah zamu rayu tare muyi aure mu haihu, kuma in Allah ya yarda mu mutu a tare."



Amir ya numfasa, sannan yace " to yanzu ya zamu yi, ina zamu nufa?"



Amira tace nima shine abinda nake ta tunani cikin raina, inda zamu je mu kaucewa Yahya daga neman da nasan yana yi mana a yanzu haka," dogon numfashi ta ja, sannan kuma kowanne daga cikinsu yai shiru yana tunanin mafita.



Can Amira ta d'ago cikin sauri tare da fad'in " na tuno inda zamuje ba tare da kowa ya ganmu ba, amma dole sedai mu hak'ura da makaranta in kuma zamu fita to dole sedai mu rufe fuskarmu yanda ba wanda zai gane mu, ina ganin kawai mu tafi gidan marayun nan mu zauna na wasu lokuta kafin mu san abun yi a gaba."



Amir yace " sam komawarmu cikin gari a yanzu be kamata ba kamar mun kai musu kanmu ne, sedai mu nemi wata mafitar, suna cikin wannan shawarar ne suka hango motar su Insp Yahya suna nuna hotunansu suna tambayar inda suke, kuma ganinsu tare da d'an sandan da ya raka Amira aka duba Amir a asibiti ya k'ara tayar da hankalinsu matuk'a, ko kafin suyi wani yunk'uri 'yan sandan nan sun hango su, domin Insp Yahya ya haddace lambar motar Amir da Amira duka a kanshi.



Cikin sauri Amir yace wa Amira ta dawo mazauninshi suka yi canje yaja motar cikin k'warewa Amir ke tuk'a motar a yayin da Insp Yahya da tawagar shi suke biye dasu suma da gudu, haka sukaita tsere kan ti-ti k'ok'arin 'yan sandan nan kawai suga sun sha gaban su, a yayin da shi kuma Amir ya dage kawai k'arawa motar gudu yake yi yak'i bari su shiga gaban su.



A haka har su Amir suka fara yi musu nisa, cikin hukuncin Allah kuma suka b'ace musu, Insp Yahya ya daki kan sitiyarin motar yace " shettttt sun gudu," dole suka juya kan motar su domin kuwa hanyar ta kasu har uku ko kafin su k'araso sun b'ace a wajen shiyasa basu san wacce ce hanyar da su Amir d'in suka bi ba.



Su Amir kuwa duk da sunyi nisa sun ma fita daga kano gaba d'aya sun shigo zaria amma ya kasa tsayawa da motar gudu kawai yake yi, har Allah ya kawo su wani k'auye da ake kira Damari, anan suka yada zango a galabaice, suka fito daga motar a dai-dai wani bawan Allah ya biyo hanya yana sab'e da fatanya zai tafi gida, ga dukkan alamu daga gona ya fito.



Amir ya kalleshi yace "sannu Baba ina wuni," dattijon nan ya tsaya tare da amsa gaisuwar su, Amir ya cigaba da cewa " Baba taimako muke nema daga gareka dan Allah, dattijon nan yace " to yaro Allah yasa wanda zan iya ne."






_ayi hakuri da wannan wayar huk take idan nai typing me yawa a bini bashin gobe insha Allah._πŸ™









Muje zuwa








*πŸ…±K CEπŸ˜˜πŸ’‹*
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜






RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U οΌˆπŸ…±KοΌ‰*
(Autar marubuta)





SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
(MamieοΌ‰







*πŸ‡ΈπŸ‡¦ZAMAN AMANA WRITER'S*
(Gidan zaman lafiya da amana insha AllahοΌ‰πŸ€œπŸ€›







*AUNTYNAH AISHAN UMMA tana gaishe da kowa da kowa, kuma tace tayi kewar dukkanin masoyanta, tace mu kwantar da hankalinmu tana nan cikin k'oshin lafiya, wayarta ce ta sami matsala amma kwanan nan zata sake wata, tana nan tafe nan bada dad'ewa ba insha Allah, mun gode Allah da jin kina nan lafiya AUNTYNAH😍*







*Ina baiwa MASOYANA hak'urin jina shiru na kwana biyu, mun d'an sha shagalin bikin sister na ne, sannan ranar Alhamis nayi typing nai mistake d'in number, a maimakon insa 95 to 100 sai nasa 90 to 95, dan haka zan gyara lambobin in turo su a tare saboda sam bana so masoyana su shiga rud'u, wallahi ina alfahari daku da yawanku masoyana, da bazarku nake taka rawa.*πŸ’ƒπŸ˜‰





*MOMYN KHADEEJAπŸ§•*πŸ—£πŸ—£πŸ—£πŸ—£
*ungo taki gaisuwar ta musammanπŸ™πŸ™πŸ™πŸ™πŸ™ sannan Amir da Amira suna gaishe ki sosai sunce suna mugu mugun yinki, Allah ya bar k'auna da zumunci🀝😍.*









PAGE 95 to 100







Dattijon nan ya kalli Amir yace β€˜β€™to yaro ina jinka Allah yasa zan iya, wane irin taimako kake nema daga gareni? β€˜β€™



Amir yace β€˜β€™mu bak'i ne a garin nan, dan Allah ka taimaka mana da masauki.β€˜β€™



Dattijon nan yai shiru can sai ya numfasa, kafin yai magana Amir ya sake cewa β€˜β€™dan Allah Baba ka taimaka mana mu ba masu cutarwa bane nasan tunanin da kake yi kenan a zuciyarka, wallahi ba zamu cutar daku ba, ka taimake mu domin girman Allah zaka ji dukkanin labarin mu daga baya.β€˜β€™



Baba yace β€˜β€™to shikenan yaro ku biyo ni muje,β€˜β€™



Shi dai Baba ya yi shahada ne ya tafi dasu ba don hankalin shi ya kwanta da bayanan da suka yi mishi ba, haka suka tafi Baba yana gaba suna binshi a baya har cikin k'auyen, suka tsaya a bakin wani k'aramin gida irin gidajen k'auyen nan amma k'aramin gida ne sosai.



Kai tsaye Baba ya basu izini suka shiga gaba d'ayan su, matar shi ta amsa tare da fitowa daga d'aki tace β€˜β€™sannu da zuwa mai gida, tare da bak'i kake tafe ne sannunku da zuwa,β€˜β€™ ta shiga cikin d'aki ta fito da k'atuwar tabarma ta shimfid'a sannan suka zazzauna.



Bayan sun gaggaisa sannan mai gidan wanda su Amir suka kira da Baba ya kalli matar shi yace β€˜β€™wad'annan bayin Allahn bak'inmu ne, a hanya na had'u da su suka nemi taimakon masauki a wajena na wasu kwanaki, tunda wancan d'akin da A'i tai aure ba kowa a cikinsa to a gyara musu su sauka a ciki.β€˜β€™



Wannan dattijuwar matar da Baba ke mata dukkanin wad'annan bayanin sai ta sake kallon su Amir cikin fara'a ta sake musu sannu da zuwa, ta mik'e da nufin zuwa ta gyara d'akin, sai Amir ya dakatar da ita ta hanyar fad'in β€˜β€™ dan Allah Umma ki bar gyaran d'akin zamu gyara, ai mun gode ma da kuka bamu masauki Allah ya saka muku da alkhairi, Allah ya biyaku da gidan aljanna firdausi.β€˜β€™



Duk yanda su Amir suka so su hana Umma gyara d'akin tak'i bari, a cewarta ai su bak'in su ne be dace ace yau daga zuwansu ta barsu sunyi aiki ba, dolen su suka hak'ura suka k'yaleta, bayan ta gama gyarawa ta yi musu izinin shiga, suka shiga suka zauna aka kawo musu abinci da ruwa.



Suka ci abincin suka sha ruwan sannan suka ci gaba da kallon d'akin suna tunanin yanda zasu kwana a cikinsa, tabarmi ne guda biyu a cikin d'akin aka had'e su waje guda, sai wata tsohuwar gana mas go, Amir yace β€˜β€™kiyi hak'uri Amira ni na jawo miki kwana irin wajen nan, gobe in Allah ya kaimu zamu san yanda zamu yi mu sami 'yar k'aramar katifa mu sa a d'akin kafin mu tafi.β€˜β€™



Amira ta kalle shi tace β€˜β€™ a'a in dai don saboda ni ne to karka damu, ina ma muka ga kud'i mu da muka fito ko shiri babu, ka kwantar da hankalinka zan iya zama a ko ina ne muddin ina tare da kai, amma d'azu a hanya naji ka cewa Baba zaka bashi labarin mu, to kar ba shiba ma karka tab'a fad'awa wani abinda ya faru har abada, ko da ka tashi baiwa Baba labarin kawai kace musu mu miji da mata ne, kan hanyar mu ta zuwa garinmu akai mana fashi shiyasa muka sauka a wannan k'auyen.β€˜β€™



Amir ya kalleta yace β€˜β€™to shikenan Amira ta, yanda kika ce haka za'ai.β€˜β€™



Da dare yayi suka ja tabarmin suka raba su shi Amir yana farkon d'akin, ita kuma Amira tana can ciki, sedai sam sun kasa bacci, daga k'arshe ma hirarsu suka sha, sannan suka yo Alwala suka yi nafila da addu'o'in neman mafita wajen Allah mahalicci, sai da asuba sannan suka kwanta amma sam bacci yak'i ziyartar su.



Washe gari Amir da Amira suka tashi suka je d'akin su Umma suka ci sa'a Baba yana nan, bayan sun gaisa sai Baba ya kalle su yace β€˜β€™ya kamata ku sanar da mu sunanku da labarin ku da kuma abinda ya kawo ku wannan k'auye namu.β€˜β€™



Amir ya gyara zama sannan yace β€˜β€™sunana Amir, wannan kuma ya nuna Amira matata ce sunanta Amira,β€˜β€™ nan fa ya kwashe duk yanda Amira ta zayyana musu ya fad'a musu, sun tayasu jimami tare da yi musu Allah kyauta gaba, nan shima Baba ya basu labarinsa a tak'aice ya fad'a musu yana da yara har hud'u dukkansu mata, kuma dukkansu an yi musu aure, kasancewar auren k'auye daban da na cikin birni, sun dad'e suna hira kafin daga k'arshe Baba ya tashi zai tafi gona Amir ma yace zai bishi suka tafi tare, a ranar tare suka yi aikin gonar domin Amir ya dage lallai sai ya yi, haka itama Umma da Amira tare suka yi dukkanin aikin gidan.



Bayan kwana biyu Amir da Amira suka murmure suka saki jikinsu tare da sabawa da komai na k'auyen daga kan cimarsu har zuwa suturun da suke sakawa kasancewar su Amira dama ba kaya suka shigo k'auyen daga su sai na jikin su.



Kuma daga lokacin da suka shigo k'auyen basu k'ara barin iyayen gidan su sunyi wani aiki ba, Amir shi yake wa Baba duk wani aiki na gonarsa, itama Amira ita take duk aikace aikacen cikin gida, sun hutar da wad'annan dattijan daga yin kowane irin aiki, to dama shi Amir ya riga da ya saba da wahalar rayuwa tun yarintar shi, Amira ce ma kafin ta saba ta sha wahala sosai saboda rashin sabo ta riga da ta saba komai se dai ai mata, d'an aikin da take wa kanta be taka kara ya karya ba.



....................




Insp Yahya ne zaune a office yana waya, be wani d'auki lokaci me tsaho ba ya gama wayar, d'agowa yayi ya kalli d'an sandan da ke k'ame a gaban shi yace β€˜β€™ya ake ciki, an samu nasara kan abinda na turaka bincike akaiοΌŸβ€˜β€™



'Dan sandan da ke tsaye gaban Insp Yahya yace β€˜β€™yes sir na samo bayanai gasu nan a cikin wannan takardar, mahaifin ita Amira shine shugaban k'asar nan ma a yanzu, kuma har lambarsa ma duk na samo, shi kuwa Amir bamu samu wani cikakken bayani a kanshi ba, sedai labari da muka samu ya tab'a rayuwa a kusa da gidan su Amira amma ba wani labari kan iyayensa,β€˜β€™ ya 'karashe maganarsa tare da mi'ka mishi takardar bayanin dukkanin abubuwan da ya fad'a mishi.



Insp Yahya ya karb'i takardar nan ya duba sannan ya d'ago fuskar sa d'auke da murmushi, yace β€˜β€™da kyau mutumina kayi aiki me kyau, zan kira mahaifin Amira in sanar dashi duk abinda ke faruwa, kaga shi zai taimaka mana sosai wajen kama Amir cikin sau'ki, kuma dole mahaifin Amira shima ya d'auki mataki akan Amir in yaji 'yar shi bata makaranta tana tare da wani 'kato 'katon ma makashi, zaka iya tafiya kayi aiki me kyau na jinjina maka.β€˜β€™



Bayan d'an sandan nan ya yi godiya ya sara sannan ya fice, Insp Yahya ya d'auko wayarsa ya shigar da lambar mahaifin Amira cikin waya sannan ya rangad'a kira.



Dad da ke zaune cikin iyalen shi suna hira yaji wayarsa ta fara 'kara alamun ana kiransa, bayan ya d'aga tare da sallama, Insp ya amsa cikin girmamawa bayan sun gaisa sannan yace β€˜β€™dama na kira ne in sanar da kai abinda ke faruwa da halin da 'yarka take ciki, wani yaro ne Amir yai kisa,β€˜β€™ mahaifin Amira cikin sauri tare da 'kosawa ya mi'ke cikin sauri tare da katse shi ta hanyar fad'in β€˜β€™to miye had'in kisan shi da lamarin yarinyata? Insp Yahya yace saboda saurayin Amira ne, kuma tunda aka gano shi yai kisan anzo kamashi suka gudu tare shi da Amiran har yanzu bamu gano inda suke ba, shine na kira domin in sanar da kai halin da ake cik....... kafin ya 'karasa maganarsa Dad ya katse shi cikin tsawa yana fad'in karka 'kara had'a 'yata da makashi in ba haka ba zan hukunta ka wallahi, Insp Yahya yace β€˜β€™ka yi ha'kuri amma in baka yarda ba kayi bincike akai,β€˜β€™ Dad be tsaya cigaba da sauraren sa ba ya katse wayarshi, lambar kwamishina dake kano ya fara kira bayan sun gaisa ya tambayeshi waye Insp Yahya, kwamishina ya fad'a mishi cewa jami'i ne 'kwararre kuma me sanin makamar aiki, sai Dad ya bashi umurni akan yana so aje makarantar da Amira ke ciki a bincika mishi Amira tana nan ko bata nan, kuma a binciko mishi waye Amir kuma yanzu yake so, Kwamishina ya amsa suka yi sallama nan da nan ya tashi da kanshi tare da yara suka tafi makarantar, shi kuwa Dad banda kai kawo a tsakiyar d'akin ba abinda yake yi, su kuwa k'aninshi da matarshi da sauran 'yan gidan binshi kawai suke da kallo domin jin wayar da yake sun san tabbas maganar ta shafi 'yar su Amira, suna so suji 'karin bayani amma kowa shakkar yiwa Dad magana yake ganin halin da yake ciki, dama muddin ya shiga irin wannan yanayin to tabbas babu me iya tanka mishi saboda gudun abinda zai biyo baya.



_Hmmm tab' da sauran rina a kaba, Amir ka lallab'a ka tsere tun kafin Dad ya gano kaine._






Muje zuwa







*πŸ…±K CEπŸ˜˜πŸ’‹*
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜






RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U οΌˆπŸ…±KοΌ‰*
(Autar marubutaοΌ‰







SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
(Mamie)





*πŸ‡ΈπŸ‡¦ZAMAN AMANA WRITER'S*
(Gidan zaman lafiya da amana insha AllahοΌ‰






*MASOYANA NA NESA DA NA KUSA BANDA ABINDA ZAN SAKA MUKU DASHI KAN K'AUNAR DA KUKE GWADA MIN, SE DAI IN ROK'I MAHALICCINA ALLAH YA BIYAKU DA KYAKKYAWA KUMA YA K'ARA MUKU SONAπŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜˜πŸ’‹*







*Tabbas komai yai farko zai yi 'karshe, RAHEENAT M. ABBAKAR ina tayaki murnar kammala Novel d'inki mai suna 🌲HALIN RAYUWA,🌲 Allah ya bamu ikon amfana da tarin darussan dake cikinsa, ya bamu

13 / 31