Author : Bilkisu Z Ya'u Category : Romantic Hausa Novels
sha'awa, Amir da Dad kuwa wata soyayya suke gwadawa juna kamar d'a da mahaifi, sha'kuwarsu abun mamaki cikin 'kan'kanin lokaci kuma.
*BAYAN WATA UKU*
Bayan wata uku su Dad suna zazzaune a falo sai ga sallamar su Abba sun sake yi musu dirowar bazata.
Cikin tsananin farin ciki da walwala suka tarbesu, suka zauna aka gaggaisa, bayan sunci sunsha suka ce zasu tafi masaukinsu, da yake gidajen Abba a garin sunada yawa, sai suka yi musu sallama suka tafi.
Washe gari Abba ya sake zuwa shi da matarshi, bayan an gaisa sannan yai gyaran murya yace "wannan karon abinda yasa muka taho tare da yi muku zuwan bazata abu uku ne, na farko duk na taraku ne domin ku zama shaida na baiwa abokina wato mahaifin Amira naira million hamsin da kamfanoni na guda biyar da gidajena guda biyar, nayi iyakar 'ko'karina wajen ganin an binciko su Nura amma kwata-kwata babu labarinsu, ina tunanin basa 'kasar nan ma, abu na biyu kuma kai Uncle na baka kamfanina guda d'aya dake Abuja, idan zamu koma sai mu tafi tare dakai ka ganshi, sai abu na 'karshe shine, a 'yan kwanakin nan ina yawan yin mafarkin d'an uwana Salisu, dan haka inaso kai Amir ka shirya kai da matarka gobe in Allah ya kaimu muje kontagoran domin ganin halin da suke ciki."
Nan fa d'akin ya karad'e da koke-koken farin ciki, Dad cikin kuka yace "ha'ki'ka ka saka min da alkhairi wanda ni na kasa kwatanta hakan a kanka kaida d'anka Amir, ni nasan babu ranar da zan daina jin kunyar abinda na aikata muku, dan Allah ku yafemin, ni bansan ma me zan fad'i ba wajen gode maka Ahmad," ya cigaba da kuka.
Amir ne yai murmushi, sannan ya 'karasa kusa dashi yace "haba Dad menene hakan kake yi, yanzu haka zaka ri'ka yi idan jikokin ku suka fara zuwa suna ganin kana kuka wallahi dariya zasu ri'ka yi maka ba ruwana," duka d'akin aka kwashe da dariya.
Washe gari su Abba da su Amir suka shirya suka fito suka yi sallama da kowa sannan suka shiga motoci sai hanyar kontagora.
Suna d'aukar hanyar kowa yai shiru kowa da abinda yake sa'kawa a ranshi, shi kuwa Abba komai dawo mishi sabo yayi, nan da nan yaji hawaye na gangarowa daga idanuwanshi.
Basu d'auki lokaci me tsawo ba Allah ya kawosu cikin garin kontagora lafiya.
Ta 'kofar gidan iyayenshi suka bi Abba yace a tsaya suka fito suka shiga cikin gidan, ba kowa a ciki duk ya lalace, nan Abba yaci kuka mai isarshi na tunowa da iyayensu ya gode Allah sannan ya kallesu duka yace "nan ne gidan iyayena, yana gama fad'in haka ya fito suma suka biyoshi suka shiga mota suka cigaba da tafiya.
Nan da nan gari ya fara d'auka Ahmad ya shigo gari, mutane suka cika wajen motocin suna bin motocin da gudu suna murna da farin cikin sake ganin Ahmad.
'Daya daga cikin wad'anda ke bin jikin motar Abba ya tambaya gidan yayanshi suka yi mishi kwatance, suka karkata motarsu domin 'karasawa gidan.
Jikin wani katafaran 'kerarren gida sukai fakin, gidan babban gida ne kuma me d'an karen kyau da tsada, zamu iya cewa ma duk garin ko kuma ace duk unguwar da kewayenta babu mai 'kerarren gida na gani na fad'a irin na yayan Abba Ahmad.
Bayan sun shiga da motocin su sun faka sannan suka fito suka shiga cikin gidan, tun daga 'kofar gidan suke ganin 'yan sanda cikin kakinsu da kuma security's har suka shiga ciki, inda Amir da Amira suka ga abin mamaki kuma suka ga abinda yai matu'kar d'aure musu kai, Insp Yahya suka gani zaune cikin falon gidan shi da wata mata wadda suke matu'kar kama da Insp Yahya, kamar tasu har ta b'aci, saboda tsabar kama da ace tsohuwar namiji ce in aka ganta za'a ce Insp Yahya d'in ne.
Amir ya yiwa mahaifinsa rad'a yace "Abba kaga wanda yaso halakamu ni da Amira, kuma harda shi aka yashe dukiyar Dad d'in Amira, yana wajen ranar da abun ya faru, yau me rabani dashi sai Allah."
Amir cikin zafin nama ya kutsa cikin falon har gaban Insp ya sha'koshi tare da fad'in "nan ma ka biyomu ne ka kashemu, to kafin ka kashemu ni zan kasheka," Amir ya sha'keshi sosai da hannunsa duka biyun.
Abba ma yayi-yayi ya cire hannunsa daga wuyan Insp amma ya kasa, saida ya sharara mishi mari sannan ya sakeshi.
Abba ya kalli Insp da wannan matar da suka gani tare dashi yace "dan Allah kuyi ha'kuri da abinda ya faru, ku bamu dama mu zazzauna akwai muhimmin abinda ke tafe damu."
Matar nan tace "bakomai ku zauna ga kujera nan," kowa ya zauna sannan Abba yai gyaran murya ya fara magana, "ni sunana Ahmad ni 'kani ne ga Salisu wanda aka tabbatar mana da nan ne gidanshi, wad'annan iyalina ne, wannan matata ce sunanta Khadija, ya nuna Umma, sannan ya 'kara nuna Amir yace wannan d'ana ne, sunanshi Amir, wannan kuma matarsa ce sunanta Amira.
Wannan matar ta fad'ad'a fara'arta sosai tare da sake yi musu sannu da zuwa.
Insp Yahya kuwa jin wannan bayanin yasa ya fara du'kar da kai kamar tsohon munafuki, su kuwa Amir da Amira duk sun 'kosa suji matsayin Yahya cikin wannan gidan, a yayin da shi kuma Abba ya 'kosa a nuna mishi inda d'an uwanshi yake domin yaje ya ganshi.
Wannan matar ce ta bud'e baki alamun zatai magana sai Insp Yahya yai zumbur ya mi'ke yace "um ni bari in tafi zan dawo wani lokacin."
Wannan matar tace "a'a zauna tukunna mu gama yin maganar."
Insp Yahya ya bud'e baki zai sake magana Matar nan ta sake fad'in "ka zauna mana."
Ba yanda ya iya ya koma ya zauna, matar nan ta sake bud'e baki tace "
_Wai wacece wannan matar, kuma wanene Insp a gidan kodai akwai wajen wanda yazo ne? ina yayan Ahmad? ku dai ku biyo Autar marubuta dai_
Muje zuwa
*π
±K CEππ*
ππππππππππ
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
ππππππππππ
RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (π
±K)*
```(Autar marubuta)```
SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
```(Mamie)```
*πΈπ¦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```π€π€
*~Safiya Bello K*
*Wannan shafin kyauta ne a gareki sister Safiya Bello saboda soyayyarki gareni da kuma dukkanin littafaina, dan haka nima dole na baki tukuicin 'kauna, wannan page d'in naki ne ke d'aya kiyi yanda kikaso dashi,πππ i love you over over soyayyar sojojiππ*
*YAN NIGERIAπ£π£π£π£π£*
*DAN GIRMAN ALLAH MU TAIMAKI KANMU MU FITO RANAR ZAB'E DUK MU DANGWALAWA BABA BUHARI YA CIGABA DA AIKI DAGA INDA YA TSAYA, KARMU BAWA AZZALUMAI DAMAR SAKE MULKARMU BILLAHIL AZEEM IN HAKAN TA FARU ABINDA SUKA FARU SHEKARUN BAYA ZAMANIN MULKIN MUGAYE SU ZASU CIGABA DA FARUWA, KARKI BARI AI ASARAR 'KURI'ARKI KI AJIYE KATIN ZAB'ENKI A GIDA KICE KE BAZAKIY ZAB'E BA, WANNAN BA DAI-DAI BANE, AI DUK ME KATIN ZAB'E KAWAI YA FITO YA DANGWALA, IN KUMA KIKA FITO KIKA ZAB'I MUGU WANNAN SHIMA BA DAI-DAI BANE, KUMA YIN HAKAN ASARA CE BABBA, KINYI ASARAR LOKACINKI DA KUMA 'KURI'ARKI, WALLAHI ALLAH MU DA KANMU MUNGA CANJI A RAYUWA A SHEKARUN NAN DA BABA YAYI YANA MULKI, HMMMM SAURAN JIN DA'DIN MA DA KWANCIYAR HANKALI YANA GABA INSHA ALLAH, SABODA HAKA IDAN KA SAKE KA BAIWA MUGAYE MASU BURIN CUTA K'URI'ARKA TO WALLAHI KANKA KA CUTA, MUDAI MUNCE SAI BABA BUHARI INSHA ALLAH BAZAMU TAB'A GAJIYA DA MULKINSA BA HAR ABADA, KARMU SAKE MU BAR HASKE MU TSUNDUMA A CIKIN DUHU*
ππππππππππ
PAGE 225 to 230
Wannan matar ce ta kalli Abba Ahmad ta fara magana tace "sannunku da zuwa, munji dad'in ganinku sosai wallahi, ni sunana Rabi'atu kuma nice matar Salisu, wannan d'ana ne, ta nuna Insp Yahya wanda kanshi ke sunkuye yaketa faman had'a zufa, sannan ta cigaba da cewa yana da 'kanni maza guda biyu, a ta'kaice dai 'ya'yanmu uku kuma duk maza ne, biyu Ishaq da takwaranka Ahmad wanda muke kira da Baba 'karami suna 'kasar waje suna karatu, gaskiya munji dad'in had'uwa daku sannunku da zuwa, sedai abinda ban gane ba shine naga Amir ya sha'ke Yahya meyasa, kuma me ya faru?"
Ahmad yai murmushi, sannan ya bata labarin duk irin abinda ya faru a baya.
Banda harara da tsananin tsana babu abinda Amir da Amira suke yi akan Insp Yahya, shi Amir ma haushi yake ji a zuciyarshi yana fad'in Allah ya sawwa'ke mutum irinka me halin karnuka ya zama d'an uwana.
Amir yace "banyi mamakin abubuwan da ka aikata ba duba da irin gidan da ka fito a cikinsa," Abba ya daka wa Amir tsawa, abinda bai tab'a yi mishi ba, yace "ka kiyaye harshenka kuma kasan me zaka fad'i akan d'an uwana."
Abba Ahmad ya kalli Mahaifiyarsu Insp Yahya yace "ni yanzu duk ba wannan ba, ina d'an uwana Salisu yake?"
Nan da nan idanun Rabi suka ciko da hawaye, tace " labarin yayanka ba dad'in ji, domin yana kwance rai a hannun Allah, bambancin shi da matacce kawai shi yana da rai har yanzu."
Abba ya hau salati tare da mi'kewa tsaye yana fad'in "yanzu yana ina?"
Mahaifiyar su Yahya tace "yana cikin d'akinshi a kwance."
Cikin sauri Abba ya nufi d'akin da ta nuna mishi da hannu, su Amir suma suna biye dashi a baya.
Kwance suka tarar da Salisu ya tsomare ya rame kamar me ciwon 'kanjamau, idan ma ba ka sanshi ba mugun sani in ka ganshi zaka rantse ba shi bane saboda rama da kuma canjawa da halittarsa tayi.
Babu inda yake motsi a jikinshi, kuka sosai Abba keyi, suma kansu su Amir kukan sukeyi domin duk mai imani in yaga halinda Salisu ke ciki sai yayi kuka mara iyaka.
Abba cikin kuka yace "yaya kaine a cikin irin wannan halin," ya sake fashewa da kuka, su Amir kuwa tsoron Allah ne ya 'kara ziyartarsu, ganin gadai dukiyar da yake kwad'ayin samu ya tara kamar hauka amma babu halin morarsu, tunda gashi nan kwance yana tsakanin rayuwa da mutuwa sedai a juyashi a kwantar a tayar kamar gawa baya iya komai ko motsi baya yi.
Abba ya kalli matar yayan nashi yace "yanzu saboda Allah yana cikin irin wannan halin kuma kuka barshi a gida kuka zuba mishi ido a haka ba'a kaishi asibiti ba?"
Mahaifiyar su Yahya tace "wallahi babu irin asibitin da bamu jeba har fita dashi 'kasashen waje munyi amma ina jikin ya'ki dad'i har yanzu."
Abba yace "gaskiya bazan barshi a irin wannan halin ba in cigaba da kallonshi, zan fita dashi India gobe in Allah ya kaimu, yau zanyi mana tanadin komai ni dashi."
Washe gari jikin Salisu ya 'kara tsananta ko kafin su bar gidan yace ga garinku nan, Allah ya karb'i abinshi, shima yabi iyayenshi da ya kashe, yaje yai zaman jiran ranar hisabi.
Sai da akayi arba'in sannan kowa ya watse, har su Dad ma anan suka zauna akayi zaman makoki dasu.
Abba Ahmad yaci kuka kamar me, be so d'an uwanshi ya yi irin wannan rayuwar ba, kuma be so ya mutu a haka ba, yaso sai ya nemi gafara mai yawa wajen mahalicci, wad'annan abubuwan sune idan ya tuno suke sakashi kuka.
Rayuwa kenan, abinda yake yi mawa wato dukiya da jin dad'in duniya duk ya barsu a inda ya tarar dasu, bayan rasuwar tashi ne ma suke jin labarin wai ya dad'e yana jinya kafin ma ta kwantar dashi yana ciwon sama - sama har ta kai ga yi mishi kwaf d'aya, ance yaita kuka yana surutai marasa kan gado dan shi beyi tunanin Abba Ahmad yana raye ba.
To dama dai 'karshen kowa kenan 'kabari, sedai duk wanda yai me kyau shi yake murna da ita, wanda yai mara kyau kuma kuka yake mara iyaka domin tanadin da Allah yai mishi na azabobi iri-iri.
Bayan arba'in aka raba gado yanda addinin musulunci ya shar'anta aka baiwa kowa nashi, sannan Abba yace zai tafi da su Ishaq da Baba 'karami wanda yaci sunan Abba, idan sun dawo daga waje karatu zai ri'kesu a wajenshi, sannan zai cigaba da kulawa da hidimomin karatun nasu kafin su dawo.
Shi kuwa Insp Yahya da yake tun bakwai shi ya koma kano, to hakan yasa Abba ya barwa Mahaifiyarsu sa'ko akan in yazo tace yaje yana son ganinshi.
Kwance tashi ba wuya yau wata uku kenan da rasuwar Salisu, tuni yaran Salisun suka koma hannun Abba da zama a Abuja tunda dama Amir ya zama d'an Dad.
Duk wani gata yana basu wanda ko shi ya haifesu sai haka.
Bayan sati d'aya Abba ya zowa da su Dad albishir d'in ya gina musu gida kusa da juna su hud'u harda na su Amira a Abuja dan haka zasu koma can da zama gaba d'aya.
Haka kuwa akayi suka koma Abuja da zama gaba d'ayansu.
Bayan komawarsu da sati d'aya Amir da Amira suna zaune a sabon gidansu sai suka ji sallama suka amsa tare da bada izinin shigowa.
Insp Yahya ne ya shigo kanshi sunkuye ya shigo ya 'karaso har kusa da Amir, maimakon ya zauna kan kujera sai ya tsugunna a 'kasa kanshi a sunkuye ya fashe da kuka tare da cewa "dan Allah yaya Amir ka yafemin dukkanin abinda nai maka, dan girman Allah, wallahi ina cike da nadama mara iyaka ban tab'a tunanin kai d'an uwana bane, nayi takaicin irin abubuwan da nai muku, dan Allah Aunty Amira ku yafemin," yana kai aya a zancensa ya sake fashewa da kuka.
Amir ya d'agoshi tare da zaunar dashi, sannan yace "wallahi na yafe maka duniya da lahira, kuma naji dad'i da ka gane gaskiya ka kuma nemi afuwa, yanzu banda kamarku duk duniya, fatana dai Allah ya 'kara had'e kawunanmu."
Soyayya ce mai 'karfi ta 'kullu tsakanin Insp Yahya da Aneesa 'kawar Amira, ba tare da b'ata lokaci ba aka sha biki ango da amarya suka tare gida d'aya da su Amir, domin dama Amir ya rantse gida d'aya zai zauna da 'yan uwansa idan sun yi aure.
Su kuma Ishaq da Baba 'karami sun kammala karatunsu aiki suke yi sosai a cikin kamfanonin Abba.
*BAYAN SHEKARA 'DAYA*
Amir ne ya fito daga d'aki cikin sauri ya d'aga labule yana fad'in "fito a hankali," Amira na gani ta fito da 'katon cikinta tana tafiya da 'kyar, har zuwa kan kujera ta zauna.
Amir ya kalleta yace "sannu Amirata, wallahi tausayinki nake ji, kuma Allah Allah nake inga kin haihu ko ma huta da wannan laulayin da muketa fama dashi ni dake."
Amira tai dariya, sannan tace "wato mu biyu ma muke na'kudar ko," Amir yace "eh mana in aka bincika ma wallahi na fiki shan wahala saboda ni nake d'awainiya dake kuma duk ciwon da kikaji sai na jishi a zuciyata, kinga ke kina jin ciwon a jiki ni kuma ina jinshi a raina kuma ciwon dake cin rai yafi azabtarwa."
Haka dai ya zauna yanata fad'a mata dad'ad'an kalamai masu dad'i itama tana mayar masa, kaji masoyin gaske, wasu mazan da matansu sun sami ciki daina kulawa dasu sukeyi, wasu ma 'kyamarsu sukeyi, amma shi tunda ta samu ba inda yake zuwa koda yaushe suna tare yana kula da abarshi har cikin ya tsufa.
Yau litinin zaune suke a falo suna kallon labarai na 'kasar waje.
Kawai sai suka ga an nuno gawarwakin Baban Nura da shi kanshi Nuran ana sanarwa cewa sun mutu sakamakon harbesu da 'yan fashi sukayi, bayan sun yashe dukiyarsu kuma suka harbesu, wai ana cigiyar 'yan uwansu da suzo su d'ebi gawarwakin.
Amir ya kalli Amira yace "dan Allah duba ki gani," Amira tace "na gani menene abin mamakin to, ai duk wanda yai dakyau to zaiga dakyau wanda yai akasin hakan kuwa sakamakonsa ba zaiyi kyau ba."
Amir ya d'auko wayarshi ya kira Dad ko gaisawa basuyi ba yace ya kunna tv ya gani.
Dad yace "na gani Amir na gansu yanzu haka shi nake kallo, duniya ba'a bakin komai take ba."
Bayan sun gama waya Amir ya kira Abba shima ya fad'a mishi yace ai yanzu suka gama waya da Dad ya sanar dashi.
Bayan kwana biyu da faruwar hakan ashe Dad ya tura an kwaso mishi gawar su Baba da Nura, sudai su Amir da Abba kawai yace musu su shirya zasuje sallar jana'iza nan 'kofar gida.
Sai bayan an idar an kaisu an dawo sannan Dad ke sanar dasu ko su waye, sunsha mamakin faruwar hakan, Abba yace "lallai Dadyn Amir zuciyarka mai kyau ce," Dad yace "ai daga wajenka na koyi wannan d'abi'ar, yafiya ga wanda ya zalunceka."
Amira da Amir na zaune suna buga game na mota, idan Amir ya wuce Amira sai itama ta wuceshi, ganin yana 'ko'karin cinyeta sai tace wash Allah," nan da nan sai ya karkato da hankalinshi kanta, tana ganin haka tai sauri ta wuceshi, shi yana aikin tambayarta lafiya, yaji tana ihu tana fad'in "na cinye - na cinye."
Tana cikin murna yaga ta fara yamutsa fuska tana ri'ke 'kugu, Amir yace "lafiya?" Amira tace "jikina ciwo wayyo Allah nah, ai Amir be tsaya wata wata ba ya sunkuceta sai cikin mota sedai ya kasa tu'kawa cikin gidan iyayenshi ya shiga da gudu yace "Abba kuzo ku kaimu asibiti bamu da lafiya, wallahi nima ciwon nakeji kamar a jikina bazan iya jan motar ba," aikuwa ba shiri suka rankaya sai asibiti .
Bayan an shiga da ita emergency room har zai shige shima aka dakatar dashi, sai ya kira su Dad ya sanar dasu, cikin 'kan'kanin lokaci sai gasu sunzo.
Bayan lokaci 'kan'kani sai ga Doctor ya fito bayanshi Norse ce d'auke da 'yan biyu mace da namiji, baby kyakkyawar jaririya me kama da Amira sak, sai jaririn wanda yake kama da Amir, Doctor yai musu albishir ta haihu, ana mi'kawa Amir jaririya amma fad'i yake a ri'kesu tukun wallahi shi sai yaga lafiyar matarshi tukun, ya shige cikin d'akin yaje ya zauna kusa da Amira wadda ke mishi murmushi, yace "sannu Amirata, ya jikin naki, sannu Allah ya baki lafiya, saida Amir yaga