SO MAHADIN RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVELS PDF BY BILKISU Z YAU.txt

Author :  Bilkisu Z Ya'u Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   11 / 31

30K to 33K   out of 90.7K words

"to bari in je in fad'a wa Ameeru in dawo," har ta juya da gudu Dad d'inta ya k'wala mata kira ta dawo yace ta bari sai goben in zasu wuce sai taje suyi sallama, haka nan ta hak'ura ba dan taso ba.



Washe gari tun asuba kowa ya tashi ya shirya, itama Amira ta tashi tazo sakkowa taji maganar Dad d'inta yana fad'in ai bazan bari su had'u da Ameerun ba," jin ya ambaci sunan Ameeru tasan zancensu ake, hakan yasa ta tabi ta k'ofar baya ta fice, sai kuma ta dawo taje d'akin Dad d'inta ta d'auko k'atuwar jakarshi wadda ke cike da kud'i ta fito da ita kamar zata rinjayeta ma, ta shiga cikin d'aki tare da kwaso hotunan su da wanda suka yi tare da wanda take ita kad'ai shima haka, ta ware d'ai-dai ta saka mishi cikin zip d'in jakar, sannan ta fita tana share hawaye har bakin gate d'in gidan marayun, ta shiga ta tarar da me kula da su Ameerun, bayan sun gaisa ta tambayeta ina yake tace ya shiga wanka, sai Amira ta bata jakarnan tare da rok'on ta ta baiwa Ameeru injita harda 'yar takarda, sannan ta juya ta tafi, a hanya taga su Dad sun fito nemanta sukai kicibis, ya kama hannunta suka shiga gida jikinta duk a sanyaye, aka shiryata suka shiga mota tare da security's d'insu bayan an rufe ko ina, sun fara tafiya kenan sun wuce gidan marayu kenan sai ga Ameeru da gudu yana k'wala musu kira amma ina sesai Amira ta hango shi, bin motar da gudu yake yana kuka, itama tana kuka har ya gaji da gudun ya durk'ushe a k'asa kan ti-tin yana kallon motar Amira na d'aga mishi hannu tana kuka.



Komawa cikin gidan marayun da ya zama gidansu ya yi, ya shiga d'akin da yake mallakin shi ya jawo akwatin da Amira ta bashi, dan Amira ta cewa maman kayan sawanshi ne a ciki saboda su zasuyi tafiya shine ta kawo mishi, hakan yasa bata bud'a ba taga ko miye a ciki har ta bashi.



Koda ya bud'e kud'i ya gani masu uban yawa 'yan dubu dubu cike da jakar, wanda suka sashi mugun razana harda matsawa da sauri kamar wanda yai gamo, hakan yasa yai sauri ya maida zif ya rufe kar a shigo a gani, ya d'auko takardar da ta bayar a bashi had'e da jakar ya bud'e tare da fara karantawa:

_Ameeru nah Dad ya shirya mana ziyara zuwa kano, amma yace bazamu dad'e ba, duk da haka ga kud'i nan ka yi amfani dasu kafin na dawo dan banaso ka koma rayuwar da na sameka a ciki a baya, Dad yak'i bari muyi sallama nasan zaka jirani duk rintsi zanyi kewarka._




*CI GABAN LABARI*




Amir ya k'araso kusa da ita tare da tsugunnawa yace " Amira dan Allah ki saurareni kiji, wato abinda ya faru shine, " sai kuma yai shiru, Amira ta d'ago ta kalle shi sannan tace "ni nasan dama babu abinda zaka fad'i ka kare kanka a wajena, k'aunar da na nuna maka tun yarinta rabinta baka nunamin ba," Amir yace " haba Amira in har kika fad'i haka bakiy min adalci ba, ki tsaya mana kiji abinda ya faru bayan tafiyarku."



Amira tace " ina saurarenka," Amir yace " _tunda naga wasik'arki kuma naga Dad yak'i bari muyi sallama nasan tabbas ba zaki dawo ba naci kuka kamar me, amma ina ganin wannan kud'in sai tunanin biyoki kano yazo raina, amma na fara tunanin be kamata na rik'a yawo da kud'in a haka ba, hakan yasa na saka jakar kud'in cikin gana masgo d'ina na saka kayana tare da kinkimar jakar na fito, Allah ya taimakeni babu kowa me gadi ma baya nan maybe ya zagaya baya, hakan yasa na runtuma a guje duk da gudun ba sauri sosai saboda jakata dake rinjayata, dama kafin na fito daga cikin gidan na zaro dubu biyar a cikin kud'in nasa a aljihu, ina fitowa na tari adai-daita sahu sai tasha, ina zuwa naci sa'a saura mutum d'aya ta cika na biya kud'i sannan na shiga, ba yanda ba'ayi ba kan in bada jakar a samin a baya nak'i yarda, a haka aka ja motar jakar na k'afata har muka iso kano, tunani na fara yi kan ina zan dosa ni da bansan kowa ba gashi kano akwai girma ta ina zan fara nemanta, ina cikin wannan tunanin na hango wani dattijon Arzik'i cikin tashar wanda ke zaune cikin wata kwarab'ab'b'iyar mota yana cin tuwo, k'arasawa nai kusa dashi sannan na gaishe shi, bayan mun gama gaisawa yace min "yaro ina zaka je kai kad'ai haka ina iyayenka, ko kai Almajiri ne, koda yake jikinka be nuna ba," nan na fad'a mishi cewa iyayena ne da 'yar uwata nake nema a nan garin, tare da ciro hotunanmu duka ina nuna mishi, bayan ya duba yace " yaro gaskiya ban san inda suke ba kuma bansan inda za'a gansu ba, kuma kasan kano da girma, amma zan taimake ka, in ka yarda zaka zauna da ni to zan taimaka maka insha Allah za'a gansu wata rana, ba ko tunani nace na yarda zan bishi, ya siya min tuwo naci sannan ya d'aukeni ya kaini shagon wani gida yace nan ne makwancinsa domin shima ba d'an garin nan bane d'an zaria ne, neman kud'i ya kawoshi nan, mota yake ja duk ta tsufa ma kuma beda halin da zai dawo da iyalinsa nan, bayan kwana biyu na yanke shawarar rik'a bin Baba in zama kwandastan shi, wata k'ila ko ta sanadin haka Allah yasa in ganki, a haka na cigaba da rayuwa kullum bayan mun fita sai na nemeki haka ma in mun dawo, ban tab'a tunanin tab'a kud'in nan ba saboda komai nakeso Baba yana min, bayan shekara biyar lokacin shekarata sha shida kenan jikin Baba yai tsanani har saida ya koma gida, komawar da be sake dawowa ba sai labarin mutuwarshi naji wanda ya sani kuka sosai, rayuwa tai tsanani hakan yasa dole na fara tab'a kud'in nan ina biyan kud'in shago, sannan na cigaba da zuwa makarantar da Baba ya sani, da cigaba da biyawa kaina kud'in makaranta, Baba yana d'aya daga cikin mutanen da har in mutu bazan iya mantawa dasu ba, a haka har na girma nakai shekara Ashirin da bakwai ina nemanki a lokacin ne na shiga makarantar da kike aka yi sa'a kuma daga shigana Allah ya had'a mu a kan hanya, sedai tun a ranar na fahimci kece Amira ta saboda har lokacin kina tare da 'yan kunnayen da na siya miki da wannan zoben da yai miki d'as a yanzu a hannu, shaida ta gaba itace sunanki da sunan Dad su suka k'ara tabbatar min da kece, kafin had'uwata dake na siya gida duk a cikin kud'in nan, sannan kuma na fara sana'a yanzu kasuwancin gida da filaye nake yi._



Amir ya numfasa sannan ya cigaba da fad'in " taya zan manta da masoyiyata tun ta yarinta wadda take sona da gaske kuma ta zama silar canzawar rayuwata."



Amira wadda idanunta suka yi ja kuma suka kunbura saboda kuka tace " amma meyasa da ka gano nice ka b'oye kanka gareni, kuma ka canza sunanka daga Amir zuwa Ameeru?"



Amir yace " zan baki amsa yanzu ma kuwa amma kafin in fad'a miki inaso ki fad'amin gaskiya me ya faru bayan dawowarku nan, kuma tunda kuka dawo garin nan kin koma Abuja, kuma meyasa kike karatu anan bayan su su Dad sun koma Abujan da zama?"









_ku biyoni muje_πŸƒβ€β™€










*πŸ…±K CEπŸ˜˜πŸ’‹*
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜





RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (πŸ…±K)*
```(Autar marubuta)```





SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
```(Mamie) ```







*πŸ‡ΈπŸ‡¦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah) ```πŸ€œπŸ€›











*πŸ‡ΈπŸ‡¦ZAMAN AMANA WRITER'S kullum fa burgeni kuke wallahi, Allah ya k'ara d'aukaka mini ku, ya k'ara muku basira, ya k'ara mana k'aunar juna, a cigaba da basu mamakin kawaiπŸ˜‰πŸ˜˜*




*MUMCYN MU ALLAH YA K'ARA 'DORAR DA LAFIYARSA GAREKI, TAWAN ALLAH YA K'ARAWA MUMMY LAFIYAπŸ‘πŸ˜­πŸ˜­πŸ˜­*




*MY NAMECY BILKISU (QUEEN BK) ALLAH YA KARA MIKI LAFIYAπŸ‘πŸ˜­*




*MY LISSA Amir yace yaji sak'on gaisuwar ki amma be amsawa saboda kin b'ata mishi rai,😏 sannan yace in mik'a gaisuwa da ga magoya bayansa QUEEN RUQEEY HABIBTY, da MAMAN LABYB MAMIE NAH TA KAINA, da BABYNAH HAUWA, da MY HEENAT, yace duk wata k'auna taku da kuke gwada mishi yana gani kuma yana godiya, sannan yana so yasan iya adadin 'yan team d'insa duk da yasan masoyanshi sunfi yawa Lissa ce kad'ai bata sonshi kuma yace a fad'amata yana mata i hate youπŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚*








PAGE 80 to 85







Amira ta kalle shi tace _" bayan tahowarmu abun be dameni ba sosai sai da naga anyi sati d'aya biyu har wata shiru ba'a ma maganar komawarmu gida, koda na jewa da Dad d'ina da maganar komawarmu sai naji sab'anin haka yana fad'in ai a nan zamu cigaba da zama yanzu haka ma makaranta yake so ya sakani in cigaba da karatuna, dama shi ya yi haka ne dan ya rabamu tunda mun k'i maida hankali a karatu amma in kwantar da hankalina yana kula da kai da kuma karatunka, a ranar ma fad'ar halin da na shiga b'ata baki ne, anan na cigaba da karatuna har na girma, ana fara shirin sakani jami'a Dad d'ina ya koma Abuja da 'yan uwana da zama sakamakon tsayar da shi da aka yi na zama takarar shugaban k'asa kuma cikin ikon Allah ya samu nasara, ranar da na fara zuwa gida shima bikin murnar samun kujerar mahaifina ne, da naje ba irin neman da ban maka ba aka tabbatar mun da cewa ai tun ranar da muka tafi kaima ka gudu basu san inda ka shiga ba, na ci kuka na gode Allah amma har lokacin gani nake yi duk daren dad'ewa zamu had'u shiyasa duk na koma garin Abuja sai na fita neman labari a kanka amma shiru, duk tsawon wannan shekarun na kasa cireka a raina Amir koda na kwana d'aya ne, kullum sai na d'auko hotonmu na kalla ina kuka ina tuna rayuwar da muka yi a baya, se dai duk in na tunaka a raina ina ji a cikin zuciyata tana tabbatar mun cewa tabbas wata rana zamu had'u kuma in har Allah ya had'amu banda wani miji sai kai, ko cikin k'awayena a ko'ina nake in aka yi maganar aure sai ka fad'o raina domin da kai kad'ai na saba, kaine ma namiji na farko da ya tab'a shigowa cikin rayuwata, kullum tunanina zan ganka, sam Dad baya son ina kai ziyara gida saboda kar mu had'u dakai, shi burinshi kar na dawo sai na gama karatu gaba d'aya tukun, kasan dai yanda na shak'u da kai kuma nake sonka, shiyasa na dad'e tunanin ka na tab'amin zuciya."_




Amira ta cigaba da fad'in "kaji abinda ya faru bayan barinmu garin."



Amir ya numfasa sannan ya kalleta yace " to nima zuciyata ta tabbatar min da cewa saboda ni kuka tafi kuka canza gari kuka yi nesa dani, domin na dad'e da sanin cewa Dad baya sona tare dake, hakan ne yasa na canza suna daga Ameeru na koma Amir kuma bayan na ganoki na cigaba da b'oye miki kaina, burina muyi aure tukun kafin ki gano ko ni waye kar kizo ki gano kuma Mahaifin ki ya hanani mallakar ki matsayin mata."



Amira tace "duk da haka wannan dalilin be isa saka ka cigaba da b'oye min kanka ba, kai da kanka kace kaga abubuwan da ka siya a tare dani duk da cewa ko da nake yarinya ma na wuce da ajinsu balle da girmana, amma soyayyar da nake maka tasa nake kallon su a gagarumar kyauta mafi tsada a duniya, kasan wahalar da nake kan sha har yanzu wajen nemanka kuwa domin saida zuciyata ta bani nan kano ka taho saboda na rubuta maka inda zamu taho a wasik'a, kasan mutane nawa na kasa su cigaba da bincikamin labarin duk wani mutum me suna Ameeru kuwa? kasan iya adadin maza nawa nabi masu irin sunanka ina bibiyarsu domin gano wanene kai a cikinsu? haba Amir meyasa da ka gano nice ka b'ata lokaci wajen sanar da ni kaine Amir d'ina? haba Amir ya zaka min haka."



Amir ya dafa Amira sannan yace kiyi hak'uri Amira, harga Allah zuciyata bata yi tunanin har wannan tsawon lokacin ina cikin ranki ba saboda mutanen da nazo na tarar dasu a tare dake musamman Sadeeq da Abdul, kuma dukkanin su na hango alamun k'aunarki a cikin ransu, hakan yasa na bari tukun sai na farfad'o da soyayyata da wasu suke k'ok'arin k'waceta daga gareni, kinji dalili wallahi banyi tunanin har zuwa yanzu ina ranki ba haka saboda ganinsu a tare dake, amma gani a gabanki guiwoyina a k'asa ina rok'on ki dan Allah ki amince ki taimaka ki sake shigowa rayuwata, wallahi a yanzu ke kad'ai ce abar da na rasa a rayuwata."



Amira tace " wallahi duk cikin su babu wanda na tab'a jin sonshi a raina, shak'uwa ce kawai da sabo amma ban tab'a sonsu ba kamar 'yan uwa na d'aukesu kuma abokan shawara."



"Dama wannan shine dalilin da yasa ka bisu d'aya bayan d'aya ka kashe su?" maganar da su Amir da Amira suka ji anyi kenan daga bayansu, koda suka juyo dukkansu ba wanda suka gani sai Insp Yahya, jingine da jikin k'ofa yana hard'e da hannayen shi.



Insp Yahya yace " wannan labarin da kunnena yaji ya k'ara tabbatar min da cewa kaine kayi kisan nan Amir, ko ba kai bane to kana da hannu a ciki."



Amira ta tashi tsaye tare da takawa har inda Insp Yahya yake tace " Insp rashin mutuncin naka ya isa haka, taya za'ai wai ka rik'a jifan Amir da wad'annan kalaman ko dan kaga ina dakatar dashi kan d'aukar mataki a kanka, karka manta ubana shine shugaban k'asar nan zai iya sanadin rabuwarka da aikin nan, kuma karka manta wanene kake fad'awa magana a kaina, jarumi ne shi kuma sadauki wanda zai iya yin komai a kaina."



Insp Yahya yai dariya sosai tare da tafa hannaye, sannan ya kalleta yace "gaskiya naji dad'in furucinki na k'arshe da kikace Amir zai iya yin komai a kanki, tunda kin tabbatar da haka bakya tunanin har kisa ma zai iya yi a kanki? ko kin manta cases d'in da aka yi a baya na dukan maza da yaita yi a kanki, kin manta furucin da ya yi a k'arshen ranar da na kulle shi a gabanki? to bari na tuna miki cewa ya yi in har za'a cigaba da tab'aki to bazai tab'a daina kai duka ba, wannan fa akan wanda ya kulaki ne kawai ko ya tab'aki Amira to ina ga kuma wanda yaji yace yana sonki ko yaga yana gwada miki k'auna."



Amira ta dakatar dashi tare da d'aga mishi hannu, tana nuna mishi k'ofa alamar ya fita ya bar mata gida, Insp Yahya yace "na tafi amma kiyi dogon tunani akai ki gani," yana kai nan a zancensa ya fita ya bar gidan.



Amira ta duk'e a k'asa tana dafa kai tare da fashewa da kuka, Amir ya k'araso zuwa inda take ya duk'a tare da dafata, fad'awa jikinsa tayi tana kuka tace " Amir d'ina kayi hak'uri dan Allah da k'azafin da wannan d'an sandan ke jifarka da su, babu wanda ya isa ya canza min ra'ayi a kanka, ni na fara tunani ma ko Dad ya sashi ya rik'a bibiyarmu, to wallahi Amir ko kisan kai ka yi a gabana ina tare da kai ban tab'a gudunka duk rintsi, nan fa sukai ta kuka daga k'arshe kuma suka rarrashi kansu, sauk'in da Amir yaji ma da bata yarda da zancen Insp ba.



Amir yace " bari inje gida in d'an kwanta duk da yamma tayi ma," Amira tace " ka kwanta a nan mana," Amir yace " a'a Amira kalli fa yanda na fito daga singileti sai gajeren wando ni tsoro na ma kar wannan masharrancin ya sake yimin wani sharrin."



Amira kuwa sai a lokacin ma ta lura da yanda yake, duk da halin da suke ciki amma be hanata dariya ba kamar me harda rik'e ciki tana nunashi tana dariya, shima sai a lokacin ne yai murmushi sannan yace " duk ba ke kika jamin ba kukanki ya birkita tunani da duk wani lissafi nawa ya sakani fitowa a haka ba, wallahi kaf duniya b'acin ranki kad'ai yafi komai d'aga hankalina balle kuma har inji kukanki sai inji kamar na haukace saboda tashin hankali, kafin had'uwa dake bana tunanin rayuwa tana da sauran amfani gareni kuma banyi tunanin zan samu canji haka ba, amma bayan had'uwa had'uwa dake na gane cewa wannan tunanin da nake kuskure ne, wallahi mijinki ya more da mata, iyayensa sun more da suruka yaranki sun more da uwa ta gari ina kaunarki Amirata."



Amira tai murmushi sannan tace "ina sonka Amir d'ina matarka zata more da kulawa tare da dad'ad'an kalamai," Amir yai murmushi sannan yace "zan tafi anjima zan dawo," Amira tace "wallahi idan muna tare bana so mu rabu Amir."



Amir yace "karki damu bazan d'auki lokaci me tsawo ba zan dawo gareki, wanka kawai zanyi domin baccin da nake ji ma ya gudu kamar yanda duk lokacin da kike cikin bak'in ciki walwalata ke guduwa hakama baccin da ke idona ya gudu na nemeshi na rasa," dukkanin su suka sakarwa juna murmushi sannan ya saka d'aya daga cikin kayan da zata wanke mishi dan tace bata yarda ya koma a haka ba matan dake waje su gane mata jikin miji, daga nan suka yi

11 / 31