Author : Bilkisu Z Ya'u Category : Romantic Hausa Novels
be gasgata zancenta ba saida yai waya tareda bada umurnin ai mishi binciken wanene Mahmud.
Bayan Dad ya gama wayar sai bambami yake shi kad'ai, yana cikin fad'a wayarsa tai 'kara, wani babban yaron Dad ne kuma aboki na wajen aiki mai suna Haladu wanda ya aminta dashi domin Dad ya maida shi tamkar d'an uwa saboda yardar dake tsakaninsu, abokinshi ne sosai, kuma suna tattauna dukkanin matsalolin su tare, kuma suna baiwa juna shawarwarin da suka dace, bayan haka Haladu yana d'aya daga cikin wad'anda Dad ya yarda dasu kuma yana d'aya daga cikin wad'anda suka san komai na harkar dukiyar Dad, yanzu haka Haladu shine shugaba a cikin d'aya daga cikin kamfanin Dad dake kano, kuma duk wasu harkoki nashi na kano Haladun ne ke kula dasu, a ta'kaice dai sun d'auki juna kamar 'yan uwa ba wai abokai ko bare ba kawai.
Bayan Dad ya d'aga suka gaisa sai Haladu yace "dama zan fad'a maka ne gobe insha Allah muna tafe zuwa gidanka ni da yaronka ze gaisheka, amma ya naji muryarka kamar kana cikin damuwa?"
Dad yace "kai dai bari kawai, tunda mijin Amira ya rasu gaba d'aya komai nata ya shiririce, na kawo mata wani domin su daidaita kansu shima ta koreshi," Haladu yace "ka kwantar da hankalinka, harda wannan maganar ma zai kawoni wajenka gobe insha Allah karka wani damu.
Nan suka yi sallama Dad ya ajiye wayar tare da sauke ajiyar zuciya sakamakon samun 'yar natsuwa da yayi, domin yasan in har Haladu yazo insha Allah zai samar mishi da mafita.
Washe gari ita dai Amira taga ana ta hidimar shirye shirye a cikin gidan, to da yake yanzu bata shiga lamarin kowa yasa bata tambaya ba ta zuba idanu taga wad'anda ake yiwa wannan shirin.
Dad ne ya shigo a bayanshi Haladu ne da d'ansa Nura suka shigo babban falo, kowa sai sannu da zuwa ake yi musu tun daga shigowarsu har suka zauna, nikam a zuciyata nace ga dukkan alamu Haladun nan yana da matsayi a wajen 'yan gidan nan, amma kamar ya dad'e baya zuwa inda suke.
Bayan an gaggaisa aka cika musu gabansu da abinciccika kala-kala, Dad yace a kira Amira itama tazo su gaisa, aka kirata ta gaishe su sannan ta koma cikin d'akinta, tun daga lokacin da Amira ta fito har ta koma Nura kallonta kawai yake yi, ga dukkan alamu ta tafi dashi, mahaifinsa Haladu yana lura dashi, a zuciyarsa yace bazan sha wahala ba wajen cimma manufata kenan.
Dad ne ya katse masa tunanin da yake yi ta hanyar fad'in Nura an girma, yanzu babu abinda ya rage sai ka fito mana da mata musha biki, Nura ya sosa 'keya tare da yin murmushi.
Amira ce ta fito daga cikin d'aki zata fita Dad ya kalleta yace "Doughter ina zakije?" Amira ta bashi amsa a ta'kaice tace "lambu zani shan iska," ta juya tare da ficewa, Haladu yace "Nura kaima kaje can kai hira da 'yar uwarka, muma ka barmu mu zanta nida d'an uwana."
Cikin rawar jiki kuwa ya fice ya nufi inda Amira take zaune yai mata sallama ta amsa sannan ya samu waje ya zauna, yace "'kanwata kwana biyu mun dad'e rabonmu da ganin juna," Amira tai banza dashi, can ya 'kara cewa "koda yake ke nasan baki sanni ba, sedai ni na dad'e sa saninki, domin kuwa kin dad'e da zama a cikin zuciyata da mafarkina sai yau Allah ya bayyanamin ke," nan ma tai shiru bata ce mishi komai ba, ya sake cewa "mutane nawa ne a duniya suka tab'a fad'a miki cewa in kika d'aure bakya yin kyau?" se anan ne tai mishi magana tace "mutum d'aya ne tak sunansa Amir," Nura yace "Allah sarki Amir mutumin kirki ai inada labarinsa nima, gaskiya samun masoyi kamarsa sai an tona," jin anzo inda take so wato maganar masoyinta yasa ta fara d'an amsa mishi jefi-jefi, shima ya dage sai hirar Amir d'in yake mata domin ya riga da ya gano cewa da hirarsa ne kad'ai zai iya samu tai magana dashi.
Dad ya kalli Haladu yace "ya kamfani ina fatan ana samun cigaba sosai?" gaban Haladu ya fad'i, amma sai ya dake yace ana samun cigaba sosai, kwanan nan ma zaka ji alart na biliyoyin kud'i na ribar da muka samu kad'ai," bayan sun gama wannan maganar suka gangaro magana kan Amira, Dad ya fad'awa Haladu abinda ke faruwa, Haladu yace "ikon Allah ashe dai na dad'e rabona da gidan nan ranka ya dad'e shiyasa duk wad'annan abubuwan suka faru ban sani ba.
Amma ga shawara guda biyu, na farko ka d'auketa daga garin nan muddin kana so ta manta da komai kuma walwalarta ta dawo, abu na biyu shine ka had'ata aure da yarona Nura in sun daidaita junan su kaga se ayi tuwona maina kenan."
Dad yai dum yana tunanin maganar da Haladu yazo masa da ita, tabbas yaji dad'in shawarar Haladu ta farko domin shima yana da tunani da kuma 'kudurin canza musu gari ko Allah zaisa ta sanadin haka 'yarsa ta manta da komai har farin cikinta ya dawo, sedai maganar had'a d'ansa aure da Amira gaskiya yana shakku saboda baya 'kaunar wani nashi ya auri talaka balle kuma ace 'yarsa ta cikinsa, amma saboda zuciyarshi na bashi wata 'kila ba mutuwa Amir yayi ba tunda har yanzu ba wanda yace musu yaga gawarsa, shi kuma da Amir ya dawo ya cigaba da zaman aure da Amira gwara ya aurawa Nuran ita, da wannan shawarar da zuciyarsa ta bashi ya yanke hukunci, ya kalli Haladu yace "gaskiya naji dad'in shawararka, Allah ya tabbatar mana da alkhairi, Allah yasa su fahimci junansu."
Amira da Nura sun dad'e suna hira kuma ba hirar kowa suke ba illah ta Amir, labari take ta bashi tun farkon had'uwarsu har zuwa yanzu, bayan ta gama bashi tace "a halin da ake ciki a yanzu rasashi da nayi ji nake kamar na rasa wani b'angare ne na jikina, kuma zuciyata na bani cewa nima ina gaf da binshi," Nura ya kalleta harda guntun hawayenshi irin na tausayi, yace "gaskiya na tausaya muku, kuma duk duniya babu inda na tab'a jin labarin cikakkun masoya irinku, nima ina ji a jikina kamar yanda kike ji har yanzu Amir na raye be mutu ba, zan tayaki Addu'a Allah ya bayyana miki shi, amma ina fatan zaki d'aukeni a matsayin aboki kuma d'an uwa sannan abokin shawararki?"
Amira ta numfasa sannan tace "ba damuwa, Nura yaji dad'i sosai, yai mata godiya, suna cikin magana sai ga su Dad sun fito, sunji dad'in yanda suka gansu, ga dukkan alamu abinda suka 'kudurta zai tabbata nan bada dad'ewa ba.
Nan suka yi sallama da Amira Dad ya bisu a motarsu domin rakasu har inda sukace zasu biya domin duba wani, suna cikin tafiya kamar ance Dad ya kalli gefen ti-ti ya hango wani yaro sak Amir cikin farar shadda ga sojoji da 'yan sanda da kuma masu ba'ka'ken kaya duk sun kewaye shi, cikin zaro idanu tare da jin fad'uwar gaba matsananci ya 'kwala mishi kira yace "Amir," cikin sauri kuwa Amir ya waigo amma be hango wanda ya kira sunanshi ba saboda motarsu ta riga da ta wuce, tunani ya shiga yi anya Amir ne kuwa, Amir fa'kiri ne baida komai, amma in ba shi bane meyasa ya waigo lokacin da na kira sunansa.
Haladu ya kalli Dad yace "lafiya ya naga yanayinka ya canza, wancan waye shi d'in?" Dad yace "shine annobar da ya rusamin farin cikin gidana gabad'aya ban tab'a tsammanin yana raye ba," Haladu yace in kuwa hakane to tabbas yana da kyau kayi gaggawar canza gari dan kuwa tunda har yana raye bazai tab'a barin Amira ba, wa ya sani ma ko d'an shan jini ne yarinya duk tabi ta 'karmashe ta lalace."
Babu abinda Dad ya 'kara cewa, har ya rakasu inda zasu sauka sukayi sallama ya juyo shi da masu tsaronsa, a hanyarsa ta dawowa ma saida ya sake duba wajen amma sedai kash baya nan, da wannan tunanin suka 'karasa gida tare da yanke shawarar cikin satin nan zai koma kano shi da iyalansa da zama.
Bayan tafiyar Dad Haladu ya kalli yaronsa Nura yace "my son ya kukayi da yarinyar ina fatan kun daidaita kanku?" Nura yace "Dad akwai matsala gaskiya, shawo kanta ta soni zaiyi matuk'ar wahala saboda akwai wanda ta ajiye a ranta kuma take zaman jira, Haladu yace "haba my son kaifa namiji ne kuma jajirtacce akan komai, meyasa zakai saurin karaya akan haka."
Nura yace "ba damuwa nasan yanda zanyi na shawo kanta ayi auren, amma na tabbatar ba zata soni ba."
Haladu yace "ai dama burinmu kenan ayi auren d'an baba," Nura yace "but Dad ni ina sonta fa, ba fatana muyi aure mu rabu ba," Haladu yai murmushi, sannan ya dafa kafad'ar Nura yace "kai yarone Nura, ba zaka gane komai ba sai nan gaba, kaidai yi 'ko'kari ka shawo kanta ayi auren.
…………………………………
*BAYAN SATI 'DAYA*
Abba ne zaune a falo matarsa na gasa mishi 'kafa da kuma goshinsa da yaji rauni.
Amir ne ya fad'o gidan a guje yana runtumawa mahaifinsa kira, ya 'karaso kusa dashi ya zube a 'kasa yana kuka yace "Abba kaga irinta ko, taya za'ai ace kana shugaban 'kasa kace baka son masu tsaro, kuma bayan kasan ba zaka rasa ma'kiya ba da 'yan adawa, yanzu gashi nan ana neman ranka, Abba ko so kake mu rasaka?"
Abba yai murmushi sannan yace "haba Amir kwantar da hankalinka mana, bafa su sami galaba a kaina ba, wad'annan raunikan da na ji duk wajen ceton raina ne ba su suka jimin ba, kayi shiru ka daina kuka Allah ya kub'utar dani daga sharrinsu, kuma a baya ma na shiga had'arurrukan da suka fi wad'annan."
Amir yace "gaskiya Dad in har kana son farin cikinmu to karka 'kara fita kai kad'ai, dan ni wallahi a kanka na fara jin shugaban 'kasa yace wai baya son masu tsaronshi na binshi a baya duk inda zai tafi, dan haka dan Allah Dad ka janye wannan ra'ayin naka, kaga ka sakamu kuka ni da Umma ka gani ko tunda na shigo naga tana ta faman kuka."
Abba Ahmad ya kalli Umma ya yafitota da hannu, cikin sauri kuwa ta rarrafo zuwa gareshi ya rungumeta da hannunshi na dama, sannan ya yafito Amir shima da hannu yai mishi kamar yanda yaiwa Umma da d'ayan hannun, sannan ya kallesu duka yace "ku kwantar da hankalinku, in dai akan wannan ne kuke kuka to bakwa 'kara zubar da hawayenku a karo na biyu domin kuwa na amince da bu'katarku dan haka ku share hawayenku," Amir ya sharewa Ummansa, itama ta share mishi, sannan suka sharewa Abba shima wanda yake kukan farin cikin samun iyali nagartattu.
Amir ya mi'ke tsaye sannan ya ajiye wayarshi yace bari yaje ya watsa ruwa ya fito, Amir na shiga ya cire kayanshi sannan ya d'aura tawul ya shiga wanka, bayan ya fito ya shirya tsaf agogo ne kad'ai bai d'aura ba, sai ya shiga duba agogon da zai shiga da kayansa, laluben shi ya kaishi har kan wata drower wadda tunda ya shigo d'akin be tab'a bi ta kanta ba, yana bud'ewa yaga hotuna birjik na yara ne guda biyu, d'aya yaro ne sosai dan bazai wuce shekara d'aya da wata uku ba, d'ayan kuma wani yaron ne a kusa dashi d'an shekara biyar, da yaron nan dan shekara d'aya da rabi da yaron nan d'an shekara biyar kamarsu har ta b'aci, banda d'aya ya girmi d'aya da cewa za'ai 'yan biyu ne su.
Abinda ya d'aurewa Amir kai shine yaron nan d'an shekara biyar kamarsu d'aya sak da Amir, sedai yasan tabbas ba shi bane wannan, to ina su Umma suka samo yaro mai kama dashi, kodai shine wanda ya b'ace suke nema, kardai ace su Umma iyayena ne? hotunan ya d'iba da sauri tare da yin falo domin samo tarin amsoshin dake ranshi.
Muje zuwa
*🅱K CE😘💋*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (🅱K)*
```(Autar marubuta)```
SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
```(Mamie)```
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```🤜🤛
*INA BU'KATAR ADDU'A DAGA GAREKU MASOYANA ALLAH YA BANI LAFIYA 'DORARRA*👏👏👏👏👏
PAGE 165 to 170
Amir ya fito daga d'akinshi cikin sauri tare da nufo iyayensa hannunshi ri'ke da hotunan da ya gani.
Zama yai kusa da Abbanshi sannan ya nuna mishi hotunan yace "Abba su waye wad'annan?" Abba Ahmad ya gyara zama tare da karb'ar hotunan yana kalla yace "yarana ne wad'anda na rasa, ya nuna mishi babban yace wannan shine Ammar, d'ayan kuma wato 'karamin sunanshi Bilal, shine wanda ya b'ata, babban kuma ya mutu ne."
Amir kuka yake sosai yana kallonsu, daga Ahamd har Khadija sunji tsoron halin da Amir ya shiga cikin 'kan'kanin lokaci daga tambayar hoto, nan suka shiga rarrashinsa domin yai shiru suji dalilin yin kukansa.
Amir ta kallesu yace "indai hotunan nan da na gani hoton 'ya'yanku ne to tabbas nine d'anku wanda ya b'ata nine d'anku wanda kuka dad'e kuna nema."
Amir ya d'auko wayarsa ya nuna mishi hotunansa lokacin yana 'karami da wanda ya d'auka shi kad'ai da wanda suka d'auka tare da Amira, bayan ya nuna musu na cikin waya sai ya shiga d'aki jikinsa na rawa ya kwaso mishi duk hotunan da ya nuna mishi a waya ya nuna musu a zahiri, Khadija ce ta mi'ke tsaye cikin sauri ta fizge hoton dake hannun Amir ta duba, haba kawai sai ga Khadija a 'kasa anyi suman farin ciki ne zamuce ko na firgicin ganin abinda bata yi tsammani ba.
Cikin hanzari suka watsa mata ruwan sanyi ta dawo hayyacinta amma har yanzu kuka take, ta rungume Amir gam kamar wadda za'a sake rabata dashi tana cigaba da kuka tare da godewa Allah da 'karfinta, Abba kanshi da yake namiji saida yai kukan farin ciki, Amir yace "Abba ashe dama kune iyayena ban sani ba Allah ya fad'o dani hannunku," Abba ya kalleshi yace "dama mu jinka muke kamar d'anda muka haifa tun ranar da muka fara ganinka," Amir yace "ina godewa Allah mahalicci da ya bayyanamin ku, kuma ya zab'amin ku a matsayin iyayena."
Umma kuwa ta kasa cewa komai banda kallonshi da take yi tare da cigaba da zubar da hawaye, fuskarta kuwa tana d'auke da farin ciki mara misaltuwa, Amir ya kalleta yace "Ummana bakice komai ba," Umma tace "Allah na gode maka da ka dawo da yarona gareni na sake ganinshi kafin ka d'auki raina," tana gama fad'in haka ta sake saka kuka me had'e da dariya, a ranar dai sai suka koma kamar zararru saboda tsabar farin cikin ganin yaron da suka rabu dashi tun yana 'karami, tun bashida wayau.
Bayan sun gama koke kokensu da murnar had'uwa da juna sai Amir ya kalli mahaifinshi yace Abba me ya faru har na b'ace daga gareku, kuma ina d'an'uwana Ammar?"
Abba yai shiru na wasu lokuta, sannan ya numfasa yace "My Son bana son tuno dukkanin abubuwan da suka wuce a baya, amma ya zama wajibi in fad'a maka komai, Abba ya sake numfasawa, sannan ya cigaba da fad'in "labarina ni da mahaifiyarka labari ne me tsawo, amma zan gajarta maka shi in baka shi a ta'kaice."
Amir yace "to Abba fara bani labarin ina saurarenka," Abba ya gyara zama sannan yace.
_"Kamar yanda ka sani ne sunana Ahmad, ni haifaffen garin Kontagora ne, iyayenmu mu biyu suka haifa, kuma tun muna yara har tasowarmu suna nuna mini 'kauna fiye da d'an uwana yayana Sunusi, wanda ni nasan ba komai yasa suka fi 'kaunata ba illah biyayyar da nake yi musu da kuma kyautata musu, amma ni kaina sam bana jin dad'in abinda iyayena suke yiwa Sunusi domin har akwai ranar da nai musu magana akan be dace suna fifitani akansa ba, sukace ba dan komai suke yin haka ba sai domin ya shiryu ya zama na 'kwarai ya daina abubuwan da yake yi, dan maganar gaskiya Sunusi baya ji kuma baya ganin girman iyayenmu sam, sedai da na nuna musu cewa ai yin hakan ga yaro irinshi kuskurene babba iyaye suke yi, domin tsana bata tab'a gyara kangararren yaro sedai ta 'kara busar mishi da zuciya, suka yi na'am da zancena, kuma daga ranar basu sake nuna mana bambanci ba a tsakanina dashi, to ada kafin nan idan iyayena suka yi wa Sunusi irin haka yana nuna jin haushinsa har yai zuciya da ni, to sedai ni kuma ina 'kaunar d'an uwana har ga Allah bana son ganinshi a irin wannan halin, hakan yasa ma har nakai ga yiwa iyayenmu magana su kuma suka gyara, to daga lokacin muka daidaita da d'an'uwana babu abinda ya sake shiga tsakaninmu har Allah ya rayamu muka girma, ni da Sunusi muna 'kaunar juna sosai, ko kad'an baya 'kaunar yaga wani abu ya sameni, kulawar da muke baiwa juna takai 'kololuwa, iyayenmu talakawa ne ba wasu masu kud'i bane, amma a haka sukaita fad'i tashi sukaita kula da karatunmu hakan yasa muka tashi da burika a ranmu rututu na ganin mun kyautatawa iyayenmu sunji dad'i ta dalalinmu, sedai kash, bayan mun kammala makaranta duk result d'in yayana basu yi kyau ba, ganin yanda yayana ya damu yasa na kwantar mishi da hankali tare da tabbatar mishi da cewa idan har na fara aiki albashina dai-dai zan ri'ka rabawa ni da shi kafin in nema mishi aiki a kusa dani, a zahiri ya nuna yaji dad'in haka, sedai a bad'ini ashe haushina da hassada ce a ransa, bayan na samu aiki a Abuja na fara zuwa duk albashin da na samu rabawa nake kamar yanda na fad'i in baiwa yayana Sunusi rabi in d'auki rabi, kuma ni nawa da yake garin namu a cikinsa ma mu a 'kauyen garin muke kuma duk talakawa ne irinmu, hakan yasa duk na d'auki albashina gaba d'aya talakawan nan nake raba mawa, da yake muna da 'karancin ruwa a wajen sai an sha wuya, hakan yasa shima nasa akai musu famfo da kuma burtsatse, nasha albarka da kuma addu'a wanda nasan sune sanadin da sukaja har nakai wannan matsayin a yanzu, ina matu'kar jin tausayin