SO MAHADIN RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVELS PDF BY BILKISU Z YAU.txt

Author :  Bilkisu Z Ya'u Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   17 / 31

48K to 51K   out of 90.7K words

shaidun da yake da su na tabbacin Amir yai kisan bayan wad'anda ya bayar, Insp Yahya ya kira wasu daga cikin student d'in makarantar guda uku su bada shaida, sedai dukkansu a bayanan su kaf sun tabbatar da cewa basu ga Amir ba a wannan daren, lokacin da Sadeeq ya shigo a buge Abdul ne ya biyo bayan shi ba Amir ba, bayan an sallame su sun koma sun zauna Alk'ali yace " Amir shima ya gabatar da shaidun sa wad'anda zasu tabbatar da baya nan ma aka yi kisan kuma be san ma da rasuwar ba sai washe gari da ya shigo makarantar domin d'aukar karatu.


kafin ma Amir ya bada amsa nan da nan gurin ya hargitse d'alibai sama da Ashirin suka d'aga hannayensu suna fad'in zasu bada shaida akan Amir besan komai ba hatta ma kisan, sai da ya shigo makarantar ya ga gawarshi, Allah sarki cikin masu d'aga hannu harda Amira jikinta har tsuma yake, Allah-Allah kawai take a kirata.


Al'kali ya buga guduma alamar kowa ya natsu yai shiru.


Bayan an natsu sai Al'kali yace " ya kamata ku gane nan kotu ne ba makaranta ba, dan haka kowa ya shiga taitayinsa har sai an kira mutum tukun, Al'kali ya cigaba da cewa amma idan na fahimta yawancinku kunsan duk abinda ke faruwa ko?" da 'karfi suka amsa da "eh" musamman Amira 'kararta tafi ta kowa harda mi'kewa tsaye sai da taga Al'kali ya kallo inda take tai sauri ta koma ta zauna, hakan da suka yi ya baiwa Al'kalin dariya wanda har saida ya murmusa, sannan ya jinjina farin jinin Amir gun mutane, ko be bincika ba hakan ya tabbatar mishi da yana da kyakkyawar ala'ka da mutane.


Alk'ali ya d'an yi rubutu, sannan ya d'ago yace " yanzu lokaci ya tafi, kuma akwai sauran cases a gaba, amma in Allah ya kaimu wani satin zamu dawo domin cigaba da sauraron wannan shari'ar."


Nan aka cigaba da gudanar da sauran k'ararrakin, ana gamawa kowa ya watse.


Aka fito da Amir da ankwa d'aure a hannunsa inda Amira ke bayanshi, su Insp suna biye da su, Amira ta kalli Amir shima ya kalleta suka kwashe da dariya, har aka saka su a bayan mota da wasu 'yan sandan, inda Insp ya shiga gaban motar shi da wani d'an sanda suka ja.


Suna cikin tafiya Amira ta sake yin dariya ta kalli inda Insp Yahya yake tace " Insp Yahya ya kaji shari'ar ta yau, kasan me? shari'ar yau tai dad'i, da alamu wani zai sha kunya, ta juya ga Amir tace Amir d'ina kaima kaji dad'in wasan yau a kotu ko?" Amir yace "sosai ma, wani 'kato zai sha kunya nan gaba kad'an," "Amira tace ai nasan dama nasara tana tare damu, ni fa wallahi saboda ina tare da kai har mantawa nake da wai muna cikin tashin hankali," suka kwashe da dariya, ya d'aga mata hannayenshi da ke cikin ankwa itama ta d'aga nata suka tafa, Insp ba bakin magana amma ya mugun hassala da maganganunsu, sai huci kawai yake, su kuwa cigaba da hirarsu suka yi yanda kasan ba abinda ke damunsu.






Muje zuwa






*πŸ…±K CEπŸ˜˜πŸ’‹*
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜









RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (πŸ…±K)*
```(Autar marubuta)```





SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
```(Mamien Bk)```





*πŸ‡ΈπŸ‡¦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```πŸ€œπŸ€›






*MADEENAT*
```(My Deenat)```
*Na gode sosai da kulawarki kan rashin lafiyata, Allah ya saka miki da mafificin alkhairinsa, Allah ya 'kara miki basira marubuciyar SAI NA KASHE MAHAIFIYATA, muna mugun jin dad'in novel d'innan naki a cigaba da antayo mana shi muna 'kwamushewa.πŸ˜‰πŸ˜˜*






*Babu wanda Allah yake nufinsa da alkhairi sai wanda ya sashi a hanyar addini, mu tashi, mu dage, musan addininmu, domin shine sanadin kasancewarmu cikin duniyar nan, Allah kasa mu dace.*






*AUNTY LIPSON*
(Maman Saleem)

*'Yar uwa ina ro'kon mahaliccina ya d'orar da lafiyarsa garekiπŸ‘πŸ˜°πŸ˜°πŸ˜°πŸ˜°πŸ˜°*






PAGE 125 to 130





Bayan sun isa station d'in aka sake gar'kame su Amir da Amira a cikin cell, Insp Yahya ya d'aga waya ya kira Dad d'in Amira yai mishi bayanin duk abinda ke faruwa, dai yai shiru na wasu lokuta, daga 'karshe yace su jira tukun suga yanda 'karshen shari'ar zai kasance, amma kafin zagayowar ranar zai turo 'kwararren lauya.



Bayan sun kammala wayar sunyi sallama Dad ya fara kai kawo a 'kerarren 'kayataccen d'akin shi, tunani yake a ranshi me ya kamata yaiwa yaron nan yana nema ya rabashi da 'yarshi, yaro d'aya tak ya zame mishi matsala yana nema ya zauta shi, cikin b'acin rai ya kaiwa iska naushi, tunani ya cigaba da yi yasan yana da damar da zai iya yin komai a kanshi ba tare da an sake koda waiwayen labarinsa ba ma, amma in yace zai b'atar dashi to siyasar shi yake ji, saboda sabon zab'e ya kusa, kawai mafita shine ya bari tukun a gama shari'ar in basu yi nasara ba sai ya nemo wata mafita amma bazai tab'a bari ya yarda ta auri Amir ba, da haka ya tsayar da tunanin tare da cigaba da harkokin shi.



*BAYAN SATI 'DAYA*

Yau litinin, kamar kullum yau ma kotu cike take ma'kil da mutane, Al'kali ya d'an yi rubuce-rubuce, sannan ya d'ago tare da fad'in " ina fatan dai masu 'kara da wanda ake 'kara sun tanaji lauyoyin su?"



Wani ne ya tashi cikin isa da ta'kama, ya sha ba'ka'ken kaya irin na lauyoyi, ya d'an rissina sannan yace " sunana barista Kamal Ibrahim lauyan gwamnati, ni ne nake wakiltar b'angaren wanda ke 'kara wato b'angaren Sadeeq," bayan ya kammala jawabinsa ya koma ya zauna.



Sai Al'kali ya kalli Amir yace "malam Amir kai baka da lauya ne?" har Amir ya bud'e baki zai yi magana kenan sai suka jiyo maganar wata matashiyar kyakkyawar mace ta shigo cikin takunta na 'kasaita, itama sanye take cikin kayan lauyoyi wad'anda suka yi matu'kar yi mata kyau, shigowa take tana magana tana fad'in "ayi ha'kuri ranka ya dad'e nazo a makare cinkoson ababen hawa ya hanani 'karasowa da wuri," ta k'araso wajen da aka tanada domin zaman su ta tsaya a tsaye tare da rissinawa tace "sunana barista Yasmeen Ahmad Abubakar, ni lauya ce me zaman kanta nice lauyar da ke kare wanda ake 'kara, wato Amir" tana gama fad'in haka ta samu waje ta zauna tana dudduba abubuwa a takardun dake gabanta.


Amir yayi matu'kar mamakin jin abinda Baristan nan tace, saboda shi yasan be d'auki lauya ba, kuma ba wani wanda sukai maganar d'aukar lauya dashi, kallon gefen da Amira take yayi ya d'aga mata gira da d'an d'aga kai alamar tambayar itace ta kawota, sai Amira tai murmushi sannan ta d'aga mishi kai itama alamar eh itace.



Barista Kamal ne ya fara mi'kewa yace "ina son kotu ta bani damar yiwa Amir da Amira tambayoyi," Al'kali yace "an baka, ina Amira take ta fito," Amira ta fito ta tsaya ya kusa da Amira, suka kalli juna suka sakarwa junansu murmushi, ni kuwa nace ikon Allah har a kotun ma sai kun nuna ku masoya ne.πŸ€”



Barista kamal ya matso kusa da inda su Amir suke a tsaye, sannan ya kalle su yace "bari na fara da kai Amir, lokacin da aka yi kisan Sadeeq kai kana ina ne?" Amir yace "ina gida," "amma ance an ganka da Sadeeq a ranar har kun yi wasan tsere harda Amiran ma kafin daren ranar?" barista kamal ya sake jeho mishi wata tambayar, Amir yace "tabbas munyi tsere da shi da Amira a ranar da za'a kashe shi da safe, shiyasa mutuwarshi ta girgizani sosai," barista yai murmushi sannan yace " me ke tsakaninku da Amira, ina nufin kuna soyayya ne?" Amir yace " eh muna soyayya da ita," barista yace wannan ne dalilin da yasa tun farko ka shirya kashe masoyinta Sadeeq sannan ka d'ora hujjojin laifin a kan Abdul aka kashe ahi baiji ba bai gani ba?" "objection my lord, abinda barista Yasmeen tace kenan cikin sauri tare da mi'kewa tsaye tace ya kamata lauyan masu 'kara yasan irin tambayoyin da ya kamata ya ri'ka yiwa Amir, domin har yanzu zargi ake a kanshi ba'a tabbatar ba da zai ri'ka d'aura alhakin kisan kai tsaye a kanshi, nagode ya mai girma mai shari'a," tana gama fad'in haka ta koma ta zauna, Al'kali ya kalli barista Kamal yace "barista Kamal ka kiyaye," barista yace "nagode ya mai girma mai shari'a, yana gama fad'in haka ya sake kai dubanshi kan Amir yace "meyasa baka bayyanawa Amira soyayyarka ba tun suna da rai sai da kaga sauran samarinta basa raye sannan ka nuna kana sonta?" Amir yace " tun lokacin ina sonta abinda yasa ban bayyana mata komai ba saboda naga kamar hankalinta yana kansu shiyasa ni na dannewa zuciyata," Barista Kamal yace " to nagode malam Amir, ya juya kan Amira yace saura ke Amira, kiyi mana bayanin yanda ala'kar Sadeeq da Abdul da Amir take da kanki," nan Amira ta koro bayani tiryan-tiryan, bayan ta kammala bayaninta sai yace " yanzu ke a tunaninki duk rashin jituwarsu d'aya zai iya kashe d'aya?" Amira tace "gaskiya a'a saboda koda Sadeeq ya rasu akace Abdul ne ya kashe shi zuciyata ta kasa yarda da hakan har yanzu, amma duba da yanayin rashin jituwarsu hakan zata iya faruwa tunda a bige akace Sadeeq d'in yake ba mamaki kokawa suka yi har takai ga faruwar haka," Barista Kamal yace " malama Amira nagode, ya juyo ya kalli Al'kali yace iya tambayoyina kenan ya mai girma me shari'a, amma yana da kyau kotu tai duba da wasu abubuwa, Amir da kansa yace ya dad'e yana 'kaunar Amira, amma meyasa be sanar da ita ba tun a lokacin ai mace allura ce cikin ruwa me rabo ke d'auka, Abin lura kawai anan shine yasan tunda hankalinta yana wajen su Sadeeq shiyasa ya dakatar da sanar da ita sai bayan ya cimma manufarsa na kashe su sannan ya zama ba wanda take tare dashi zai sanar da ita yasan a lokacin shawo kanta bazai mishi wahala ba kuma babu wani wanda zai yi takara da shi, iya abinda zan iya cewa kenan ya mai girma mai shari'a."



Al'kali ya d'an yi rubutu a takardar da ke gabansa, sannan ya d'ago kai ya kalli Barista Yasmeen yace "ko lauyar wanda ake 'kara tana da 'karin bayani ko hujjoji da zata gabatar a gaban kotu, ko tambaya da zatai wa su Amir?" Barista Yasmeen ta mi'ke sannan tace "eh ya mai shari'a ina ro'kon kotu da ta kira sani aboki ne ga su Sadeeq da Abdul, da kuma k'awar Amira guda d'aya, me suna preety sai d'aya daga cikin 'yan makarantar me suna Yusra wadda ba 'yar depertment d'insu bace," aka kira duk wad'anda ta lissafo suka fito suka tsaya a gaban kotu, nan tabi d'aya bayan d'aya tana tambayarsu halaye da d'abi'un Amir da yanayin mu'amalarsa da mutane, suka bata amsa da cewa shi mutum ne me kirki na gari baida abokin fad'a kuma baida hayaniya, sannan baya bari ko wanene yaci zarafin mata a gabansa, bayan sun gama koro bayani ta sallame su, sannan ta kalli Alk'ali tace " ya mai girma mai shari'a daga malamai har d'aliban makarantar kaf da za'a tara su a tambayesu abubuwa game da Amir tabbas duk amsa d'aya za'a samu wajensu cewar shi mutum ne na gari me kyakkyawar mu'amala da kowa, sannan ba abinda yasa a gaba sai karatunsa," ta 'karasa wajen su Amir da Amira tace "malam Amir meyasa kowa ke yabon halayenka," Amir yace " saboda kowa nawa ne, bana wula'kanta kowa dan bansan ranar da zasui min ba a nan gaba," Barista Yasmeen tace "wannan haka yake Amir halin mutum jarinsa gashi yau mutane fiye da daruruwa suna bada shaidar halayenka na gari sai ka gode wa Allah, malam Amir inaso ka fad'awa kotu da yaushe kuka gama wasan tseren da kukayi da su Sadeeq da Amira, ina ka tafi kai tsaye, da ina da ina kaje a wannan ranar, kuma kana ina a daren ranar da aka kashe Sadeeq? Amir yace "gaskiya na manta tym d'in da muka gama wasan tseren, daga nan kai tsaye gida na wuce na kwanta saboda bana jin dad'i, kuma a ranar tunda na dawo daga makaranta na shiga gida banje ko'ina ba ina gida kwance ko sallolina duk a gida na yi su," Barista Yasmeen ta kalli Amira tace "malama Amira na dawo kanki, yaushe kuka fara soyayya da Amir?" Amira tace "an kwana biyu gaskiya, zamu kai wajen shekara d'aya da rabi tare," Barista tace "nasan a iya wannan dad'ewar kin fahimci wanene Amir hakane?" Amira tace "eh sosai ma," Barista tace " kin karanci yana da wasu mugayen halaye, kuma a tunaninki Amir zai iya iya kisa?" Amira tace "gaskiya baida wani mummunan hali ko guda, kuma bana tunanin Amir ko kyankyaso wannan zai iya kashewa balle mutum," Barisata ta kalli Amir tace da gaske sai da su Abdul suka rasu ka bayyanar da soyayyarka ga Amira? Amir yace "eh hakane."



Barista Yasmeen ta kalli Alk'ali tace " ya me girma me shari'a wannan kotu me adalci tai duba na tsanaki kan Amir da Amira bayanai sun nuna basa nan lokacin da aka yi kisan kuma munyi bincike mun tabbatar da gaskiyar su in ana son tabbatarwa a tura jami'ai su sake zuwa suyi bincike akai, sannan Amir duniya ta shaida mutumin arzi'ki ne ta yiwu ya sadaukar da soyayyarsa ne a lokacin domin samar da farin cikin wasu, mutum ne shi mai damuwa da damuwar wasu yafi so akan komai shi ya rasa wasu su samu, hatta lakcarori da d'alibai mun d'auko bayanan su kan halayen Amir da suka bayyana mana gasu a tare da ni, sannan a baya anyi wannan case d'in a wata kotu An tabbatar da Amir ne yai kisan saboda ga hoton yatsun shi nan a jikin wu'kar duk nazo da wu'kar da ma ita kanta takardar likita da aka tabbatar da shaidar yatsun hannunsa, ana iya 'kara gwaji domin a 'kara tabbatarwa," barista ta kwaso dukkanin takardun da kuma wuk'ar ta bayar aka mi'ka su ga Al'kali, sannan tace "ina ro'kon wannan kotu me albarka da ta kori wannan 'karar ta kuma wanke Amir tare da yin hukunci ga masu son b'ata mishi suna," tai godiya sannan ta koma ta zauna, tana zama gaba d'aya kotu ta hau yi mata tafi, Al'kali ya tsawatar aka yi shiru sannan ya yi d'an rubutu, daga 'karshe ya d'ago yace "duba da yanayin lokaci mun d'aga sauraren wannan shari'ar sai sati mai zuwa, kuma a ranar zamu k'ar'kareta insha Allah," daga haka Al'kali ya buga guduma ya tashi ya fita sannan kowa aka watse d'aya bayan d'aya.








*Nima yasin cajina ya 'kare balle in le'ko muku wainar da za a toya a gaba*😜






Muje zuwa






*πŸ…±K CEπŸ˜˜πŸ’‹*
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜









RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (πŸ…±K)*
```(Autar marubuta)```





SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
```(Mamie)```





*πŸ‡ΈπŸ‡¦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```πŸ€œπŸ€›




PAGE 130 to 135






Bayan an fito da su Barista Yasmeen na tsaye dama a 'kofar kotun tana jiran fitowarsu, suna fitowa Amira taje suka rungume juna tare da yiwa Yasmeen godiya kan taimakon su da tayi, Amira ta kalli Amir ta nuna Yasmeen tace " 'kawata ce ita kuma aminiyata tun a makaranta, ta rigani farawa gashi kuma ta rigani kammalawa har ta samu aiki gashi muna amfana da aikin nata, Yasmeen nagode sosai ni kika taimaka a rayuwa wallahi, Allah saka miki da alkhairi, Yasmeen tai dariya, sannan tace " dukkaninmu godewa Allah zamu yi, domin shi ya bamu ikon yin nasara dan kinga wannan lauyan da ke kare masu 'kara ba'a kayar dashi a case ina ganinshi sai da naji fad'uwar gaba, amma da yake nai addu'a sai Allah yai ta bani nasara a kansu duk da dai na fishi shaidu da hujjoji, sai mu gode wa Allah," Amir ya kalleta yana murmushi yace " nagode," Insp Yahya yace "malamai sai ku wuce muje koh," Amira tace " gaskiya kam Yasmeen bari mu tafi gidanmu cell dan wallahi bacci nake ji ma ni," Yasmeen da Amir ta basu dariya sosai, suka yi sallama aka tasa 'keyarsu aka saka su a mota suka d'auki hanya.



A hanyar su ta komawa gidansu cell kamar yanda Amira ta fad'i sukai ta gode wa Allah kan nasarorin da yake basu.



Bayan an saka su a cell d'in ne Amir ya kalli Amira yace "malama ina da tambaya fa," Amira tace nasan tambayar, yanda aka yi na yi magana da 'kawata barista bayan ko da yaushe muna tare a gar'kame kake so ka sani koh, to kwantar da hankalinka yanzu zan fad'a maka, akwai ranar da aka kawo mana abinci har na ro'ki wanda ya kawo abincin a bani biro da littafi ya kuma bani har kana tambayata me zan yi dashi nace maka zan yi zanen lalle ne saboda ina son yin zane musamman na 'kunshi kala-kala saboda in munyi aure in ri'ka yi maka har kayi dariya, to a lokacin bayan mun ci abinci kayi bacci na rubuta wasi'ka cewa su taimakeni zan basu sa'ko su kaiwa Barista Yasmeen zan rubuta musu adress d'inta, in har suka kai min zan basu zoben hannuna wanda na siye shi 10k su siyar su ri'ke kud'in, bayan na gama rubutawa na saka a gefen farantin da muka gama cin abinci, can sai ga wani jami'i yazo d'aukar kwanikan a lokacin ne na mik'a mishi harda wasi'kar, bayan minti biyar sai gashi ya dawo yace in bashi sa'kon, yana tsaye na rubuta na m'i'ka mishi wasi'kar tare da sake yagar 'karamar takarda na rubuta mishi adress d'inta, har da lambar waya koda ya je ya tarar bata nan be sameta ba sai ya kira lambar, bayan minti talatin sai

17 / 31