Author : Bilkisu Z Ya'u Category : Romantic Hausa Novels
ma da yana tashi a shiga tasha ko cikin kasuwa domin samo abinda zai saka a bakinshi, amma yanzu baya zuwa ko ina saboda akwai me bashi.
Yana zaune ba dad'ewa sai ga Amira ta taho, tana zuwa ta tarar dashi yana kuka, zama tayi cikin sauri kusa dashi tana tambayarshi dalilin kukanshi, Ameeru cikin kuka yace " wani almajiri ne ya d'auke min tabarmar da na tara kud'i na siya nake kwana akai, da kwanon abincina, harda takalma na, ina k'ok'arin karb'a ya dukeni da aka taru ana tambaya yace wai nashi ne naje na sato, aka zane ni, jiba har ciwo ya jimin, ya d'aga hannunshi da guiwoyinshi yana nuna mata ciwukan, har gefen bakinshi ma ya fashe.
Kuka itama Amiran ta fashe da shi har Amir d'in ma yai shiru amma ita tana kuka, kallonta yake yana fad'in "kiyi shiru to nima na daina kukan ai."
Ya share mata hawayen da hannunsa, Amira ta mik'e tsaye tare da fad'in "ina zuwa," ta juya da gudu tai hanyar gidansu, ko da shigarta d'akin mahaifin ta ta shiga ta jawo drowar ajiye kud'in sa ta d'ibo masu yawa ko rufe drowar bata yi ba ta sake kwasawa a guje ta fito, da yake gidan su yana kusa da inda Ameeru d'in yake, koda isarshi ta mik'a mishi kud'in tare da fad'in ka siya wata tabarmar da takalmi, harda kaya ma ka siya, cikin farin ciki had'e da tsoro ya karb'i kud'in da bai tab'a ko tunanin ma zai rik'e irinsu ba ko a mafarki.
Ameeru yace " duka wannan nawa ne! kud'in ai sun yi yawa, ya zanyi dasu, k'wacewa ma za'ai," Amira tace " ai b'oyewa zaka yi inda baza'a gani ba, kad'an kad'an zaka rik'a kashewa, ya yi mata godiya, suka yi hira kad'an sannan tace bari ta koma gida kar a nemeta.
Tana kowama gida Mahaifin ta na fitowa daga cikin d'aki, yana tambayar waye ya bud'e mishi drowa, Amira tace " nice Dad," Dad yace " meyasa kika bud'e?" tace "na yi taimako ne da kud'in Dad, a makaranta malamin mu kullum yana yi mana nasiha akan me kud'i ya rik'a taimakawa mara shi, shiyasa na taimaki wani, kaima baka ganshi ba sai ka tausaya mishi in ka gan.........." kafin ta k'arasa magana Mahaifin ta ya daka mata tsawa abinda bai tab'a yi mata ba, aikuwa nan da nan ta razana tare da fara hawaye, ta ruga d'akin Mum d'inta tana kuka.
Dad ya zauna a d'aya daga cikin kujerun da suke falon nan, tare da zaunawa yana tunani gaskiya yarinyar nan ta fara canzawa, wani yaro ne wannan ta damu da lamuranshi haka, wayarshi ya d'auka ya kira d'aya daga cikin manyan security's d'in da ke kula da ita a ko ina musamman idan zata je makaranta, bayan yazo ya kalle shi yace " wane yaro ne Amira take min maganar shi kullum?" Securityn nan yace " ba d'an makarantar su bane, wani Almajiri ne a tsallaken bakin ti-tin unguwar nan da yake ta bayan gida, duk in zamu je makaranta tana tsayawa su gaisa sannan ta wuce, ai yarinyar akwai taimako da tausayi tun tana k'aramarta wall......." Dad ya katseshi cikin fushi me tsanani, yace " akwai taimako tabbas amma gashi nan ai ya jawo ta fara tunanin d'aukar min kud'i ba tare da ta tambayeni ba, zan canza mata makaranta kuma daga yau bana so ku sake barinta ta kula wannan yaron.
Yau Litinin da zumud'inta ta shirya tare da zarar kud'i cikin na break d'inta da d'aukar jaka ta fito, Dad d'inta ya kalleta yace " ai ba zaki cigaba da zuwa wannan makarantar ba, na canza miki makaranta Daughter na samo miki wadda tafi wannan kyau da tsada," an gama komai, ga ma uniform d'in nan zo kisa in kaiki da kaina," jiki a sanyaye ta k'arasa wajen Mahaifin nata ya cire mata na jikinta tare da saka mata na sabuwar makarantar da aka canza mata, yana lura da yanayin ta ya kalleta yai mata murmishi sannan yace " nasan me kike tunani, yaron nan kike tunani yau bazaki had'u dashi ba ko, to zamu biya ku gaisa sannan mu wuce makarantar," ai kuwa nan da nan ta saki ranta sai zubo mishi surutu ma take," Dad kaima kaje ka ganshi ko, ka tausaya mishi ko, yana ban tausayi Dad kuma inaso ka sashi makaranta kuma ya dawo gidanmu mu cigaba da zama tare," shi dai banda to da eh baya ce mata komai, bayan ta shirya suka fito security's suka taho da gudu aka bud'e musu mota suka shiga suka fita da motoci masu yawa kamar shugaban k'asa ne ya fito.
Suna k'arasowa kuwa suka ganshi yana zaune a wajen da ya saba zama, ga dukkanin alamu shima ita yake jira domin sai waige waige kawai yake yi, suna k'arasowa wajen shi Ameeru ya taso da sauri ta kalle shi ya canza kaya yai kyau, tace " kayi kyau sosai," Ameeru yai murmushi sannan yace "nagode," ya mik'a mata wani abu a cikin leda yace "dama ke naketa jira ki k'araso kin gani abubuwan da na siya miki," wani agogon roba ne ba ma na gasken nan ba irin wanda yara ke siya su d'aura, sannan ya ciro tabarau shima kalar agogon ya bata, ya sake ciro wani zobe k'ato da warwaro ya bata se dai zoben da tasa yai mata yawa, amma duk da haka tace tana so zata aje har ta girma sannan ta saka, duk da kasancewarta 'yar hamshak'in me kud'i amma haka taita murna akan kayanda dukkansu bazasu siya ribom d'in kanta guda d'aya ba, yanda suke murna hatta Mahaifin ta sai da yai mamaki, sai bayan sun gama murnarsu sannan ta nuna mishi Dad d'inta ya k'arasa kusa da shi ya durk'usa ya gaishe shi, Dad ya kalli wasu daga cikin security's d'in wajen yace su d'auke Ameeru daga nan baya so ya sake ganinshi a wajen nan, nan da nan suka sab'a shi a kafad'a yana zillewa yana kuka, itama Amira na k'wala mishi kira tana kuka, haka Dad d'inta ya jata ya turata cikin mota suka tafi makaranta, su kuma sauran suka tafi nisanta Ameeru da kusa da gidan su Amira.
Dad d'in Amira ya kalleta yace " ko kukan jini zaki yi sedai kiyi, karatu nakeso inga kin zage kinyi kafin ki fara tunanin taimakawa wasu ba shirme da shiririta ba.
Kuka take sosai kamar me har suka k'araso makarantar, ya yi magana da malaman wajen kan kar su rik'a barin Amira tana fitowa har sai an tashi.
Daga wannan ranar bata sake saka Ameeru a idanun ta ba, bata san kuma a wane hali yake ciki ba.
Kuma daga wannan lokacin ta daina walwalarta kamar yanda take yi ada, in ta dawo makaranta tana shigewa d'aki bata k'ara fitowa, haka zata tasa kayan da ya bata taita kuka, duk ta rame bata wani ko cin abincin kirki.
Bayan kwana biyu Dad ne da matar shi da Uncle shima da matarshi suna hira sai matar Dad tace " gaskiya halin da Amira take ciki kwanan nan ya fara bani tsoro, bata cin abinci duk ta rame kullum cikin kuka ta dena walwala, koda yaushe tana d'aki," Dad yace taje ta taho da ita, ta tashi ta tafi, tana zuwa d'akin ta tarar da jikinta yai zafi sai rawar sanyi take yi, hakan yasa ta dawo da sauri ta fad'awa Dad d'inta halinda take ciki, hakan yasa suka garzaya aka d'auketa sai asibiti, a asibitin ne Uncle ya kalli Yayan nashi yace " Yaya kasan yanda shak'uwa take tsakanin yaro da yaro, in kace zaka rabasu ta haka tunda sun saba ta rik'a shiga cikin irin wannan halin kenan, kaima ji yanda duk ka rud'e kafi kowa son yarinyar nan in wani abu ya sameta sai ka fimu shiga cikin tashin hankali, saboda haka tunda dama ta rok'i ka taimaka mishi to ko bazaka kawo shi cikin gidan nan ba be kamata ka rabasu ba sai kasa a kaishi koda gidan marayu ne, kuma kasa a sakashi a makarantar su kaga ka samarwa Amira da farin ciki kan taimakon da takeso taga kayi, kaima kuma hankalina zai fi kwanciya akan irin halinda take ciki a yanzu."
Suna cikin maganar ne sai ga kiran shugaban makarantar su Amira tana fad'a mishi cewa sam Amira bata maida hankali kan karatunta, banda ma tunani da kuka babu abinda take yi, ya kamata su binciketa kan abinda ke damunta.
Jin hakan yasa jikin Dad d'in Amira ya k'ara yin sanyi, babu abinda yafi k'auna sama da yaga 'yar shi ta maida hankali tai karatu ta zama wata abu a duniya ta d'aukaka fiye dashi ma, Uncle ya kalle shi yace " Yaya lafiya meyafaru?" Dad ya fad'a mishi duk abinda aka kira aka fad'a mishi yanzu, Uncle yace "to kaga irin ta ko, yara ba'a rabasu ta k'arfi da yaji in dai suka shak'u, ta dabara ake yi musu yaya, yanzu ina dad'i ace duk k'ok'arin da Amira keda shi ada ace yanzu babu shi, gaskiya kai tunani akai yaya kuma abinda Amira keso kayi abu ne me kyau fa wanda in kayi lada zaka samu tunda kaga ta fad'a mana labarinshi tun farkon had'uwarsu," Dad yace "shikenan zan yi amfani da shawararka Adam."
Bayan kwana biyu Amira ta gyagije Dad d'inta yai mata Albishir zai kai Ameeru gidan marayu kuma zai saka shi a makarantar su kamar yanda ta nema, tun daga lokacin farin ciki da walwalar Amira suka dawo, sedai abinda yafi damunta da d'aga hankalinta shine ina za'a ganshi, domin an dudduba ko ina da ake tunanin za'a sameshi ba'a ganshi ba, kullum sai sun fita nemanshi amma basa ganinshi, kamar wasa Amira tace a duba wajen da yake zama a wautarta wai tasan zai dawo ya jirata.
Ana dubawa wajen kuwa suka tarar dashi zaune ya kod'e yai bak'i ya rame yana ta kare ranar da take ta kashe mishi ido, tana fitowa daga cikin mota ta kwala mishi kira, yana waigowa ya hangota da gudu ta taho shima ya tashi da gudu suka rungume juna suna kuka, Ameeru cikin kuka yace " tunda kika tafi na dena samun abinci kalli yanda na rame, kud'in da kika bani wannan mugun ya k'wace, dan Allah karki sake tafiya ki barni," hatta Mahaifin nata da sauran tawagar sai da tausayin Ameeru ya saka su hawaye, d'an k'aramin yaro d'an shekara goma amma Sam be san jin dad'in rayuwa ba, Amira ta kalle shi tace "bazan sake tafiya ba, yau ma zamu tafi dakai za'a saka a makarantar mu, za'a kaika gidan marayu kusa da gidanmu nan zaka cigaba da zama muna tafiya makaranta tare."
Dad yace " kuzo mu tafi to sai kuyi hirar a hanya, cikin mota ma suka karad'e su da surutu, Ameeru yace kullum sai na tuno dake, kefa?" Amira tace nima haka ta nuna mishi hannunta tace kaga ma abubuwan da ka siyamun nasa," Ameeru yace "dagaske makarantarku za'a kaini, kuma zamu rink'a had'uwa dake har muna yin wasa?" Amira tace "eh mana," duk hirarsu Dad da uncle suna ji, zuciayar Dad ce ke sak'a mishi cewa tabbas ko yanzu yasan Amira bazata maida hankali ba kan karatunta, dole ya d'auki matakin da zai nisanta su da juna ko ba yanzu ba, cikin hikima ta yanda ba zata gane komai ba kuma ta yanda dole zata hak'ura dashi, har suka k'arasa gida tunanin da yake ta yi cikin ranshi kenan, tabbas yana son farin cikin 'yarshi amma tabbas baya son kasancewarta da yaron nan.
Muje zuwa
*π
±K CEππ*
ππππππππππ
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
ππππππππππ
RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (π
±K)*
```(Autar marubuta)```
SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
```(Mamie) ```
*πΈπ¦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah) ```π€π€
*Ina mik'a ta'aziyyata ga HAUWA JAMIL, na d'an'uwa da muka rasa, Allah ya ji kansa ya kyautata makwancinsa, Allah ya haskaka kabarinsa, ya yafe kurakurensa, Allah yasa mutuwar ta zamto hutu a gareshi yasa aljanna ce makomarsa, Allah ya bamu sa'an tarar dasu, ya k'ara muku hakurin jure rashi.πππππ*
PAGE 75 to 80
Ameeru yai kwana biyu a gidan su Amira hakan ya k'ara musu shak'uwa sosai, sannan aka d'aukeshi aka kaishi gidan marayun da yake kusa da gidan su Amira, bayan sun gama da nan aka kaishi makarantar su Amira aka gama mishi komai.
Tun daga wannan lokacin tare suke zuwa makaranta, idan Ameeru ya shirya sai ya taho gidan su Amira a d'auke su gaba d'aya a kaisu.
Tun daga wannan lokacin k'ok'arin Amira ya dawo sosai, sedai sam shi Ameeru baida k'ok'ari baya gane komai, to da yake ajin su Amira d'aya dashi idan an tashi break zama suke yi tai ta koya mishi tana nuna mishi itafa bata jin dad'in dariya da ake mishi kullum be iya komai ba, Ameeru ya bata amsa da zai dage yai karatu ko dan ita in ya girma ya kyautata mata kamar yanda itama tai mishi, cikin ikon Allah kuwa ya d'an fara ganewa.
Daga kan Malaman makarantar kaf har zuwa d'alibai Ameeru da Amira suna burge kowa, duk inda suka shiga sha'awarsu ake, had'in kansu da shak'uwarsu abun burgewa.
Ko laifi d'aya daga cikinsu yaiwa malami to basa yarda a hukunta d'aya, se dai a hukunta su gaba d'aya, idan horo aka baiwa d'aya dukkansu suke fitowa, in za'ai duka kuma dukkanin su suke mik'a hannu da wanda yai laifin da wanda be yi ba, kowanne daga cikin su k'ok'ari yake yaga an dakeshi shi an k'yale d'an uwansa, wannan shak'uwar tasu ce tasa suka k'ara burge kowa, kuma kowane malami yake k'aunarsu.
Abu d'aya ne yake damun Dad d'in Amira shine, Ameeru baya so koda kallon banza aiwa Amira balle har a tab'a lafiyar jikinta in kuwa kai mata hmmm, yasha targad'a yara da karyasu kai raunika iri-iri a kan Amira, iyayensu na zuwa suna kai k'ara gun shugaban makarantar, da abun ya ishe su sai shugaban makarantar ya kira Dad d'in Amira ya sanar dashi.
Kuma kullum Ameeru yai fad'a kan Amira sai an zane shi, amma hakan be hana shi gobe ma ya yi, shi in za'a tab'ata sau dubu to shima zaiyi fad'a a kanta sau dubu, dukan da ake yi mishi sam be damunsa.
Zaune Ameeru yake a kusa da ajinsu, koyarwa ma ake yi a ajin, wani ya harari Amira ya mareshi, shine malamin ya zaneshi kuma yace ya fito ya bar mishi ajinshi ya saka guiwarsa a rana har sai ya gama ya fito.
Amira na ganin an koreshi itama ta fito, malamin su na kira amma ina sai ma ta danno a guje tazo kusa dashi itama tayi irin horon da aka sashi, suka kalli juna sukai murmushi, Ameeru yace " wato saida kika fito ko," Amira tace " eh mana kana waje saboda ni sai in zauna a ciki," suka yi dariya sannan Amira ta sake kallon shi tace " meyasa kake fad'a a kaina Ameeru?" Amir yace saboda ina sonki, kuma bazan tab'a bari a tab'aki ina kallo ba," Amira tai dariya tace " laaaa ashe kaima kana sona," dukkansu suka sa dariyar murnar suna k'aunar juna, Amira ta sake kallonshi tace " jiya Dad ya kirani yace wai anyi mishi waya ance bama k'ok'ari a makaranta, sai nace mishi eh mana Dad koyaushe cikin karb'ar hukunci muke," Ameeru yace " ni fa tsoron Dad nake kar ya dukeni," Amira ta b'ata rai tana fad'in ka tab'a ganin ya dukemu ne," sufa gaba d'aya rayuwarsu basu da matsala muddin suna tare.
Abun nasu fa sai gaba gaba yake sun fitini kowa dan yanzu itama Amira in d'alibai suka daki Ameeru taron dangi suke yi su biyu su daki koma waye, sannan itama haka in ita aka tab'a taruwa suke su daki mutum, gaba d'aya makarantar yanzu shakkar su ake.
Akwai ranar da Amira ta taho da gudu tana fad'awa Ameeru ga wani can yazo yace yana sonta, da gudunsu dukaje shima suka yi mishi duka, ashe sun mishi targad'e a hannu, tun daga ranar Ameeru ke bawa duk yaron da yaga ya kula Amira kashi, in ma be gani ba ita tana fad'a mishi, domin ta sanar dashi tana jin dad'in yanda yake cin uban mutane a kanta.
Abu fa ya ishi Dad d'in Amira kullum cikin waya ake mishi sunyi kaza da kaza, hakan yasa ya fara tunanin lallai muddin yana so 'yarshi tai karatu to sai ya bar garin nan sun koma wani garin da zama, akan wannan shawarar ya tsaya.
Zaune suke a falo dukkanin 'yan gidan Dad ya fad'a musu shawarar da ya yanke, kuma yace ya gama magana babu me canza mishi, zasu koma gidanshi da yake kano saboda 'yaranshi sami ilimi me kyau, kuma ya fad'a musu akan 'yarshi babu abinda bazai iya yi ba kuma zai iya barin k'asar ma da ita domin ta samu ilimin da yake buri, sun riga da sun san halinshi murd'ad'd'en mutum ne in ya kafe a abu juyo dashi abune me wahala, sun gama maganar kenan sai ga Amira ta dawo daga makaranta, tana shigowa Dad d'inta ya kalleta yace " oyoyo My Daughter, zo in miki albishir zamu je kai ziyara kano gobe in Allah ya kaimu, amma bazamu dad'e ba zamu dawo, kuma in har kina sona kuma kina son farin ciki na ban yarda ki b'ata rai ba ko kiy kuka," Amira ta kalle shi tace " harda Ameeru na za'a tafi?" Dad yace a'a ai ba zamu dad'e ba zamu dawo, " ita har ga Allah bata son tafiyar nan, amma sai tace