Author : Bilkisu Z Ya'u Category : Romantic Hausa Novels
fito ba," Amir yace " kaiiii na jira ki har na gaji baki zo ba."
Amira ta zuba abincin itama ta fara ci, suna ci suna hira har suka gama.
Haka suka cigaba da gudanar da rayuwar su, koda yaushe suna tare, kuma komai tare suke yi, hatta girki tare suke yi, gyaran gidan tare suke yi, cin abinci a tare, hakan ya k'ara musu matsananciyar shak'uwa mai tsanani a tsakanin su, tsakanin Amir da gidansa se dai ya koma da dare ya kwanta gari na wayewa ya sake fitowa sai gidan amira.
Yau ya rage musu saura kwana d'aya tak a koma makaranta hakan yasa suka fara shirin komawa.
Bayan sun koma makaranta Amira taga canji sosai a makarantar su, domin duk wad'anda ta shak'u da su sun gujeta, ko cikinsu taje d'aya bayan d'aya suke guduwa, a tunanin su duk wanda ke tare da ita kashe shi ake yi, a aji ma haka ita da Amir kad'ai suke zama waje d'aya babu wanda yake shiga harkarta da shi kanshi Amir d'in.
Wannan canjin yai matuk'ar d'aga musu hankali daga Amiran har Amir d'in.
A ranar da ta fara ganin wannan canjin bata ma gama lecture ba ta bar makarantar, tana komawa gida taita kuka kamar ranta zai fita.
Amir ya fito daga lecture ya nemi Amira ya rasa, ya kira wayarta amma bata d'aga ba, ba shiri ya figi motarsa sai gidan Amira, ko motar be kashe ba ya fito ba tare da ya rufe murfin motar ba ya shige gidan, zaune ya ganta kan kujera ta kifa kai da gwiwa tana kuka, wata irin doguwar ajiyar zuciya ya saki na jin dad'in ganinta.
Amir ya k'arasa inda take ya zauna, kallonta ya yi sannan yace " ba sai na tambayeki dalilin kukanki ba Amira tunda na riga da nasan dalili, se dai ina mamakin inda tunaninki ya tafi kika manta cewa akwai wani bawan Allah guda d'aya a gefenki wanda yake da niyyar faranta miki har k'arshen rayuwa, ya kamata a ranki kiji in duk duniya ta gujeki to mutum d'ayan nan tak ya wakilci dukkanin mutanen duniya a wajenki, Amira kukan ki yasa naji ba dad'i gani nake kamar na gaza wajen baki dukkanin farin ciki da kuma mantar dake kowane irin b'acin rai da na alk'awarta, kiyi hak'uri ki daina kukan nan zuciyata na fitar da wani irin tiririn zafi.
Ta daina kukan da taimakon Allah da taimakon nagartattun kalaman shi, labarai ya fara bata na ban dariya yace " bari na baki wani labari."
_"lokacin da nake boarding a secondary school muna kwakkwance da dare wajen k'arfe takwas ina karatu sai fitsari ya matseni, inata juyi nak'i tashi inje in yi kuma ban dena juyin ba, wanda yake can saman gadona yana kwance yana kallona, zabura nayi da gudu dan inje in yi futsarin, se dai gani nai wanda ke can saman gadona yazo ya rigani shallakewa a guje, ina ganin ya d'iba a guje sai nima na bishi a guje, shi kuma koda ya juyo yaga na biyo shi sai ya k'ara dannawa a guje sauran d'alibai kowa sai gudu, saida suka ci karo da malam ya tsayar da shi yana tamayarsa me ya faru yace malam Amir ne yaga wani abu shine na gudu kafin abun k'araso kaina, koda na k'araso malam ya tambayeni me na gani nace malam banga komai ba, akace to meyasa kake gudu nace wannan naga ya runtumo a guje shine na biyo shi, malam ya sake tambayata me yasa na zabura daga kwance nace futsari ne ya matseni, mallam yai dariya mai isarsa, sannan yace shi yana gudunka kai kuma kana gudun abinda yake wa gudu baka san cewa kai yake gudun mawa ba kar abinda yai tunanin ya biyoka ya cimmashi, su kuma sauran d'alibai suna gudun rashin dalili, to ku wuce kuje ku kwanta Allah ya shiryeku tsoro kamar kuraye, malam yana juyawa zai tafi gidanshi sai d'aya daga cikinmu yace malam ga wani abu nan yana binka a baya ai ko juyowa malam be yi ba ya runtuma a guje sai gida d'alibai kowa akaita yi mishi dariya."_
Amira saboda tsabar dariya harda hawaye, a kan kujera take amma har ta kai k'asa tana rik'e ciki, tana dariyar ne taji Amir yace " Amira ina son......., Amira cikin dariyar labarin da ya bata tace "me kake so?" Amir yace " ke nake so, ina sonki Amira."
Lokaci d'aya dariyarta ta tsaya cak, ta mik'e tsaye, shima ya mik'e suna kallon juna, Amira tace " d'an maimaita abinda ka fad'i yanzu," Amir yace " cewa nai ina sonki Amira."
Amira ta zaro idanu jin abinda yace tare da d'aga hannunta ta wanka mishi mari har uku.
Muje zuwa
*π
±K CEππ*
ππππππππππ
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
ππππππππππ
*RUBUTAWA*
*BILKISU Z. YA'U (π
±K)*
```(Autar marubuta)```
SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
```(Mamie)```
_ina matuk'ar jin dad'in yanda kuke k'aunar wannan novel d'in, da yanda kuke tattaunawa akai masoyan *SO MAHA'DIN RAYUWA* ina godiya kuma ina alfahari da ku wallahi I hrt u allππ_
_'yan uwa muna barar addu'arku *Kaduna* ba lafiya Allah ya kawo mana k'arshen wannan bala'o'in dake addabar mu a rayuwa._
PAGE 45 to 50
Amira ta kalle shi ta sake wanka mishi mari cikon na hud'u, sannan ta kama hannun shi ta jashi har k'ofar d'aki ta tura shi waje sannan ta maida k'ofarta ta rufe tare da dark'ushewa a jikin k'ofar tana kuka.
Amir daga waje bugun k'ofar yake yi kamar me, yana fad'in " Amira kece tubali na ginina, kuma kece *mahad'in rayuwata,* har ina jin babu sauran numfashi a tare da ni duk ranar da bana tare da ke, ki duba yanda muka shak'u da juna kiy min sassauci dan Allah, koda bakya k'aunata ki bar zuciyata ta rab'u da taki," yana magana yana kuka tare da cigaba da buga k'ofar.
Amira ganin ya fara karya mata zuciya yasa ta tashi ta bar bakin k'ofar ta koma kan kujera ta zauna, ji ta yi ta zauna kan wani abu ta d'aga bak'ar ledar da Amir ya shigo da ita ce, bud'e ledar ta yi, wani k'aramin kwali ne a ciki sai wani kati me d'auke da kalamai na so, kwalin ta fara bud'ewa wani had'ad'd'en zobe ta gani na zinare da na azurfa, Amira mamaki kawai take yanda akai ya san irin zobunan da tafi so a rayuwarta.
Tsintar kanta ta yi da ciro su d'aya bayan d'aya ta saka a hannunta, ai kuwa sun yi mata kyau sosai kamar dama don ita kad'ai aka had'a su.
Katin nan ta ciro ta fara karantawa
_So wani abu ne da yake jigatar da zuciya ya cikata da damuwa a wasu lokutan, amma tunda na same ki nasan zaki zamo min maganin warakar dukkan wata damuwata a so, dan Allah ki taimaka ki amince da ni mu rayu tare._
Bayan ta gama karantawa ta yi ajiyar zuciya tare da juya bayan katin taga an rubuta
_Amira ta Amir_
Amir ne ya cigaba da bugun k'ofar tare da yin magana da k'arfi yanda zata ji, yana kuka yace " Amira ya kike so in yi ne wai, da k'aunarki da ta maida ni tamkar mahaukaci zan ji ko da hukuncin da kike min a yanzu, haba Amira ki ji tausayina mana, ki tausayawa zuciyar da bata san komai ba sai so da k'aunarki da kuma farin cikin ki, karki barta mu rayu tare mu mutu tare dan Allah, wallahi in baki bud'e min k'ofar ba zan kwana a nan."
Amira tana jin duk abinda Amir yake cewa, itama kuka take sosai amma har yanzu bata da niyya ko alamar zuwa ta bud'e mishi k'ofar.
A haka suka kasance abinda ke tayar da Amir daga bakin k'ofar nan sallah ce kad'ai har dare ya rufa yana zaune bakin k'ofar, itama Amira a falo ta kwanta se dai bacci babu shi a idanun su duka daga Amir d'in har Amira.
Amir rakub'ewa ya yi a jikin k'ofar ya kwanta kamar wani mara gata, a haka suka kasance har zuwa k'arfe uku na dare idanun su biyu, se dai ita Amira duk a tunaninta Amir ya tafi gida saboda jinshi shiru.
Amira ta ji gabanta ya fad'i a zuciyarta tace yanzu idan har yanzu yana waje fa, mik'ewa tsaye ta yi, so take kawai ta tabbatar yana nan ko baya nan lek'awa ta yi ta windon d'akin amma da yake windon a can gefe yake bata hango k'ofar d'akin ta ciki, hakan yasa ta hak'ura ta koma kan kujera ta kwanta.
Amir sanyi ne ya fara kad'a shi, nan da nan ya fara rawar sanyi, zazzab'i ya fara kama shi.
Washe gari wajen k'arfe takwas Amira ta gama shirin tafiya makaranta, haka ta tashi sukuku ba k'arfi a jikinta, abun kari kuwa dama bata ta tashi, bud'e k'ofar ta yi domin tafiya ta ci karo da Amir kwance a bakin k'ofar, shima jin bud'ewar ne yasa ya bud'e idanun da su kansu zafi suke yi mishi saboda ciwon kai.
Jakarta ta yar, tare da duk'awa inda yake cikin sauri ta tallabo shi sannan ta fashe da wani irin kuka jin jikin shi da ta yi kamar garwashi saboda zafi, tabbas tasan a nan ya kwana.
Amira kuka take tana fad'in baka da hankali ne Amir, meyasa zaka kwana a nan," ta sake fashewa da kuka.
Amir cikin wahalalliyar murya yana fitar da numfashi da k'yar yace " ina hankali da tunani ga wanda yai zurfi a so, dan Allah Amira karki gujeni, ki amince da ni, Sonki ne *mahad'in rayuwata,"* hawaye ne yake gangarowa kan fuskar shi, a yayin da Amira kuma ke kuka sosai kanshi yana jikinta tama rasa da me zata fara taimaka mishi, ji ta yi yai mata nauyi a jiki, ta jijjiga shi tana fad'in tashi in kama ka mu shiga ciki," ina babu amsa Amir ya sume.
Rud'ewa ta yi tana kurma kuka me d'an karen k'ara tana fad'in "shikenan na kashe shi."
Sauke kanshi ta yi daga jikin ta, ta fita waje neman taimako, wani dattijo ne Allah ya had'ata da shi suka shigo tare har zuwa inda Amir yake, tab'a shi ya yi, yace ta kawo mishi ruwan sanyi, da gudu Amira ta shiga ciki ta fito da ruwa a gora ta kawo mishi, karb'a ya yi, ya bud'e ya zuba a hannu ya shafa mishi a fuska da wuraren wuyan shi, ya ajiye ruwan a gefe, ba'a fi minti biyar ba da watsa mishi ruwan sai ya fara motsi da hannu tare da k'ok'arin bud'e ido, bakin shi na ambaton sunan Amira.
Wannan tsohon yace " Alhamdulillah tashi ki kama shi mu shiga da shi ciki," suka kama shi suka kaishi cikin d'aki suka kwantar dashi kan kujera.
Tsohon nan ya kalleta yace " ki samu ruwa me sanyi da tawul ko tsumma ki rik'a sawa cikin ruwan sanyin kina goge mishi jikin shi saboda a samu zazzab'in jikin shi ya sauka, Allah ya k'ara sauk'i."
Amira tace " ameen Baba, nagode da taimakon da kai min Allah saka da alkhairi," bayan tafiyar wannan tsohon Amira ta yi duk yanda ya fad'a mata cikin ikon Allah zazzab'in ya fara sauka, kuma sai a lokacin ya samu bacci.
Itama Amira tana zaune a doguwar kujerar ta jingina, shi kuma Amir yana kwance kanshi na jikin Amira hannunta na dafe da jikinshi a haka dukkan su bacci ya d'auke su suna ramuwar na jiya da basu samu sun yi ba.
Sai wajen k'arfe d'aya Amira ta tashi, cikin sauri ta zame kan Amir daga jikinta ta kwantar da shi kan kujerar sannan ta yo alwala tai sallah, bayan ta idar ta fad'a kicin domin nema musu abinda zasu ci.
Jelop d'in taliya tai musu wadda ta ji kayan ciki, _ni kuwa BK har ina had'iye miyau ina fad'in Allah sa su rage min, saura makaranta kuce inada kwad'ayiβΉπ_
Bayan ta gama girkin ta zuba a kula tana jira sai ya tashi su ci tare kamar yanda suka saba.
Amira ta ci gaba da gyara ko'ina na gidan, sannan ta turare ko ina, a tak'aice dai ranar dukkan su ba wanda ya lek'a makaranta, ta fad'a band'aki ta shek'a wanka sannan ta fito, bayan tai wanka ta shirya cikin riga da siket na atamfa wad'anda suka yi matuk'ar yi mata kyau, kuma sun karb'i jikinta sosai, hakan yasa kyawunta ya k'ara fitowa fili ya k'ara bayyana.
Falon ta dawo ta tarar Amir ya tashi amma har lokacin yana kwance, cikin hanzari ta k'arasa kusa da shi ta daga kanshi ta zauna sannan ta maida kanshi jikinta ta kwantar kamar yanda suke a d'azu ta kalle shi tace " sannu Amir ya jikin, Allah k'ara sauk'i, yanzu me ke damunka, ko zamu tafi asibiti ne?"
Amir binta kawai yake da kallo yana mamakinta, gashi dai a haka ta damu da shi amma kuma bata son shi, kallonta ya yi sannan yace " ba sai mun je asibiti ba zazzab'in ya sauka mura ce kawai sai ciwon kai, suma a hankali zasu warware, amma Amira ni maganin dukkanin wata cuta tawa tana wajenki, soyayyarki nake nema kin hana ni ban san dalilin ki na yi min hakan ba."
Amira tace " yanzu dai mu bar wannan maganar har sai kaji Sauk'i," ta zuba musu abinci suka ci, bayan sun gama ta zuba mishi ruwan wanka yaje ya watsa ruwa, bayan ya gama ta bashi t.shet d'inta da jeans yasa duk sun matse shi amma haka nan zai saka tunda nashi sun yi datti, se dai kayan sun yi mishi kyau sosai.
Tun daga ranar kayanta yake sakawa har Allah ya bashi lafiya, yau kwanan shi uku kenan a gidan, tattali kam da gata ya sha shi, hakan ya k'ara sa mishi son mallakar Amira matsayin matar aure.
Yau lahadi ba makaranta, Amir ne zaune gaban Amira ya k'ureta da idanu, kallon shi tayi tace " yallab'ai lafiya kake kallona haka?" Amir ya numfasa sannan yace " Amira bana gajiya da kallon wannan kyakkyawar fuskar, Amira ina sonki k'aunarki ta kama zuciyata, dan Allah ki amince da ni,"
Amira ta share shi tare da kawar da kai, Amir ya taso daga inda yake zaune ya tsugunna a gabanta yana zubar da hawaye sannan ya dafata yace " Amira wallahi in na rasaki mutuwa zan yi, ki taimake ni so nake in mallake ki matsayin matar aure mu yi rayuwa dake ta har abada, ki karb'i tayin soyayyata."
A fusace Amira ta juyo ta sake d'aga hannu ta wanka mishi mari wanda ya fi ukun da tai mishi a baya zafi, sannan sai ta fara kuka itama, zamowa tai daga kan kujera ta tsugunna a gabanshi sannan ta kalli Amir wanda yake dafe da kuncin shi har yanzu yana binta da kallo.
Kama kwalar rigar shi tai kamar zata yi dambe da shi tana jijjiga shi tace " kasan kana sona meyasa zaka b'ata lokaci wajen fad'a min, meyasa ka d'auki tsawon lokaci kafin ka sanar min iyeeeee, kasan iya tsawon lokacin da na d'auka ina jiran zuwan wannan ranar da zaka furta kana sona, to in baka sani ba ka sani tun had'uwar farko yanayin kallonka ya tabbatar min da kana sona, kuma nima tun ranar na kamu da k'aunarka, amma shine zaka tsaya jamin aji, kana turo da sak'onni a b'oye yanzu da ka rasani fa wani ya aureni kasa mun yi asarar juna," jijjiga shi take yi da k'arfi, can sai ta kwantar da kanta a k'irjin shi tana ci gaba da kuka, cikin kukan ta cigaba da fad'in na d'auki alk'awarin hora duk wanda na gano shine me turo min da sak'onni duk da dama zuciyata ta dad'e tana bani cewa kai ne, na so in hukunta ka amma saboda k'aunar da nake maka tai min yawa shi ya hanani yin hukunci a gareka."
Amir kam farin ciki ba'a magana, ko a haka Amira ta tsaya ya san tana k'aunarsa, kusan ma zai iya cewa lokaci d'aya suka kamu da k'aunar juna, d'agota ya yi sannan ya share mata hawayen dake fuskarta, itama ta share mishi na shi, sannan suka kalli juna suka sakarwa junan su murmushi, Amir yace " ai ko a haka aka barni na horu wallahi, amma meyasa kika mareni?" Amira ta kalle shi tace " ladan k'in fad'a min sirrin zuciyarka da ka yi da wuri har sai da k'aunarka ta gama galabaitar da tawa zuciyar sannan ka fad'a min, Allah naji haushin rashin sanar min da ka k'i yi kan lokaci, kuma har kana ikirarin kana k'aunata amma ka iya b'oyewa tsawon lokuta, bayan ni nasan zuciya babu abinda ya kaita tonon asiri, tuni ta bankad'eka na gane kana k'aunata ta yanayin tattalinka, kulawarka, damuwarka a kaina, kawai na zuba maka ido ne ka gama kewaye kewayen ka."
Amir yai murmishi, sannan yace " amma fa gaskiya na maru," Amira tai murmushi itama sannan tace " shine salon naka tukuicin soyayyar," dukkan su suka kwashe da dariya sannan suka rungume juna.
_ina barar addu'arku masoya Allah ya d'orar min da lafiya.π_
Muje zuwa
*π
±K CEππ*
ππππππππππ
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
ππππππππππ
RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (π
±K)*
```(Autar marubuta)```
SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
```(Mamie) ```
*πΈπ¦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```(Gidan