Author : Bilkisu Z Ya'u Category : Romantic Hausa Novels
yanzu gashi nan ai kana komai da kanka, kai kasan ma'abocin taimako ne, kai na talakawa ne, be dace ace baka fita da kowa ba sai mu kad'ai."
Ahmad yai murmushi yace "idan bu'katar hakan ta taso ina nemansu ai, ni dai kawai bana so suna bina a baya gaskiya, ba burina duk inda na fita aga jerin motoci suna kewaye da ni ba, nafi so in ri'ka fita ni kad'ai, bana son duk wani abu da zai yi silar saka min girman kai da d'agawa ya jawo in nisanci talakawa na."
Asibitin suka 'karaso shiyasa ya dakata da maganar, cikin sauri suka fito, aka kira norses aka d'aukeshi kamar matacce aka shiga dashi cikin emergency.
Khadija ta kalli mijinta Ahmad tace "Allah sarki Allah kad'ai yasan halin da iyayensa suke ciki a yanzu, kyakkyawan yaro dashi," nan da nan 'kwalla ta taru a idanunta tana nema tai kuka, Ahmad ya 'karaso kusa da ita, sannan yace "zaki fara ko, kina farawa nima zan tayaki wallahi kuma kinsan zan iya, yanzu kiga kukana ya tara miki jama'a domin kinsan kukan namiji akwai tada hankali saboda an san ba 'karamin abu bane zai saka maza yin kuka."
Khadija ta share hawayenta tare da yin murmushi, shima Ahmad murmushi yayi, sannan ya ciro wayarshi ya kira jami'ai ya sanar dasu hatsarin da kuma inda abun ya faru domin suje su gudanar da bincike a san daga ina yake a nemo iyayensa a had'ashi da su.
Bayan wasu lokuta sai ga likita ya fito ya tunkaro su yana yarfe gumi, Ahmad ya kalle shi yace "mun yi 'ko'karin tsayar da jinin dake fita daga kanshi, kuma duk raunukan da yaji an wanke wurin an saka magani, se dai ya yi muguwar buguwa, kuma kunsan hatsari irin wannan sai an yi gwaje-gwaje domin gane dukkanin inda suka samu matsala a jikinsa, saboda haka zamu cigaba da kula da shi, da bashi agajin gaggawa bari in koma wajenshi."
Bayan wasu awanni sai ga jami'ai sun shigo asibitin, da zuwansu suka 'kame domin girmamawa, daga nan babban cikin su ya shiga korawa Ahmad bayani cewa sunyi bincike a motar amma ba abinda suka samu wanda zai basu shaidar da suka samu, sai wata takarda da aka rubuta wanene ni da manyan ba'ki, sauran rubutun na 'kasa kuma adress ne," yana gama magana ya mi'ka mishi takardar.
Suna cikin magana Doctor ya fito da sauri ya nufosu yana fad'in "yallab'ai jikin shi yai tsanani gaskiya mun yi iya 'ko'karin mu abun yafi 'karfinmu, a shawarce zaifi kyau ku wuce dashi india kawai tunda yanzu garin ya waye da sauran lokaci, akwai wani 'kwararren likita da zan tura ku wajen shi a duba shi a can.
Ahmad yace "ok to hanzarta ka sallame mu, sai mu tafi, ya kalli matarsa yace "kije su kai ki gida sai mu wuce ni da shi," Khadija tace "hidimomin dake gabanka fa wa zai yi maka, ai gwara ka tura shi su tafi da wani cikin amintattun yaranka."
Ahmad ya dafe kai yace "af ni nama manta shaf wallahi, amma ai duk abinda ke gabana zan ajiye shi domin ceton rai domin yafi muhimmanci, ke dai kawai kice bakya so nai nesa da ke ai na ganoki tsaf, dukkan su sukai dariya, yace amma bari na kira Aleey su tafi tare daga baya mu sai muje," ya d'aga waya ya kira Aleey ya fad'a mishi yazo yanzu yana son ganinshi, kuma yazo da shirin tafiya india, bayan sun gama waya yai kiran wani d'aya daga cikin shugaba na jirage da ya sani ya tambayeshi ko akwai jirgin da za'a samu yanzu wanda zai tafi india, ya shaida mishi akwai amma suyi sauri su 'karaso kafin jirgin ya d'aga dan lokaci ya kusa bai fi minti talatin ba.
Ahmad yana gama waya a dai-dai Doctor ya gama had'a musu komai har an fito da Amir d'in, Aleey ya shigo cikin sauri rungume da 'yar jakarshi, babu b'ata lokaci gaba d'aya suka rankaya filin jirgi, already Ahmad ya riga ya bada izinin a tanadar da wajen zaman mutum biyu, hakan yasa suna zuwa basu wani b'ata lokaci sosai ba suka shige Ahmad na 'kara jaddadawa Aleey ya kula da Amir, kuma da sun je ya siya layi yasa ya kira yai musu magana domin su ga lambar su ri'ka kira suna jin halinda suke ciki, daga nan suka yi mishi sallama, da yake lokacin tashin jirgin ya yi, hakan yasa su Ahmad suka shiga motarsu suka juya domin komawa gida fitar da suka yi niyya ta rushe, dama amininsa zai kaiwa ziyara, amma ko ba komai fitarsu a ranar alkhairi ne, kuma sun samu ladan taimako.
Ahmad ya kalli matarsa yace "kalli wani rubutu kuma da ya yi a bayan takardar, wai be san iyayensa ba ta ina zai fara, kuma a haka daga gani d'an gata ne yana cikin daula," khadija ta karanta, sannan tai murmushi tace "my love kenan, ai tana iya yiwuwa ba tashi bace takardar," Ahmad yace "hakane, to koma dai menene mu jira ya dawo muji komai daga gareshi, fatanmu dai Allah ya bashi lafiya," matarsa Khadija tace "Ameen."
…………………………………
B'angaren Amira kuwa kamar kullum yau ma bayan fitarsa ta fito ta tafi d'akin Mummynta domin yin hira, dan zama ita kad'ai zai sa tai ta tunanin mijinta, duk da ko ta shiga cikin mutane ma be canza komai bata fasa tunanin nashi, amma dai yana raguwa ba kamar tana ita kad'ai ba.
Da shigarta ta fad'a kan jikin Mummynta tana fad'in "Mum na zo miki hira," Mum tace "bana bu'kata tashi ki koma d'akinki rasa kunya," Amira tace "au korata ma kike yi Mum, dan ma kin samu na zo, Allah nasan a ranki kinji dad'in ganina amma kike nuna kamar ranki be so ba, ai yau ba hira me tsawo zanyi ba Mum, yau Amir da wuri yace zai dawo, yana dawowa zan tafi," Mummy ta kai mata bugu Amira ta goce tana dariya, Mum ta kama hanyar 'kofar fita zata fice daga d'akin, Amira tace "Mum wajen Dad zaki tafi ko?" Mummy tace "wai Amira ni kakarki ce?" ta juyo tana tambayarta, Amira tace "bafa wani abu zance ba kawai zan ce miki ne in kin je kice ina gaishe shi," Mummy ta girgiza kai kawai ta fice daga d'akin.
Amira ta d'auki wayarta ta shiga wajen message ta fara rubuta wa Amir sa'ko.
_Na yi kewarka mijina ka dawo da wuri mu ci abincin rana tare._
Mum ce ta turo 'kofa ta dawo ta zauna, Amira sai fakaitarta take tana dariya a 'kunshe, Mum kuwa abinda yasa ta dawo saboda mugun sa mata ido da Amira tayi shiyasa ma tai saurin dawowa kar taga ta dad'e tai mata wata fassarar ta daban.
Lura da hakan da Amira tayi ne yasa ta mi'ke tsaye, sannan ta cewa Mum d'inta zata je d'aki ta kwanta, Mum tace "Allah raka taki gona," Amira tai dariya sannan ta tafi d'akinta ta kwanta.
Haka kawai kuma sai taji baccin ya'ki d'aukarta gabanta yana fad'uwa, tasan hakan baya rasa nasaba da rashin amsa ko ji daga mijinta, wayarta ta sake jawowa ta sake tura wa Amir sa'ko.
_Adadin bugawar zuciyata ya nunku Amir d'ina, a yayin da tunaninka ya 'kara yawaita, ina fatan kana lafiya?_
Tana turawa a dai-dai an kawo musu abinci, ta aje wayar taje ta bud'e 'kofar domin ta saka key ta ciki, 'karar message taji da zumud'inta ta taho tana d'okin ganin amsar da ya bata, sedai tana duba wayar taga ashe delivering report ne, hakan yasa ta jinkirta domin ganin amsar da zai turo mata.
A ta'kaice har ta dafa mishi abinci ta gama domin baya cin girki in ba na Amirarsa ba, amma ba message d'insa ba kuma kiransa, kai hankalin Amira fa ya fara tashi, dan gaskiya ko a ina yake kuma ko menene yake yi baya share sa'konninta, dole yai d'aya cikin biyu ko ya kira ko ya turo mata da amsa, in ma yana wani abun ne yana sanar da ita, hakan ne yasa hankalinta ya tashi ta d'auki wayarta domin kiransa taji a wane hali yake ciki, abunka da me rauni har ta fara hawaye, ta kira lambar tare da karawa a kunne, se dai abun mamaki jin 'karar wayarsa tayi a cikin d'akin, bin inda taji 'karar tayi, a wajen kayansa take jin 'karar cikin wata doguwar rigarsa, ta saka hannu a aljihun rigar ta ciro wayar, zaro idanu tayi tare da dafe kai ganin da gaske kuwa wayarsa ce, a gida ya barta, tace "na shiga uku! yanzu Amir d'ina a gida ya bar wayarsa," tunani ta fara yi ta yaya zata ji halin da yake ciki, a wane hali yake ciki bata sani ba, agogon d'akin ta kalla wanda ya nuna 'karfe uku dai-dai, sake zaro idanu tayi, Amir be tab'a wannan dad'ewar a waje ba in ya mugun dad'ewa biyu ya dawo cikin gida, balle wannan tun safe, kuma ya riga da ya shaida mata ba dad'ewa zai yi ba yau zai dawo.
Girgiza kai ta fara yi tana surutu ita kad'ai, "Amir d'ina ba 'kalau yake ba," sai kuma ta bud'e 'kofa cikin sauri ta fita da gudu, d'akin Mum d'inta ta nufa ta fara 'kwala mata kira, "Mum! Mum!! Mum!!! Amir d'ina ba lafiya yake ba, bansan a wane hali yake ciki ba."
Mum tai sauri ta ri'keta tana fad'in "kinga natsu Amira, natsu kiy min bayani yanda zan fahimta, Amira ta fashe da kuka tana baiwa mahaifiyarta labarin abinda yasa tace Amir baya lafiya, Mum d'inta ta ja tsaki, sannan tace "daga ya manta wayarsa kuma yau bai samu damar kiranki ba, to ta ina zai nemeki ga wayar a gida, kika san uzurin da ya ri'ke……………" kasa 'karasawa tayi saboda jin labarai da ake gabatarwa na wani hatsari da ya afku a kan hanya, motar da Amira ta gani ne yasa ta 'kara matsawa wajen t.v d'in domin ta tabbatar ta Amir d'inta ce, tabbas ba gizo idanunta ke mata ba motar Amir ce, kuma in ta saurari bayanin da kyau wai motar kad'ai aka gani ba'a ga mutum ba a cikinta.
Kanta ne ya fara juya mata, idanunta sukai mata nauyi, ta fad'i 'kasa sumammiya.
Muje zuwa
*🅱K CE😘💋*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (🅱K)*
```(Autar marubuta)```
SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
```(Mamie)```
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```🤜🤛
PAGE 150 to 155
Cikin 'kan'kanin lokaci kowa na cikin gidan ya san abinda ke faruwa, Amira kuwa an yayyafa mata ruwa amma har yanzu bata farfad'o ba, nan da nan aka kinkimeta sai asibiti.
Bayan an duddubata aka bata gado, likita yace su kwantar da hankalinsu, akwai abinda ta gani wanda ya mugun razanar da ita har yasa tai wannan doguwar suman, kuma ya basu tabbacin zata farfad'o.
Bayan kwana uku Amira na a sume sai a ranar Allah yasa ta farfad'o, doctor ya 'kara yi mata gwaje-gwajensa, a yayin da ita kuma ba abinda take yi banda rizgar kuka, ta suma yafi a 'kirga, duk ta farfad'o in ta tuno da abinda ya faru shikenan ta rasa Amir sai ta fara kuka da magiyar a kaita wajen Amir d'inta, daga haka kuma sai ta 'kara sumewa, hakan yasa doctor ya zauna da iyayenta.
Doctor ya kalle su yace "gaskiya akwai abinda yarinyarku take so, kuma in tana shiga cikin irin wannana yanayin akwai matsala, domin kuwa yanzu haka zuciyarta ta buga, a shawarce yana da kyau ku bata abinda take so," Mum ta share hawayen dake zarya kan fuskarta, sannan tace "Doctor mijinta ne ya rasu kuma ba'aga gawar ba, shiyasa ta shiga cikin irin wannan yanayin," Doctor yace "Allah sarki, Allah ya ji'kansa, to amma gaskiya yana da kyau ta daina yawan tunani, kuyi 'ko'karin samar mata da farin ciki."
Sai da tai wajen wata uku a asibiti sannan ta fara samuwa.
'Bangaren Amir kuwa har yanzu be san inda kanshi yake ba, amma su likitocin sun tabbatar wai yana samun sau'ki kuma kwanan nan zai farfad'o.
Ahmad ne zaune cikin kujera me zaman mutum biyu a falon su shi da matarshi Khadija suna hira, can sai Ahmad yace "naso inje india domin duba halin da wannan yaron ke ciki, gashi kuma zab'e ya kusa, cikin wannan watan ne kinsan zab'en namu, da ni da shugaban 'kasan da yake kai a yanzu, shiyasa komai ya rincab'e min, ya zama lokacina kad'an ne," Khadija ta kalle shi tace "to ka bari mana idan har aka gama zab'en sai mu tafi," Ahmad yace "kin kawo shawara mai kyau, amma a maganarki naji kamar kince sai mu tafi ko?" Khadija tace "eh mana haka nace, ai duk inda zaka tafi 'kafata 'kafarka, shiyasa ma nace karka wani sha wahalar tsayar da mataimaki, tunda gani ni zan zama mataimakiyarka kawai," Ahmad yai dariya itama matarshi tana tayashi.
Amira kam se dai muce Allah ya kyauta domin kuwa komai nata ya sukurkuce, ta daina walwala, ta daina fara'a, ta daina hira da kowa, abinci ma sai mahaifiyarta ta bata a baki take ci, shima kad'an, ta dai koma kamar 'karamar yarinya, ko ta shiga cikin mutane bata walwala sam, sannan bata cewa um bata um-um, babu inda ba'a je da ita ba, babu abinda ba'a kawo mata ba domin ya d'ebe mata kewa amma ina, duk ta rame tayi ba'ki kamanninta duk sun canza, koda yaushe bata da wani aiki sai tunani, wayar Amir kuwa tana hannunta dare da rana tana duba sa'kwannin da ya tura mata da wanda itama tai mishi, munji yanda rayuwar Amira ta cigaba da kasancewa.
Yau talata, kuma a yau ne aka yi za'be, yanzu kowa kawai jiran fitar da sakamako daga al'kalan zab'e ake yi, to bamu san waye kuma zai yi nasara ba, Dad d'in Amira ne ko kuwa Ahmad.
Dukkaninsu gidajen nan biyu suna gaban t.v da redio suna jiran sakamako, biyar na yamma dai-dai aka fara sanar da 'kuri'un shugabannin 'kasa, inda aka tabbatar da Ahmad shine wanda ya lashe wannan kujerar ta shugaban 'kasa.
Murna kam wajen bayin Allahn nan ba'a magana, a yayin da Dad d'in Amira da iyalensa suke ba'kin ciki da rasa wannan kujera da suka yi, kuma ikon Allah sai a ranar ba'kin cikinsu suka ga Amira tai dariya, harda tsalle da murna tana fad'in "Dad ya fad'i Dad ya fad'i."
Gaba d'ayansu tunani suke anya Amira bata samu tab'in hankali ba kuwa, Dad ji yai kamar ya kwad'eta dan ba'kin ciki, tashi yai ya shige cikin d'akinsa.
*BAYAN WATA D'AYA*
Wata biyar kenan cur da fitar da fitar da Amir waje, inda su can gidan su Amira suke ganin yana da wata biyar da rasuwa, shi kuma Ahmad zai ce bayan wata d'aya da hawar shi kan kujerar shugaban 'kasa.
Kwatsam yau suna zaune a d'aki sai ga wayar Aleey yana shaida musu cewa majinyacin nan fa yau ya farka ya bud'e idanu, harma yana ta kiran sunan wata yarinya wai Amira yana cewa a kaishi wajenta, Ahmad ya shaida musu cewa insha Allah suna nan tafe zasu taho gobe in Allah ya kaimu shi da matarsa.
Bayan zuwan su president Ahmad da wata d'aya Amir ya samu sau'ki sosai, amma har yanzu be daina damun su da tambayar ina Amirarsa take ba, ganin da likitoci sukai Amir ya warke yasa suka sallame su gaba d'ayansu su hud'un suka juyo domin dawowa 'kasarmu ta gado wato Nigeria.
Suna durowa already dama motoci guda biyu suna jiran 'karasowar su, suna sakkowa daga jirgin suka shiga mota guda d'aya, d'ayar kuma tana binsu a baya har zuwa gida.
Suna shigowa jami'ai suka zagaye wajen, nan da nan suka bud'e musu mota suka fito, Ahmad da kanshi ya kamo Amir ya fito dashi daga cikin motar, a haka suka shiga har cikin babban falon dake cikin gidan.
Ya zaunar da shi a kujera, sannan shima ya zauna a kusa dashi, Khadija ta zauna a kujerar da ke kallon su, Aleey ma ya zauna a 'kasan kafet, a yayin da security tsaye kowace kusurwa a 'kame.
Ahmad ya cewa securitys d'in su je daga waje zasu yi magana, dukkaninsu suka fita, sannan ya kalli Aleey yace "haba Aleey tashi kaima ka hau kan kujera mana," Aleey ya tashi daga 'kasa ya hau kan kujera.
Ahmad yai gyaran murya sannan yai bismillah ya kalli Aleey yace "Aleey sannu da 'ko'kari, Allah ya baka ladan jinya, a koda yaushe ina 'kara alfahari da kai Aleey, Allah yai maka albarka, ka tashi kaje domin kaga iyalenka kaima, ga wannan dubu d'ari biyar ne ka tafi dashi duk abinda ya 'kare sai ka siya musu tunda mun d'auke musu kai ba aiki har tsawon wata bakwai," Aleey ya karb'a tare da yin godiya, sannan ya fice da zumud'insa yana farin ciki.
Ahmad ya dawo da kallonsa ga Amir yace "bawan Allah mun gode wa Allah da ya dawo da kai gida lafiya, Allah ya 'kara maka lafiya, yanzu kamata yai ka 'kara samun hutu a nan kafin muji inda kake muje mu kaika mu yi musu bayanin hatsarin da ya faru da kai, mu sanar da su komai.
Amir kuwa jin an ambaci hatsari ya tuno mishi da komai, yanda aka bugi motarsa ya tabbatar masa da cewa lallai turo su aka yi, cikin sauri ya kalli Ahmad yana hawaye yace "Abba yanzu zan kai kwana nawa ina jinya?" Ahmad yace "ba kwana bane, watanka bakwai kana kwance ba lafiya."
Amir yace "Akwai wani nawa da yasan ina wajenku ne Abba?" Ahmad yace "a'a sai jami'an tsaro wad'anda suke d'aya daga cikin masu kula da ni," Amir yace "to dan Allah ka fad'a musu bana so kowa ya san inda nake har sai na gama binciken da nake yi na gano asalina, kuma in kun yarda zan zauna daku na wasu lokuta, kuma nagode sosai da taimakon da kuka yi min."
Ahmad yace "bamu fahimci bayaninka ba yaro, in ka zauna a nan iyayenka fa?" Amir yace "bansan iyayena ba, zan baku labarina ko dan taimakon da kuka yi min a rayuwa," nan ya fara basu labarin tarihin rayuwarsa tun yana 'karami har girmansa da