SO MAHADIN RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVELS PDF BY BILKISU Z YAU.txt

Author :  Bilkisu Z Ya'u Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   3 / 31

6K to 9K   out of 90.7K words

PAGE 20 to 25






Su Sani kuwa saboda tashin hankalin da suke ciki yasa basu tafi wajen Amira ba su dubo halin da take ciki.



B'angaren su Amira kuwa tunda Amir ya kaita bata farka ba sai cikin dare.



A hankali ta bud'e idanunta ta d'ora su kan Amir wanda ke ta faman zuba gyangyad'i kan kujera, kallon d'akin ta fara yi sannan ta fahimci a inda suke, nan da nan kuma abinda ya faru ya dawo mata sabo.



Kuka ta fara yi, wanda yai sanadin bud'e idon Amir, ya kalleta yace " wai sai yaushe zaki daina wannan kukan ne Amira, dukkan mai rai fa mamaci ne, ya kamata ki saka wa ranki hak'uri tunda ke da kanki kinsan kukanki bazai tab'a dawo dashi ba."



Da k'yar Allah ya taimake shi ya samu tai shiru ta daina kukan.



Washe gari jikinta ya yi sauk'i sosai ya had'a mata tea tasha sannan ya bata magunguna suma ta sha, likita ne ya shigo tare da sallama Amir ya amsa suka gaisa sannan likita ya gaishe da me jikin ya kuma k'ara dudduba ta, bayan ya gama ya kalli Amir yace " Matarka ta samu sauk'i an sallameku dama damuwa ce tasa jikinta ya rikice kuma a guji b'ata mata rai zai iya sanadin kamuwarta da hawan jini," ya rubuta mishi maganin da zata cigaba da sha sannan suka yi mishi godiya Amir ya biya dukkanin kud'in da ake binshi, dan lokacin da ya kawota kud'in jikin shi bazai ishe shi ya biya kud'ad'en ba, sai da yaje ya ciro.



Bayan sun fito daga asibitin suka shiga motar Amiran suka doshi hanyar gida, Amira ta kalli Amir tace dan Allah ka kaini makaranta inaso inga Abdul akwai maganar da nake so muyi dashi ne," Amir yace " a'a kiyi hak'uri sai kin k'ara jin sauk'i," rau - rau tayi da idanu alamun zata yi kuka, hakan yasa ba yanda ya iya ya karkato da motar hanyar makarantar su.



Suna zuwa bayan sun gaisa da su sani Amira take tambayar su ina Abdul, nan take suke shaida mata ai tun jiya 'yan sanda suka zo suka tafi dashi, kuma sunje da yamma sun hana su ganshi, sannan basu fad'a musu komai ba akanshi.



Amira tace "wai akan me suka kama shi to?" daga baya taji ance " saboda muna zargin shine ya kashe Sadeeq."



Gaba d'ayansu juyowa suka yi domin suga mai maganar, wani d'an sanda ne, a gaba bayanshi kuma ga wasu jami'an nan dukkansu sun sha uniform, ga dukkan alamu na gaban shine me maganar.



'Dan sandan nan ya kallesu yace " sunana insfecto Yahya (kafi k'arfin mugu), mun samu labarin cewa kaf makarantar nan Sadeeq bai da wasu abokai sai ku musamman ma ke Amira, saboda haka mun zo ne domin mu tafi daku station domin amsa mana wasu tambayoyi, sai ku wuce mu tafi koh, suma haka nan suna ji suna gani aka tasa su dukkan su har Amir aka tafi da su.



Ko da isar su insp Yahya ya kalli Amira yace " dake zan fara domin kamar yanda muka gani tare da hujjoji da bayanan da suka gabata a garemu ya nunar mana cewa Sadeeq da Abdul suna sonki, kuma a kanki ne aka kashe su."



Amira ta zaro idanu tare da fad'in " so, ni, a kaina kuma aka kashe shi, tabbas nasan mun shak'u da Sadeeq amma gaskiya babu wata kalma ta so da ta tab'a had'amu, haka shima Abdul d'in."



Insp Yahya yai murmushi sannan yace " ba lallai bane ke sun fad'a miki, amma duk suna sonki in kika lura da abinda Abdul yai miki cikin jama'a da kuma yanda Sadeeq yayi a kanki da furucin da ya yi shima Abdul ya mayar mishi da martani, sedai soyayyar tasu zata iya zama da bambanci, shi Abdul ta iya yiwuwa sha'awarki kad'ai yake, idan muka yi la'akari d rungumar da yai miki da yanayin yanda yake shafa jikinki, duk da dai a cikin maye ne yake, amma abinda ke ranshi ya nuna a wannan lokacin, a yayinda Sadeeq ke yi miki so na gaskiya, amma in baki yarda ba me zakice akan wannan hoton?"



Wani hoto ya nuna mata d'aya daga cikin hoton gawar shi da aka d'auka, ya rubuta sunanta b'aro b'aro a jikin hannun shi.



Bayan ta gama gani sai ya karb'a tare da sake mik'a mata wata takarda yace ta karanta, a cikin litattafan Sadeeq suka gani, karb'a tayi shima ta karanta an rubuta.


_Amira ina k'aunarki k'auna ta hak'ik'a amma ina tsoron bayyana miki saboda bansan yanda zaki karb'e ni ba, ko ki amince ko kice min a'a._


Daga k'arshe wasu hotuna ya nuna mata wanda suka d'auka su biyu a bayan hotunan duk ya rubuta _i love you Amira,_ wanda suke tare da Abdul kuwa sai ya soke Abdul d'in ya bar nasu, shima a bayan shi an rubuta _babu abinda zai rabamu dake sai mutuwa insha Allah._



Kuka take yi mai tsuma zuciyar sauraro, cikin kukan tace " wallahi be tab'a fad'a mun ba, ana gobe za'a kashe shi ya sanar dani cewa akwai abinda zai fad'amin washe gari, ashe so yake ya fad'a mun yana sona," ta cigaba da kuka mai tsuma zuciya.



Insp Yahya yace " yi hak'uri kiy shiru insha Allah zamu yi iya bakin k'ok'arinmu wajen kama wanda ya kashe miki masoyi."



Amira ta kalli Insp Yahya tace " duk da haka ni bana zargin Abdul shi ya kashe Sadeeq."



Insp Yahya yace " in ba shi bane waye to?"



Amira tace " bansan ko waye ba, wannan aikin ku ne gano mai laifin."



Insp yai murmushi sannan yace " abinda muke kan yi kenan, amma ke akwai wanda kike zargi ne a ranki?"



Amira tace " a'a bana zargin kowa dan bashi da abokin fad'a sam, da Abdul d'in ne ma basu wani cika shiri ba."



Insp yace " meyasa basa shiri?"


Amira tace " wallahi ban sani ba, k'ila jinin su ne be had'u ba," Insp yace " amma ai bayanai sun nuna a kanki kad'ai ne suke samun matsala, shikenan dai abar wannan maganar, tambaya ta gaba a bayaninki na d'azu kince ana gobe za'a kashe shi yace miki akwai maganar da yake so ya fad'a miki koh," Amira tace " eh haka ne yallab'ai," Insp yace " zaki iya tuna waye a tare daku a lokacin da ya sanar dake hakan?"



Amira tace " daga ni sai shi sai kuma Amir mu uku ne a ranar."



Amir yace " eh tabbas muna tare a ranar ni da su."



Insp ya kalli Amir yace " ok kaine Amir d'in kenan?"



Amir yace " eh yallab'ai, Insp yai murmushi yace " to malam Amir tambaya ta dawo kanka, malam Amir yaushe ka shigo makarantar nan?"




Amir yace " yallab'ai ni sabon d'alibi ne bazan wuce wata biyu ba, Insp Yahya yace " yana son sanin alak'ar shi da Sadeeq da kuma ita kanta Amiran, labarin had'uwar su da ita ya bashi daga farko har k'arshe, sannan ya k'arashe da fad'in "Sadeeq kuma ta sanadinta na sanshi, amma cikin k'ank'anin lokaci muka shak'u da shi."



Insp Yahya yace " meyasa ka zab'i k'awance da Amira ita kad'ai duk da yawan 'yan matan jami'ar, kodai kaima kana sonta ne?"



Amir yace " kamar yanda na fad'a maka ne, mun had'u da ita bamu san juna ba, bansan 'yar makarantarmu bace ma sai da zamu rabu take shaidamin za'ai gasar tsere a makarantar su kuma ta gayyace ni tare da fad'amin sunan makarantar, a lokacin ne na gane cewa makarantar mu d'aya da ita."



Insp yace " a d'an zamanku tare da Sadeeq d'in ka tab'a ganin abokin fad'an shi, ko wanda cacar baki ta tab'a had'a su?"



Amir yace " gaskiya babu, saboda Sadeeq baida matsala da mutane sam, yana da kyakkyawar alak'a da kowa kuma bashi da abokin fad'a, se dai kamar yanda kaji ne da Abdul ne kad'ai suka tab'a samun matsala kan Amira."




Bayan sun gama magana da Amir ne ya bi sauran d'aliban kuma abokan Sadeeq da Abdul d'aya bayan d'aya yana yi musu tambaya akai, daga k'arshe ya sallame su, tare da tabbatar musu da cewa in yiwuwar sake tattaunawa dasu ta taso zasu neme su, har sun juya zasu tafi Amira ta juyo sannan tace " yallab'ai dan Allah a barmu mu ga Abdul d'in, Insp Yahya yace " karki damu kuje kawai shima gobe ko jibi zamu sake shi dan nafara tunani da kuma zargin wani bayan shi," yana yin maganar yana kallon Amir.




Ita kuwa Amira jin ance za'a sake shi yasa hankalinta ya d'an kwanta, ta juya suka fice dukkan su.



Bayan tafiyat su ne Insp Yahya ya kalli kofur sale yace " nifa ban yarda da Amir d'innan ba, ko kai baka zarginsa?"



Kofur yace " gaskiya da alamar tambaya a kanshi, amma yallab'ai shi babu laifin da aka kama shi dashi akan kisan, sai Abdul, kuma ni a ganina tunda Abdul da Sadeeq suna son Amira dukkansu zasu iya yin fad'a da junansu a ranar har takai ga d'aya ya kashe d'aya," Insp yace " Kofur kenan, in haka ne meyasa tun baya Abdul be kashe Sadeeq ba sai da yace zai yi magana da Amira, kuma babu wanda yaji maganar nan daga su sai Amir d'in, ai kuwa in dai na ci sunana Yahya (kafi k'arfin mugu) to sai na zurfafa bincike a kansu d'aya bayan d'aya musamman ma Amir d'in domin gano gaskiya.









Muje zuwa










*πŸ…±K CEπŸ˜˜πŸ’‹*
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜






RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (πŸ…±K)*
```(Autar marubuta)```






SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
_(Mamie)_






*πŸ‡ΈπŸ‡¦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```{Gidan zaman lafiya da amana insha Allah}```





_*MASOYAN MAHAD'IN RAYUWA* ku cigaba da bibiyar labarin domin yanzu aka fara fa labarin fa bakuji komai ba fa, ku dai ku biyo 'yar gidan *MAMIE* wato *Bk* domin jin cigaban labarin._






*MAMIE NAH* _Ina rok'on mahaliccinmu Allah, mad'aukakin sarki, mai ikon komai akan kowa ya baki lafiya d'orarra, Allah ya dauwamar da ruhinki cikin farin ciki har k'arshen rayuwa, ya d'orar da lafiyarsa gareki.πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ˜­πŸ˜­πŸ˜­πŸ˜­πŸ˜­_







PAGE 25 to 30






Tun daga ranar Insp Yahya ya fara bincike sosai akai amma har yanzu bai sami wani abu ko shaida da zai kama ya rik'e yace ga mai laifin ba.



Hakan yasa ya dakatar da binciken shi ya tsaya jiran sakamakon gwajin da aka bayar na gano tambarin yatsun wanda yai kisan.



Bayan kwana biyu likita ya gabatar musu da dukkanin sakamakon gwajin da ya yi, wanda ya tabbatar da lallai tambarin yatsun Abdul ne kuma a ranar a buge Sadeeq yake, wad'annan shaidun yasa yak'i sakin Abdul, sannan ya fara shirin tura shi kotu a yanke mishi hukunci.



Su Amira kuwa jin shirun ya yi yawa har yanzu ba'a sakoshi ba yasa suka sak'e komawa station d'in, a yayin da shi kuma insp Yahya ya tabbatar musu da cewa yanzu case baya hannunshi domin kuwa ya mik'a shi kotu ranar litinin in Allah ya kaimu za'a shiga kotun in suna so su ganshi to su je kotun, had'ashi da Allah sukai ta yi akan ya bari su ganshi, da k'yar da sid'in goshi suka samu ya yarda, amma minti biyar kacal ya basu, kuma saida ya had'asu da jami'i, sannan yace be yarda ya matsa ba ko me zasu fad'i su fad'a a gaban shi.



Koda suka ga Abdul saida suka yi kuka har Amir sai da ya koka, balle uwa uba Amira me saurin kuka.



'Yan kwanaki biyu kad'ai da ya yi a hannunsu har ya yi bak'i ya rame, shima yana ganinsu fashewa yai da kuka mai tsuma zuciya, cikin kukan yace " wallahi tallahi ba ni na kashe Sadeeq ba, a ranar ma mun wuni tare da shi, har club ma tare muka je, duk yanda muka kai ga rashin jituwa baya hanamu yin mu'amalar mu a tare, dama rashin jituwar mu a kanki ne, amma wallahi koda ace nai k'aurin suna wajen rashin imani bazan iya kashe koda dabba ba balle mutum, mutum d'in ma wanda na sani muka saba."



Cikin kuka Amira tace " nima ban yarda kaine ka kashe shi ba Abdul, tabbas akwai wani b'oyayyen abu wanda mu d'in bamu san dashi ba, sedai mu rok'i Allah ya fitar da kai ta hanyar bayyana gaskiya."



Suna cikin magana jami'in nan da aka had'asu su zo wajen shi tare yace " lokaci ya cika ku wuce muje."



Haka nan suka yi sallama da shi suka fito suka tafi, tare da shirin zuwa kotu domin jin yanda zata kasance, amma kafin ranar saida suka sami nagartacciyar lauya wadda zata tsaya mishi a kan case d'in.



*MONDAY (LITININ)*



Yau litinin, kuma a yau ne aka shiga kotu, ko ina ka duba cike take taf da mutane, 'yan makarantar su duk sun hallara harda su Amira da Amir da sauran wad'anda abun ya shafa, kowa ya hallara Alk'ali kawai suke jiran zuwan shi.



Bayan 'yan mintuna sai gashi ya shigo kowa ya mik'e, sai da ya zauna sannan kowa ya koma wajen zaman sa ya zauna.



Bayan ya zauna ya shirya sannan ya bada umurnin a fara gabatar da jerin k'ararrakin da suke da su a yau, me gabatarwa ya tashi ya fara jawabi kamar haka " shari'ar mu ta farko a yau itace ta su marigayi Sadeeq wanda ake zargin Abdul abokinsa ne ya kashe shi ta sanadin wata yarinyar makarantar su mai suna Amira," yana gama fad'in haka ya koma ya zauna.



Bayan alk'ali ya yi 'yan rubuce rubucen shi sannan ya d'ago yace " malam Abdul ka ji irin tuhumar da ake yi a kanka?" Abdul yace " eh naji ranka ya dad'e," Alk'alin yace " ka fad'a mana gaskiya karka wahalar da shari'a fad'in gaskiya shi zaisa a sassauta maka, shin kai ka kashe Sadeeq?"



Abdul yace " wallahi ba ni na kashe shi ba, bansan komai ba game da kisan da aka yi mishi."



Alk'ali ya yi rubutu sannan ya sake kallon shi yace " ko kana da lauyan da zai kareka?" Abdul yai shiru, can sai ya ji wata lauya ta mik'e tace " ranka ya dad'e sunana barista Aisha Isa, ni ce lauyan da zan kare wanda ake zargi," ta koma ta zauna, wani ya sake tashi yace " sunana barista Muhammad Auwal, ni nake kare b'angaren da suke k'ara," shima ya koma ya zauna.



Can sai Alk'ali yace an basu dama kowanne daga cikin su ya tashi ya gabatar da tambayoyin shi ko hujjar da yake da ita.



Barista Aisha ce ta fara tashi ta je gaban Abdul ta tsaya tace " malam Abdul menene alak'arka da Sadeeq?" Abdul yace " makarantar mu d'aya, kuma abokina ne," Aisha tace " da gaske ne dukkan ku ku biyun kuna son Amira?" Abdul mamaki ya kama shi ta yanda akai suka gano yana son Amira, yai shiru tare da kallon saitin da Amira take, d'aga mishi kai ta yi alamar ya amsa, Aisha ta sake maimaita tambayarta, Abdul yace " eh dukan mu muna nuna mata alamu se dai duk cikarmu babu wanda ya tab'a furta mata," Aisha tace " har tsawon wani lokaci kuka d'auka kuna sonta kai da shi Sadeeq d'in?" Abdul yace " shekara biyu."



Aisha ta juyo ta kalli Alk'ali tace " ranka ya dad'e abun lura anan shine Abdul da Sadeeq sun dad'e suna k'aunar Amira har tsawon shekaru biyu ba tare da sun fad'a mata ba, kuma kowanne daga cikinsu ya san d'an uwansa yana sonta, se dai meyasa tun a wancan lokacin Abdul d'in be kashe shi ba sai yanzu, nagode ranka ya dad'e, ta koma ta zauna.



Bayan Alk'ali ya kammala rubutun shi sai ya baiwa Barista Muhammad Auwal damar yi wa Abdul tambayoyi, ya mik'e tare da zuwa gaban Abdul yace " malam Abdul fad'a ya had'aku da Sadeeq a kan Amira sanadin rungumarta da kayi kana cikin maye har kun yi cacar baki da shi ko baku yi ba?" Abdul yace " eh mun yi," Barista Muhammad yace " wane furuci kuka fad'awa juna a ranar?" Abdul yace " Sadeeq ne ya ce min sai ya kashe ni idan na k'ara tab'a Amira, ni kuma b'acin rai yasa na mayar mishi da martani kan cewa nima sai na kashe shi," Barista Muhammad yace " ok shine ya baka damar kashe shi?"



Objection my lord abinda Aisha ta fad'i kenan bayan ta mik'e, tace ya kamata Barista ya san irin maganar da zai rik'a fad'a, har yanzu ana kan bincike ne ba'a tabbatar da shine ya yi ba ko ba shi bane nagode," Barista ya kalli Alk'ali yace ranka ya dad'e abinda yasa nake mishi tambayar nan saboda akwai wasu hujjoji na ne wad'anda suka sa dole sai na yi mishi wannan tambayar."



Alk'ali yace " Barista Aisha k'orafi be karb'u ba, Barista Muhammad kana iya cigaba da yi mishi tambayoyin."



Barista Muhammad yace " muna saurarenka Abdul nace wannan b'acin ran yasa ka kashe shi saboda kar ya zama barazana a soyayyarku da Amira?" Abdul yace " wallahi ba ni na kashe shi ba," Barista yace " da kyau dama amsarka nake jira," Barista ya dawo wajen zaman shi ya d'auko wuk'ar da aka kashe Sadeeq da ita tare da takardu, ya nuna wa Alk'ali tare da fad'in " ranka ya dad'e wannan wuk'ar da ita aka yi amfani wajen kashe Sadeeq bayan kokawar da suka sha dashi wajen ceton ransa da yai k'ok'arin yi, wannan takardar kuwa hotunan d'akin shi Sadeeq d'in ne wanda 'yan sanda suka d'auka ranar da abun ya faru, d'aya takardar kuwa ta likita ce wadda ya tabbatar mana da cewa shaidar hannun Abdul ne a kan wuk'ar," bayan ya gama fad'i sannan ya bayar aka mik'awa Alk'ali domin ya nazarce su, sannan ya sake cewa " kafin kisan bincike ya nuna cewa a daren da abun zai faru Sadeeq ya shawu kuma hakan ne ya

3 / 31