SO MAHADIN RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVELS PDF BY BILKISU Z YAU.txt

Author :  Bilkisu Z Ya'u Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   26 / 31

75K to 78K   out of 90.7K words

da 'kyar ya samu tai shiru sannan ya zaunar da ita kan kujera, suna zama sai ga Nura ya fito kamar an jeho shi.








Muje zuwa









*πŸ…±K CEπŸ˜˜πŸ’‹*
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜






RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (πŸ…±K)*
```(Autar marubuta) ```





SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
(Mamie)






*πŸ‡ΈπŸ‡¦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```







PAGE 190 to 195







Nura yazo ya zauna kan kujera yana kallon Amir dake 'kokarin komawa wajenshi ya zauna yace "ba dai har zaka tafi ba? haba kai ka fara ma kazo gidana kace zaka tafi yanzu."



Amira kuwa idanunta na kan Amir sam ta kasa d'aukesu daga gareshi.



Amir yace "a'a karka damu ina nan har sai kun gaji dani sedai in amarya ce da kanta ta koreni," ya 'karasa maganarshi yana kallon Amira.



Amira tai murmushi me had'e da dariya tana cike da farin cikin sake ganin masoyinta kuma mahad'in rayuwarta, sannan tace "haba dai, wallahi har abada bazan tab'a korarka ba ko a mafarki bana fatan haka."



Nan fa sukaita hira sai can wajen yamma sannan Amir yace zai tafi.



Nura yace ya manta da makullin motarsa bari ya shiga ciki ya d'auko, bayan ya shiga Amir ya kalli Amira yace "yi sauri ki bani lambarki kafin ya fito, Amira ta fad'a mishi ya rubuta, yana cikin saving sai ga Nura ya fito, Amir ya mi'ke sukayi sallama da Amira sannan suka fice daga gidan, Amira kuwa akwai tarin tambayoyi a cikin ranta kuma a zuciyarta tana ji kamar ta ri'keshi ta hana shi tafiya, amma haka ta bar Amir ya wuce ya tafi ba yanda ta iya dole tai ha'kuri, tambayoyin dake ranta kuwa ta bari sai ya kira sai suyi duk maganar da zasu yi.



Suna tafe a mota suna hira, Nura yace "wallahi tunda muke da Amira bata tab'a zama dani haka munyi hira da ita haka ba har naga ha'koranta sai yau, Amir a zuciyarshi yace "to ba dole ba ai duk wanda yace yana 'kaunarta har ya aureta kallo take a duk duniya bata da ma'kiyi sama da shi," ashe Amir be sani ba maganar da yayita a zuciya ta fito fili, kawai ji yayi Nuran yace "nima kallon ma'kiyinta take yimin kenan, kuma meyasa ma ka fad'i haka?"



Amir yace "eh mana saboda kaima ka shaida mutum d'aya tak take so, to wannan dalilin zaisa taji haushinka tunda ka aureta ka 'kara nisantata da masoyinta na farko."



Nura yai murmushi yace "ba zaka gane ba abokina, duk akwai dalilin yin haka, watarana zan sanar dakai, bayan dalilan ni kaina ina son yarinyar, ban tab'a had'uwa da yarinya me kyau da diri irinta ba," habawa yana fad'in haka Amir yaji kamar an saka mishi garwashi a zuciyarshi saboda tsabar jin rad'ad'in maganar Nura, nan da nan kuwa idanunshi sukai ja ya dage iya 'karfinsa ya buga kanshi jikin glass d'in murfin motar, nan da nan kuwa glass d'in da kanshi duk suka fashe, Nura yace "Subhanallah!" ya faka motar sannan ya cigaba da yi mishi sannu, sannan Nura ya sake cewa "meyasa kayi haka Amir?" Amir yace "wallahi ciwo kan yake min, gashi kuma ka 'kara b'ata min rai, ni yanda na d'aukeka kamar d'an'uwa ashe kai ba haka bane, a tunanina damuwarka damuwata ce, kullum se dai kaita ce min akwai dalilin auren matar da kake tare da ita, to menene amfanin fad'amin akwai dalilin tunda baka iya sanar dani, ka sani ko akwai shawarar da zan taimakeka da ita."



Nura yai murmushi, sannan ya dafa kafad'arshi yace "ba haka bane abokina, kayi ha'kuri yanda ka d'aukeni nima haka na d'aukeka amma dan Allah ka ri'ke min sirrina," nan Nura ya kwashe duk wani 'kuduri nasu akan su Amira da Dad d'inta ya fad'a wa Amir, Nura ya cigaba da cewa "amma fa ni ko na samu biyan bu'kata bazan rabu da Amira ba, shi kuma Dad ya dage indai muna son dukiyarsu muna son zama lafiya dole sai mun kawar da su.



Bayyana tashin hankalin da Amir ma ya shiga ai baya misaltuwa, amma sai yai saurin b'oye razanarshi, sannan yai murmushi yace "gaskiya Dad d'inka yayi tunani, kaga fa in kuka samu yanda kuke so zaka iya mallakar koma wace macece a rayuwa, bayan haka kome kaga dama zakayi domin kud'i sune abokan rayuwa."



Nura ya she'ke da dariya, sannan yace "ashe kaima irin ra'ayinmu d'aya shine na b'ata lokaci wajen sanar dakai tun tuni."




Haka dai suka cigaba da tafiya suna hirar su, abinda yasa Amir ya biye mishi yasan in ba haka yayi ba bazai cigaba da samun labarin komai daga wajenshi ba.



Suna cikin hira wayar Nura tai 'kara, ya cewa Amir ya d'an d'auka ya cewa koma wanene yana tu'ki zai kira later.



Amir na d'agawa kafin yace komai sai yaji mahaifin Nura yana fad'in "Nura ko me kake ka bari kazo, na samu labarin wai anga Amir a garin nan, maza kazo muyi shawarar abinda ya dace muyi a gaba," yana gama fad'in haka ya katse kiran.



Gaban Amir ne ya fad'i, sam be so komai ya fito tun yanzu ba, Amir ya mayar da wayar gefe ya ajiye, sannan yace "mahaifinka ne ya kira yace kaje yana nemanka, wai ya samu labarin anga Amir a cikin garin nan kaje ku shirya abinda ya kamata a gaba."



Wani irin birki Nura yaja tare da kallon, Amir had'e da zazzaro ido, yace "meyasa wannan d'an iskan zai bayyana yanzu?" wayarsa ya d'auka ya kira Babanshi suka tattauna sannan ya tabbatar mishi da yana zuwa nan bada dad'ewa ba.



Bayan sun gama wayar ya tayar da motar suka cigaba da tafiya.




Amir sam baya son Nura ya gane gidansu balle har ya gane wanene shi, gashi yau ya d'aukoshi a motarsa dan yau cewa yai masu tsaronsa su juya da dukkanin motocin, dan haka suna zuwa dai-dai wani super market yace ya ajiyeshi a nan zai duba wani abokinshi a ciki.



Bayan Nura ya faka motar Amir ya fito, suka yi sallama yaja yai gaba a yayin da shi kuma Amir ya koma gefe ya samu wani benci dake kusa da 'kofar shiga super market d'in ya zauna, ya ciro wayarshi ya kira lambar da Amira ta bashi, ringing d'aya tayi Amira ta d'auka tare da karawa a kunne, sallama tayi da sassanyar muryar nan ta-ta me d'an karen dad'i, lumshe idanu Amir yayi sannan ya bud'esu, shima a hankali ya kira sunanta yace "Amira."



Amira cikin sauri ta mi'ke tsaye tace "Amir d'ina ina ka shiga har zuwa tsawon wannan lokacin, kasan halin da tunaninka ya jefa rayuwata a ciki kuwa? kowa yana ta cewa ka mutu amma ni nasan ba zakaimin haka ba, ba zaka mutu ka tafi ka barni ba," ta fashe da kuka, sannan ta cigaba da cewa "amma meyasa tsawon wannan lokacin ka tafi ka barni ba tare da ka nemeni ba?




Amir yace "haba Amira ta ina zan nemeki bayan mahaifinki ya dage sai ya rabamu ta 'karfi da yaji," nan ya kwashe duk abinda ya faru ya fad'a mata, Amira ta tayashi murnar ganin iyayensa da yayi, yai mata godiya sannan ya cigaba da fad'in "yanzu abinda yasa na kiraki shine in fad'a miki ki kwantar da hankalinki, zaki dawo wajena nan bada dad'ewa ba mu cigaba da zaman aure, amma yanzu idan nace zan bayyana gaban Dad inaso a dawo min da matana bazai yarda ba rigima za'ai ta tafkawa, shiyasa nafi so sai na tona duk wani asiri nasu tukun, na samowa Dad babbar hujja a kansu, abinda nakeso dake shine karki tab'a yarda dashi domin kuwa nafara gano manufar abinda yasa aka aureki, kiyi taka tsan-tsan dashi, kuma zamu ri'ka waya dake duk in baya nan," Amira tace "to shikenan," nan suka d'an tab'a hira daga 'karshe suka yi sallama.



B'angaren su Nura kuwa zaune suke shi da Baban shi suna magana akan Amir, Nura yace "waima to kai wa yace maka ya ganshi anya shi aka gani kuwa Baba?"



Baba yace "to ni na ganshi da idanuna kaine baka sanshi ba, baka tab'a ganinshi ba, amma ni na sanshi, mahaifin Amiran ya nuna min hotonshi lokacin da mukaje gidan da kai maganar aurenku, sai gashi yau na ganshi da idanuna sun wuce tare da wasu mutane masu ba'ka'ken kaya a mota, saboda haka yasa na kiraka mu nemi mafita."



Nura yace "in kuwa haka ne bayyanarsa a dai-dai wannan lokacin zata b'ata mana shiri, amma kar kaji komai Baba in dai ka yarda dani kabar komai a hannuna," da wannan maganar ta Nura suka kawo 'karshen maganar.



Bayan sati d'aya ko da iyayen Amir suka ga ya fara warwarewa damuwarshi tayi sau'ki sai suka shirya suka koma Abuja saboda harkokin Abbansa na siyasa dama wasu da yawa da suke can, suka bar Amir da bataliyar masu gadi da tsaronsa a nan kano saboda karatunshi da ya koma babu damar su koma tare dashi, basu san cewa Amir hankalinshi baya wajen karatu sam yana can wajen fafutukar 'kwato soyayyarshi.










Muje zuwa









*πŸ…±KπŸ˜˜πŸ’‹*
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜





RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (πŸ…±K*
```(Autar marubuta)```






SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
```(Mamie)```






*πŸ‡ΈπŸ‡¦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```πŸ€œπŸ€›








*SO TARI DA DAMA MU MUKE BARI SO YANA KUB'UCEWA DAGA HANNUNMU, TA HANYAR RAGE KULAWA, TATTALI, YARDA DA JUNA, RAGE WA'DANNAN ABUBUWAN GA MASOYA SHI KESA SHA'KUWA TAI 'KARANCI, LOKUTA DA DAMA ZAKA GA MASOYA SUNA 'KAUNAR JUNA AMMA SAKAMAKON JA BAYA DA KAYI DA KULAWARKA SAI ALLAH YA KAWO WANDA YA FIKA DUK WA'DANNAN ABUBUWAN TO WALLAHI CAN ZAI KARKATA, DOMIN AKODA YAUSHE ABINDA BAWA YAFI SO A SO SHINE KULAWA, BA TA YANDA ZA'AI MASOYI YA RASA WA'DANNAN ABUBUWAN DAGA GAREKA KUMA KACE DOLE SAI YA CIGABA DA ZAMA DAKAI, IN HAR BAWA YANA SO SOYAYYARSA TA 'DORE FIYE DA YANDA TAKE A BAYA TO NUNKA TATTALINKA DA KULAWARKA ZAKA YI, MU SANI CEWA ITA KULAWAR NAN ITACE JIGON SO BAKA BARI KAI SAKACI DA ITA, WANNAN MUKA RASA SHIYASA LOKUTA DA YAWA ZAMU MALLAKI MASOYA AMMA DAGA BAYA SU ZAMA BA NAMU BA TO WALLAHI SAKACIN DAGA GAREMU NE, BA TA YANDA ZA'AI MA KA DAINA BAIWA MASOYINKA KULAWA KUMA YA YARDA CEWA WAI HAR YANZU KANA 'KAUNARSA, SHIYASA 'KAUNAR YANZU TA ZAMA TA 'DAN LOKACI 'KALILAN SABODA BABU KULA, DOLE IN KA SAMU WANDA ZAI BAKA DUKKANIN KULAWARSA KA KAR'B'ESHI HANNU BIBBIYU, YA ALLAH KA BAMU IKON CIGABA DA BAIWA DUKKANIN MASOYANMU KULAWAR DA TA DACE.*








PAGE 195 to 200









Amir yaji dad'i sosai da tafiyar iyayensa, domin yasan wata 'karin dama ya samu na aiwatar da shirinsa cikin kwanciyar hankali, dan yasan muddin su Abba suna garin wata rana zasu gano komai, kuma idan suka gano zasu dagula komai domin zasu ce zasu d'auki mataki, dan ba zasu tab'a barin duk wani abu da zai tab'a d'ansu ba suna kallo su 'kyale shi.




Bayan kwana biyu Nura yaje ya sami mahaifinsa ya shaida mishi gaskiya shi fa ya gaji, taya za'ai ace sunan yana da mata amma bata bashi duk wata kulawa ta aure.



Bud'ar bakin mahaifinsa sai yace "to ka saketa mana."



Nura yace "ai ina 'kaunarta bazan iya rabuwa da ita ba," mahaifin Nura yace to kuwa tunda kasan haka sai ka daina wannan maganar ma, mata a hankali ake shawo kansu, kuma koda zaka nuna mata halinka sai ka bari sai mun samu biyan bu'katar mu."



Yanzu Amir da Amira har chat suke yi a waya yau ma chat d'in suke tana fad'a mishi cewa ita fa ta gaji zata fad'a cewar ya dawo a maidata d'akinshi.



Amir ya rarrasheta yana fahimtar da ita cewa yin hakan ba abu bane me sau'ki.




Bayan sati d'aya Amir da Nura suna tafiya kan hanya a cikin motar Amir wanda Nuran ne ke jansu zai kaishi gida sai ya d'auki motarshi ya wuce gida shima, suna tafe sai wayar Nura tai 'kara, yana dubawa yaga Dad d'in Amira ne ke kira, Nura ya kalli Amir da ya du'kar da kai yana chat da Amira yace "d'an akuyan Dad d'in Amira ne ke kirana," Amir ya d'ago yai murmushi sannan yace "to d'aga kaji mana."



Bayan Nura ya d'aga suka gaisa sannan Dad yace "ya kuke ina fatan dai kuna zaune lafiya ba wata matsala ko?"



Nura yace "eh lafiya lau muke zaune babu wata matsala."



"Bayan sun gama wayar ya mayar aljihu sannan yace "sai kayi dana sanin sanina Dad, wai shi me kud'i koda yaushe cikin wula'kanta talaka, hmm."



A dai-dai nan suka kawo 'kofar gidan su Nuran, Nura ya kalli Amir yace "yanzu wucewa zaka yi ba zaka shiga ku gaisa da Madam ba?"



Amir yai murmushi sannan yace "muje," suna shiga cikin falon suka tarar da Amira zaune a kan kujera tana daddanna wayarta, wanda ba da kowa take chat ba face Amir.



Cikin hanzari da farin cikinta ta tashi tana fad'in "barka da zuwa mai gidana, kar kaso kaga farin cikin da zuciyata ke ciki a yanzu na murnar sake ganinka a karo na biyu," Nura ya washe baki tare da d'agowa yana kallonta da mamaki 'karara a fuskarsa na irin tarbar da yake samu a wajenta duk lokacin da suka shigo tare da Amir, sedai abinda ya lura dashi shine sam ba shi take kallo ba, kamar ba shi take yiwa sannu da zuwa ba.



Nura ya wuce ciki tare da kawar da komai daga ranshi, saboda yana tunanin abinda yasa take haka 'kila saboda kar wasu su gane irin yanayin zaman da sukeyi ne.



Yana shiga ciki Amir ya kalleta cikin sauri yace "meyasa kike yin irin haka a gabanshi, so kike sai ya gano mu."



Amira ta turo baki tare da cewa "ai ba laifina bane, bana iya control d'in kaina ne a duk lokacin da na ganka."



Nura ne ya fito daga cikin d'aki tare da zama kusa da kujerar dake gefen Amira, sedai ya lura sam hankalin Amira baya gareshi, ko magana take idonta na kan Amir, shima Amir jefi-jefi yana satar kallonta, haaaaaa wa ya fad'a musu dama soyayyar gaskiya tana b'uya koda anyi 'ko'kari aga anyi hakan.πŸ˜‚



Ganin haka yasa walwalar Nura ta ragu, kuma sannan ya 'ki tashi ya 'kara zuwa ko'ina, hakan ne ya hana su Amir samun damar tattaunawa, daga 'karshe ma tashi yayi yai musu sallama Nura ya rakoshi bakin motarsa ya shiga sukai sallama ya tayar ya tafi.



Sedai abinda ya 'kara d'aurewa Nura kai shine yana dawowa ya tarar Amira bata falon ta shige d'akinta, kuma wannan ba shi bane karo na farko da take yin hakan, idan Amir yazo ya tafi sai ta canza ta koma kamar ba ita ba, ko ta tashi ma tai tafiyarta ta barshi shi kad'ai kamar yanda tayi a yau.



Haka suka cigaba da kasancewa a matsayin ma'aurata har tsawon shakara d'aya harda watanni.



*BAYAN KWANA BIYU*


Yau ta kama Alhamis, Nura na zaune a falo sai ga kiran Dad, koda Nura ya d'aga wayar gaisawa kawai suka yi sannan Dad yace "Nura ko me kake yi ka ajiye kazo office d'ina yanzu ka sameni ina jiranka."



Nura ya amsa da "to," suna gama wayar Nura ya kira wayar Mahaifinshi, bayan ya d'aga sun gaisa sai yace "Baba ina kyautata zaton ranar da muka dad'e muna jira ne yau tazo, domin yanzu Dad d'in Amira ya kirani yace in yi maza inje yana son ganina."



Baban Nura yace "Allah mun gode maka, to me kake jira har yanzu baka tafi ba?"



Nura yace "ai yanzu zan tafi Baba, sai na dawo duk yanda ake ciki zaka ji," daga nan suka yi sallama ya fito ya tafi.



Duk wayar nan da yake a cikin gida ya yita, amma duk a tunaninsa Amira bacci take yi shiyasa ya saki jikinsa yai wayarshi hankali kwance.



Bayan fitarsa Amira dake lab'e ta gama jin komai ta kira Amir ta fad'a mishi duk abinda taji da kunnenta, dama Amir ya fad'a mata duk maganar da taji Nura yayi ta kira ta fad'a mishi.



Nura ne zaune gaban Dad, yana matu'kar martaba Dad da 'kas'kantar da kai a gabanshi kamar mutumin arzi'ki.



Bayan sun gaisa Dad ya kwaso wasu takardu dake gefenshi ya kalli Nura tare da mi'ka mishi takardun nan yace "ungo ri'ke nan, bayan Nura ya karb'a Dad ya cigaba da fad'in wad'annan takardun dukkanin kadarorina ne da na mallaka, na dam'ka su a hannunka ne ba dan komai ba sai dan na riga da na mallakawa Amira su, sedai bana so ta ri'ke a hannunta sai nan gaba tukun in ta 'kara girma da hankali, dan haka ka cigaba da juyawa tare da kulawa dasu har ranar da Allah zai hukunta ta karb'a."



Nura yace "amma Daddy a ganina ya kamata Amira tazo ayi komai a gabanta daga nan kuma mu sassaka hannu."



Dad yai murmushi sannan yace "karka damu Nura na yarda da kai, ban tab'a tunanin cikin talakawa akwai masu amana irinka ba, na baka kamfanina ka juya tsakani da Allah, sannan na d'auki yarinya na baka itama ka ri'keta da hannu biyu, tare da bata duk wata kulawa, abinda yasa ma har aka kai tsawon wannan lokacin ban baka ba

26 / 31