SO MAHADIN RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVELS PDF BY BILKISU Z YAU.txt

Author :  Bilkisu Z Ya'u Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   5 / 31

12K to 15K   out of 90.7K words

nake se dai zuciyata da ke yi min zafi saboda addabata da take yi da tunaninki, dama saboda kizo in ganki ne in samu maganin rad'ad'in da take min ne kawai, haba Amira tun jiya fa da muka dawo daga asibiti ban k'ara ganinki ba a tunaninki baran cutu ba."



Amira ta harare shi tare da kai mishi duka da hannu ya goce tare da yi mata dariya harda kashe ido d'aya, Amira ta kalle shi tace " ka daina yi min irin wannan wasan bana so, da ka fad'a min gaskiya kana son ganina ne ai zan taho gareka ba sai ka tsoratani da rashin lafiya ba," ganin ranta ya b'aci da yawa yasa ya taso ya duk'a a gabanta yana bata hak'uri amma ta kauda kanta, plet d'in wak'ar d'an kuka ya saka sannan ya kunna mik'ewa tsaye ya yi, wak'ar cikin film d'in na d'an kuka yake rera mata _(abinda nai kiy hak'uri na yi nadama)_ yana rawa a gabanta yana had'a hannaye tare da kakkantarewa tamkar yanda ake yi a cikin wak'ar, duk yanda taso kartai dariya saida ya sata dariya sosai har saida wak'ar ta k'are sannan ya hak'ura da rawar, zama ya yi a gabanta ya tasa ta kamar tv yana kallo, ta kalle shi tace " wallahi ka bani dariya," Amir yace haka nake fatan ki kasance a koda yaushe."



Amira ta sake kallon shi sannan tace " ya k'arfin jikin?" Amir yace " na ji sauk'i nan ne kawai yake min ciwo ya nuna saitin zuciyarsa da hannu, share shi ta yi, tare da mik'ewa zata tafi shima ya tashi yace " naga kin mik'e ina zaki je?"



Amira tace zan tafi gida mana, Amir ya b'ata rai sannan yace " dan Allah karki tafi, idan muna tare wallahi bana so mu rabu koda na minti d'aya ne kuwa," Amira ta kalle shi tace " meyasa?" Amir yace " nima tambayar da nake ta wa kaina kenan, meyasa nake jin hakan a tare dake, yanzu dai abar wannan maganar wannan ne karonki na farko zuwa gida na saboda haka da kaina zan shiga kicin in miki girki, me kike so a dafa miki?" Amira tace " tab' bazan ci kwamacalarka ba bakina ya b'aci, in girki kake so bari in shiga in girka maka," Amir ya kafe kan shi zai yi mata girki haka nan ta hak'ura ta k'yale shi, ya shiga kicin yana aiki a yayin da ya hanata taimaka mishi da komai, bayan wani d'an tak'aitaccen lokaci Amir ya kammala abinda yake girkawa, ya zubo mata sannan ya zuba mata lemo, cikin fargabar yanda bakinta zai b'aci ta kai cokali d'aya bakinta tare da fara yamutsa fuska, a hankali kuma sai ta ware tare da kallon shi, bata ankara ba ta tayar da girkin Amir tas, bayan ta gama ta sha lemo kad'an sannan ta kalle shi tace " ka bani mamaki matuk'a, wallahi ka iya girki, matarka ta huta."



Amir yai karaf yace " to ai kece matar," d'agowa ta yi tare da wurga mishi wani irin kallo mai kama da harara da kuma tuhuma, shima kallonta ya yi tare da rik'e bakin katob'arar da ya yi, a ganinshi ba yanzu bane lokacin bayyana mata abinda ke ranshi, kallonta ya sake yi sannan ya turo baki kamar k'aramin yaro yace " maida wuk'ar wannan fushi da harara haka, to wasa nake yi, 'yar daba kawai, wannan kallon da kike min 'yan daba kad'ai ke yin irin shi," sannan ya murgud'a mata baki.



Girgiza kai Amira ta yi, tare da yin murmushi, a zuciyarta take fad'in tabbas Amir yai gaskiya da yace zai sakata ta manta da duk wata damuwa gashi kuwa ta tabbatar, harga Allah zama da shi yana sata cikin farin ciki a koda yaushe, tana jin dad'in kasancewa tare da shi sosai.



Amira ta duba agogo, sannan ta d'ago ta kalle shi tace " lokaci ya tafi zan koma gida, tun da safe da ka sani na fito ba shiri gashi yanzu har biyu ta yi," Amir ya kalle ta yace " dan Allah karki tafi, ki zauna da zuciyar da take muradin kasancewa da ke a koda yaushe."



Amira ta kalle shi tace " wallahi kana bani mamaki ka fiye rigima sai kace mace, jiya fa muna tare yauma gamu a tare, da yaushe ne bama kasancewa da juna."



Amir yace " shikenan bari in zo in kai ki," Amira tace " a'a ka barshi nafi so ka huta ka k'ara wartsakewa," Amir yace " taya za'ai in wartsake kina tafiya ki barni ni kad'ai, dan Allah karki tafi, wallahi bana so kina yin nesa da ni," kallon shi Amira ta yi sannan tace " wai da gaske kake dama, kai in nace zan zauna sai ka yarda?"



Amir yace " wallahi da gaske nake yi bana so kina yin nesa da ni, kuma duk abinda nake fad'a miki sak'o ne daga zuciyata zuwa ga taki zuciyar."



Amira tace " ka k'ware wajen iya tsara kalamai, da kallon k'urulla da kake yiwa mutane da kuma kalamanka da za'ai gasa a kansu ina tsammanin kai zaka zo na d'aya," Amir yai murmushi karo na farko da ya ji dad'i a ranshi sanadin Amira ta yaba mishi."



Sallama suka yi da shi ya shaida mata yana nan zuwa anjima zai zo su sha hira, tace ya bari sai gobe in Allah ya kaimu lokacin jikin ya k'ara warwarewa, Amir yace " wallahi sai nazo anjima ko zaki kwana kina rok'ona kar nazo ehe," haka ta fito tana dariya ta barshi yana mita tana jiyo shi wai bata so yazo.



Haka suke kasancewa a koda yaushe suna tare, bayan kwana biyu da yamma wajen k'arfe hud'u Amir ya faka motar shi k'ofar gidan Amira, hon ya danna ba tare da ya shiga ba sai gata ta fito, to dama yanzu sun saba kullum zasu fita da yamma suje wurin shak'atawa da sauran wurare dai na jin dad'i da more rayuwa, to duk in zasu yi irin wannan fitar basu cika zuwa a mota ba, da yake daga gidan Amira ba nisa zuwa wajen.



Fitowa Amir ya yi shim daga mota suka d'auki hanya, kowa ya gansu tamkar miji da mata, sun zuba anko kamar had'in baki kayan da Amir yasa shadda ce milk, itama atamfar da ta saka milk d'in yafi yawa a jiki, sun sha anko sunyi kyau sosai, duk inda suka gifta su kawai ake kallo, suna cikin tafiya sai Amira ta hango fura da nono, to ita dama tana masifar son fura da nono, kuma duk inda ta gani bata wucewa sai ta tsaya ta siya, hakan yasa Amira ta nuna wa Amir tace ya jirata taje ta siyo ta dawo, da yake can tsallake ne, dole sai an tsallaka ti-ti sannan za'a k'araso inda me furar take Amir yace " a'a babu inda zaki je, ki jirani in siyo miki in dawo, Amira tace to tsaya ka karb'i kud'in ya harareta sannan yace " kaji son a sani, ai ko banda kud'i a aljihuna ko rigar jikina sai na siyar na se miki abinda kike buk'ata wallahi," Amira tace " ai kuwa duk ranar da kai haka ban jerawa da kai babu riga," juyawa ya yi yana dariya ya tsallaka ti-ti domin siyo mata abinda ta buk'ata, ya juyo zai dawo ya hango wasu maza kewaye da ita, da alamu magana take gaggaya musu, da gudu Amir ya tafi wajen su, wani ne ya d'aga hannu zai mari Amiran a dai-dai Amir ya k'araso kawai ji ya yi an rik'e mishi hannu ta baya Amir be sakin mishi hannu ba saida ya karya, nan fa Allah ya bashi sa'a yai musu shegen duka, yana cikin dukan su 'yan sanda suka k'araso wajen ciki kuwa harda Insp Yahya (kafi k'arfin mugu), kallon kallo suka yi tsakanin Amir da Insp Yahya, can sai Yahya ya baiwa jami'an umurnin su tafi da su station gaba d'aya, haka kuwa aka yi, aka sa su a mota sai station.



Dukkan su a tsugunne suke gaban Insp Yahya yana kallon su d'aya bayan d'aya, sai da yaji duk abinda ya faru, kuma dama tun a can ya yi bincike an tabbatar mishi da cewa Amir ne ya hau dukan su saboda kawai sun kula Amira.



Dukkan su cikin sel aka gark'ama su, Amira tana ta faman rok'on sa akan cewa ya yi hak'uri dan Allah ba zai sake ba, Insp Yahya ya kalleta yace " ai bazan iya sakin d'aya in bar d'aya ba, se dai in duka zakiy belin su to," Amira tace "eh na yarda a bani belin d'in su gabad'aya," saka wa ya yi a fito da su, sannan suka saka hannu d'aya bayan d'aya kan in suka sake sai an hukunta su hukunci mai tsanani, ya sallame su, amma banda Amir da Amira.



Bayan sauran sun tafi Insp Yahya ya kalli Amir yace " wai kai menene alak'arka da wannan yarinyar ne," Amir kai tsaye yace " sonta nake kuma aurenta zan yi, Insp Yahya yace " ai naga alama tun kafin ka fad'i, to wannan dalilin ne yasa ka shek'e samarinta har biyu?" Amir yace " yallab'ai kawai dan na yi soyayya da Amira sai ya zama laifi har ana tuhumata da aikata kisa, kenan duk wanda ya yi soyayya da ita tuhumar kisa zaku yi mishi, kiji fa abinda d'an sandan nan ke fad'i Amira, " ya juya yana yi wa Amira magana.



Amira ita kanta bata ji dad'in maganar da Insp ya fad'a wa Amir ba, ta kalli Insp tace " yallab'ai a tunani tunda an riga an gano mai laifin har an hukunta shi to be dace kana tuhumar wani daban ba kuma babu shaida ba komai, mun gode da taimakon da kai mana a yau," ta kalli Amir tace suje.



Har sun kai bakin k'ofa Insp yace " idan ka k'ara shigowa hannunmu kan ka daki wasu ko ka yi fad'a da wasu to zaka yi watanni a kulle," cikin sauri Amir ya juyo ya dawo tare da fad'in yallab'ai kawai in zaka kulle ni ka kulle ni, amma na rantse maka da Allah akan Amira ba wanda zan k'yale, ko kallon banza akai mata to wallahi sai na kai duka, tun yanzu na fad'a maka gaskiyata gwara kawai ka maida ni cikin sel d'in zai fi," yana fad'in haka yana kuma tunkaro inda Insp d'in yake, Amira ce tai sauri ta rik'o hannun Amir d'in sannan ta kalli Insp tace " yallab'ai ka yi hak'uri, insha Allah zamu kiyaye, ta ja hannun Amir d'in suka fice daga station d'in, gida suka wuce kai tsaye fitar da ba'a yita ba kenan a ranar.



Insp kuwa koda suka fita binsu yai da kallo yana huci sannan ya girgiza kai yace " tun ganina da Amir d'innan naji ina zargin shi, kuma itama Amiran yanzu na fara zarginta ban yarda da su ba, kuma daga yau wallahi sai na sa musu ido a kan duk wani motsi nasu, hmmmmm baku san wanene kafi k'arfin mugu ba labarina kawai kuke ji, ba dai shaida kuke nema ba, zan nemota duk inda take."







Muje zuwa







*πŸ…±K CEπŸ˜˜πŸ’‹*
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜





RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (πŸ…±K)*
```(Autar marubuta)```





SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
_(Mamie)_







*πŸ‡ΈπŸ‡¦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```







PAGE 40 to 45






Zaune suke kowanne daga cikin su ranshi a b'ace saboda abinda ya faru yau ya b'ata musu shirin su, Amira ta d'ago kai ta kalli Amir tace " Amir kulawarka ta yi yawa a kaina meyasa, gaskiya in kana so mu shirya ka daina yin fad'a da mutane kaina."



Amir ya ji ba dad'i a cikin maganarta ta yanzu, kuma itama ta lura da hakan, ya kalleta yace " kiyi hak'uri ban yi hakan domin b'ata ranki ba, kuma bansan yin hakan zai zama laifi a gareki ba ko abun b'acin rai da ban yi ba, na yi haka ne domin kare ki daga sharrin su, kiyi hak'uri laifina ne da na biyewa umurnin zuciyata na aikata abinda ya zama silar b'acin ranki," yana gama fad'in haka sai ya tashi ya fito daga d'akin, lambun gidan yaje ya zauna tare da kife kanshi yana kuka.



Amira ce ta fito itama ta biyo shi tana neman inda yake, fita k'ofar gida ta yi tana dubawa, se dai ganin motar shi a k'ofar gidan ya tabbatar mata da ba tafiya ya yi ba, to yana ina tambayar da take ta yiwa zuciyarta kenan, nadamar maganganun da ta fad'a mishi take yi domin tasan duk a kanta da kulawar da yake mata ne tasa yai komai, nan ta ji gaba d'aya bata kyauta ba, tunaninta a yanzu kawai kar b'acin ransa ya sa ya jawo ya yi abinda zai cutar da shi, nan da nan itama ta fara hawaye, tana kukan tana waige waige ko zata ganshi can sai tunanin shiga lambu yazo mata, da sauri ta nufi wajen har tana cin tuntub'e.



Tana shiga wajen tun daga nesa ta hango shi, ta k'arasa da sauri har lokacin kuka yake yi ta zauna kusa da shi, sannan ta dafa shi tace " haba Amir meyasa kake yi min asarar hawayenka daga yin wannan maganar."



Amir ya d'ago ya kalleta da idanunsa da suka koma ja, kuma har sun fara kumbura saboda kuka, yace " ba ina yin kuka bane saboda maganar da kika fad'a min a'a, ina yin kuka ne a kan b'ata ranki da na yi, duk duniya idan da akwai abinda ya fi zama tashin hankali a gareni to b'acin ranki ne," yana gama fad'in haka ya koma zai mayar da kanshi ya cigaba da sana'ar tashi, sai ta hanashi komawa ta hanyar rik'e shi.



Amira ta kalle shi sannan tace " ka daina kukan haka to dan Allah bana so, ka yi hak'uri da abinda na fad'a maka, bana so ka sake yin rigima ne shiyasa na fad'a maka haka, amma nima naji zafi a raina lokacin da nake fad'a maka, kuma ni raina bai b'aci ba, koda ya b'aci ko na ji haushi bazan gwada shi a kan wanda yake zama sanadin farin cikina ba a koda yaushe, wanda ke samar da walwalata kuma yake farin cikin kasancewar shi a tare da ni a koda yaushe."



Amir yai murmushin jin dad'in maganarta, Amira ta kalle shi tace " yauwa ko kai fa, ta share mishi hawayen fuskarsa da hannunta ta mik'e sannan ta mik'o mishi hannu tare da fad'in taso mu koma falo, Amir ya kama hannunta tare da mik'ewa suka koma cikin d'aki.



zama suka yi a kujera sannan Amir ya kalleta yace " naga kema kamar kin yi kuka, fad'amun me ya saki kuka?"



Amira tace " yo ba dole in yi kuka ba bansan ina ka shige ba," Amir yai murmushi zuciyar shi na fad'in lallai Amira ta fara damuwa da shi, dama abinda yake so kenan, ta shak'u dashi, ta damu da shi kafin ya kai ga furta mata, cikin ranshi yace lallai lokacin bayyana mata sirrin zuciyata ya kusa.



Amira ta kalle shi tace " me zan dafa maka, dan nima yau sai ka ci irin girki na, " Amir yace "a'a ki bari zan dafa mana kije ki kwanta kawai," Amira cikin ranta tace " dama so nake kace zaka yi shiyasa na fad'i haka saboda kar na nuna maka ina son girkin ka kai min dariya," Amir ya kwashe da dariya yace to ai ko yanzu na ji tunda a fili kika fad'i, inma a zuciya kike tunanin kin fad'i to ya fito fili," ya sake kwashe mata da dariya tare da yi mata gwalo, tab'e fuska tai kamar zata yi kuka, ta biyo shi da gudu sai da suka gama zagaye falon duk abinda ta samu tana wurga mishi duk sun haukata d'akin, sannan daga k'arshe Amir ya shige cikin kicin d'in tare da rufo k'ofar, daga falon Amira na numfarfashin wahala tace zaka fito ka sameni ne ai.



Amir yai murmushi, jin takunta alamar ta juya yasa ya k'arasa ciki ya fara gudanar da aikin da ya shigo da shi ciki, da yake akwai komai a cikin kicin d'in shiyasa sam bai fito ba.



Sai da ya kammala dukkanin abinda yake yi sannan ya fito, gani yai d'akin yai ras ko'ina an gyara shi, ga wani dadda'dan k'amshi da ya cika ko ina murmushi ya yi sannan a fili yace " kamar kin san ina mugun son mace me tsabta gaskiya na dace," bayan ya gama jera abincin ya shiga cikin d'aki domin kiran gimbiyar, se dai tarar da ita ya yi ta yi wankanta ta kwanta tana ta bacci, har ya duk'a zai tashe ta sai ya fasa, ya bar ta sai ta tashi dan kanta.



Makullin motar shi ya d'auka ya fita ya tafi gidan shi, wanka ya yi yai sallah sannan ya sake cakarewa cikin k'ananan kaya, ya sake d'aukar makulli ya fito sai gidan Amira.



Wani katafaren shago ya biya ya siya wani abu wanda ban lura da ko menene ba ya biya aka sa mishi cikin leda ya fito ya shiga motar shi, bai sake tsayawa ko ina ba sai gidan Amira.



Bayan yai fakin ya fito ya shiga ciki, koda ya shiga bai tarar da ita a falo ba, wucewa yai ciki ya tarar da ita har yanzu bacci kawai take sha, bubbuga gadon ya hau yi yana fad'in " malama ki tashi ni fa yunwa nake ji ke nake ta jira."



Amira ta tashi tare da ambaton sunan Allah, ta fad'a ban d'aki ta sake yin wanka sannan ta canza kaya ta fito, a falo ta tarar da Amir ya zuba abincinsa ya fara ci.



Amira ta kalle shi tace " shine baka jira ni na

5 / 31