Author : Bilkisu Z Ya'u Category : Romantic Hausa Novels
abubuwan da sukai ta faruwa da shi a rayuwa har zuwa wannan hatsarin, sannan Amir ya d'ora da fad'in "abinda yasa nace ina so na zauna daku na wani lokaci saboda in cigaba da neman iyayena a hankali har Allah yasa in gansu, nasan Dad ne yasa ai min haka, 'kila idan na nemo iyayena zai sassauta tsanar da yake yi a kaina."
Dukkaninsu kuka suke yi, musamman ma Khadija kukanta har da shesshe'ka, labarinshi abun tausayi ne matu'ka ace tun yana yaro be san wani abu wai shi jin dad'in rayuwa ba har girma, kuma sai labarin shi yai musu famin wata dad'ad'd'iyar damuwa da take damunsu a rai.
Ahmad ne ya share hawayensa, sannan ya kalli Khadija da har ta fara tari ciwonta naso ya tashi saboda kuka, cikin sauri, Ahmad da Amir d'in suka 'karasa wajenta a tare suna mata sannu, Ahmad fad'a yake yi, "kinsan yanayin ciwonki baya son damuwa amma daga jin labari kinbi duk kin d'aga hankalinki," maganinta ya d'auko mata ya bata ta sha, sannan yace "muje in kaiki ki kwanta," Khadija tace "a'a barni a nan ma kawai."
Ahmad ya zauna kusa da ita yana yi mata sannu, Amir kuwa ji yayi yanayin rayuwar bayin Allahn nan ta burgesu, kuma sai yaji yana matu'kar 'kaunarsu.
Muryar Ahmad ne ta katse mishi tunani, yace "Amir munji labarinka, kuma mun tausaya maka matu'ka, muma ka ganmu nan, muna jin kusan irin rad'ad'in da kake ji, yaron mu ya ya b'ata tun yana 'karami baida wayau be san kanshi ba, amma har yanzu mun kasa mantawa dashi, gani muke kamar ma zamu ganshi, tun farkon ganinmu da kai Allah ya saka mana 'kaunarka cikin ranmu, irin soyayyar da iyaye ke gwada wa kan 'ya'yansu, idan ba zaka damu ba ka zauna tare da mu, mu zame maka iyaye, ka d'aukemu ka kaimu gidan su yarinyar a matsayin iyayenka na asali."
Amir yace "Abba nagode da 'kaunar da kuka nuna kaina, kuma na yarda zan zauna daku, zan ri'keku matsayin iyaye a gareni na har abada koda kuwa naga iyayena bazan manta da ku ba bazan ma gujeku ba muna tare, amma sedai maganar zuwa gidan su Amira a barta kawai, saboda idan munje yanzu nan gaba zasu iya gano gaskiya, ko kuma bayan munje na nunaku daga baya sai naga iyayena yaya kenan? kawai mu cigaba da addu'a Allah ya bayyana su, kuma Allah ya bayyana muku d'anku, amma kar kuji komai ina tare da ku."
Ahmad da Khadija sun ji farin ciki sosai, domin har ga Allah suna 'kaunar yaron, suna ji a ransu kamar d'ansu ne ya dawo, shiyasa yau suka shiga farin ciki mara misaltuwa, shi kuwa Amir yanda yaga suna farin ciki abin sai ya bashi mamaki da tausayi.
*BAYAN WATA BIYU*
Amir ya warke sarai har sun fara fita da Abbansa, babu inda basa zuwa tare sai d'ad'd'aikun wurare.
Har yanzu Ahmad yana nan da a'kidarsa na 'kin son security na binsa a baya, amma kuma baya yarda Amir ya fita ko nan da can shi kad'ai, koda fita akai dashi ma baya fitowa se dai masu tsaronshi suyi masa komai, duk hanyar da zai sadashi da inda zai ga Amira baya binta kwata-kwata.
Amir sosai yake jin dad'in zama da mutanen nan, mutane ne masu taimako, sam abin hannunsu da daular mulki bata rufe musu idanu ba, kullum gidan nan cike yake da talakawa mabu'kata suna neman taimako, sai ya sallami na gida kuma zai fita ya kewaya gidan marayu asibitoci, unguwanni domin duba lalatattun hanyoyi yaga masu matsala a gyara, kullum aikinsa kenan, kuma kullum sai yayi haka, yama zama d'abi'arsa, sai ya gama da talakawansa sannan yake shiga office, canma kome zai tattauna duk a kansu ne, mutum me gaskiya da son Al'umma kenan, be yarda yaci ko sisin mutane ba, shiyasa ma ya cigaba da kula da kamfaninsa da duk kadarorin da yasan guminsa ne, kuma duk abinda zaiyi na bu'katarsa da ta gidansa baya yin amfani da ko 'kwandalar talakawansa, sedai yai amfani da abinda yake mallakinsa ne tun kafin ya hau mulkin, bayan ya gama nunawa Amir komai na siyaysa ya sani, sai ya kaishi d'aya daga cikin manyan kamfanoninsa domin ya cigaba da kula masa da shi, wannan kenan.
…………………………………………
B'angaren Amira kuwa har yanzu tana jiya yau, ba um ba um-um.
Dad kuwa yanzu ya saki ranshi, saboda yasan ya tara biliyoyin kud'i da kadarori wad'anda zasu ci shi da iyalinshi kuma har su mutu be 'kare ba, hakan yasa ya cigaba da harkokinsa, tare da cigaba da kula da dukiyarsa.
Muje zuwa
*🅱K CE😘💋*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (🅱K)*
```(Autar marubuta)```
SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
```(Mamie)```
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```🤜🤛
*INA BAIWA MASOYANA MAKARANTA LITTAFIN SO MAHA'DIN RAYUWA HA'KURI, PAGE 'DIN JIYA NAYI MISTAKE 'DIN LAMBA 150 NE TO 155, NA YAU KUMA 155 TO 160 KAR KUI TUNANIN NA JIYA NE NA SAKE TUROWA YAU, NAGODE👏😍😘*
PAGE 155 to 160
Kamar kullum yauma Khadija zaune take tana sana'ar ta tunani, sai ga Amir ya shigo cikin gidan d'auke da sallama, har inda take ya k'araso tare da tsugunnawa kusa da ita, sanna ya dafa ta yace "Umma shin har yanzu ba zaki daina wannan tunanin ba, dan Allah ki daina tunani idan muka rasaki ba zamu tab'a samun farin ciki ba," yana fad'in haka yana kuka, 'karshe ma sai ya du'kar da kanshi jikinta yana cigaba da kukansa.
Amir ya cigaba da fad'in "kamata yayi ki gode wa Allah da ya musanya muku da ni, har ga Allah kuma har a zuciyata jinku nake kamar iyayena wad'anda suka haifeni, to banda abinki ma Umma kina da d'a kamar ni me zaisa ki cigaba da damuwa, ki daina kuka banaso ina jin ba dad'i a raina," yana fad'in haka yana share mata hawaye.
Abba Ahmad dake bakin 'kofa yai murmushi tare da share hawayen da suke ta yawo kan fuskarshi, har cikin ranshi yake jin 'kaunar yaron, yanda ya shiga ransu da yanda yake nuna kulawarshi a kansu ko d'ansu na cikinsu ne sai haka.
Gyaran murya yayi sannan yai sallama ya 'karaso ciki, Amir da Umma Khadija suka yi mishi sannu da zuwa, sannan Amir ya kalli Ahmad yace "yauwa Abba gwara da ka dawo, kai wa Umma fad'a ta dena tunani kaga rashin lafiyarta baya bu'katar hakan, bazan juri rashinku ba Abba, kuma ko kad'an bazan so wani abu ya sameku ba," yana zuwa nan a zancen shi sai ya sake fashewa da kuka.
Ahmad da Khadija suka kalli juna jikinsu duk yai sanyi, harga Allah suna jin mamakin irin matsananciyar k'aunar da Amir ke nuna musu cikin 'kan'kanin lokaci, Abba ya taso yazo kusa da Amir ya tsugunna, sannan ya dafa shi yace "yi shiru d'ana dena kuka daga yau insha Allah ba zata sake yin kuka ba ko dan farin cikinka," Ahmad ya d'ago kai ya kalli Khadiha yace "haba my love shin soyayyar da yaron nan ke gwada mana da kuwarashi da damuwa da dukkanin wasu lamura namu be isa yasa ki manta da komai ba ki rungumi kyautar da Allah yai miki hannu biyu, in kina kukan me kikai haka kenan, godiya wa Allah ko butulce masa? kina da tabbacin idan d'an namu ya dawo zamu samu farin ciki daga gareshi kamar yanda muke samu a yanzu? to ko d'an da ka haifa da cikinka ba kowanne ke kyautata maka ba, ya kamata ki manta da komai my love indai kina son farin cikin yaronmu da walwalarshi."
Khadija ta share hawayen da suke gangarowa kan fuskarta, sannan tace "abinda ya sakani tunani da kuka ba abinda yake tunani bane, ina kokawa ne akan ban tab'a tunanin zan samu d'a wanda zai kirani da Umma kuma har ya bani dukkanin kulawarsa bane sai gashi Allah ya bani, ni kukan farin ciki nake yi d'ana, ta dafa Amir sannan ta cigaba da cewa, kuma daga yau ka daina sake ganin tunanina ma balle zubar hawayena."
Amir yai murmushi sannan yace "Allah yasa," dukkansu suka amsa da "ameen," Abba ya kalli Amir yace "yarona wai meyasa naji ka dakatar da maganar neman iyayenka?" Amir yai shiru ya kauda zancen, Abba ya sake nanata zancenshi, Amir yace "to me zaisa in cigaba da neman su bayan ina da ku, addu'ar da nake ta wadatar, in Allah yaso mu had'u zamu had'u wata rana, Abba yace "hakan be dace ba ya kamata ka cigaba da nemansu kamar.........." Amiya ya katseshi ta hanyar fad'in "Abba bari inje in dawo na tuna naiwa wani alk'awarin zamu had'u dai-dai wannan lokacin a office, Abba yace "amma yarona.........." "Abba dan Allah ka barni in tafi," Amir ya sake ro'konsa a karo na biyu, Abba yace "shikenan sai ka dawo Allah ya tsare, Allah yai maka albarka," Amir yace "ameen Abba, ya matsa gun Umma ya d'an duk'a sannan yace "Ummana ke baki sa taki albarkar ba, Umma tai murmushi, sannan ta dafashi tace "Allah yai maka albarka d'ana ya dawo mana da kai gida lafiya," Amir yace "ameen Ummana," yana gama fad'in haka ya doshi hanyar fita, saida ya kai bakin 'kofa sannan ya juyo ya kalle su, suma shi suke kallo dukkansu, ya 'kyal'kyale musu da dariya sannan yace "yeeeee nai musu wayau hahaha," yana fad'in haka ya gudu, Abba yace "zo nan Amir z.........." ina ya gudu, dukkansu dariya suke yi, Ahmad yace "wai yai mana wayau, na sani sarai maganar da nai masa ce yasa ya fita kawai na 'kyaleshi ne," Khadija wadda har yanzu dariya take yi tai magana tana dariya tace "ni yanda yai maganar ne ma ya bani dariya harda su gwalo, kai Amir naga randa zai girma."
Abba ya 'kura mata idanu yana murmushi ya d'aga hannu sama yace "Allah na gode maka da ka azurtamu da yaron da ya dawo da farin cikin gidana da na matata.
Amir kuwa yana fita yaje ya samu gefen wani waje a unguwarsu ya zauna ya had'e kansa da guiwa ya fashe da kuka, babu abinda ya sashi kuka sai Amira da ta fad'o mishi a rai, kullum haka yake tsintar kanshi a ciki duk lokacin da ya tuno da ita, tunani yake ko a wane hali take ciki Allah kad'ai ya sani, koda yai niyyar zuwa gidan su domin ya ganta sai ya tuno da irin abubuwan da mahaifinta yai mishi sai ya fasa zuwa, ya dad'e a wajen yana hawayensa tare da tunane-tunanensa, sai daga baya ya tashi ya shiga mota suka bar unguwar.
…………………………………
B'angaren Amira kuwa to Alhamdulillah dai za'a ce domin kuwa an samu cigaba, tunda zata yi magana, amma itama sai ta kama irin in tana bu'katar wani abu ko kuma in ita an tambayeta wani abun, Amma maganar walwala ko hira da mutane har yanzu babu ita, koda yaushe fuskar nan ba annuri.
*BAYAN SHEKARU UKU*
Amira haka ta cigaba da rayuwarta an kuma maida ita makaranta domin karatun ya ri'ka d'ebe mata kewar kad'aici, sedai abinda basu sani ba shine sam bata gane komai yanzu a karatun nata.
Yau laraba, Dad ne ya shigo cikin gidan cike da farin ciki a fuskarsa, ya kalli dukkanin mutanen falon bai ga Amira ba, ya kalli Mum yace "ina Amira?" Mum tace "tana d'akinta, kasan yanzu bata shigowa cikinmu," Dad yace "to ku shirya ina da ba'ko yau a gidan nan, ba ba'kon kowa bane kuma illah ba'kon Amira, d'an wani d'an sanata Bashir ne, sunansa Mahmud daga Kano, yanzu haka yana tafe, bari inje da kaina in sanar mata."
Mum ta dakatar dashi, sannan tace "a tunanina ba a irin wannan halin ya dace mu je wa da Amira da zancen mijin aure ba, kamata yai mu bari har 'karasa dawowa normal kamar yanda take a da."
Dad yace "shekaru uku kenan da mutuwar mijinta, sai mu cigaba da zuba mata ido kike so ko me? ni dai na gama magana sun je sun sameni sun nemi izini wajena kuma na yaba da hankalinsu, dan haka na basu izini suzo su daidaita da ita," ya haye sama domin zuwa gun Amira ya sanar da ita.
Yana shiga ya tarar da ita ri'ke da wayar Amir tana kallon hotunanshi hawaye na wanke fuskarta.
Dad ya zauna kusa da ita, sannan ya kalleta yace "My Doughter ya kamata ki cire tunanin Amir daga ranki damin ni dake duk mun sani wanda ya tafi baya tab'a dawowa, dan haka ki yawaita yi mishi addu'a ne kawai itace soyayyar da tai saura a tsakaninki da shi."
Amira ta gyad'a kai alamun amsawa, Dad ya cigaba da cewa akwai wani yaro da yaje ya sameni ya fad'amin yazo Abuja wakiltar mahaifinsa wani taro ya ganki a hanyarki ta zuwa makaranta bai miki magana ba har saida ya bi ki a baya ya tambayi 'kawayenki sukai mishi bashi bayani game da ke sannan ya taho wajena, a ta'kaice yana sonki da aure, yanzu haka yana hanya zai zo kuga juna in ya yi miki shikenan.
Amira iya kad'uwa da razana tayi, amma sai ta dake tace "to Dad," iya abinda ta iya cewa kenan, Dad yace "Allah yai miki albarka, sai ki tashi ki shirya kafin ba'kon naki ya 'karaso," ya tashi ya fice daga d'akin.
Yana fita Amira ta fad'a gado ta fara kuka, tana fad'in "Amir why! meyasa zakai min haka, meyasa zaka tafi ka barni, taya zan iya cigaba da rayuwa ni bayan rabinta ya tafi, sai kuma ta hau girgiza kai, tana fad'in a'a wallahi Amir bai mutu ba, ina ji a jikina Amir d'ina bazai min haka ba, nasan ba zai mutu ya barni ni d'aya cikin wannan duniyar ba," ta dad'e tana kuka babu me rarrashi, a dai-dai wannan lokacin irin halin da take ciki shima Amir yake ciki, so kenan, masoya na ha'ki'ka sukan iya tsintar kansu cikin yanayi iri d'aya, tunani iri d'aya, damuwa ma iri d'aya, ikon Allah kenan.
Bayan ta gama cin kukanta ba mai rarrashi sai ta bawa kanta ha'kuri kamar kullum ta tashi ta shirya.
Ta shirya ba dad'ewa Dad d'inta ya kirata a waya ya sanar da ita cewa ba'konta ya iso yana b'angaren d'akin ba'ki.
Cikin rashin kuzari ta yafa mayafi tare da ficewa daga d'akin ta tunkari b'angaren masaukin ba'ki.
Tana zuwa bakin 'kofa taja ta tsaya tana jiyo wayar da yake yi kuma yana 'kyal'kyalar dariyarsa.
Da farko abinda yasa ta tsaya fad'uwar gaba taji matsananci saboda zuciyarta na ayyana mata kamar in ta kula wani ta ci amanar Amir, sedai fara sauraron abinda saurayin nan ke cewa a kunnuwanta yaja ta 'kara tsayawa tsayuwa me dalili tare da 'kara matsawa tana saurare, abubuwan da taji yasa ta 'kara sarewa da lamarin duniya ta kuma razana abun ya bata mamaki kuma, koda yake ba mamaki in dai wannan zamanin da muke ciki ne.
Cikin sauri ta yaye labulen tare da kutsawa cikin falon, tace "in ka gama wayar sai ka tashi ka tafi, kuma naji duk abinda ka gama fad'i yanzu, inada damar tona maka asiri, amma sedai nasan muddin 'yan gidan nan suka ji sai sun kashe ka, saboda haka fice mana daga gida da kai da dogarawarka kuje ku kwashe motocinku ku bar gidan nan kafin raina ya b'aci in tona maka asiri kowa yaji."
Mahmud ya tashi sum-sum ya fice daga d'akin, cikin 'kan'kanin lokaci suka tattara suka bar gidan.
Nan ma Amira sai da taci kuka sosai sannan ta tashi ta koma cikin gida.
A falo ta tarar da Dad d'inta, har zata wuce ya tsaida ita yace "zo nan 'yata," Amira ta 'karasa kusa dashi ta zauna ya kalleta yace "ba'kon naki har ya tafi?" Amira ta gyad'a kai alamar eh.
Dad yace "to fad'amin ya kukai yadai yi miki ko?"
_Ayi ha'kuri da wannan banjin dad'i wallahi👏_
Muje zuwa
*🅱K CE😘💋*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
*SO MAHA'DIN RAYUWA!*
💘💘💘💘💘💘💘💘💘💘
RUBUTAWA
*BILKISU Z. YA'U (🅱K)*
```(Autar marubuta)```
SADAUKARWA GA:
*MAMAN LABYB*
```(Mamie)```
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
```(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)```🤜🤛
*MAMIEN BK SANNU BAIWAR ALLAH😰 ALLAH YA 'DORAR MIKI DA DAUWAMAMMIYAR LAFIYA TARE DA DUKKANIN MUSULMI BAKI 'DAYA👏😭😭😭😭😭*
*TAWAN INA RO'KON ALLAH YA BAKI LAFIYA, YA KAWO MIKI SAU'KI DA 'DORARRIYAR LAFIYA, YA YAYE MIKI DUKKANIN DAMUWARKI.*👏😭
*HABIBTY NAH INA RO'KON ALLAH YA BAIWA 'DAN UWANMU LAFIYA 'DORARRA*👏😭
*ALLAH SARKI MASU KU'DI ABUN TAUSAYI,😰 KAFIN SU GANE MASOYI NA GASKIYA SAI SUN SHA MATU'KAR WAHALA, SABODA YAWANCI BA DAN ALLAH AKE 'KAUNARSU BA SAI DON ABUN HANNUNSU, YA ALLAH KA SADA KOWA DA MASOYI NA GASKIYA MAI YIN 'KAUNA DOMIN ALLAH👏*
PAGE 160 to 165
Dad ya sake maimaita tambayarsa ga Amira yace "tambayarki nake Amira kinyi shiru, nace ya kukai dashi ya yi miki?"
Amira tace "Dad Mahmud ba d'an kowa bane, duk abubuwan da yazo dasu hayarsu suka yi saboda kwad'ayin abun duniya, kuma duk abinda ya fad'a maka game dashi 'karya ne, Dad bansan ya akai ba har kai saurin amincewa dashi ba tare da kayi bincike ba, Dad ashe abinda yasa ka 'ki Amir saboda shi ba d'an kowa bane kenan, da ace yana da kud'i zaka 'kaunace shi koda babu asalinshi kuma kai saurin amincewa dashi kamar yanda kayi wa wannan mutumin?"
Dad ya daka mata tsawa tare da fad'in "wato saboda bakya son auren shiyasa kika zo da wannan 'karyar domin kiy masa sharri koh, to ban yarda da wannan tsarin naki na 'karya ba, saboda haka kije sai nayi bincike na tabbatar, tashi ki bani guri mutuniyar kawai na kawo mutum kin wula'kantashi da wannan banzan halin naki da kika canza."
Amira tace "Dad wallahi tun kafin na shiga d'akin naji yana waya da wasu yana.........." Dad ya sake katseta yace "ba zaki yimin shiru ba, tashi ki bani waje," Amira ta tashi ta haye sama da sauri tana kuka, zuciyarta na zafi saboda 'kin gasgata zancenta da Dad yayi, duk da Dad