Chapter 1 Reading RUDANI COMPLETE HAUSA NOVELS BY LASHMINZY.txt Arewa Novels

RUDANI COMPLETE HAUSA NOVELS BY LASHMINZY.txt

Author :  LASHMINZY Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   1 / 27

1 to 3K   out of 79.1K words

ο»Ώ[2/2, 10:07 AM] Lashminzy😎: πŸ’«πŸŒžπŸ’«πŸŒžπŸ’«πŸŒžπŸ’«
*RUDANI*
πŸ’«πŸŒžπŸ’«πŸŒžπŸ’« 🌞
Story
&
written by
Lashminzy

πŸ’₯GΓ”LDΓˆΓ‘"S WRÎTÈRS_
_Γ€SSΓ”Γ‡ΓŒΓTΓŽΓ’Γ‘_πŸ’₯

Komai yayi farko zaiyi karshe Allah nagode maka daka nuna mun na kawo karshen littafina na RAYUWAR UMMIEY. Allah yasa kamar yadda naga farkon wannan littafin yasa naga karshen shi, Masoyana ina mika sakon godiyata zuwa gareku
πŸ™πŸ™πŸ™

BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Page 1_2

mummy! mummy!!!Tun shigowarta take faman kwala wa mummynta kira, mummy dake cikin dakinta duk hankalinta ya tashi da jin irin kiran da Amatu_rahman keyimata da sauri ta fito tayi hanyar sauka palour

Cin karo sukayi da ita cikin tsoro da firgici mummy tace Amatu meke faru dake?? Fadawa jikinta tayi tace wallahi mummy naga Abdul a waje yanxu yanxu nan kuma ina son iyi mashi magana sai bata karasa fadar abunda zata fada ba sakamakon tsawar da mummy daka mata aikuwa da hanzarinta ta daga kanta data dora saman kirjinta

Tsuki mummy tayi tace amma dai Amatu kinyi asara yanxu akan wannan abun neh zakiyi ta faman kwala mun kira haka?? Ai na dauka ko wani abunne ya sameki Ashe akan wannan neh toh wallahi kibi a hankali karki zauce, tana gama fadar haka ta kara gaba

Kuka Amatu tasa gami da haurawa sama, dakinta ta shiga ta fada saman gado tana zubar da hawaye ta rasa dalilin dayasa ta kasa cire Abdul a ranta. Tana cikin kukan neh wayanta ya hau ruri

Dubawa tayi taga aunty hajara ce ke kiranta, ba bata lokaci ta amsa kiran daga bisani kuma ta tashi ta fita kodata fito palour mummy ta tarar sai data sanar da ita kafin ta wuce

Tafiyar minti biyar tayi se gata a cikin wani Dan karamin flat mekyau, kai tsaye ta shiga cikin gidan, a palour ta tarar da aunty hajara tana cin abinci kallonta tayi tace Amatu lafiya naganki a haka?

Dan jimmm kadan tayi sannan tace aunty yauma na sake ganin Abdul a banki amma kafin inyi mashi magana harya wuce shine dana fadawa mummy ta fara yimun fada

Ohhhh Allah me iko gaskiya Amatu ya kamata ace kin rabu da Abdul hakanan kusan shekara biyu kenan babu labarinshi kuma ma idan yana sonki ai duk inda yaje ze iya nemanki amma kawai kinsawa ranki damuwa kila ma yayi aure ya manta dake

Saurin isowa wurin aunty hajara tayi ta rufe mata baki da hannuwanta tace Allah aunty Abdul beyi aure ba saboda yayi mun alkawarin baze taba auran wata ya' mace idan bani ba kum.........

Dakatar da ita aunty hajara tayi tace anya baki fara tabuwa ba kuwa ko an fadamaki kowani dan Adam neh keda tabbaci?? Nidai shawarata kawai ki manta dashi ko kya hutawa ranki

Badan ta gamsu da maganar tata ba tace toh, zama tayi suka faracin abincin tare, bayan sun gama neh Aunty hajara tace tazo ta tayata gyara dakin baki kanwarta ameera ceh zatazo

Ba karamin dadi Amatu taji ba tace aunty bari inyi sallah inzo

Daga nan ta shige toilet tayi alawla tayi sallah bayan ta fito neh ta tarar da aunty harta fara kakkabe dakin. Hira suka shigayi inda aunty ke bata labarin ameerah duk da cewar Amatu ta Santa amma bata taba ganinta ba sai a hoto shiyasa take zumudin ganinta

Suna cikin aikin neh sai ga mijin aunty hajara yazo, gaishe shi Amatu tayi taci gaba da aikinta aunty kuma jan mijinta tayi zuwa dakinshi.

Bayan ta dawo neh sukaci gaba da aikinsu basu suka gama ba sai kusan magariba, suna gamawa Amatu tayiwa aunty sallama ta wuce

Tafiya take a nutse cikin kwanciyar hankali nan kuwa ba'asan tunani neh fal cikin ranta ba

Tunanin maganar da aunty hajara ta fadamata takeyi na cewar datayi kila ma ya manta da ita tana cikin haka neh taji an damkota da karfi ansa cikin mota, zata kurma ihu kenan taji an....................

Yawan comments
yawan rubutu😎
[2/2, 4:29 PM] Lashminzy😎: πŸ’«πŸŒžπŸ’«πŸŒžπŸ’«πŸŒžπŸ’«
*RUDANI*
πŸ’«πŸŒžπŸ’«πŸŒžπŸ’«πŸŒž

Story & written by
Lashminzy

πŸ’₯GΓ•LDΓŠΓ‘"S WRÌTÊRS
Γ€SSΓ”Γ‡ΓŽΓƒTΓŒΓ’Γ‘πŸ’₯

Wannan shafin sadaukarwa neh ga my real Momcy da kakata fatima, ina yinku irin ehhh dinnan, Allah yabar zumunci

Page 3&4

Zata kurma ihu kenan taji an rufe mata baki da wani kyalle, haka tayi ta mutsu mutsun ta Har suka iso wani tangareren gida, ba shakkah duk inda ake neman gida mekyau da girma wannan yakai, a takaice dai gidan flat flat neh Guda uku duk iri daya kuma kowanne da girmansa

Fitowa sukayi daga cikin motar, daya daga cikin su neh ya jawo hannunta zuwa daya daga cikin flat din, itako dake tun cikin mota sun rufe mata baki da fuska sai ya zamana bata ganin komai sai duhu

Wani daki suka kaita suka aje ta sannan daya daga cikin su da gani shidin yana sama dasu, kallon su yayi batare da yayi magana ba yayi musu alama dasu kunceta kuma su fita

Yadda ya umarce su haka ko sukayi shi kuma fuskar shi rufe take da bakin mask, ya karaso gab da ita yace keee bani number mahaifinki!! da sauri ta dago kanta dan jin muryar da bazata taba iya mantawa dashi a rayuwarta ba

Shuru tayi masa tana kallonshi taji ko shine me muryar, shiko ya tsani kyaliya shiyasa a zafafe yace keee dan ubanki bada ke nake magana ba, cikin muryar kuka dan yanxu ta gama tabbatar da abunda take zargi tace Abdul kaineee murya na rawa ta karasa maganar

Shiko kallon mamaki yakeyi mata dan beko taba ganinta amma ya akayi tasan sunan shi?
Cire mask din dake fuskan shi yayi ya kare mata kallo dakyau yaga ehh din pah shi be taba ganinta ba

Ita kuma a razane ta mike tsaye tana nuna shi da dan yatsa tace Abdul daman kana duniyar nan?? Ina ka shiga neh tsawon shekara biyu?? Kuma meeeeee

Katse ta yayi ta hanyar daka mata tsawa yace what the hell are u?? Ke wacece da zaki dinga jero mun irin wa'annan tambayoyin??

Abdul nice pah amatu amatullahi masoyiyar ka, Abdul meyasa zakayi mun haka? Meyasa zaka tafi ka barni?? meyasa yanxu kuma zaka satoni?? dan Allah ka amsa mun tambayoyi na

Gabadaya ta gama sashi a RUDANI duk ta rikita mishi tunani ga kuma kukan da takeyi wanda duk sadda hawaye ya gangaro mata sai yaji zafi a zuciyar shi kuma ya rasa dalilin dayasa hakan ke faruwa

Matsowa yayi daf da ita, ya kalli cikin idanunta yaga duk fuskarta ta kumbura tayi ja saboda kuka, yace keee ni fah ban sanki ba kuma ban taba ganinki ba hasalima bani nasa a satoki ba baba nah ya nuna mun hotonki yace da komai naki yace naje duk inda zan sameki na kawo mashi ke maybe dai nayi miki kama da wani neh amma bani bane

Cikin wata iriyar murya me ban tausayi ta kira sunan shi dan ita fah bata yadda bashi bane, tace plsss ka taimaka ka fitar dani daga cikin wannan rudanin

Murmushin da yafi kuka ciwo ya saki yace wai kee wace irin yarinya ceh a ina kika sanni tell me?? Ya fada gami da fincikota, kuka ta sa tace wallahi Abdul Kaine idan ba kai bane meyasa kake amsa sunan Abdul idan nakira ka iyeee tambayar ka nake??

Haushi neh ya kamashi ya saketa gami da watsa mata mari a fuska sai data ga taurari guda dari bakwai da hamsin,

saura kuma kuce karya neh 😏

Duk da cewar taji zafin marin da yayi mata amma daurewa tayi ta dago da fuskarta ta kalleshi ido cikin ido tace wallahi ka ban mamaki Ashe duk sonda kake yimun na banza neh?? Abdul me nayi maka da zaka hukunta ni ta hanyar kuntatawa zuciyata??

Toh bari kaji ko zaka shekara kana gana mun azaba bazan taba canza maka suna daga abdul din dana sani ba saboda Kaine ba wani ba

Wannan karon tausayinta yaji sai yaji dama be mareta, juyawa yayi ze fita sai kuma ya dawo, gabanta ya iso zeyi magana sai aka fara knocking a bakin kofar

Kyallen da aka rufe mata fuska dashi ya dauko ya rufa mata, tana kokarin hana shi yace shhhhhh duk abunda zakiji karki kuskura kice wani abu, idan ba haka ba u are on ur own

Mikewa yayi yaje bude kofar, wani katon dattijo ne Wanda a kalla zai kai shekaru hamsin a duniya, murmushi ya saki gami da jinjina wa abdul yace aikin ka yayi kyau son yanzu abu na gama shine kayi amfani da layin dana baka ka amshi number mahafinta ka kirashi ka fada mashi duk yadda mukayi dakai kaji ko

Amsawa Abdul yayi da toh kafin dattijon ya fita yana mai farincikin nasarar daya samu, shiko zuwa yayi ya bude mata fuska yace karki damu da abunda kikaji ya fada nidai abunda nakeso dake shine Ki dan bani takaitaccen labarin Abdul din da kika sani

Kallon rainin wayo tayi mishi tace haba Abdul me kakeson na fadamaka cikin rayuwar da mukayi wanda kai baka sani ba?

iska ya fuzar cikin nuna damuwa da tausayinta yace wallahi ban sanki ba amma sunana Abdul

Jin yayi rantsuwa yasa ta dan Ji ta yadda dashi sai tayi tunanin toh kodai su yan biyu neh? Batare da tasan maganar da tayi ta fito fili ba sai jin tayi yace a'a ni kadai mahaifiyata ta haifa

Shuru tayi tana kare mishi kallo lallai tabbas Abdul neh amma shi gashi ya musa yace bashi bane toh kodai mafarki nakeyi neh

Kawar da tunanin tayi ta kalleshi tace tunda kace ba kai bane zan baka labarin Abdul dina amma kasani Allah yana kallon ka

Girgiza kai yayi alamar ya yarda, nan ta fara bashi dan takaitaccen soyayyar da sukayi tsakaninta da Abdul kamar haka...............



Ku biyoni dan jin yadda zata kasance
[2/3, 9:29 AM] Lashminzy😎: πŸ’«πŸŒžπŸ’«πŸŒžπŸ’«πŸŒžπŸ’«
*RUDANI*
πŸ’«πŸŒžπŸ’«πŸŒžπŸ’«πŸŒž

Story & written by
Lashminzy

πŸ’₯GΓ•LDΓŠΓ‘"S WRÌTÊRS
Γ€SSΓ”Γ‡ΓŽΓƒTΓŒΓ’Γ‘πŸ’₯

Masu bibiyar wannan littafin ina godiya kuma nima ina yinku kamar yadda kukeyi nah

Wannan shafin SADAUKARWA neh ga duk mabiyan RUDANI

Page 5-6

ASALIN SU
Amatu, cikakken sunanta Amatullahi kuma ya' ce kwalli daya tak ga Alhaji Muhammad lemi da mahaifiyarta hajiya rukayya wadda take kira da mummy

Alhaji Muhammad lemi shahararren dan kasuwa neh kuma su yan jahar kano neh, kasuwanci ya dawo dashi abuja,

Amatu yarinya ceh kalar chakulati doguwa me kirar koka kola, shekarunta sha takwas a duniya, amatu ya'ce me hankali, da tarbiya da tunani ga kuma girmama na gaba da ita

Iyayenta na matukar kaunarta kuma suna ji da ita sosai kasancewar ta ita kadai Allah ya basu, hatta da mota an koya mata amma bata fara tuki ba sai data karasa secondary schl dinta

sun bata tarbiya da kulawa, tun tasowarta take cikin gata, komai na rayuwa amatu ta samu daga wurin iyayenta shiyasa a kullum idan tayi sallah take rokon Allah daya saka musu da gidan aljannah

Amatu ta kammala secondary schl dinta a wannan shekaran amma taso taci gaba da karatu sai kuma Allah yasa bataci jamb ba shiyasa take zaune a gida

amma duk da hakanan tana zuwa saloon dinda mahaifinta ya bude mata wanda tun tana ss1 ya bude mata amma saboda makarantar da take zuwa yasa bata da lokacin zama shagon sai dai inta samu hutu akwai wurin da take zuwa ana koya mata kwalliya da gyaran kai da dai sauran su

Tun tasowarta take da son kwalliya ko shopping sukaje kayan saloon na roba take siyowa dasu baby tayi ta musu kwalliya a gida tun abun yana kamar wasa harta girma abun na ranta dake kuma iyayenta masu hali neh kuma duk abunda take so indai bai kaucewa addini ba sunayi mata shiyasa suka bude mata shagon saloon,

Yanxu da take da lokaci kullum tana hanyar saloon idan kuma bataje ba toh tana gidan aunty hajara

WACECE AUNTY HAJARA
Aunty hajara makwabciyar su ceh, tun zuwanta anguwar suka hadu da ita Wanda a halin yanxu kowa na gidansu ya santa kuma sun matukar shaku da ita tamkar yan uwan juna

CIGABAN LABARI
Abdul dina na hadu dashi neh a shagon koyon kwalliya shima a lokacin ya kawo kanwar shi neh, bayan na fita neh sai na tuna da ban dauko wayana ba, toh na juya kenan sai na ganshi a gabana, wayata ya mikon nikuma na ansa ina mishi godiya

Harna juya zan tafi sai kuma ya kirani na dawo nace gani, kallona yayi yace miye suna na sai na fada mishi, dan murmushi yayi yace toh tunda na fada mishi sunana na fanshi kaina daman ladan kawo mun waya zan bashi amma tunda na fada mishi sunana kuma ya wuce

dariya nayi dan ya matukar shammata ta nace mishi toh nagode kaifa miye sunanka? Bata tare da wani daukan lokaci ba ya fada mun sunan shi, nan muka dan fara hira har zuwa lokacin da aka zo daukata, exchanging number mukayi dashi kafin na wuce ina mai jindadi a raina dan hankalina ya kwanta dashi

Tun daga wannan rana Abdul yake kirana muna gaisawa kuma yana fadamin irin sonda yake yimun duk da cewar a lokacin ina da Karancin shekaru a haka nake zuba masa shirme na kuma shi din haka yake bina dan yasan akwai kuruciya a kaina

Amma duk da kuruciyar dake kaina nasan yana matukar sona kamar yadda nima nake sonshi

A haka muka dade dashi muna zuba soyayya duk wani kulawa da masoyi ze baiwa masoyiyar shi ina samun irinshi a wurin Abdul, hatta mummy na da aunty hajara sun San da zaman shi,

Amma wata rana kwatsam sai aka wayi gari babu shi babu labarin shi, nata kiran number shi bata shiga kullum sai na fita bakin titi ko Allah zai sa in ganshi amma shuru gashi ni bansan kowa nashi ba balle naje nayi cigiyar shi

Nayi kuka harda zazzabi akan rashin shi saboda ba karamar shakuwa mukayi ba, tun ina sa ran zan ganshi har aka kai wata daya, wata biyu, shekara daya yanzu kuma shekara biyu babu shi babu labarin sa

Amma wani abu dayake bani mamaki kuma yake sani cikin RUDANI shine yan kwana biyun nan ina ganin shi amma duk yadda naso na tare shi muyi magana sai abun ya faskara, tun ina fadawa mummy na tana kwantar mun da hankali harta kai ga yanxu ma fada takeyi mun idan nace na ganshi

Gashi ni kuma na kasa cire Abdul a cikin raina saboda ina yi mishi sonda ni kaina bansan iyakacin shi ba, kullum cikin addu'a nake Allah ya bayyanar mun dashi dan har yanzu ban fidda ran sake ganin shi ba, ta karasa maganar tana zubar da hawaye

Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya kalleta cikin tausayawa yace kiyi hakuri amma Allah yana gani bani bane Abdul din da kike magana a kanshi ba amma kuma nine nayi ta bibiyar ki cikin kwana kinnan saboda inyi kidnapping dinki

Kuma nima zanso inga wannan takwaran nawa wanda muke matukar kama dashi haka,

Share hawayenta tayi tace toh ku meyasa kuka sato ni??? Dan jimmm kadan yayi sannan yace bazan boye miki komai saboda ko ban fada miki ba idan kika fita daga nan zakiji dalilin satoki da mukayi

Abbana neh yasa a satoki saboda yana bin mahaifinki kudi masu yawa Wanda a kalla zasu kai million goma , abbana yayi iya kokarin shi kan mahafinki ya bashi amma yaki shiyasa ya yanke shawarar sato ki dan ya karbi kudin shi

Amma kisani bawai na fada miki wannan maganar bane dan ki tayar da hankalinki a'a sam kawai dai saboda na fahimci ke mutuniyar kirki ceh kuma nasan hakan da abbana yayi ba abu bane mekyau

Nikuma bani da halin da zan hanashi, amma nayi alkawarin ko an kawo kudinnan sai na mayar dasu kuma nasan yadda zanyi mahaifinki ya biya abbana kudin shi batare wata hargitsi ba

Kuma kiyi hakuri da abunda abbana yasa akayi miki kinji? ko kala bata ceh ba sai tsura mashi ido datayi shiko sai faman surutu yakeyi

Jin bata ansa shi ba sai yace ta kawo number mahaifinta yanzu ze kirashi, bata musa ba ta bashi, shi kuma mikewa tsaye yayi ya nuna mata toilet da hannun shi yace taje tayi sallah shima masallaci zashi kuma anjima ze dawo

Dakyar ta samu ta mike tsaye Dan kakafuwanta sun mata nauyi sosai, shiga tayi ta dauro alawla, kodata fito dadduma taga an shimfida mata, hijabin dake jikinta ta gyara wa zama sannan ta fara sallah

Shi kuma bayan ya fita masallaci ya nupa dan gabatar da sallar magriba data wuce shi, nan ya zauna har akayi isha'i sannan yaje ya siyo mata abinci, bayan ya dawo neh ya shiga part dinshi ya zauna sannan ya kira number mahaifinta

Ko daya kira mummy da daddy suna nan zazzaune fuska babu annuri, harda aunty hajara na gidan dan hankalinta ba karamin tashi yayi ba, dan a lokacin da mummy ke fada mata Amatu bata dawo ba sai dataji tsoro kuma babbar tashin hankalinta shine an kira number ta ashe ta manta wayanta nan gidan aunty hajara

Amsa wayar daddy yayi yana mai sauraron abunda aka ce mashi daga bisani kuma ya katse wayar yana.........................




Muje zuwaπŸ‘‰πŸΏ
[2/3, 1:44 PM] Lashminzy😎: πŸ’«πŸŒžπŸ’«πŸŒžπŸ’«πŸŒžπŸ’«
*RUDANI*
πŸ’«πŸŒžπŸ’«πŸŒžπŸ’«πŸŒž

Story & written by
Lashminzy

πŸ’₯GΓ•LDΓŠΓ‘"S WRÌTÊRS
Γ€SSΓ”Γ‡ΓŽΓƒTΓŒΓ’Γ‘πŸ’₯

Page 7-8

Amsa wayar daddy yayi yana mai sauraron abunda aka ce mashi, daga bisani kuma ya katse wayar yana salati. a firgice mummy tayo kanshi tana sharar hawaye tace alhaji waye ya kira kuma meya faru??

Kallonta yayi da idanunshi da suka canza launi zuwa ja yace anyi kidnapping din amatu kuma wai se an bada naira million goma za'a saketa, salati mummy ta farayi tana kuka haka ma aunty hajara itama kukan take sosai.

Wata nannauyar ajiyar zuciya daddy ya saki yace kuyi hakuri insha Allah zan kai kudin nan dan bazan bari su halaka mun da yarinya ba kuma wallahi duk Wanda ya aikata haka a gareni toh ya guji ranar haduwata dashi.

Yana gama fadar haka a fusace ya haura sama. mummy kuma kallon aunty hajara tayi tace hajara kije gida kinga yanxu dare yayi zuwa da safe sai ki dawo kinji.

Girgiza kai hajara tayi ta fice daga gidan mummy kuma dakin daddy ta wuce.

*********
Bayan ya gama waya da daddy dakin da aka akai Amatu ya nupa. da shigar sa ya mika mata abinci gami da zama cikin daya daga cikin kujerun robar dake wurin. Kallonta yayi yaga yadda ta kawayar da abinci gabanta alamar bazata iya ci ba kenan.

Wayar shi ya zaro daga aljihu ya kira number daddy ya mika mata. Bakinta har rawa yake tayi magana dan ta matsu ba'a dauka ba. Haka ta katse

1 / 27