Author : LASHMINZY Category : Romantic Hausa Novels
dakatar dashi tace sai yaci abinci, haka ko ta zauna gaban shi saida yaci ya koshi kafin ya tashi ya fita, "ammie kuma na binshi da adawo lafiya.
Motar shi ya shige, mai gadi yayi saurin bude gate ya fice, "a hankali yake tuki dan shi baya tsala gudu kamar Abdulrahman".
Tuk'i yake hankali kwance duk da cewar yana tunanin yadda zasu kwashe dasu daddy hakan bai hanashi tafiya a hankali ba. Harya iso asibitin a slow yake tafiya.
Direct wurin da yake paka mota yaje ya paka motar sannan ya fito yasa kai cikin asibitin, kodaya shiga dak'in da aka kwantar da ameera baiga kowa ba, ita kuma idanunta rufe suke kamar mai yin bacci.
"Zuwa yayi can karshen gadon ya jawo plastic chair ya zauna yana facing dinta, "cikin sanyin murya ya kira sunanta, "zuciyar tace da buga a lokacin dataji ya kira sunanta dan yayi amfani da wata iriyar murya ce ya kira sunanta.
Kara runtse idonta dake rufe tayi batare data kalle shi ba.
"Shi kuma jin tayi shuru sai ya kara kiran sunan ta, "a hankali ta amsa shi gami da bude idonta ta watsa su akan nashi. Abdul yace ameerah damuwa bashi da amfani, ita karan kanta kalmar damuwa ba'a sonta saboda ba karamin illatar da dan adam take ba.
Ameerah duk wani abu dazai zama damuwa ga zuciyar dan adam guje mashi akeyi saboda illolin shi, naga ke ba wata ma'abociya "kasuwanci ko hulda da jama'a bace" amma ace wai damuwa tayi maki yawa?? Gaskiya dai akwai wani abu.
"Shuru yayi na yan dakika sai can "yace ameerah ki daure ki fada mun damuwarki saboda ayi gaggawar warware maki ita, "kinga auntyn ki da Amatullahi suna cikin damuwa sosai, "yanzu haka su suka sani in tambaye ki abunda ke damunki ko Allah zai sa ki fada mun".
"Dan Allah ki fada mun nayi maki alkawarin bazan fadawa kowa ba kinji? Kamar bazata yi magana ba sai kawai ta daure tace "ni babu abunda ke damuna" Abdul yace akwai", shuru tayi bata sake cewa ko ufan ba.
"Haka yayi ta shan cikinta wai ko zata fada mashi amma fur taki, "daga karshe wata dubara ta fad'o mashi, "ya kalleta sannan ya zaro wata allura daga cikin aljihun rigan shi na likita ya hada ta. "Yace ameerah tunda bazaki fada mun ba yanzu zanyi maki allura ki fita daga hayyacinki, "nasan idan nayi hakan duk abunda na tambaye ki zaki fada mun.
'''A tsorace ta d'ago daga kwance da take ta zauna, gami da had'e hannuwanta duka biyu tana rokon shi tace dan Allah abdul kayi hakuri karka yi mun. Abdul "yace indai baki fada mun ba tamkar nayi maki ne.
Ita kuma cike da tsoro da fargaba, "danta yadda cewa idan yayi mata allurar komai zata iya fad'a "sai kawai ta fara hawaye tana cewa karka yimun na rokeka zan fada maka.
Murmushin zuci Abdul yayi yace ina jinki, "cikin muryar kuka tace ko ban fada maka ba kasan yadda "SO" yake, "Abdul miye amfani kaso mutumin da beko San kanayi ba??
"Abdul yace ban fahimta me kikeson kice?? Hawayen da suka zubo mata tayi saurin sharewa kafin tace, "ni naja wa kaina wannan damuwar saboda ina son abunda nasan har abada bazan taba samun shi ba".
"Abdul yace ameera miye ne haka da kike cewa bazaki samu ba?? "Ameera tace "SO" Abdul ina son wani ne can daban wanda baiko San ina yi ba, yanxu haka shi kuma yancan zai auri kawata nan da dan wasu lukuta. "Abdul nikuma bazan iya tukarar shi da cewa ina sonshi ba.
"Cike da jin tausayinta Abdul yace gaskiya naji dadi dabaki furta wannan Kalmar ba" saboda a matsayin ki na ya' mace mai hankali da tunani bai dace ace duk tsananin sonda kike wa d'a namiji kin furta Kalmar so a gareshi ba. Domin kuwa ba karamin rage kimar ya' mace yake a wurin namiji ba.
"Kinyi kokari.
Ameerah shawara daya ce zan baki shine kiyi hakuri ki cire shi a cikin ranki, "duk da nasan ba abu bane me sauki amma ki roki Allah ya kawo maki wanda ya fishi kuma dan Allah "kibar raina damuwa koda kuwa na dan cikin cokali ne"
Kallonshi tayi da rinannun idanunta tace nagode Abdul Allah ya saka da alkhairi, hannu ya daga mata yace nop karki damu ai tamkar kanwata na dauke ki.
"Murmushi tayi ta share hawayenta", har suka dan fara hira sai ga mummy ta shigo, "cikin dan jin kunya dan baiso mummy ta tarar dasu ba, 'ya fara sosa keya, sannan ya samu ya fice daga dakin".
••••••
"Tun isar sa cikin makaranta yake zaune cikin mota, yana kiran number amatu bata dauka ba, "abincin da ammie ta bashi ya fara ci, "sai daya cinye tas yace alhamdulillah kafin ya sake trying number amatu duk da be tsammaci zata dauka ba sai kawai bugu daya yaji dauka".
"Farinciki ne ya ziyarce shi, sai cikin zazzakar muryar shi yayi mata sallama. "Ita kuma tun daga jin sallamar shi ta gane mai magana"
Tsaki tayi ta katse wayar.
"Shi kuma be daddara ba sai ya kara kira sam taki dauka, "haka yayi ta kira yana tura mata sakonni da soyayya dana ban hakuri amma ba reply.
"Gajiya yayi ya tada motar shi ya wuce class, lokacin har karfe tara yayi kuma tun karfe takwas ya kamata ya shiga. Tunda ya shiga class din babu annuri a fuskar shi, kamar yadda ya saba, sai dai na yau yafi ko wane lokaci dan hatta da sallamar da yakeyi idan zai shiga yau beyi ba".
"Haka dai wani sukuku jiki ba kwari ya dan taba wani abu dasu ya fita tun ma kafin lokacin fitar shi bai yi ba".
"Yana fita gida direct ya koma, dakinshi ya shiga kwanta yana jin zuciyar shi ba dadi".
"Bayan la'asar" Abdulraheem ne tare dasu mummy dasu ameera a harabar asibiti yana musu sallama dan yanzu aka sallame su. "Amatullahi ta dan yi muryar ta kasa kasa ta kira abdul, "shi kuma dama idonshi na kanta shiyasa datayi mishi alamar yazo ya gane.
"Matsowa yayi kusa da ita, cikin maganar kurame yace mene? cikin yin kasa kasa da murya tace Abdulrahman ya kirani dazu! waro ido yayi yana tunanin ina ya samu number ta sai Amatu ta katse ta hanyar cewa karka damu ko zai shekara yana kira kalmar nan da yake so bazai samu ba".
"Murmushin jindadi yayi ya daga mata babbar yatsa 👍🏻alamar tayi daidai.
Itama Murmushin tayi ta shige mota, tana daga mashi hannu.
"Mummy ma zagayawa tayi ta shiga gidan baya ta zauna ita da ameera da aunty hajara. Musa direba yabawa mota wuta".
"Bayan sun wuce ne shima ya shige tashi motar ya wuce gida. Part dinshi ya nupa direct inda yayi wanka yayi shigar kananan kaya, kuma ba karamin kyau sukayi masa ba.
"Fitowa yayi da dan murmushi a fuskar sa dan yana tunanin yau za'a kai karshen komai kuma insha shi keda nasara tunda ko tambayar amatu akayi wa takeso shi zata zab'a.
"Da wannan kwarin gwiwar ya nupi inda ya paka motar shi ya shige sai gidan su Abdulrahman.
"Lokacin daya isa gidan yana paka motar shi sai ga daddy
[2/21, 11:44 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫
*RUDANI*
💫🌞💫🌞💫🌞
Story & written by
Lashminzy
💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS
ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥
'''vote me on wattpad @lashminzy'''
*سْــــــــــــــــمِ اللَّهِ الرَّحْمَ* الرَّحِيْمِ
_*May Allah (SWT) Bless you and your family with a restful mind, useful soul, peaceful home, commendable effort, acceptable worship, and a successful end. May He beautify your tongue with truth, heart with sincerity and count you among the dwellers of Jannatul Firdaus, Insha Allah.
ʝυммα'т мυвαяαк тσ αℓℓ мυѕℓιмѕ.
Page 57-58
''''A daki kuma Abdulrahman ne zaune a bakin gadon shi yana dialing number Amatullahi, "ita kuma amatu lokacin tana palour tana jin wayarta na ringing amma sanin ko waye ke kira yasa ta buga tsuki taci gaba da kallon ta".
"Abdulrahman ko sai faman kiran ta yake, data gaji da jin karar wayar ne ta d'auka zata kashe ta gabadaya sai kawai taji tana son ta d'auka. Haka dai ta d'auka.
"shi kuma cikin so da kaunar ta yace baby da fatan kina lafiya? Ita kuma cikin masifa tace lfya kalau nake "ka fad'i abunda zaka fad'a saboda ina da aikin yi"
Murmushin jindadi yayi yace baby kiyi hakuri da abunda ya faru ki amince danii......cikin tsawa ta katse shi tace wallahi Abdul ban tab'a ganin mutum mara zuciya irinka ba, kai ko acikin dabbobi babu kamar ka, kuma ka rubuta ka aje, ni "AMATULLAHI MUHAMMAD LEMI", bana sonka, bana kaunar ka, "kai kasani koda duka mazan duniya zasu kare bazan taba aurenka ba because "I hate you!! "I hate you!!! Ta karasa maganar a tsawa ce. Sannan ta katse wayar.
"Shi kuma a firgice ya mike tsaye da jin irin munanan kalaman da take fad'a dan duk wani zagi da barazanar da take mashi bata tab'a furta irin wa'yannan kalmomin ba shiyasa take yaji zuciyar shi ta dau zafi, duk jijiyoyin kanshi sun tashi sunyi rud'u-rud'u. Idonshi kuwa sun canza launi zuwa ja kamar garwashi. "sai ya fara tari gami da dafe zuciyar shi yana k'ok'arin ya kai zaune amma ya kasa".
"Abdulraheem daya shigo kiran shi, jin kamar nishi da tari yasa yayi saurin k'arasawa wurin da Abdulrahman ke shirin zubewa k'asa.
"Taro shi yayi ya fad'o saman jikin shi. "Cikin tashin hankali Abdulraheem yace d'an uwa meya faru dakai?? meke damunka?? Waya yayi maka haka? Duk cikin rud'ewa yake mashi wannan tambayoyin.
" Abdulrahman dake nishi sama-sama hawaye na zuba a idanunshi yace d'an uwa "mutuwa zanyi, "mutuwa zanyi". Abdulraheem yayi saurin rufe mashi baki da hannun shi, shima duk yanayin shi ya sauya yace insha Allah babu abunda zai sameka.
"D'aura kanshi yayi saman pillow, yaje ya bud'e d'an k'aramin fridge d'in dake d'akin ya d'auko ruwan faro yazo wurin shi ya d'aga shi sannan ya bashi yasha.
''A hankali yake saukar da ajiyar heart bayan yasha ruwan, sai kuma wasu zafafan hawaye suka fara zubo mashi.
"Cikin zubar da hawaye yace d'an uwa kaje nabar maka Amatullahi, "kaje a d'aura muku aure. Abdulraheem dake kallonshi kamar wani tababbe yace Abdul bakai ya kamata kabar mun amatu ba ni nafi cancanta dana bar maka ita, saboda bana son in rasa ka akan abunda baifi karfina ba "dan haka ni nabar maka ita badan komai ba sai dan Allah.
"Abdulrahman yace a'a amatu bata sona, wallahi amatu bazata aureni ba....Abdulraheem ya katse shi yace ba haka bane Amatullahi na sonka, kawai tafiyar dakayi ne harna tsawon shekara biyu yasa ta fita batunka amma ina da tabbacin har yanzu tana sonka". Saboda a lokacin dana fara soyayya da ita na fahimci tana tsananin sonka sedai nikuma nayi k'okarin cire soyayyar ka a ranta na d'aura nawa.
"Amma duk da haka na bar maka ita domin kuwa da tsohon zuma ake magani.
"fashewa da kuka Abdulrahman yayi ya kara rungumo Abdulraheem jikin shi, cikin rawar murya yace d'an uwa bani da bakin gode maka, Allah ya saka maka da gidan aljannah kuma Allah ya....
"Abdulraheem da yake jin zuciyar shi kamar zata fashe, dan k'aramin jarumta yayi ba ya katse shi yace d'an uwa karka damu ko rayuwata zan iya sadaukarwa saboda farincikin ka".
" kukan farinciki Abdulrahman yakeyi, yana kallon shi yana jin wani son d'an uwanshi na karuwa a zuciyar shi, daman can yana sonshi kawai wannan abun ne daya faru yasa shed'an yayi tasiri a zukatansu har yasa sukayi ta samun sab'ani.
"D'aga shi Abdulraheem yayi yace yaje toilet ya wanko fuskar shi saboda su daddy na neman su. Ba musu ya shiga toilet ya wanko fuskar shi, sedai daga gani zaka gane yayi kuka.
Abdulraheem ne ya ciro handkerchief daga cikin aljihun shi, ya goge wa Abdulrahman danshin dake kan fuskar shi sannan ta d'anyi dama-dama dan inba k'are mashi kallo kayi ba bazaka gane yayi kuka ba.
"Murmushi suka sakarwa junan su a tare, kafin Abdulraheem yaja hannun shi suka nufi part din daddy".
"Da shigar su daddy ya fara musu fad'a yana cewa waton ku kun maida mu dattijan banza ko?? Yau kwana nawa da maganar da mukayi daku?? Kowannensu kanshi na duke basu ce kala ba.
"Daddy yace tau bari kuji ko kuna so ko baku so na yanke hukunci, kuma "ba shawarar ku nake nema ba umarni na baku", dan haka kar wanda ya musa mun".
"Abba kuma cikin sigar lallashin daddy yace alhaji kayi hakuri mana mu bisu a hankali! Daddy yace su kananan yara ne da zamu bisu a hankali??
Abba yace gaskiya ba kananan yara bane amma muji ta bakin su tukunna kafin ka zartar da hukuncin ka. Daddy baice komai ba.
"Abdulraheem cikin sanyin murya yace Abba, daddy mun sulhunta kanmu. "Daddy yayi saurin kallon shi suka had'a ido, Abdul yaci gaba da cewa "a matsayina na d'an karami kuma d'an uwa ga Abdulrahman na hakura da Amatullahi har abada, "kuma nayi hakan badan komai bane sai dan gujewa halin da d'an uwana zai shiga. Kuma duk wani abu danayi na bikin Amatullahi nabar mashi kyauta
"Abba yayi saurin kallon shi suna had'a ido Abdulraheem yayi saurin saukar da idonshi kasa.
"Daddy daya taso da fad'a jin sun sulhunta Kansu sai ya sauko daga hawan da yayi yace Alhamdulillah Allah yayi muku Albarka, Allah yasa ku gama da duniya lafiya, kai kuma Allah ya had'a ka data mata ta gari.
"Dukansu suka amsa da ameen, sai Abdulraheem yace amm wani hanzari ba gudu ba, dan Allah ina neman wata alfarma a wurinku.
"Abba yace fad'i koma menene indai bai kauce wa addini ba zamu muyi maka Insha Allah. "Abdulraheem yace abba dan Allah banason a fadawa Amatullahi cewa bani zan aureta ba saboda wasu yan' dalilai nawa.
"Daddy yace maganar banza maganar wofi, ya kake tunanin haka zata faru?? Abba ya katse shi yace alhaji hakan zata yiwu kuwa amma sai an fad'awa shi baban yarinya, idan ya amince da hakan tau komai zai tafi yadda akeso.
" tunda kaga kamar su d'aya koni sai na kare musu kallo nake iya tantance su. Daddy yace tau shikenan tunda kace haka. "Allah yasa shi yafi zama alkhairi, suka amsa da ameen kafin daddy yayi musu izinin tafiya.
" nan suka tashi suka fita, hannun su sarke dana juna, Abdulrahman yace d'an uwa bani da kamar ka, ka gama mun komai, bansan da wani baki zanyi amfani dashi wurin gode maka ba.
"Abdulraheem yace karka damu u deserve it that's why, dan haka kaje ka huta ni zan wuce gida, insha Allah zuwa gobe zamuyi magana, "murmushi yayi ya mik'a mashi hannu sukayi musabaha sannan ya shige motar shi ya wuce.
"Bayan ya iso gida, ko cikin gida bai shiga ba ya paka motar shi ya wuce masallaci dan lokacin sallar magariba tayi, bayan an idar da sallar magariba, nan ya zauna har akayi isha'i kafin ya dawo gida.
"Part din ammie ya nufa, lokacin ammie na palour ita da hanan suna kallo, jin bugun kofa yasa hanan tayi saurin zuwa ta bud'e, tana ganin shi ta rungume shi had'e da tambayar shi ina yaje dan tun dawowar ta makaranta bata ganshi ba.
"Murmushi ya kakaro yace sis naje wani wuri ne shiyasa baki ganni ba. Ammie dake zaune tana kallon su tun kallo daya datayi mashi ta gane yana cikin damuwa.
"Shiyasa ta dakatar da hanan dake ta faman zuba surutu dan taga baya cikin yanayin jindadi, "ita kuma hanan dake akwai yarinta saman kanta shiyasa bata wani lura da yanayin da yake ciki ba.
"Tasowa ammie tayi ta jawo shi suka zauna tana kallon shi tace son meya faru?? Fad'awa yayi jikinta hawaye na zuba a fuskar shi yace ammie na rasata, na rasa Amatullahi.
"Cikin rud'ewa tace Abdul fada mun abunda ya faru. Nan ya fara bata labarin tun daga halin da yaga Abdulrahman har zuwa zaman da sukayi dasu daddy.
"Ammie ji tayi kamar tayi kuka dan ba karamin tausayin shi taji ba, dan ita kanta tasan yana matukar son Amatullahi, kuma da'ace ba Abdulrahman bane wani daban ne bazata taba bari Abdulraheem ya sadaukar da ita ga wani ba.
"Cikin lallashin shi tace Abdul kayi hakuri ka mika lamuran ka ga Allah kuma ka dauki kaddara, saboda soyayyar dakayi da Amatu kaddara ce kuma ba matar ka bace dan kuwa wani baya auren matar wani.
"Plsss karka sawa ranka damuwa wani abu ya sameka Kuma wannan sadaukarwan dakayi Allah yasa alkhairi ne kuma Allah ya saka maka da mafificin haka Allah ya baka wadda tafi Amatullahi.
"Cikin zuciyar shi ko cewa yake ammie na bazan taba samun kamar Amatullahi ba domin kuwa komai nata na daban ne. A fili kuwa cewa yayi ameen ammie ki tayani da addu'a kinji?? Ammie ta amsa da toh.
"Hanan dake zaune kusa da ammie wani irin tausayin yayan nata ne ya mamaye zuciyarta, duk da cewar batasan ko menene so ba amma tasan zafin idan mutum ya rasa abun shi.
" kusa dashi tazo ta rungume shi ta baya, dan a duke yake ya d'aura kanshi saman cinyar ammie tace yaya kayi hakuri Allah zai baka wadda tafi aunty amatu.
"Murmushi yayi wanda a iya leb'on sa kawai ya tsaya yace ameen sister nagode. Daga nan ya mike zai wuce part dinshi, ammie ta taro shi tace ya tsaya yaci abinci, amma fur yaki wai ya koshi.
"Saboda karta takura mashi kawai ta rabu dashi ya wuce. Yana shiga dakinshi ya fad'a saman gado yana rusa kuka. "Yana cikin kukan ne yaji wayar shi na ringing.
Plsss share
[2/24, 7:53 AM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫
*RUDANI*
💫🌞💫🌞💫🌞
Story & written by
Lashminzy
💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS
ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥
'''vote me on wattpad @lashminzy'''
Wannan shafin kyauta ne ga duk mabiyin baba buhari, insha Allah sai kayi. Su oyy ban fada ba aje gida zuwa hutawa.
Page 59-60
"Dubawa yayi yaga Amatullahi ce ke kiranshi, "dumm yaji gaban shi ya fad'i, "sai kawai ya kifar da wayan, yayi mata wani irin damk'a kafin ya saketa had'e da zubar da wasu hawaye masu zafin gaske.
"Cigaba da kiran shi Amatullahi tayi, shi kuma yana ji tana ringing amma ya kasa d'auka. "Tau idan ma ya d'auka yace me, tunda yanzu ba budurwar shi bace.
"Gyara kwanciyar shi yayi ya kashe wayar gabad'aya dan bata bar kiran shi d'in ba. Haka yaci gaba da kukan shi yana jin wani irin zafi a zuciyar shi, "har baccin wahala ya d'auke shi.
Washe gari
"Amatullahi ce a