Author : LASHMINZY Category : Romantic Hausa Novels
ba tare da an dauka ba. Ansar wayan Abdul zeyi sai kuma kira ya biyo baya.
Da sauri ta amsa a rikice tana kiran daddynta tana cewa ina mummy. Sai da suka gaisa tukunnan yana kokarin mikawa mummynta Abdul ya anshe wayar gami da kashe ta gabadaya.
Kuka ta saki tana rokonshi daya sake kira mata su amma fur yaki sai ma tashi da yayi yana kokarin fita dan kukan da takeyi ba karamin sa zuciyar shi zafi takeyi ba.
Tashi tayi ta biyo shi tana kara rokon shi sai ya juyo ya kalleta ya kalli kuma abincin daya kawo mata yace indai kinason nakira maki mummy toh sai kin cinye abincin nan duka.
Girgiza kai tayi alamar zataci sannan ta koma wurin abincin ta faraci. Duk cewar ba wani dadin shi takeji ba kawai dai tana ci neh dan ya kira mata mummynta. Haka yayi tsaye yana kallonta Har sai data gama ci sannan ta kalleshi tace ya kirasu.
Murmushi yayi a cikin zuciyar shi yace lallai amatu baki da wayo yanzu idan na sake kiran iyayenki ai zasu iya ganoni. Amma a zahiri wata number yayi dailing wadda yasan bata shiga yasa a hands free yace kindai ji a kashe take ko??
Kwalla ceh ta fara taruwa a idanunta tace Abdul yaushe zaka kaini gida?? Tabe baki yayi yace Gobe. Wani sanyi taji a ranta tace kona fita Abdul bazan barka ba zan kasance tare dakai Har zuwa lokacin da zaka bayyana mun dalilin guduna dakayi.
Niko nace Amatu har yanzu baki yadda ba Abdul dinki bane??π€
Kee me kika ceh?? Saurin girgiza kanta tayi tace bance komai ba kawai nayi missing din yan gidan mu neh. Murmushi yayi mata a karo na farko kenan daya taba sakar mata murmushi yace ni fah zakiyi missing dina??
Rufe fuskarta tayi da hannuwanta tace a'a nikam bazan yi missing dinka ba. Waro idanunshi yayi yace Ashe kenan bazaki bar gidan nan ba.
Bude fuskarta tayi ta dan marairaice fuska tace Allah wasa nakeyi maka zanyi missing dinka. Sosai?? Eh sosai mana ta bashi amsa a takaice.
Toh yanxu ki cire duk wata damuwa ki kwanta kiyi bacci me dadi kinji ko?? Amsawa tayi da toh sannan ta kwanta saman dan karamin gadon dake dakin.
Shima kashe mata wuta yayi sannan ya sawa dakin makulli ya wuce part dinshi. Yana shiga ruwa ya watsa ya shirya tsaf cikin kayan bacci sannan yabi lafiyar gado.
Kwance yake amma sai faman sake sake yake tayi. Yana tunanin yadda zai mayarwa daddy kudin shi ba tare da ansamu matsala ba. Wata zuciyar shi ko cewa take kawai basai ka anso kudin shi ba ka mayar da ita inda ka daukota sai ka fadawa daddynta dalilin satota da akayi inyaso duk abunda zai faru ya faru.
Tsuki ya ja da jin irin muguwar shawarar daya ba kanshi yana girgiza kanshi yace no no bazan yi haka ba idan nayi haka banyi wa abbana adalci ba kuma na raba zumuncin dake tsakanin su kuma bazan so hakan ta faru ta dalilina ba.
Mirginawa yayi ta gefen daman shi jin wata shawarar daya yanke. A take murmushi ya bayyana a fuskar shi yace yesss haka zanyi dan bazan bari wannan damar ta wuceni ba. Yana cikin wannan sake saken neh bacci yayi a won gaba dashi.
Bayan kwana biyu
Haka daddy yayi ta fafucikan neman kudi dakyar ya samu ya hada kudin. har yaso ya dawo da kudin dayayi order motoci dasu sai kuma ya fasa saboda kudin sun kai.
Mummy duk ta fita hayyacinta a cikin kwana biyun nan ko abinci bataci sai daddy ya tilasta mata. Haka ma bangaren aunty hajara duk ta shiga damuwa komai bata tabukawa hatta abinci sai ameera ke dafawa dake tun shekaran jiya ameera tazo kuma itama tayi kuka dataji labarin an sace Amatu.
Amatu ko tun randa Abdul yace gobe zata gida bata kara sashi a idonta ba. Shiyasa duk tabi ta daga hankalinta. Ko abinci aiko mata akeyi kuma ba'a Bari tako iso bakin kofa balle tasa ran zata fita. haka take zama ta narki kukanta ita kadai babu me lallashinta.
Zaune yake a gaban abban shi suna tattauna yadda zasuyi da kudin. Shi dai Abdul sauraron shi kawai yakeyi dan ya rigada ya gama shirin shi, duk yadda zeyi bazai taba bari kudin nan su shigo hannunshi ba sai dai in shine ya dawo masa da kudin sa da kansa yace gashi.
Bayan ya gama magana neh Abdul ya kalleshi yace Abba wani hanzari ba gudu ba. daman ina son idan an kawo kudin ban kar'a tabasu saboda naga muna da isassun kudi anan kuma akwai wasu motoci da zasu shigo Nigeria nan bada dadewa ba shine naga ya dace a bar kudin sai ayi order motocin dasu in an kawo.
Shafa kanshi Abba yayi yace gaskiya ka kawo shawara mekyau daman nima ba tabasu zanyi ba saboda akwai uzurin da zanyi dasu idan ya tashi kaga yanxu idan kun anso kudin sai ka rikesu a wajenka amma ka kula sosai fah.
Farinciki neh ya mamaye Abdul yana gaf da samun nasara yace toh abbana insha Allah zan kula. Daga haka suka rabu.
Yana fita dakinshi ya nupa ya kira daddy ya tabbatar mishi da su kawo kudin nan gobe idan ba haka ba kuma zasu kashe ta. Aikuwa sai da hanjin daddy suka kada yace ayi hakuri Dan Allah kada ku cutar mun da ya'ta wallahi mun samun kudin daman kiranku muke jira.
Nan Abdul ya fada mishi inda zasu kai kudin da kuma lokaci.
Washe gari
Ko cikakken bacci daddy be samu ba shida mummy dan sun matsu safiya bata waye sunkai kudin nan ba. Haka daddy yayi zaune daram yana jiran kiransu.
Da misalin sha daya na safe Abba ya aiko da wasu gardawan mutane dansu mayar da amatu su anso kudin. Abdul kuma tun wurin karfe goma ya shiga dakin da amatu take. tana ganinshi ta mike da sauri ta karaso kusa dashi tace ina ka shiga kwana biyu ka barni anan? Dan Allah ka mayar dani gida walla..................
Shhhhhh karbi wannan ki share hawayenki. Karba tayi tana share hawayenta dan gani tayi kamar babu annuri fuskar shi. Jawo kujera yayi ya dawo gabanta ya zauna yace zauna ki saurareni kiji abunda zan fada miki.
Ba musu ta zauna bakin gado tana sauraron shi dan dataji abunda zai fada.
Iyayenki sun taba ganin Abdul dinki?? Cikin mamakin jin irin tambayar dayayi mata tace a'a basu taba ganin shi ba amma sun San da zaman shi.
Owk naji dadin haka.
Toh ki bude kunnuwanki dakyau ki saurareni kiji abunda zan fada maki kuma idan..........................
Muje zuwa ππΏππΏππΏ
[2/4, 11:25 AM] Lashminzyπ: π«ππ«ππ«ππ«
*RUDANI*
π«ππ«ππ«π
Story & Written by
Lashminzy
π₯GΓLDΓΓ"S WRΓTΓRS
ΓSSΓΓΓΓTΓΓΓπ₯
Page 9-10
"Toh ki bude kunnuwanki dakyau ki saurareni kiji abunda zan fada miki kuma idan kika kuskura ki kayi kunnen uwar shegu da abunda zan fada miki sai jikin ki ya gaya maki"
"Abu na farko shine koda wasa kikayi subutar baki yan gidan ku ko kuma wata kawarki can tasan dalilin satoki fa to ki kuka da kanki"
"Abu na biyu shine karki yadda ki sake ki fadawa daddynki ga wanda ya satoki ko kuma dai wani abu game damu dan nasan zai tambayeki"
"Abu na uku shine duk abunda zakiji ko zaki gani daga gidanku karki yadda ki musa ko ki kawo korafi"
"kina jina ko? Cikin rawar murya kamar me shirin yin kuka tace eh.
"Abu na karshe yana cikin wannan takardar. Duk shawarar da kika yanke ki sanar dani. Ya karasa maganar gami da mika mata wata farar envelop.
''Karba tayi tana share hawayen da suka zuba mata. Cikin ranta ko haushi takeji da irin yadda ya tsareta kamar wani ubanta yana bata umarni.
''Shi kuma a bangaren shi ji yake kamar karta tafi dan yasan yanzu shi daya kara ganinta sai in gidansu yaje. Shuru sukayi na yan mintuna kafin ya dauko kyallen da aka rufe mata fuska ya karaso daf da ita cikin rada yace ba nayi hakan dan in bata maki rai bane kawai umarni ne daga abbana. ya fada yana mai rufe mata fuska da kyallen.
''Hannunta yaja zuwa farfajiyar gidan. Har sun kusa kai wurin shiga mota sai yajiyo muryar mahaifiyar shi dake daya bangaren saman bene tana magana da mai gadi.
''Dummm gaban shi ya fadi. Aikuwa da sauri ya jawo Amatu da karfi ta fado saman kirjin shi suka buya bayan flawoyin gidan.
''Haka suka tsaya manne da juna dan har suna jin hucin junan su. Sai daya tabbatar data koma cikin gida kafin suka fito ya jawo hannunta suka fita daga gidan. Ita kuwa sai binshi takeyi batare da tasan inda zasu ba kuma ta kasa tambayar shi.
''Bayan gidansu ya nupa da ita inda ya tarar da gardin mazan da Abba ya aiko dasu. Nan suka bude mota yasa ta aciki shima ya shiga da driver na tukawa. Dayan motan kuma sauran mazan ne suka shiga kuma Sune a gaba saboda tsoro.
*************
''Daddy ko cikin hanzari yake shiri dan sunce ya iso wurin kafin nan da minti talati. Bayan ya gama shiryawa ya dauki jakar kudin ya rataya a kafardar shi zai fita sai mummy tayi saurin shan gabanshi tace Alhaji ya zaka fita kai kadai ba yan tsaro?? Kallonta yayi yace haba Rukayya kina nan zaune fah suka ce idan na kuskura nazo da wani sai dai na samu gawar ya'ta.
''Shine kike son naje da wani? Rukayya nikam ban damu ba a halin yanxu saboda ya'ta tafi mun komai mahimmanci kedai kawai ki kwantar da hankalinki kiyi mana addu'a Allah ya tsare mu, sai na dawo.
''Tsaye tayi tana kallon mijinta dan harya bata tausayi. Cikin yan kwana biyun nan duk ya firgice. Hawayene ya gangaro mata a kumatu tayi saurin sharewa ta haura sama dan tayi alawla tayi nafila.
''Gudu yake tsalawa sosai sai daya kawo dai dai inda sukace ya paka motar sannan ya paka ya fito ya fara tafiya da kafa dan mota bata iya shiga wurin. Su kuma sun dade da isowa dan ta baya suka biyo shi kuma ta gaba sukayi mishi kwatance shiyasa yanxu duk taku daya yayi suna iya hangoshi.
''Abdul dake rike da waya a kunnen shi kuma yana hangoshi yace ya cigaba da tafiya sai ya kawo wurin wani jan kyalle da suka aza ya tsaya.
''Haka yaci gaba da tafiya sai daya kawo dai dai wurin kyallen ya ajiye jakar sannan ya koma wurin motar shi kamar yadda suka umarce shi.
''Bayan ya koma da kusan minti biyar sai Abdul yaja hannun Amatu zuwa wurin. Sannan ya dauki jakar ya mikawa wani gardi daya rakosu shi kuma ya kwance mata fuska yace tayi shuru kuma karta kara koda taku daya neh. Da haka suka juya suka shige mota. A matsiyacin gudu suka bar wurin.
''Sai da suka kawo bakin titi sannan suka tsaya suka kira daddy daya koma inda yakai kudin nan. Haka ko yayi yana zuwa ya iske Amatu a tsaye tana kuka. Aikuwa tana hangoshi tayi saurin zuwa ta rungume mahaifinta tana sharban kuka. Lallashinta ya shiga yi yace su shiga mota subar wurin dan akwai hadari zama cikin irin wannan dajin.
''Wuta ya karawa motar suka tafi. Direct gida suka nupa. Ko gyara parking beyi dakyau ba Amatu ta fito a guje sai cikin gida. Da shigarta ta tarar da mummy zaune duk ta tsure tana tunanin ko zasu dawo tare. Aikuwa kamar a mafarki taji an rungumeta ana kuka.
''Dagowa tayi da idonta caraf suka hade dana juna. Nan fa murna ya tashi mummy harda kukan farinciki. Karewa Amatu kallo tayi taga duk tayi baki ga wani dan bashi bashi da takeyi dan tun zuwanta bata taba yin wanka ba sai dai tayi alawla kawai tayi sallah.
''Daddy daya shigo yanxu shima ba karamin dadi yaji ba dan rabon da yaga mummy tayi dariya haka tun randa aka sace Amatu.
''Rungume suke da juna na kusan yan mintuna kalilan kafin mummy ta saki Amatu tace ga wayata ki kira hajara ki fada mata Allah ya kubtar dake ni zanje in hada miki ruwa kiyi wanka kinji? Amsawa da toh Amatu tayi ta karbi wayan ta kira aunty hajara.
''Ita kuma kamar jira take a kirata ta dauki wayan. Da jin muryar Amatu ko amsa sallamar batayi ba ta kwalawa ameerah kira tace tayi sauri ta fito Amatu ta dawo.
''Cikin minti uku sai gasu sun shigo gidan. Aikuwa Amatu da gudu ta rungume aunty hajara tana dariya ita kuma kukan farincikin dawowar take.
''Ameerah dake bayan aunty hajara tace Amatullahi niko murnar ganina ba'ayi ba kenan ko??
''Sai a sannan ta lura da ita taje ta rungumeta dan ko ba'a fada mata ba tasan ameerah ce. Nan suka zazzauna ana hira. Mummy da yanxu ta fito murmushi tayi cikin zolaya tace to hajara yanxu sai a karbi girki tunda Amatu ta dawo.
''Waro idanu Amatu tayi tace girki kuma mummy to da wakeyi? Hararanta mummy tayi tace bansani ba kidai tashi zuwa wanka. Ameerah ko dariya tayi tace Amatullahi jeki ki dawo kisha labari.
''Amatu na dariya ta haura sama. Dakinta ta shiga taga tsaf yake kamar akwai mutum ciki, murmushi tayi dan tasan aikin mummynta neh.wardrobe ta bude nan ma taga kayanta tsaf a gogen su.
''Towel ta zaro sannan ta fara cire kayan ta sai farar envelop dinda Abdul ya bata ta fado. Ita harta manta dashi dauka tayi tasa a cikin handbag dinta kafin ta shige toilet. Ta dade tana zubama jikinta ruwa sai wani nishadi takeji gata a cikin gidansu.
''Takai kusan minti ashirin tana watsa ruwa daga bisani kuma ta fito. Gaban dressing mirror ta nupa dan goge danshin dake jikinta tayi sannan ta fara shafa mai ta kuma lailaye jikinta da turaruka masu kamshi. Yar simple make-up tayiwa fuskarta sannan ta tashi ta shirya cikin daguwar riga baka da ratsin ja.
''Flat shoe ta saka sannan ta fito zuwa kasa. Ameerah na ganinta tayi saurin karasa inda take tace wannan irin kyau haka sai kace me barin gari. Cunno dan karamin bakinta tayi tace a haka din?? Duba fa ki gani ko gira ban zana ba fa.
''Dariya ameerah tayi to naji kar kiyi kuka muje ga abinci can kici. Ta karasa maganar gami da jan hannunta zuwa dinning table.
''Dake Ameerah ma bataci abinci ba, zama tayi sunaci tare. Mummy da Aunty hajara sai kallonsu suke suna dariya daddy kuma yana can part dinshi.
''Bayan sun gama cin abincin suka kwashe plates din suka wanke, amatu yasa kwando tace suje su kai gida. Zaro ido ameerah tayi tace lallai Amatullahi ke yanxu baki ko tsoron fita? Murmushi tayi tace wani tsoro kuma ai Allah ne ke karewa kawai dai mu tafi nayi missing din gidan aunty neh.
''Hararanta ameerah tayi tace nidai bada yawu na ba kidai bari idan muka tashi zuwa gida sai mu tafi dashi kinji? Badan taso ba suka koma Palon ana ta hira dasu.
''Su ameerah sun dade a gidan kafin suka wuce. Amatu kuma mummy ta hanata fita tace kozata fita sai an kwana biyu.
''Da daddare Amatu na kwance sai tunanin maganganun da Abdul ya fada mata takeyi. Ita a niyar ta taso idan ta dawo gida ta fadawa daddynta wanda ya satota da kuma dalilin haka sai kuma Abdul yaja mata burki kuma ta rasa dalilin dayasa taki musa masa.
''Tunowa tayi da envelop din daya bata tayi saurin dauko handbag dinta ta cire envelop din. Sai data yi addu'a kafin ta bude ta fara karantawa kamar haka...................
ππΏππΏππΏππΏ
[2/5, 12:36 PM] Lashminzyπ: π«ππ«ππ«ππ«
*RUDANI*
π«ππ«ππ«π
Story & written by
Lashminzy
π₯GΓLDΓΓ"S WRΓTΓRS
ΓSSΓΓΓΓTΓΓΓπ₯
Vote me on wattpad @lashminzy
Email:bilkisualiyu248@gmail.com
Page 11-12
"Amincin Allah ya tabbata a gareki ma'abociyar so da kauna da fatan kin isa gida lafiya" "AMATULLAH" nasan zakiyi mamakin jin abunda zan fada maki amma dan Allah karki barni da ciwon da kedai ce maganin shi!
bazan iya boye miki abunda ke cikin zuciyata ba "a gaskiya tun ranar dana fara saki a kwayar idona naji na kamu da matsanacin sonki" "banso ace ta dalilina an satoki ba amma duk da haka nayi iyakacin kokari na wurin ganin ba'a saki a halin da kika tsinci kanki ba sai kuma Allah ya kaddari haka"
"AMATULLAH Ni mutumin kirki neh tunda nake bantaba sata ba balle har inkai ga sato mutum, mutum ma irinki" Dan Allah kiyi hakuri da abunda muka aikata miki kuma na rokeki karki hukunta zuciyata ta hanyar kin karbar soyayya ta saboda idan hakan ta kasance komai yana iya faruwa dani kuma kece sila"
"na barki lafiya masoyiyata"
''wata irin nannauyan ajiyar zuciya ta sauke kafin ta nade envelop din ta rungume a jikinta tana murmushi wanda ni kaina na kasa gane kona menene.
****************
Kwance yake kamar wani mara lafiya in banda sake sake ta tunani abu abunda ke cikin ranshi. Yau kwana biyu kenan yana jiran reply dinta amma shuru shiyasa duk ya tashi jiki a mace ya kasa tabuka komai. Haka ya wuni cikin daki sai da ammie ta shigo neh ta ganshi can saman gado
Ita ta dauka ma ko baida lafiya neh shiyasa baizo gaishe ta ba. Data tambaye shi lafiya yace lafiyan shi kalau kawai yayi aikine da yawa ya gaji dake shi din likita shiyasa bata damu ba ta koma part dinta ta aiko mashi da abinci.
Tashi yayi ya wanke bakin shi ya zauna yana ci saboda gudun bacin ranta, bayan ya gama ci neh yayi wanka ya shirya cikin kananan kaya sannan yaje bakin gado zai dauki wayar shi, daidai lokacin yaji sakon text ya shigo amma dake ba shine a gabanshi ba sai daukar wayar kawai yayi ya fice abunsa.
Part din ammie ya nupa, da shigar shi hanan wacce bazata haura shekaru goma sha biyar ba tazo da gudunta ta rungumeshi tana murmushi, shima murmushin da bekai zuci ba ya sakar mata gami da jan hannunta suka zauna saman two seater
Kallonshi tayi da manyan idanunta tace yauwa yaya daman kai nake jira ka dawo ka aramun wayanka. Ke fa ina naki da kikeson aran nawa?? Dan marairaice fuska tayi tace yaya ammie tayi seizing plsss ka aramun.
Bata rai yayi yace waton ke bakya jin magana ko kusan kullum sai anyi seizing din wayar ki?? Toh wai ma me kikeyi da wayan neh har ammie ke seizing dinta? Kukan shagwaba tasa tace Allah yaya bakomai nake da ita ba kawai ina kiran friends dina neh fah.
Nidai kar kiyi mun kuka gashi kuma ki kira anan ina gani, karban wayar tayi tana kunkuni. Dake tasan pin din wayar shi yana mika mata ta