Chapter 25 Reading RUDANI COMPLETE HAUSA NOVELS BY LASHMINZY.txt Arewa Novels

RUDANI COMPLETE HAUSA NOVELS BY LASHMINZY.txt

Author :  LASHMINZY Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   25 / 27

72K to 75K   out of 79.1K words

janye wannan kudurin namu saboda ba hanya bace mai bullewa face hanyar rage mutunci da kima a idon miji.


Numfasawa Ameerah tayi tace gaskiya hakane Besty, bari ma kigani dana gama gyaran palour na zanje in hadawa Abdul delicious kuma idan ya dawo zan bashi hakuri dan wallahi jiya da yau komi ban dafa ba, dazu dazai fita takadda ma ya aje mun a palour saboda yayi yayi in bude kofa naki, babu hakurin da bai bani ba daga jiya haryau da safe amma na share shi, dan haka yanzu zanje in roki gafarar mijina.


Dariya Amatu tayi hade da zaro ido tace lallai ke kinfi iska barna, Ashe ni bankoyi komai ba? 🤔hmmm kedai wuce ki kirashi yanzu kafin yayi maki kishiya.


Harara Ameerah ta banka mata, batare datace komai ba ta wuce, Amatu kuwa murmushi tayi hade da girgiza kai ta wuce part d'inta.





****************
Abba ne tare da ammie yana bata labarin abunda su Abdulrahman sukayi kuma har ma an mayar dasu, ammie tace yaushe aka mayar dasu bansani ba? Abba yace tun shekaran jiya Alhaji Ibrahim ke fadamun.


Bata rai ammie tayi Abba yace lafiya Aisha? Dan guntun murmushi tayi tace ai da nice uwar yaran nan bazan taba bari su koma ba sai na gama wahalar dasu, wai kasan ma shekarajiya da naje saloon sai dana biya gidan? Hmmm nan naci karo da mummyn yan biyu wai tazo bada hakuri nikuwa na cije nace wa Haj rukayyatu karta yadda ta bari yaranta su koma.


murmushi Abba yayi yace ai daman ku mata haka kuke da karamin tunani, idan ba haka ba kuda ya kamata ku sulhunta su shine zaku raba kawunan su?


""""Gaskiya ku daina hakan baida kyau kinji ko! Dukar da kanta kasa tayi tace toh Alhaji insha Allah bazan sake ba, wannan ma kuskure ne, toh Allah ya kyauta, ta amsa da ameen sukaci gaba wata hirar.



************
Bayan Abdul ya dawo da daddare, sosai yaga canji a tattare da Ameerah, kuma hakan ba karamin dadi yasa shi ba dan koda yaje asibiti a takure yake harya dawo sai yanzu da yaga irin tarbar da tayi mashi, hade ba bashi hakuri, daman ba fushi yake da ba hasalima burin shi bai wuce su dawo yadda suke ba, sai gashi cikin lokaci kadan sun dawo kamar basu ba.


A tare sukaci abinci tana bashi yana bata har suka gama, da kanshi ya kwashe su plate yakai kitchen ya dawo, nan Palour suka zauna suna hira, har yake fadamata wai yana tunanin tana da juna biyu. Cike da jin kunyar shi tace ita kam bata yadda ba aiko yace toh gobe zai gwadata danya tabbatar mata.


Murmushi tayi ta shige daki da gudu, aikuwa shima ya bita, kan gado ya sameta tayi ruf ada ciki, bayan ya haye yana mata cakulkuli sai dariya take tana cewa ya dagata karya karya ta, sauka yayi ya koma gefen ta yana tsokonar ta daga nan salon wasan nasu ya canza.

Da gudu 🏃‍♀🏃‍♀na fitar musu a daki tun kafin Abdul ya koreni...😁






A bangaren su Amatu.......










Ayi manage plss

Share
[3/29, 6:53 PM] Lashminzy💞: AᏔᎬՏϴᎷᎬ ᏔᎡᏆͲᎬᎡ'Տ ᎪՏՏϴ...🏮

(Թαʆαɕε σƒ εXɕίtαtίση αηδ Թʆεαςαηt ϖɾίtεɾς)

💫🌞💫🌞💫🌞
RUDANI
💫🌞💫🌞💫🌞


Տtơɾу Ꭺηɖ Ꮤɾίttεη Ᏼу
Ꮮasིhིmིiིnིzིyི


: بِسْــــــــــــــــــــــمِ اَللّهِ الرَّحْمنِ الرَّحِيمِِ"
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِذَا نُودِيَ لِلصَّلَاةِ مِن يَوْمِ الْجُمُعَةِ فَاسْعَوْا إِلَىٰ ذِكْرِ اللَّهِ وَذَرُوا الْبَيْعَ ۚ ذَٰلِكُمْ خَيْرٌ لَّكُمْ إِن كُنتُمْ تَعْلَمُون
Alhamdulilah today is another beautiful day. Haza yaumul akbar; yaumul shukur, yaumul salama! Alhamdulillahi ala ni'matil Islam. May Allah shower His endless blessings upon U & Ur family and May He turn all your noble thoughts, feelings, wishes and heart desires into reality. Ameen
JUMA'AT MUBARAK.



Page 113-114

"Bangaren su Amatu ma hakan ce ta kasance dan itama tarba mekyau tayi mashi, sai nan take dashi kamar yadda shima hakan yake da ita. Kwana jindadi sukayi daga su Ameerah har su Amatu da kuma mazajen su dan su kwashi gara sosai.


"Washe gari da yamma Abdul ya fito zai fita sai ga su fauziya da ummi da sauran yan uwanta sunzo, Abdul na ganin su ya fasa shiga mota ya koma wurin su suka gaisa sannan yayi musu jagora har cikin gidan shi. Da sukaga Ameerah sunyi mamaki sosai dan a tunanin su koya saki Amatu ne saboda sun taba zuwa bikin Amatu akace an daga sai suka koma gida toh dazai sake auren basu samu damar zuwa saboda sunyi tafiya shiyasa ma basu San cewar Ameerah ya aura ba.


Bayan sun gaisa da ita me har suna dan hira yayan su yace wai ina Amatullahi ne? Dan murmushi Abdul yayi yace ai yayan shi ke auren ta bashi ba, cikin rudani da sonjin yadda akayi haka ta faru yace kamar ya kenan? Abdul ya fara basu labarin tun farkon haduwar shi da Amatu da kuma haduwar shi Abdulrahman wanda shine dalilin da yasa aka daga auren shi.


Fauziya tana dariya tace no wonder🤔 Ashe ranar da muka hadu da Amatu saman hanya tazo a guje bayan mun kaita gida zamu fito muka ganka Ashe bakai bane shi ne? Hmmm lallai wallahi kuna bala'in kama sosai.


Murmushi Abdul yayi yace bari ma yaje ya kirata su gaisa, fauziya tace a'a bari dai muje ko, duk suka amsa da toh suka dunguma zuwa part d'inta.


"A palour suka tarar dasu ita da Abdulrahman tana kwance saman cinyar shi tana bata labari, sosai suke nishadi sedai zuwan su Abdul ya katse musu jindadin, gaisawa sukayi kafin Amatu ke cewa ai kamar ta taba ganin su, fauziya tace Eh mune Dr Abdul ya kawo lokacin bikin ki, Ayyah Allah sarki toh bari in kawo muku ruwa, ta mike tana yamtsu fuska saboda kasalar dataji dan yanzu cikinta ya fara nauyi idan ta dade a zaune dakyar take tashi, duk ji zatayi jikinta yayi tsami.


Kitchen ta shiga ta dauko musu drinks Ameerah ta bita kitchen ta taimaka mata da dauko sauran donought da cin-cin dinda tayi dazu wanda duk kwadayinta ne yasa yinshi.

"Can gaban su ta aje musu ta samu ta zauna, Abdulraheem yayi introducing dinsu a wurin Abdulrahman da Ameerah yace musu ai wata rana sun taba accident ne su dukan su shine aka kawo su asibitin su toh babanta su mutumin kirki ne kuma dan zaman da sukayi yasa suka saba da juna.


Abdulrahman dan murmushi yayi yace Allah sarki Allah yabar zumunci, kuma dan Allah kuyi hakuri da shareku danayi rannan lokacin bana jindadi ne, a tare suka hada baki wurin cewa ai babu komai, ummi kuwa mamaki take wai danya gane su.


Nana sukaci gaba da hirara su kamar irin sun San junan su sosai dinnan, har invitation card din auren su suka bayar daman wannan ranar da sukazo sunzo kawo wa ne toh kuma ganin kamar ba lafiya ba yasa suka bari sai yau su kawo.

Aikuwa Abdul yaji dadi sosai yace zai zo har gida ya taya baba murna, sai kusan magariba suka wuce.





*******************
So, kauna, tattali, da shagwaba babu wanda Amatu bata gani a wurin Abdulrahman, duk wani motsi nata akan idonshi yake, baya bari tayi duk wani aiki dazai sata wahala, ko makaranta shike kaita, idan an tashi ya dauko ta.

"Yanzu ta kara girma da kyau fiye dana da komai nata ya cicciko, Abdulrahaman sai kaf-kaf da ita yake, ko a school duk wani motsi nata a sane yake dan yana sa mata ido sosai kada wani kato yayi ta kalle maahi ita. "Baya ga haka, duk wani abu da zata bukata Abdulrahman ya aje mata, ko aiki da bekai ya kawo ba baya bari tayi, da zarar yaji tace wash hankalin shi zai tashi ya fara cewa lafiya me kikeso, ita kuwa duk tabi ta firgita shi ko school yaje matsuwa yake bai dawo wurinta ba.



Haka ma su Ameerah soyayyar karuwa kawai take, kullum cikin nunawa junan su gata suke, cikin Ameerah watan shi uku. Kulawa kam tana samun shi sosai wurin Abdul. Lokacin da Amatu tasan Ameerah ba karamin dadi taji ba dan tafison duk wani abun Alkhairi da zasu samu su sameshi a tare.


Gidan nan nasu kam ya zama gidan kallo dan cikin su babu mai nuna ma wani iya kula da mata haka suma matayen. Kullum idan sun fita basu da aiki sai jido kayan babies dana maza dana mata, su man shafawa dasu pampers dasu kayan wasa babu irin wanda basu siya sun aje ba.


A bangaren su Ammie da mummy da aunty da kuma mummyn Amatu suma tanadi sosai sukeyi wa cikin su, fatan su dai Allah ya sauke su lafiya.





Bayan wata uku............


Amatullahi ce zaune saman kujera tayi rashe she da plate din awara mai zafi a gabanta, awarar taji yaji sosai dan yadda take hura baki tana wash amma bata fasa ci ba sai data cinye tas, tace Alhamdulillah hade da tashi dakyar dan yanzu cikin ta yayi nauyi tashi dakyar zama dakyar kai komai ba wuya yake bata.


"Ko school ba kullum taje zuwa ba balle kuma saloon dinta kwata kwata tabar zuwa sedai duk wani abu da ake bukata su bola zasu kirata su fadamata, idan ma kaya ne suka kare datayi order za'a kawo mata har shago.


Kitchen ta shiga ta wanke plate ta dawo ta zauna tana kallo danshi ke debe mata keqa idan Abdulrahman baya nan.



"Ameerah ce ta shigo tana murmushi tace me ciki ya kadaici? Murmushi Amatu tayi tace dadin abun bani kadai bace 😏 sai suka dariya. Hira suka cigaba dayi daga bisani suka shiga kitchen wurin sana'ar su waton danwake.


Kullum sai sunyi danwake, Abdulrahman kuwa bayason danwake, kullum cikin mita yake yana cewa Allah ya nuna mashi an haifi yaran nan dole yaga wacce zata kara daga mashi danwake a gida, su kuwa suyi ta mishi dariya suna cewa besan dadi ba.



***********
Kwance take a saman gado tan juyi duk ta har gitsa gadon sai faman nishi take tana wash,,,wash ash........





Share
[3/30, 6:18 PM] Lashminzy💞: AᏔᎬՏϴᎷᎬ ᏔᎡᏆͲᎬᎡ'Տ ᎪՏՏϴ...🏮

(Թαʆαɕε σƒ εXɕίtαtίση αηδ Թʆεαςαηt ϖɾίtεɾς)

💫🌞💫🌞💫🌞
RUDANI
💫🌞💫🌞💫🌞


Տtơɾу Ꭺηɖ Ꮤɾίttεη Ᏼу
Ꮮasིhིmིiིnིzིyི



Page 115-116

hawaye ne ke kwaranya a idanunta, yayinda gabadaya jikinta ya Saki tana jin duk ilahirin jikinta na ciwo, juyi take tana dafe mararta dake tsananin jinshi kamar zai balle, wani abu takeji yana mata yawo a kasanta tana jin tamkar zata yunkura ya fito sedai saboda tsananin azabar da takeji yasa ta kasa nishi balle ta fiddo da abunda takejin ya tsaya mata a gaba.


"Yunkurawa tayi cikin dauriya ta zamo kasa, duk da hakanan cikin nata sai wani irin murdawa yakeyi, hannunta tasa saman madubin dake kusa da gadonta tana laluben wayarta, daidai lokacin da hannunta yakai kan wayar taji wani irin ciwon Mara ya taso mata wanda jitake kamar za'a fitar mata da rai.


Take ta ture wayar ta fadi a kasa cikin rudewa da zafin azabar ta kurma wani irin ihu, tana fidda munfashi sama-sama, sai kiran sunan Abdulrahman take da Ameerah da mummy tana suzo su taimake ta, haka taci gaba da kuka tana juye-juye tana kiran su Suzi su ceceta har takai ga ko magana bata iya yayi, daga karshe kuwa dauke wuta tayi.



Abdulrahman na class yana lectures tare da wasu yan level 300 gaban shi ne keta faduwa tun farkon zuwan shi class din sedai be kawo komai a ranshi ba amma jin faduwar gaban ya tsananta yasa ya fita daga class din ya zaro wayar shi daga cikin aljihu ya kira number Amatu, sedai harta karaci ringing d'inta ba'a dauka ba haka yayi ta kiranta har kusan sau goma bata dauka ba.


Beyi wata-wata ba ya shige motar shi ya bata wuta, cikin yan mintuna kalilan ya iso gidan, a bakin kofa ya tsaya yana knocking ba'a bude ba, wasa-wasa harya kai mintuna goma beji motsinta ba kuma ya duba part din Ameerah basu nan. Wayar shi ya dauko yasa sake dialing ba'a dauka ba.


Amatu kuwa harta suma ta kuma farfado wa saboda jin wayar ta data fado kusa da ita tana ringing sedai azabar da take ciki ya hanata daukar wayan, kokari ma take ta jawo wayar ta dauka amma ra kasa, dakyar hannunta yakai ta jawo wayar a daidai lokacin an sake kira, batare data duba me kiran ba ta dauka hade da fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi.


Cikin firgici da tashin hankali Abdulrahman yace baby ki bude kofa gani nazo gidan, cikin galabaita da rawar murya tace inaa,,,daakin saamaaa......bazan iya fitowa baa....,mutuwa zanyiiiiiiii,,,,,,,Sai hannunta ya kashe wayar batare data sani ba. Cikin rikicewa Abdul ya fara kiranta yana maganganu marasa kai duk ya rikice, jin bata amsa shi ba yasa shi kallon screen din wayar yaga Ashe ma ta kashe.



"Wata iriya kara ya saki hade dasa hannun shi ya banki kofar da karfi, amma ina kofar bata bude ba, haka yaci gaba da buga kofar yana wasu maganganu marasa kan gado, dakatawa yayi yaje can wurin me gadi a rikice yace Auwalu bani karfe, bani karfe, Auwalu megadi ya tsaya yana kallon shi yana cewa lafiya yallabai??


Ko kallonshi Abdulrahman beyi ba ya bugeshi ya shige dakin aikuwa yaci karo da wani katon karfe dan dogo dashi, daukowa yayi ya fito da sauri ya isa bakin kofar daidai wurin lock din ya saita ya buga karfen da karfi, take kofar ta bude, da sauri ya yar da karfen ya shige a guje, megadi na take masa baya.


A kasa ya ganta tayi daddaya ko numfashi bata fitarwa ga wani ruwa dake fitowa daga jikinta, wata kara ta saki saida megadi yaji tsoro, da hanzarinsa yasa hannuwan shi ya kinkimeta ya fita da ita waje da sauri, can wurin motar shi yaje yasata a gidan baya, ya zagaya ta daya gefen ya shiga.


Wani irin gudu yake na fitar hankali, cikin ikon Allah suka iso asibitin lafiya, ko parking bai gama ya fito ya zagaya ya fito da ita, a bakin kofar shiga ciki ya hadu dasu Abdul da Ameerah, dake asibitin su Abdul ya kawota.


Wata uwar kara Ameerah ta saki a lokacin dataga Abdulrahman ya dauko Amatu bata numfashi, take taji wani irin jiri na dibarta, basuyi aune ba suka ganta tayo luuuu zata fadi kasa, Abdul ya tarota sedai ina harta suma, Amatu kuwa saman wani gado aka daurata akayi labour room da ita dan sun fahimci nakuda takeyi.


"Wani daki aka kai Ameerah aka bata taimakon gaggawa, take ta farfado tana kiran Amatullahi, Abdulraheem dake kusa da ita yace meerah kiyi hakuri Amatu haihuwa zatayi yanzu haka tana labour room plsss ki tayata da addu'a Allah ya sauketa lafiya.


Hawayene ya gangaro mata najin tausayin Amatu tace muje in ganta, ta fada tana saukowa daga kan gadon, beyi musu ba yace suje dan bayason wani abunda zai bata mata rai harya kai ga shafar abunda ke cikinta.



Waje suka fito suka nupi labour room sedai anan bakin kofar suka tsaya dan ba'a bari a shiga, ko Abdulrahman yana nan waje sedai hankalin shi ba'a jikinshi yake ba, duk yabi ya firgice sai kai kawo yake, idanuwanshi sun canza launi zuwa jaa, addu'a kawai yake Allah ya sauki babyn shi lafiya.



"Ciki room din kuwa sai kokarin taimakon ta suke wurin ganin ta haihu amma inaaa ta gaza duk wata dubara da zasuyi sunyi amma haryanzu bata haihu na kusan awa hudu suna kanta, wata likita ce tace anya kuwa haihuwar ce dan naga nakudar nata yadau lokaci kuma dai gashi abunda ke cikin yunkurin fitowa yake.


Dayar tace toh kinsan wasu suna kwana biyu suna nakuda wasu kuwa kwana daya mudai Allah dai yasa basai anyi mata operation ba. Suka ce ameen a yayinda likitar ta fito waje. Da sauri suka tareta Abdulrahman yace Dr ya matata take ki fadamun? Cikin sigar lalllashi tace kayi hakuri ta kusan haihuwa insha Allah, tana fadar haka ta wuce, Abdulrahman kofar ya nufa da niyar shiga yajita a rufe, kiran sunanta ya farayi yana kuka mai ban tausayi, Ameerah ma haka kuka take tana cewa Abdulraheem su bari ta ganta.


Shima Abdulraheem dauriya ce kawai yayi dan bayason su taru su ringa mata kuka ne bayan kuma addu'ar su kawai take bukata a hanlin yanzu. Suna nan tsaye sai ga likitar ta dawo dawani paranti a hannunta, tana bude kofar da makulli ta shiga, duk suna tsaye suna kallon ikon Allah kuma suna jin kukan Amatu da nishinta wanda duk ya kara tayar musu da hankali.




"After 8 hours"
Duk hankalin kowa ya gama tashi dajin haryanzu Amatu bata haihu ba, hatta su mummy dasu aunty hajara dasu ammie suna wurin dan tunda su Abdul sukaga haihuwar batazo ba suka sanar dasu sukazo asibitin. Kowa hankalin shi a tashe yake. Addu'a kawai suke mata, gashi an hanasu ganinta.


Suna nan jigum-jigum sai ga Dr Halima tazo wacce daga baya tazo itama tayi iya kokarin ta amma abun yaci tura, da sauri likitar ta fito tana cewa ina mijinta yake? Dama kamar jira yaje a kirashi da sauri ya mike haryana sarkewa wurin cewa gani! Matar ka nason ganinka tana fada ta koma ciki, ya shikuma yabi bayanta kafa na rawa harya isa wurin Amatu da fuskarta harta canza kala saboda galabaita.


A wahalce take magana tana cewa mutuwa zanyi Abdul dan Allah ka yafe mun kacewa su mummy su yafe mun, bakinta ya rufe da hannun shi yace a'a bazaki mutu ba, my baby ki daure kinji, toh kawai tace da dafe mararta tana cewa kaji yana yawo amma yaki fitowa ko? Cikin damuwa ya ya dawo saitin kanta yafara mata addu'a yana tofawa yana cewa ke kidingayi, a yayinda likitoci keta kasanta suna tura cikin ta a hankali.


Itama nishi take tana kara yunkurawa,

25 / 27