Chapter 26 Reading RUDANI COMPLETE HAUSA NOVELS BY LASHMINZY.txt Arewa Novels

RUDANI COMPLETE HAUSA NOVELS BY LASHMINZY.txt

Author :  LASHMINZY Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   26 / 27

75K to 78K   out of 79.1K words

Abdulrahman kuwa sai addu'a yake mata yana cewa ki daure kinji, haka sukayi tayi har kusan minti talatin sai kawai sukaji ta saki wata kara, take santaleliyar yarinya ta fado, ko mintu biyu ba'ayi ba wata ta sake fadowa, sedai fadowarta keda wuya numfashin Amatu ya dauke.


"Da hanzari likitoci suka yo kanta wasu kuma suka kwashi yaran dan su gyara su, Abdulrahman hankali ya tashi ya bubbuga Amatu yake amma inaaa ko alamun tashi batayi ba, har likitoci sunyi wa yara wanka sunsa musu kayan dasu ammie suka kawo.


Waje suka fito da yaran suka kaisu wani daki, aikuwa farinciki fal ransu Amatu ylta haifi yan biyu kowa sai murna yake, sunma manta da halin da Amatu ke ciki dan duk a tunanin su ana can ana kintsata ne shiyasa ba'a basu damar ganinta ba.


"Shigowar Abdulrahman ya katse musu rahan da suke ciki, kowa kallonshi yake ya koma kamar wani mahaukaci hawayene ke bin kuncin sa. Da sauri mummy ta taso tana son lafiya ina Amatu take??


Kuka ya fashe dashi mai sauti yana cewa bazan iya rayuwa batare da ita dan Allah kuje kuce ta tashi karta tafi ta barni, gaban mummy ya iso yace mummy kice ta tashi........



Tashin hankali ba'a sa mashi rana, mummy tace meya samu Amatu? Tana ina? Mummy Amatu ta wuce kice ta dawo.... Hankalin kowa ya tashi a wurin Ameerah kuwa da gudu ta fita suma suka mara mata baya,,,,,A bakin kofa sukaci karo da likita tace Dan Allah kuyi hakuri ba kuka zakuyi ba addu'a zakuyi mata, ammm kuma tana ciki sedai bazaku iya tafiya da ita ba sai kun cika wani file saboda duk wanda ya rasu a wannan asibitin haka ake masa so plsss ku bamu ten minut...........


Wata irin danka Ameerah takaiwa likitar tana cewa wallahi bata mutu ba ki fito mana da yar uwar mu,,,,,kuka ta fashe dashi tana dukan likitar su mummy suka kwace ta dakyar, Abdulrahman kuwa ya dade da suma, duk hankalinsu ya gama tashi.


Kowa kuka yake wiwi, Abdulrahman kuwa anyi wani daki dashi, mummy kam hawayenta sun kafe se addu'a kawai take acikin zuciyarta..........











Share
[3/31, 8:31 AM] Lashminzy💞: AᏔᎬՏϴᎷᎬ ᏔᎡᏆͲᎬᎡ'Տ ᎪՏՏϴ...🏮

(Թαʆαɕε σƒ εXɕίtαtίση αηδ Թʆεαςαηt ϖɾίtεɾς)

💫🌞💫🌞💫🌞
RUDANI
💫🌞💫🌞💫🌞


Տtơɾу Ꭺηɖ Ꮤɾίttεη Ᏼу
Ꮮasིhིmིiིnིzིyི


~Second to the last page~

Page 117-118

"Suna nan zaune jigum jigum sai ga wata likita ta fito da fara'ar ta tace ina tayaku murna patient dinku dogon suma tayi...... Ai da sauri suka shige daki, suka kuwa ga Amatu zaune a bakin gado, tana hawaye tana kiran ya Abdul, da gudu Ameerah ta fita ta shiga dakin ta aka kwantar da Abdulrahman tana haki tace ya Abdul Amatu bata rasu ba ka taso muje tana kiranka.



Kamar a mafarki yakejin ana mashi magana sedai da sauri ya bude idonshi yace ina take? Tana labour room, aikuwa harma ya rigata fita daga dakin ya isa dakin da take. " Duk mutanen dake dakin harda su likitoci dasu ammie hankalinshi beko kai garesu ba, shidai burinshi kawai yayi ido biyu da babyn shi. Da gudu ya isa wurinta ya rungumeta kamar zai mayar da ita cikinsa duk ya kanainayeta da hannunwan shi, gashi jikinta har yanzu akwai inda ke mata ciwo amma haka ta daure ta irin rungumar da yayi mata harda sumbatar ta a goshi.



"Ammie da duk kunya ta isheta tace kai Malam bakaga mutanen dake wurin nan bane? Sai a sannan ya juyo yaga kowa ya zuba mashi ido yana kallon shi, da sauri ya saketa ya koma gefe yana sunnar da kai kasa. Abdul kuwa yana daga gefe yana murmushi, a ranshi yace wannan dan uwan nawa ni control ji yadda ya dawo kamar wani zararre a cikin yini daya kawai 🤔


Barka su mummy suka shiga yiwa Amatu kafin suka fita gabadayan su dan likita zata dubata, bayan minti talatin lokacin har kusan karfe goma na dare suka shigo har an kintsa Amatu kuma an kawo mata babies d'inta masu dasu kusa da ita. Murmushi take ita daya har Ameerah suka shigo, aunty hajara sai washe baki take tanacewa wai tayi wa danta Mubarak kamu duk suka fashe da dariya.



Haka sukayi ta hira harda su daddy da Abba sai kusan sha biyun dare suka tashi zasu wuce, Abdulrahman kuwa ko kunya babu ya daddage wai shi wallahi anan zai kwana haka kuwa suka kyaleshi ta kwana tare da matar shi da twins dinshi, sai sa mata albarka yake tana ta mata sannu dan yasan ba karamin azaba Tasha wurin haifo twins din ba.



Tunda safe Ameerah ta tisa Abdul a gaba sai ya kawota ko breakfast batayi ba suka fito, lokacin da suka iso asibitin har drip dinda akasawa Amatu ya kare, a daki suka tarar dasu Abdul yana rungume da baby daya haka itama Amatu tana rike da daya.


Bakin gado suke suna hira suna kallon twins dinsu, hotuna Abdul yashiga yi musu yana posting a media, nan da nan kuwa friends dinshi suka fara mashi congratulations wasu na zolayar shi suna cewa ya zama daddy yanzu.



Suna cikin hakane sai ga su Ameerah sun shigo, gaisar da juna sukayi kafin suka samu wuri suka zauna Ameerah ta amshi babyn dake hannun Amatu tana cewa kai wallahi se yanzu na lura yarinyar nan da babanta take kama sosai. Amatu ta wani bata rai tace babu wani dani take kama, Abdulrahman yayi dariya hade da janyota jikinshi yana shafa bayanta yace ai na fiki kyau ne shiyasa sukayi kama dani, ya fada harda yar guntun dariyar sa.


"Dukan takai mashi hade da matsawa daga kusa dashi tana bata rai, Abdulraheem yace auntyn mu babu wani kin fushi kyau kuma ma yaran dake suke kama bada shi ba.


Murmushi tayi tace yauwa kanina daman nasan karya suke dani suke kama saboda jinina yafi nashi karfi, Abdulrahman ya waro ido, yace jita kamar wata likita wai jinina yafi karfi? Injiwa? Ammie dake shigowa ita da mummy dasu samha da hanan da Umar tace injini duk suka fashe da dariya.


"Ciki suka ida shigowa kowa na rige-rigen daukar twins, hanan ta anshi wacce ke hannun Ameerah samha kuwa taje zata anshi na hannun Abdulrahman ya watso mata harara yace kee dakata karki jagwalgwala mun baby da kazamin hannun ki. Aikuwa ta fashe da kuka taje jikin mummy tana kuka, ammie kuwa ta anshe babyn ta mika mata tace rabu dashi inma kinga dama ki rama duk dukanki da hantarar da yake maki akan yarshi yaji ko akwai dadi.



Duk dakin suka sa dariya banda shi daya sha toka yana wani ciccije labba, sukuwa ko ajikinsu sukaci gaba da hirar su, Ammie tabawa Amatu breakfast dinda sukazo dashi nan ta zauna tanaci tare da Ameerah dan yunwa takeji sosai.


"Da misalin sha daya na rana aka sallamesu, Direct gidansu Amatu suka wuce dan sun kira mummy sunce basai tazo ba an sallame su, nan cikin gidan suka bane kolinsu harda su Abdul ana ta hira daga bisani su Abdul suka fita su mummy da Ammie suka wuce gida samha da hanan kuwa cewa sukayi basu tashi ba Ammie tace sai sun wuce su bari gibe su dawo, dan dole suka wuce.



'""Ya rage daga Ameerah sai aunty hajara da mummy sai kuka makwafta masu zuwa barka, Ameerah sai dare Abdulraheem ta wuce da ita gida dakyar dan cewa tayi ba inda zata sai da mummy ta lallasheta kafin ta wuce, Amatu sai dariya take mata tana cewa kizo mun da kayan da muka siyo a cikin wardrope din dakina na sama Ameerah ta tsuke baki tace bazan dauko din ba. Abdulrahman kuwa shima haka ya wuce gida jiki a mace yana tunanin yadda zai kwana har arba'in batare da Amatu ba, tsaki yaja yaci gaba da tukin shi.




Washe gari da safe Ameerah ta shirya ta dauki breakfast ta kaiwa Abdulrahman, a palour ta tarar dashi, bayan sun gaisa ta mika mashi ta kuma ce zata shiga dakin Amatu akwai kayan da tace akai mata, toh kawai yace ta haura sama, yadda tace haka tayi, wardrobe ta bude ta dauko mata kayakkin da suka siyo da nata da kuma na babies.

Kodata fito bataga Abdulrahman ba kawai sai ta wuce taje ta samu Abdulraheem dake waje wurin mota yana jiranta, a boot suka sa kayan sannan ta zagaya ta gefen mai zaman banza ta shiga ya tayar da motar suka wuce.


"Bayan sun isa har cikin gida Abdulraheem ya shiga ya kara gaida Amatu da mummy sannan ya wuce asibiti. Nan dakin Amatu Ameerah da jide kayan ta hau jera mata su cikin wardrobe itama Amatu hannu tasa suna jerawa, Ameerah na cewa ta zauna ta huta ai ba'a san me jegi da wahala ba ama ina sam Amatu taki yadda, haka suka ta jera kayan tare.


"Wata takarda ce ta fado cikin kayan da Ameerah ke jerawa, da sauri tasa hannu ta dauka, Amatu tayi saurin fisgewa tana dariya tace waton zaki kallanmun sirri ko? Ameerah tace sirrin me kuma? Amatu tace ina ruwanki, marairaicewa Ameerah ta farayi tana yasata mda Allah akan ta bari ra gani sannan Amatu ta yadda tace wannan takaddar Abdulrahman ne ya aiko mun da ita.


*FLASH BACK*
Wata rana ina zaune a palour lokacin da nayi wa Abdul yaji sai megadin gidan aunty hajara ya kawo mun wannan taddar wai inji wani, nidai bansan ya akayi yasan bana gida una gidan ba, dana bude taddar shine naga abu kamar haka.........


""""Assalamu Alaikum matata farincikina, da fatan kina cikin koshin lafiya? Dan Allah kiyi hakuri bisa ga laifin da muka aikata maki ko ince na aikata maki dan nasan nine silar komai. " Nasan haryanzu kina sona sedai laifi daya dana aikata maki wanda ya shafi harda soyayyar mu nakeson in goge shi yau kuma ina fatan zaki fahimce ni?


Amatullahi wallahi nasoki kamar hauka kuma haryanzu ina kan sonki!!! Dalilin da yasa gangar jikina ta gujeki dan zuciyata a kullum cikin begenki take, shine "wata rana daddare ina kwance daddy ya aiko kirana yake fadamun ai ya Samar mun wata makaranta a Cyprus kuma Insha Allah gobe zamu wuce tare dashi saboda akwai abubuwan da yakeson yayi a can dan haka in shirya tunda safe flight dinmu zai tashi.


"Daddy na yayi mun surprise ne saboda ya burgeni in kuma jidadi dan na dade ina burin inje Cyprus karatu shiyasa daddy yayi mun surprise kuma babu halin ince a daga tafiyar gashi dare yayi sosai dan kusan karfe goma ne na dare babu halin inzo gidanku a wannan lokacin, haka na shirya da safe muka wuce badan raina yaso ba kuma abun haushin shine wayata ba bansan inda na jefar da ita ba balle in kiraki in fada maki. Kuma tun da naje ban sake dawowa naija ba dan daddy cewa yayi bazan dawo ba sai na kammala karatuna, kullum fatana da Addu'a ta itace kada Allah yasa ki manta dani kiyi wani sabon saurayi.


"Amatullahi wallahi kodana tafi can da sonki natafi kuma da sonki na dawo a ranar dana dawo nazo gidanku akace bakya nan kullum nazo haka ake cemun har wata rana nazo akace aurenki akeyi ba'a Bari ki fita ba, wannan ma shine dalilin kamuwata da ciwon zuciya.

Plsss kiji tausayi na kiyi hakuri ki dawo kinji matata! Nabar ki lafiya, ki kula da babyn mu.



Dan munfasawa Ameerah tayi tace lallai kuwa yayi kokarin rashin ki da yayi amma kuma dai toh🤔 haka dai Allah ya kaddara shiyasa hakan ta faru, amma yanzu komai ta wuce sedai labari. Amatu tace wallahi kuwa nan sukaci gaba da aikinsu suna hira har suka gama.


"Aunty hajara ce ta shigo dakin da wasu ledoji a hannunta toilet ta shiga bada dadewa ba sai gata ta fito kallon Amatu tayi tace daughter tashi kiyi wanka kar ruwanki su huce ta fada tana zama kan gado, dan tsuke baki tayi ta cire kayanta ta shige toilet tana mita wai duk za'a kona mata jiki, Aunty hajara kuwa shuru ta mata, dan yau batason rigimar ta.



Bayan kwana biyar............
Yau ake sunan Amatu ko'ina na gidan ya cika da mutane, su Ameerah sekai kawo ake da dan cikinta a gaba. Amatu tasha kyau kamar amarya haka ma babies ansa musu kaya iri daya masu bala'in kyau, yara sunci sunan.........












Share
[4/1, 10:10 PM] Lashminzy💞: AᏔᎬՏϴᎷᎬ ᏔᎡᏆͲᎬᎡ'Տ ᎪՏՏϴ...🏮

(Թαʆαɕε σƒ εXɕίtαtίση αηδ Թʆεαςαηt ϖɾίtεɾς)

💫🌞💫🌞💫🌞
RUDANI
💫🌞💫🌞💫🌞


Տtơɾу Ꭺηɖ Ꮤɾίttεη Ᏼу
Ꮮasིhིmིiིnིzིyི


Godiya ta musamman ga ɗaukacin masoyana da kuma masoyan RUƊANI.....

RUƊANI FANS GRP 1,2&3
RUƘAYYATU FANS GRP
ZUCIYAR ƊAN ADAM FANS
TAƘWACEN MIJI FANS
SO KO WAHALA FANS
JANAF NOVELS FANS
ƘADDARA KO SANADI FANS
MUNAT & KAOJE FANS
KUN CUCENI FANS
JALAL KO JAMAL FANS

na gaisheku


WANNAN SHAFIN NAKU NE.........

Bilkeesu adam meerah(takwara)
Hawwer a hisham
Babyn md
Teemah baiwar Allah
Aysha
Ummu zar'in
Ummu arfat
Aunty maryam
Aunty maymuner
Na'ima
Swt janaaf
Swt Raheenart
Mugirat Musa (ƴar garinmu)

Waƴanda ban ambaci sunanku ba kusani cewa kuna cikin raina, ni lashminzy ina ƙaunar fiye da yadda kuke zato.
One love ❤




~LAST PAGE~


Page 119-120

"""Yara sunci sunan mummy (hajara) Ana kiranta da Amrah mummyn Amatu(ruƙayya) ana kiranta da Afrah, biki yayi biki anci ansha an zubar dana zubarwa haka zalika an saci na sata domin kuwa ranar duk wani ɓarawo yayi kuɗi a gidan dan an kashe kuɗi kamar ba gobe. Komai anyi shi a wadace duk wanda yazo bikin nan yasan anyi ɓarin kuɗi hatta da gidan talabijin saida aka nuna, kayan rabuwa kuwa kama daga su jakunkuna, atampa, plates, memo, bokatai kala da kala dasu dusbin da fans kai abubuwa dai gasunan barkatai duk an bugasu domin kuwa kowa ya kawo nashi gudun mawar.


"Abdulrahman na hango can bakin gate ɗin gidansu Amatu yasha wata dakakkiyar shadda kamar ranar auren shi, fuskarshi ko ban faɗa ba ansan cike take da annuri,,,, tare yake da abokanshi ko wanne hannunshi riƙe yake da wata haɗaɗɗiyar jaka an manna hoton Amrah da Afrah a jiki, wasu sun bar nasu cikin mota wasu kuwa nasu na hannun su, da alama dai daga wurin wani taro suke (walimah).


"A gaba yake sauran abokan suna baya, cikin abokan ne na hango Abdulrahman shima sanye cikin shadda irinta Abdulrahaman sedai kowa da kalar tasa. "Tafiya suke suna hira da wasannin su irin nasu na wayayyu kowa fuskar shi cike take da annuri, can palon baƙi Abdulrahman yakai su dake ansan da zuwan su kuma an shirya musu abubuwa da yawa shiyasa batare da ɓata lokaci ba suka shiga palon, anan suka baje kolinsu, kowa abincin son ranshi yakeci dan abincin da aka dafa sunkai kala goma, kowa sai lodawa yake ana hira ana santi.



"Bayan sun gama ci ne Abdulraheem yasa Ameerah ta kira Amatu da babies ɗinta daman dalilin dayasa kenan sukazo duk da wasu sun zo barka amma da yawansu sun dawo saboda yaran akwai shiga rai gasu da kyau kamar ka sace ka gudu dasu. Ba'a ɗauki wani lokaci mai tsawo ba Amatu ta shigo ita da babies ɗinta Ameerah na riƙe da Amrah, Amatu kuma na riƙe da Afrah, har suka shigo palon idon Abdulrahman nakan Amatu dan jiyake wani irin kishinta na taso mashi dan yadda tayi shigarta riga da skirt ne sun ɗan kamata sai ta yafa gyale har kanta saboda tasan Abdulrahman da baƙin kishi yana ma iya disgataa gaban mutane.


"""Dan haka yayi mata lokacin bikin su fauziya da sukaje dinner, liƙi kawai ta tashi tayi shine wasu ƴammata da ƙannan su maza sukazo suna liƙi dan kawai by mistake namijin ya taɓeta shikenan fa Ya haukace musu seda Abdulraheem yayi ta lallaɓi kafin ya samu ya haƙura ya figi Amatu suka wuce bikin da bata ƙara zuwa ba kenan har aka ɗaura aure aka kai amare bata ƙara zuwa ba.


"Kabeer ne ya ansa Afrah dake hannun Amatu, usman kuma ya ansa Amrah, nan suka gaggaisa kowa nata yaba yaran da kuma sa musu albarka, sosai Amatu da Abdulrahamn sunji daɗin addua'rsu, Haka suka ɗanyi hira kaɗan kafin su Amatu suka fita, sedai ƙafarta ƙafar na Abdulrahman dan tana fita ya take mata baya, adaidai corridor ɗin ƙofar ya tsayar da ya anshi Afrah dake hannunta, kallonshi ta tsaya tanayi dan ba ƙaramin kyau yayi mata ba, haka shima gani yake gabaɗaya in za'a tars matan duniyar nan ita kaɗaice zai iya kallo amatsayin macce me kyau.


"Shafo fuskarta yayi ta firgigit ta kalleshi haɗr da sakar mata murmushi, shima murmushin ya sakar mata yace baby kinyi kyau sosai, anya bada ke zan wuce ba kuwa? Hararan wasa ta aika mashi gami da cewa uhmmm babu wani kaje ka sake ɗaura mun wahala nikam hakama ya isheni,,,,,Uhmmm kawai yace yana tunanin lokacin da zata haihu yasan ba ƙaramin wahala tasha ba aikuwa dole taji shakkun ƙara haihuwa nan kusa,,,,A fili yace kaji ragguwa, kallon irin dan bakai bane tayi mishi ta miƙa hannunta ta anshi Afrah su wuce dan Ameerah ta daɗe da wucewa.


"Ba musu ya miƙa mata yace sai nazo anjima dan kusan kull sai ya zo wai dan ma Ammie na mishi faɗa akan ya rage zuwa tunda ba'a kanshi aka fara mata ba. "Kafin tace wani abu ya rungumeta da tare da Afrah ya sunbace a baki sannan yabar wurin, kamar wawiya haka ta tsaya tana kallonshi harya shige palon kafin ta tattaro sauran hankalinta ta wuce cikin gida da tunanin irim ƙaryar da zatayi wa aunty hajara dan ko nam da can ba'a son tana fita wannan ma dan ya zama dole ne.



"Da shigarta ko aunty hajara ra tareta tace mekika tsaya yine naga Ameerah ta rigaki dawowa?Cikin inda inda tace toh daman wasu ne suka tsaya ganin baby,,,,,,badan aunty hajara ta yadda

26 / 27